Chapter 8
بسم الله الرحمن الرحيم
Isar su asibitin babu ɓata lokaci likitan da ke aiki wanda shi kaɗai ne a asibitin babu kowa sai majinyata ya amshi Mama tare da bata taimakon gaugawa, cikin nasara aka samu ta farfaɗo ta na ta sambatu, allurar barci likitan ya yi ma ta, ganin ta samu barci ya saka likitan sallamar su, Iya badan ranta ya so ba hakanan tabi bayan sauran suka tafi amma sai faman mita take akan ita dai da ambarta wajen Suwaiba ta rarrasheta idan ta farko, rarrashinta suka yi gami da nuna ma ta idan akaiwa mutum wannan allurar sai ya kwana ya hantse ya na barci bai farka ba.
Mamman ne ya fito zai je wajen Me gari, isarshi kusa da fadar ya fara jiwo muryoyinsu na tashi cike da nishadi inda Me gari ke fadin.
"Wallahi Allah ni kaina na so yarinyarnan kuma na daɗe ina bibiyarta dan insamu dama irin haka amma ban samu ba, ganin irin wahalar da muka sha saboda ita yasanya na yanke hukuncin ko shi
Habu din bazan bari ya aureta ba haka kawai ya kawo ma ni annoba da jaraba cikin gida, shi kuma Mamman sakaran banza da bai da tunani ya na fama da kanshi kamar na kifi daga amfaɗi cewar amfasa auren yarinya shi ne ya hasala ya zuciya wai ta yi abin kunya ya kori yar banza, ni wallahi hakan yayimin dadi sosai dan wallahi ba karamin tsoro ta bani ba ko sanda aka taru anan ana maganar a ɗofane na zauna gudun ko ta kwana." Dariya fadawan suka sake kwashewa da ita cike da nishadi, dan sun daɗe basu yi fira me tsawo irin haka da me garin nasu ba, ko da yaushe fuskarshi a ɗaure kuskure kaɗan mutum zai yi a sauke shi daga matsayinshi.
Cikin sauri Mamman ya sha kwana ya na jin zufar tashin hankali na yanko ma shi, tabbas ya yi kuskure ya tafka babban kuskure wanda bai san ta yanda zai fara gyaranshi ba, wani sashen na zuciyarshi kuma na sake tabbatar ma shi da ya yi daidai tunda ba hakanan ya kori Zulai ba sai da ya daura ma ta aure.
BAYAN AWANNI UKU
03:00am
ABUJA NIGERIA
Da tsananin gudu ya isa babban asibitin da ke cikin Estate din MUHAMMAD IMAM, kai tsaye ya danna kan motarshi cikin asibitin me wadatar haske kamar rana, mutane sai kaiwa da komowa suke saboda tsarin da aka bi wajen ginin asibitin ba zaka tantace dare da rana ba.
Kai tsaye nursing suka zo suka tura Fadeel a keken tura marasa lafiya suka yi emergency room da shi, taimakon gaugawa aka fara bashi kafin zuwan Doctors wadanda ke bawa wa su mutane da aka kawo sun yi accident taimakon gaugawa.
Babu jimawa su ka shawo kan matsalar sannan suka dawo kan Fadeel wanda numfashin shi ya tsaya cak bai da maraba da matacce, sun daɗe sosai akan shi kafin suka samu nasarar ceto numfashin shi ya dawo daidai sai de bai farfado ba.
Doctor Hafeez ne ya nufo inda waiting chairs suke ya taradda FAHAD zaune ya saka hannayenshi cikin sumar kanshi yana cakuɗawa duk ya birkice.
Dafa kafaɗarshi Dr. Hafeez ya yi wanda hakan ya saka shi ya dago birkitattun idanuwansa da suka rine saboda damuwa ya watsa su akan Dr. Hafeez wanda sai da yadan ja baya saboda kwarjinin idanuwan abokin na shi, murmushi ya sakarwa Fahad tare da kauda kai daga kallonshi sannan ya ce.
"Haba manah Man bai kamata ka dinga shiga damuwa irin haka ba, indai Fadeel ne yanzu haka ya na cikin koshin lafiya."
Hada ido suka sake yi da Fahad wanda ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tare da lumshe manyan kaifafan idanuwanshi ya na godiya ga Allah acikin zuciyar shi.
Kamo hannushi Dr. ya yi tare da mikar da shi ya nufi office din shi .
Ruwa ya tsiyaya ma shi masu sanyi ya bashi ya sha, sai da ya tabbatar da ya dan nutsu sannan ya fara bashi bayanai cikin tausasa harshe gami da nasiha da nuna ma shi dukkan abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, sanan babu wanda ya ke gujewa kaddararshi, ko wace cuta ta na da magani sai de wa ta cutar takan jima a jikin mutum ba tare da ansamu maganinta ba.
Cike da kosawa Fahad ya nemi Dr. da ya fada ma shi abin da ke damun Fadeel din, Dr. Hafeez bai ja da nisa ba ya fada ma shi abin da ya nemi tsaida numfashin shi na tsawon lokaci, sai da ya ɗau lokaci yana kokarin bude baki ya yi magana amma abin ya gagara saboda tsananin tashin hankali ganin yanda ya shiga halin rudu da dimauta ya saka Dr. Hafeen fara kwantar ma shi da hankali ta hanyar yi ma shi alkawari akan zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya bawa Fadeel dukkan kulawar da yake bukata.
Zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa daga idanuwan Fahad wanda hakan ya saka Dr.Hafeez cikin dimauta dan tun tasowarsu suna yara bai taɓa ganin abin da ya gigita abokin nashi har ya saka shi hawaye ba sai yau, rungume shi ya yi suka shiga yin hawayen a tare babu me rarrashin wani dan sosai Dr.Hafeez ke tausayawa halin da Fadeel ke ciki, ko a emergency room sai da ya yi kuka ganin halin da kanin abokin nashi ke ciki.
Sun kai kusan mintuna goma a haka babu me rarrashin dan uwanshi kafin daga bisani Fahad ya yi jarumtar shanye kukanshi ya kuma rarrashi abokin na shi tare da fadin.
"Tabbas na shiga tashin hankali da tsananin kaduwa jin cewa dan uwana mafi soyuwa a gare ni na ɗauke da wannan mumunar lalurar amma ban taba sa ni ba, ina jin haushin kaina da nakasa tsayawa wajen kulawa da dan uwana wanda ke girmama dukkan abin da ya shafi rayuwata, kaico da wannan rayuwar."
Haka ya yi ta faɗar maganganu kamar zarare yayinda Doctor ya yi shiru tare da bashi damar amayar da abin da ke damunshi, sai da yaga abin na shi bana kare ba ne sannan ya shiga rarsashinshi tare da nusar da shi kaddarar Fadeel ce a haka kuma Allah yasan dalilin boye abin ba tare da kowa ya sa ni ba sai yanzu da lalurar ta i nisa.
TAUFA WA TA SABUWA KUMA, TO KO MI KE DAMUN FADEEL DIN WANDA ANKI FADI😳 NI TSORONA MA KAR ACE A GARINSU ZULAI YA KWASO CUTAR, KOMI KENAN DAI KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YA DA ZATA KAYA, DOMIN KUWA INA ME TABBATAR MUKU DA AKWAI ZAZZAFAR CAKWAKIYA NAN GABA KADAN.
TAKU HAR KULLUM
MUN KUSA KAMMALA FREE PAGE INSHA ALLAH.