A DAREN AURENA

Chapter 10

by @maryamstar248

Dr.Hafeez tun da Zulai ta fara magana ya saki baki da hanci ya na sauraron yanda ta ke zayyano zance babu tsaitsayawa sai da takai inda take so,sannan ta ƙwace ma shi, a zuciya ya tuno yanda sukai da Carptain ɗazu.

"Please Doctor bazan samu damar dawowa duba ta ba amma idan ka duba kaga babu abin da ke damunta ka kaita gida can sashen masu aiki ka damka ta a hannun Babah Jummai ka ce ajiyata ce ta kula da ita da kyau kafin indawo, shi kuma Fadeel ina so idan na dawo inyi cuku-cukun fita da shi daga ƙasarnan."

"Insha Allah baka da matsala abokina, amma kana ganin yarinyar nan za ta iya zama cikin wannan gidan naku wanda ku kanku ya ke gagararku zama bare ita da take bakuwa?".

Shiru ya yi bai bashi amsaba a lokacin, bai ji haushin abokin nashi ba dan miskiline na bugawa a jarida yanzunma yaga jaruntarshi da ya tsaya yana magana akan yarinyar da shi kanshi bai san daga inda ta fitoba.

Dabara ce ta fadowa Dr.Hafeez dan haka ya gyara zamanshi tare da saita kanshi ya fara magana.

"To Zulai Mamman, wai ashe kin canza suna Zuly Boss na ji duk abin da kika ce, sannan kuma zan taimaka maki har ki cimma burinki ta hanyar kaiki wani gida wanda yafi dukkan wadannan wajajen da kika lissafo hatsari, gidane a suna amma a zahiri ba gida bane domin kuwa a cikinshi ba'a gudanar da rayuwa irinta gidajen da kika sa ni, sannan haɗarurrukan da ke cikin gidan da makirci gami da tuggu ya fi zaman gidan yari masifa, tabbas idan kika sadu da wannan gidan kin cika dukkanin butuka da mafarkanki."

Cike da jin dadi Zulai ta koma ta zauna akan gadon ranta fes fara'a kwance a fuskarta ta ke fadin.

"Yauwa Bokan Turai, ko kaifa, yanzu ace dama kasan da irin wannan gidan shine ka tsaya bata yawun bakinka zaka fara yimin wa'azi, aida kasan akwai irin wannan gidan da ya tara komi da nike so ba sai ka wahalar da kanka ba wajen yimin nasiha, yanzu ya kake ganin za'ayi inje gidan?."

Ta yi maganar cike da doƙin murna yayin da a zuciyarta ta ke faɗin

" Habawa Mamman wallahi kai da Me gari kun gama yawo, tun wuri ku fara lissafin tsayuwar watan tashin hankulanku da dana sa ni dan wallahi saina koya muku hankali alƙiyamarku ta kusa tsayawa'.

Sake maida fuskar shi serious ya yi sannan ya ce

"Ai karki wani damu Zuly Boss ni da kaina zan kaiki gidan amma ba yanzu ba sai zuwa anjima idan na sake duba lafiyarki na tabbatar babu wa ta damuwa ko matsala sannan mu tafi, kinsan gidan ba'a zuwa kai tsaiye dole sai ansan da zuwan mutum."

Kaɗa kai Zulai ta yi alamar ta yarda da zancen Dr. nan ya yi ma ta wayo ya sake yi ma ta allurar barci a cikin sabon drip ɗin da ya saka ma ta, aiko bata yi minti biyar ba nannauyan barci ya yi awon gaba da ita.

KAUYEN YAGAWA.

GOVERMENT HOSPITAL

Mamace kwance kamar gawa sai shaƙar barci ta ke abinta yayinda su Iya ke tsaye a kanta sunyi cirko-cirko ganin yanda ta zage ta bararraje ta na kwasar barci hankali kwance, Maradiyya ce ta ce.

"Dama hwa jiya se da Likita ya ce barci zatai ama Iya kika ki yarda kika wani tasomu tun da hwarar sahiya muka kamo hanya kamar korarru, to gashinan dai kin gani da idonki ba ta tashi ba."

tai maganar ta na tunzuro bakinta gaba.

"Oh ni Salamatu diyar Suke jikar Salmai yau naga abin da ya ishi kakata Salmai, yanzu ke Maradiyya ni za ki gwadawa kauɗin ido, wato ke yanzu kin giga kin gagari kowa, to tsaya ki ji, wallahi ni baki gagareni ba ko da kika ganni haka a koɗe ras nike da sauran ƙarfi a jikina tsaf zan nade mayafi inlakaɗa ma ki shegen duka ta yanda za ki kasa taka wadannan kafafuwan na ki masu kama da danyar doya."

Taɓar-taɓar Maradiyya ta fice bakinan gaba kamar an zunguro kare ta kofa.

A gidan Me gari kuwa yau antashi da hargitsin tashin hankali domin kuwa Habu ne yai dirar mikiya tun asubar fari shi da ƙaurayen abokanan shi su ka hana kowa barci da iface-ifacensu, tun cikin dare suka kamo hanyar Yagawa domin kuwa labari ya riski

Habu akan wai amfasa auren shi da Zulai, wannan ya saka suka tattaro inasu-inasu suka kamo hanya tun cikin dare, Audul ne ke kutuntuma manyan ashariya ya na fadin yau ko shi ko Me gari muddun sukai ido hudu babu makawa sai ya ɓare shi, babu irin haƙurin da su Audu gwangwan ba su bawa Habu ba amma ƙememe ya murje idonshi da toka ya ƙi sauraren kowa, daga karshe ma duk wanda ya zo da niyyar bada hakuri sai Habu ya sa abokanshi su sakarwa mutum mahaukacin kare, ganin yanda karnuka ke wajaga mutanen unguwa ya saka babu wanda ya sake zuwa bada hakuri kow ya ja mutuncinshi ta hanyar kamewa shi da iyalanshi cikin gida.

Habu fa ya rikice ya firgice akan shi fa dole aje a nemo ma shi Zulai duk inda ta ke idan ba haka ba ya sakawa kowa takunkumin zama a gida har sai Zulai ta dawo da kanta, idan kuma mutum ya kuskura ya fito to sunanshi gawa domin kuwa karnuka zai bawa damar yagalgala mutum, takanas Habu ya tada dan shela ya zagaye garin tas ya na fadin sakon Audul.

TOFAH, DAMA

HABU ƊIN ƊAN TA'ADDA NE, HABA NO WONDER ZULAI KE NEMA ZAMA YAR DABA ASHE SHIMA ANGON NATA JAN WUYA NE.🏃🏃🏃🏃

KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA A CIKIN WANNAN KAYATACCEN LABARI.

TA KU HAR KULLUM.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.