A DAREN AURENA

Chapter 12

by @maryamstar248

Dalla malama karki rainamin wayo, ni za ki mayar yar banza, ɗazu ki ce min likita ne ya turoki dan ki kula da ni yanzu kuma kizomin da maganar banza, wallahi zan zubar da ke anan wajen in mommore ki." ta yi maganar tana karkace baki ita a dole sai ta kwaikwayi irin maganar yan daba.

Dr.Hafeez ne ya shigo ya na sakin mutmushi dan ya ji dukkan abin da suka yi.

Kallonshi ta yi taa watsar tare da gomawa gefe ta zauna, sallamar malamar jinyar yai tana ji yana mata godiya, tsaki tayi a ranta tana mitar ko godiyar mi yake ma ta bayan babu tsiyar da ta tsinana mata.

Kallota ya yi tare da fadin.

"Ranki ya dade Boss ina mai matukar ba ki hakuri da jinkirin zuwa da banyi ba da wuri, hakan ta faru ne sanadin na tsaya nema ma ki katin shedar shige da fice a gidan da zan kaiki.

Fuska ba walwala ta tashi tana sake gyara zaman dan karamin hijabinta a ƙugu, a gaugauce ta ce.

"Dan Allah likita mu tahi ka tsaya kana bata mani lokaci."

Baice komi ba yai gaba ita kuma taa bi bayanshi fuskarta a hade, gaban motarshi ya tsaya tare da bude mata gidan gaba sannan ya rusuna alamar girmamawa ya ce.

"Ki shiga lafiya ranki ya dade." wani irin fadi dagirma taji kainta ya yi saboda yanda ya wani bata girma, a duniya in akwai abin d ake bala'in son a girmamata, dariya ce fal cikin Dr. dan shi yana hango yuyuwar zamanta a cikin wannan cakudadden familyn wadanda ba kowa ne tsoron Allah ba, duniya da mugunta gami da tuggu kawai suka sa a gaba. a gefe guda kuma ya na fatan zamanta ya kawo sauri koda kaɗan ne dan hakanan jikinshi ke bashi itadin alkairine zai kaita gidan SHUREIM MUHAMMAD IMAM.

Zaman shiru sukai a cikin motar babu me magana har suka isa MUHAMMAD IMAM ESTATE, karawa manyan idanuwanta girma tai tana kallon aljannar duniya, baki na saki kamar sakarai tana kallon yanda aka tsara tafka-tafkan gine-gine kamar babu mutuwa a duniya, sam bata damu da irin wajen da fa tsinci kaintaba sai ma ƙaguwa mu idasa isa tayi dan tasamu damar bawa idanuwa abinci, indai magana ake ta kallon kwaf daga anzo kanta anrufe kofa domin kuwa akwaiti da yiwa abu kallon ƙurulla.

Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa sassan jikin Zulai daidai lokacinda motar Dr.Hafeez ta tsaya a babban get ɗin shiga gidan SHURAIM MUHAMMAD IMAM, kamar wasa zuciyar Zulai ta shiga duka da tsananin karfi wanda hakan ya saka sai da ta lumshe idanuwanta tare da komawa lakwas ta kwanta a kujerar motar

Kallonta Dr.Hafeez ya yi azuciyar shi ya na fadin 'Allah ne kaɗai yasan dalilin zuwanki wannan gida, wa ta kila zaren kaddararki ne ya janyo ki zuwa wannan gidan, Allah ya sa ta sanadiyyarki a samu canji da zaman lafiya.'

Zulai bata daina jin sanyi jiki ba amma kuma lokacinda Dr. ya harba kan motarshi cikin harabar gida sai da ta ware manyan idamunuwanta ta na kallon wannan gida wanda aka narkarda zazzafar dukiya wajen ƙerashi.

