A DAREN AURENA

Chapter 7

by @maryamstar248

بسم الله الرحمن الرحيم.

Kallon secons biyu ya yi mata sannan ya kauda kanshi tare da fadin "Ta so muje".

Ya yi gaba abinsa ba tare da ya ankara da ba ta biyo bayanshi ba, sai da ya taimakawa Fadeel wanda izuwa yanzu k

ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi, dan har wani jiri-jiri ya ke gani, har ya shigar da Fadeel front sit shima ya zauna driver sit Zulai na inda ta ke babu ko alamar ta motsa bare ta tashi, cike da zafin zuciya matashin ya tada motar da niyyar ya tafiya zai yi ya barta anan, Fadeel ne ya dakatar da shi da fadin.

"Sorry broth ita din amanace a wajena ta sadaukar da komi nata saboda ta taimaka min, yanzu haka ta na cikin makamancitar matsalar da ka taba fuskanta a wajen Abba saboda ni, pls na damka amanarta a wajenka da ba dan ita ba da yanzu baka sameni a rayeba, sannan ita din yanzu matar...."

Bai ƙarasa maganarshi ba yai baya luuuu alamar ya suma.

Cikin kiɗimewa wanda yake kira da broth ya shiga girgiza shi tare da ambaton sunanshi amma ina babu alamun zai farko, hakan ya saka ya fito a birkice ya sabi Zulai a kafada ya saka ta gidan baya sannan da mugun gudu ya taka motar ya bata wuta ya wuce fitttttttt kamar tsuntsu.

KAUYEN YAGAWA

GIDANSU ZULAI.

Wacce ake kira da Mama ce ta cakumi wuyan rigar Mamman cikin matsanancin kuka ta ke fadin.

"Na rantse da sittin ta Ubangiji baka isa ba Mamman ka yi tsuru-tsuru dan kuwa ruwa ya fika kauri, na rantse da tsarkin Allah sai ka dawo min da Zulai yau ba gobe ba ko kuma ka sawaƙemin kafice kabar min gidana tunda ba da kudin salele aka saye shi ba ko na Jummai, inbanda son zuciya irin naka sai ka biye wancan azzalumin me garin ku aikata san ranku, kun kori yarinya cikin dare kamar de wacce tai kisan kai, koda ace kisan kai ta aukata aibata cancanci kora ba, ko dai ka je ka dawo da Zulai ko kuma ka sallameni yau ba sai gobe ba dan bazan bi wannan tsarin na ku ba, ace yarinya A DAREN AURENTA bala'u da masifu su rikito a kanta sai kace wacce ta zagi sama, yasin dubu sai ka sake ni Mamman."

Kuka ne ya ci ƙarfinta yayin wannan farar tsohuwar ta taso tinƙis-tinƙis daga inda ta ke zaune ta na sharar hawaye ta nufo wajen da Mama ke tsaye rike da kwalar Maman.

Ɓanɓare hannun Mama ta yi ta na fadin

"Rabu da Ɗan banza Suwaiba, indai duniya ce gaka ga ta nan ta isheka wanda da riga harma da singileti da dan tofi, imbanda zamani ya lalace ina kai ina korar ɗan da aka baka amana dan an yarda da kai, ni dai ba zaka mai da ni tsohuwar banza ba zan tattare inawa-inawa inkama gabana dan ban san da wane ido zan kalli Audul maliki ba."

Wa ta irin zufar tashin hankali ce ta shiga tsatstsafowa Mamman sai yanzu ya gane kwaɓarshi ta yi ruwa, sam ya mance da mahaifin Zulai na nan tafe nan da wasu yan watanni, kuma wannan karo ba iya shi kaɗai ba har da mahaifiyarta za'a zo, kafin ya gama tunanin mafita ya sake jiyo salatin matan wajen, dubawar da zai yi sai yaga Mama zube a kasa anrufu a kanta, cike da kiɗimewa ya isa wajen da nufin ya taba ta, aiko Maradiyya ta zo da iya karfinta ta bangaje shi ya yi gefe guda zube a kasa, kafin ya yunkura da niyyar tashi ya ji kugunshi ya amsa da wa ta iriyar azaba, ya yinda Maradiyya ta sabi Mama kamar ta dauki yarinya tai waje da ita ko mayafi babu, yayinda su Inno da sauran yan uwa suka rufa mata baya su na koke-koke.

KU KASANCE DA NI A CIKIN WANNAN LABARI MAI RIKITA-RIKITA SANNAN KUMA ME KAYATARWA DARE DA NISHADANTARWA HARMA DA FADAKARWA NAGODE 🙏🙏

TA KU HAR KULLUM