Chapter 9
بسم الله الرحمن الرحيم
Murɗaɗiyar ƙirar jikin shi irinta zaratan jaruman sadauke ce ta bayyana, fatar kijinshi sumul babu alamar darty ko tabon ciwo, sai siraran kwantattun gargasa wadanda ke kyalli da ɗaukar ido, kasancewar aikinshi Pilot ya saka duk wani gashi da ke jikinshi ya ke a tsaftace kuma a kwance, hatta gashin kanshi da sajenshi a kwance suke luf gwanin sha'awa.
Babban towel ya daura a gurguje ya faɗa toilet ya yo wanka, bayan ya fita ya goge jikinshi da wani farin towel sannan ya shafa lotion ya saka gajere wando da karamar farar riga ya haye kan makeken royar bed din shi ya rufu da lallausan bargo ya fara barci cikin nutsuwar da ta zama dabi'ar shi.
BAYAN AWANNI HUDU
Zulaice ta fara buɗe manyan fararen idanuwanta a slow, sai ta yi kamar za ta bude sai kuma ta maida ta kulle saboda hasken da ya wadatu a ɗakin, sai da ta yi hakan kusan sau biyar kafin tai nasarar bude idanuwanta gaba daya tar ta na kallon komi, ba ta gane inda ta ke ba har ta fara ƙoƙarin tashi zaune, nan ne ta ji hannunta yadan rike, dubawar da zata yi sai ta ga kanula makale a hannunta, bin zaren kanular ta gi da kallo har zuwa can saman dan ƙarfen d aka sagaka robar ƙarin ruwa, kanta ne ya sara da tsananin karfi, nan take hoton abubuwan da suka faru suka shiga gilmawa ta cikin kanta, saurin fuzge karin ruwan ta yi tare da dafe kanta da ke barazanar ballewa ta buga razananniyar ƙara wacce ta janyo hankulan ma'aikatan jinyar suka shiga rige-rige wajen zuwa su duba ko lafiya.
Dr.Hafeez ne ya shigo room ɗin da hanzari dan shigowarshi asibitin kenan bayan komawar shi gida ya yi break fast tare da barcin awaani uku, dama hankalin shi ya na akanta ita da Fadeel da Carptain Fahad ya damka amanar kulawa da su a hannunshi.
Iske ta ya yi ta hade kai da gwuiwa ta na ta jujjuya kanta tare da sabbatu wanda shi sam bai gane inda ta dosa ba, ahankali ya zauna saman kujerar da ke gaban gadon cike da tausayinta duk da baisan abin da ke faruwa da ita ba ya shiga yi ma ta nasiha gami da rarrashi.
Zulai sam bata kula shi ba sai da ta gaji dan kanta sannan ta ɗago da kanta idanuwannan a soye sunyi fiki-fiki babu alamar ruwan hawaye a cikinsu, sai de yanda suka kada sukai jazur zai tabbatar ma ka da cewa lallai ta na cikin damuwa wacce har hawaye suka gagara zubowa a idaniyarta.
Cike da zafin rai ta juyo ta fuskanci Dr.Hafeez ta fara magana.
"Nasan kai likita ne, ina so ka nemo allura wacce idan akaimin ita zan mance da wancan ƙauye wanda mutanen cikin shi basu damu da kowa ba sai son zuciya da gudun abin kunya, so nike kai min allurar da zata mantar da ni kowa da komi sannan inzama gagararriyar tantiriya wacce zata addabi al'umma, so nike inyi ƙaurin suna a duniya ta yanda ko suna na aka ji sai ƴan hanjin mutane sun kaɗa, so nike intsayawa kaina tare da Fadeel intaya shi kwatar hakkinsu da aka tauye sannan in temaki dan uwan shi, ka yi sauri likita ina jiranka yanzu dan Allah karka batamin lokaci dan inada abubuwan yi sosai."
Sakato Dr.Hafeeez ya saki baki da hanci ya na sauraren kalaman matashiyar yarinyar da ba zata wuce shekara sha takwas zuwa sha tara ba amma ta zage ta na zayyano irin wadanan kalaman, ko mi ke damunta, sannan inbanda hauka irin nata ta ya zata iya shiga family SHURAIM MUHAMMAD IMAM har ta kwatarwa su Fadeel hakkinsu kamar yanda ta ce, shin wai ma a ina tasan Fadeel da Carptain Fahad?.
Zulai ce ta katse ma shi tunanin da ya ke, ta hanyar kiran.
"Likita!!!!". da karfin gaske.
Inda-inda ya fara yi ganin yanda ta tsareshi da kaifafan idanuwanta masu kwarjini, Allah ya azawa idanuwan Zulai kwarjini babu me iya jure kallon cikin kwayar idonta, ko da a bisa kuskure ka hada ido da ita sai gaban mutum ya fadi saboda kaifin kwarjinin idanuwanta, fararene tas kamar farin fenti wanda ba'aima sirki ba gasu manya sosai Ma sha Allah, kwayar cikin idonta ba baka ba ce, ash ce mai kamar zaiba-zaiba brown, ta na da zara-zaran gashin gira masu tsayi da cika gasu baki ƙirin, ba karamin kyau idanuwanta ke da shi ba.
Da kyar ya bude baki tare da lalubo bargon nutsuwa ya yafawa kan shi sannan ya ce.
"To ƙanwata na ji dukkan abin da kika ce, amma wani hanzari ba gudu ba, ke kanki nasan ba za ki iya samon wadannan alluran ba bare kuma ni, amma idan kina ganin za ki iya samo su babu makawa zan zauna anan ina jiranki idan ki ka samosu da hannuwana zanyi ma ki su wannan alkawarine nai ma ki, abu na biyu kuma ya kamata kiyi nazari akan ke mace ce kuma yarinya irin wadannan kalaman basu dace da ke ba kamata yai ace yanzu kin...."
Bai karasa fadin abin da zai fada ba Zulai ta katseshi ta hanyar kwatsa tsawa kamar karamar yarinya, sannan cikin masifa ta ce.
"A'a malam sauraramin idan ba zaka taimaka min ba to karka sake yimin nasiha tun da nan din asibiti ne ba masallacin juma'a ko islamiyya ba, idan nasiha nike so zance dan Allah likita ka kaini masallaci wajen Liman yaimin wa'azi ko nasiha, ce maka na yi ina so inzama tantiriya ma'ana yar daba ko ƙauriya irin masu yawo da gorori da karnuka, ko kuma iri yan iskannan ma su zama a bakin layi su na shoshalewa su busa sigari su shaki cocain ko wiywiy, ina ma laifin kace zaka kaini unguwar karuwai inkoyo iskanci ta yanda zan dinga yaudarar mazan banza ina kwace musu kudi, ko kuma ka ce za ka kaini gidan rawa irin wanda ake zuwa cikin tsakiyar dare mata da maza ana sharholiya tare da iskanci, tsaya ka ji Likita bokan turai ni yanzu da kake ganina bani da kirki bare mutunci, na tattarasu na watsar a bola tun A DAREN AURENA yanzu na ɗaura ɗamarar iskanci tambada da watsewa dole duniya ta sanni tasan halina daga yau kuma yanzu na canza sunana daga Zulai Mamman Yagawa na koma ZULY BOSS kashe ni sai karshen film."
Tofa masu karatu kuna jin wannan Zulai Mamman din wai ita adole sai ta koma yar iska kuma harda canza suna, shin za ta koma yar dabar koko? ku kasance tare da ni dan jin yanda za ta kayya a cikin wannan ZAZZAFAN LABARIN ME TAKEN A DAREN AURENA.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.