BAYAN MINTUNA GOMA

Zulai ce zaune akan luntsumemiyar kujera ta na lumshe ido gami da kara lumewa jikin tattausar dujerar, ta na jin Dr.Hafeez na yiwa Mamy bayani akan Carptain ne ya ce ya kawota wajen Baba Jummai, ta so ta saka baki ganin yanda Dr. ya karkace ya shuto ƙarya wai wajen wata Basbah Jummai ya kawota kuma wai wani ne ya ce akawota alhalin babu wanda ta sani ko yasanta sai Fadeel da shi kuma Dr.

Yai ma ta bayani akan batada lafiya harma yakaita ta leka ta glass taga yanda yake kwance magashiyyan, har hawaye sai da ta zubar ganin halinda ya ke ciki.

Ware iyakar girman idanuwanta tai ta na karewa katon parloun kallo tare da mamakin wai wannan gidan a Nigeria ya ke, ta na mamakin wane irin rashin sanin ciwon kai ne ze saka mutum ya kashe uwar dukiya har haka wajen gina gida, gidan da mutum yasan dole ya mutu ya barshi duk kyau da tsaruwarshi.

Kallon kyakkyawar matar da Dr. ya kira da Mamie ta yi jin ta ambaci sunanta raɗau a bakinta, ɗan ɗagowa Zulai ta yi tare da mere baki gefe ta fara magana.

"Zulai Mamman sunana ne amma ada banda yanzu hajiya, ki kira ni da Boss kawai zan amsa ma ki."

Yanda Zulai tai maganar ta na wani ciccije baki gefe ya bawa Mamie dariya, a fuska dai yarinya ce sosai amma yanda ta yi maganar kanta tsaye ya burge Mamie dan sosai ta ke son mutum irin haka masu fadin gaskiya babu kwana-kwana, mutmushi ta yi tare da fadin.

"In banda abinki ƴa ta yaushe zan kira ki da wannan sunan, dade za ki fadamin sunanki na ainahi da zanfi jin dadin kiranki da shi."

Ƙuri Zulai tayiwa Mamie da Manyan idanuwanta ta na ganin nutsuwa da kamala a wajen Mamie, yanda ta ke magana kadai ya isa ya tabbatar maka cewa matar ta kai ajin karshe wajen haduwa, gayu gami da wayewa me hade da ilimi.

Zulai bata san sanda wa ta nutsuwa ta saukar ma ta ba daga kallon matar sai ji tai bakinta na furta.

"Sunana Zulaika A Maleek, amma a kauyenmu da Zulai Mamman ake kira na saboda Mamman shine wanda ya rene ni, duk da dai ba wani so na ya ke ba sosai, Mama da Iya da Anty Mardiyya giwar mata su ne kadai ke so na."

"Masha Allah sunanki me dadi kamar yanda kike da kyau, za ki zauna tare da ni ko yata Zulaika?."

Mamie ta yi tambayar cike da fatan amsawar Zulai.

Zulai na kokowa da zuciyarta da ke hanata amsawa amma bakinta ya yi caraf ba tare da shawararta ba ya amsa wa Mamie da "Zan zauna tare da ke."

Kurrrr Doctor ya kure Zulai da idanu ya na mamakin sauyawar tunaninta haka da wuri-wuri sai ya fara tunanin ko dan ta ga gidan ba yanda tai tsammani ba shi yasa, domin kuwa kowa yasan ahalin IMAM MUHAMMAD shahararrun manyan attajiraine wadanda ake alfahari da su a Nigeria saboda irin cigaban da gudumuwar da suke bayarwa ta hanyar wahaltama kasa da dukuyarsu harma da ƙarfinsu.

Assalamu alaikum masu karatu, adaidai nan na kawo karshen free fage dama na sanar zan tsaya da free page daga page 12 ku kasance tare da ni domin yanzu za'a fara ainahin labarin.

WANNAN LITTAFIN PAID BOOK NE AKAN NAIRA 300 KACAL, KI DAURE KI MALLAKI NA KI DAN KARANTAWA CIKIN SALAMA.

GA WANDA ZASU BIYA KUDI DOMIN SAMUN CIGABAN LABARIN KU TUNTUBE NI TA WANNAN LAYIN.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇

***

Chart only

TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR