A DAREN AURENA

Chapter 11

by @maryamstar248

بسم الله الرحمن الرحيم

ABUJA NIGERIA

Captain bai farka ba sai karfe goma daidai, bayan ya farka ya soma, karanto addu'ar tashi daga barci cike da nutsuwa ya zuro kyakkyawar farar ƙafars hi ya zura slipar ya nufi toilet, wanke fuskars hi ya yi tare da yin brush sannan ya fito ya cire rigar jikin shi ya saka farar jallabiya ya fice.

Kai tsaye main parlour ya nufa, tun ya na akan stairs ya ke jiyo tashin muryarta ta na magana, runtse idanuwan shi ya yi tare da ambaton tsarin Allah daga sharrinta, kamar ba zai karasa saukowaba sai kuma ya yi shahada tare da neman tsarin Ubangiji ya tako har zuwa inda suke, ƙamshin turaren shi ne ya nusar da su wanzuwar shi a wajen, yayinda ya yi sallama cikin siririyar murya kuma can ƙasan maƙoshi, bai jirayi amsawarsu ba ya rusuna kadan ya gaida kamulallen magidancin da ke zaune akan kujera fuskarshi babu walwala.

Bai amsa gaisuwarba sai daga hannu kawai da ya yi cike da izza, kallon yanda duka ahalin gidan suka hadu ya yi amma banda mutane biyu ma su muhimmancin a rayuwars hi, har zai zauna sai kuma ya fasa ya maida akalar idanuwanshi zuwaga inda wani matashi ke zaune, cikin husky voice ya ce.

"Am Abdallah Mamie fah?."

"Ta na dakinta yau ba anan za ta yi break ba Jummai ta tafi kai mata nata."

muryar wa ta matashiya da ta cake cikin ɗan ubansun ado ta karade wajen cike da iyayi.

Juyawa ya yi cikin tako me nuni da zallar jarumta da sadaukantaka ya nufi wajen wasu matattakalai ma su fadi wanda aka malale da grass carpet me zanen flower, bakin ƙofa ya tsaya tare da saka pin ƙofar ta bude, wani irin mayen kamshi ne wanda ya hade da sanyin na'urar sanyaya waje ya daki hancinshi, a slow ya lumshe manyan idanuwanshi tare da buɗesu sannan ya fara takawa a hankali ya nufi ainahin cikin kawataccen parlon, akan wa ta matashiyar dattijuwa wace a ido idan ka kalleta zaka ce bata wuce shekaru talatin ba, amma a baɗini ta wuce nan, zaune ta ke cikin shiga ta alfarma akan wa ta kujerar hannuwanta rike da ludayi ta na kokarin zuba papper soup akan soyayyar plantain da dankali.

Cak ta tsaya da abin da ta ke ganin tattausan hannunshi ya sauka akan na ta hannayen waɗanda suka ƙawatu da jan lalle, a hankali ta janye na ta hannun tare da bashi damar cigaba da zuba ma ta, bayan ya kammala ya dauki glass cup guda biyu ya hada kakkauran tea, zama ya yi akan dayar kujerar da ke fuskantar wacce ta ke a zaune tare da dauko tea cup din ya nufi bakinta, babu musu tai bisimilla tare da buɗe bakin ya saka ma ta tea din ta kurɓa, dankalin ya tsiro a forlk ya saka ma ta a baki, idan ya bata sai shima ya bawa kanshi har suka cinye na cikin plate din duka.

A jiyar zuciya ta sauke tare da jin wani sanyin salama na ratsa gangar jiki da ruhinta, ji ta ke walwala da nutsuwa na saukar ma ta gami da goge dukkan damuwar da ta wayi gari ta riska a safiyar yau, cike da kauna gami da alfahari ta daga hannunta tai ma shi masauki akan kwantacciyar suman kanshi, cikin sassanyar kamulalliyar murya me cike da nutsuwa ta ce.

"My son fatan ka wayi gari cikin koshin lafiya?."

Tattausan murmushi ya sakar ma ta tare da daura hannunshi akan na ta hannun kamar karamin yaro ya shagwabe fuska sannan ya ce

"My happiness ina cikin koshin kafiya tare da albarkar addu'arki da bata yankewa agare ni, ina fatan babu abin da ya ke damunki ya ke ma'abociyar hakuri, juriya gami da hakuri, idan akwai abin da kike bukata adoron duniya mudin zan iya samunshi ki fada mani ni kuma zan tabbatar da na sama ma ki shi da yardar Ubangijinmu."

A hankali ta janye hannunta daka kanshi ta safko da shi zuwa kumatunshi ta dan ja sannan ta saki sassanyan murmushi tare da fadin.

"Bani kai da Allah ya yi ya isheni farin ciki, bana bukatar komi a yanzu domin baka gazamin da komi ba sai de ina so idan babu damuwa ka samomin yar aiki yarinya me hankali wacce zata dinga tausamin kafafuwana, idan da hali ka samo min wa ta daban a waje banda wacce ta fito daga hannun Hajiya Turai." ta karashe maganar da yar damuwa a muryarta.

Zamewa ya yi tare da zaunawa saman tattausan carpet ɗin da ke malale a ƙasa, a hankali ya janyo kafafuwan na ta ya ɗaura akan pillows da ya jera guda biyu ya shiga matsa ma ta su, yayinda ya ke tausa ma ta ƙafa tausayin halinda ta ke ciki ne ya addabi ruhinsa, ya na tsananin tausayawa mahaifiyarshi saboda yafi kowa sanin halin da take ciki, yanzu damuwoyi biyu ne ke addabar zuciyarshi daga ciwon Fadeel sai kuma damuwar halin da mahaifiyarshi ke ciki.

Ci gaba da tausa ma ta fararen kafafuwan nata ya yi yayin da ya ke ƙoƙarin jan ta da fira wacce zata kawar mata da damuwa, sai da ta gamsu sannan ta dakatar da shi ta na saka ma shi albarka tare da addu'o'in samun nasara akan komi, sanar da ita ya yi yanada tafiya yau amma zuwa jibi zai dawo insha Allah, fatan alkairi tai ma shi tare da fatan dawowa lafiya sukai sallama cike da kewar juna.

ZULAI

Ba ita ta farka ba sai bayan sallar azahar inda ta iske har Dr.Hafeez ya dawo tare da kawo mata abinci da kayan sakawa, ma'aikaciyar jinyar da Dr.Hafeez ya kawo akan ta kula da Zulai ce ta cire ma ta karin ruwan tare da taimaka ma ta ta yo wanka a toilet, doguwar riga marar nauyi da dan karamin hijabi ta fiddo ma ta cikin kayanda Dr. ya kawo, babu musu ta saka kayan amma bata saka hijabin ba sai ta daurata a kugu, lafiyayyen girkin da ma'aikaciyar ta zuba mata ta zauna na lashe tas tare da yin gyatsa tai hamdala sannan ta haɗe gira cike da bada umarni ta kalli ma'aukaciyar ta na fadin.

"Malamar asibiti ki buga mani lambar likita kice ma shi na tashi yazo na shirya shi kaɗai ni ke jira."

kallon bangane mi kike nufi ba ma'aikaciyar ta yi wa Zulai, aiko Zulai ta hasala ta tashi daga kishingiɗen da ta yi ta na fadin.

"Dallah malama karki ra

TAKU HAR KULLUM

MARYAM STAR ⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