Page 58
*MARYAMA*
By
Ummu Fadeela.
58
Dan tsokaci:-
Ba lallai mai karatu ya samu abun da yake so hundred percent ba a littafi, ko yaya sai an samu mishkila. Kamar dai yadda muka sani no body is perfect only God, today's episode zai zo da sabon salo, so plsss ku karbeshi a yanda yazo, domin bangaren labarin Sameera is not a fictious story, ya faru a gaske ne ba kirkirarshi aka yi ba so dole a rubuta shi yadda ya faru don haka mubi labarin a yanda ya zo mana, thank you all...
_
Gudu take yi a kan hanyar iya karfinta tamkar mai gudun ceton rai. Duk horn din da ake buga mata bataji, cike da mamaki yake kallonta, tabbas ita ce amma ina zata je?
Ya yiwa kan shi tambayar lokacin da yake gangarawa gefe dan kar ya buge ta, a kokarin da yake na kauce mata ne mistakenly ya dan bugi wata mota dake tsaye gefe dashi kadan, birki ya ja ya tsaya yana balle marfin motar hadi da fitowa.
Tayi nisa sosai a gudun da take yi dan haka ya juya gabas da yamma ganin babu kowa wajen shima ya ruga a guje ya bi bayanta.
Gudun mace bazai hadu da namiji ba, dan haka baifi taku takwas zuwa goma ba ya cimmata, cidakk ya dagata ta baya kamar ya dau yar tsana haka yaji tsabar rashin nauyin ta ya nufi wajen motarshi da ita.
Kiciniyar kwatar kaina na fara jin anyi sama dani amma na kasa sai da ya bude motar ya jefa ni ciki sannan na ga fuskarshi, zaro idanu na yi cike da kidima na hade hannayena duka biyu na fara bashi hakuri da magiyar kar ya kaini gida.
Kashe ni za su yi amma bai kula niba sai motar da ya ba wuta bayan ya shiga ya zauna.a ranshi yana tunanin ba don Atm na shi da ya manto gida ba, da yanzu ta tafi ko ina zata nufa dama? Allah masani.
"Ina kika nufa yanzun?"
Ya watso mata tambayar, amma ga mamakinshi bata ce komai ba sai kukan da take yi kamar ranta zai fita,..
Calmly ya kara fadin, "Ina kika tafi? waya baki ikon fita daga gida?". Still batace mishi ko uffan ba, harzuqa ya karayi zuwa lokacin, a take ya fara jin zuciyarshi na tafarfasa wani irin tsanar yarinyar yake ji yana ruruwa cikin zuciyarsa irin wadda bai taba yiwa wani mahaluki ba a duniyar nan....
(Yan'uwa mu rike azkar na safiya da maraice, mu rike karatun Alqur'ani Insha Allah zamu fi karfin sharrin abun hallita, yawanci bayan kaddara da jarabawa da kan zo daga ubangijinmu, rashin azkar da karanta Alqur'ani mai girma shike bada gudunmawa wajen yin tasirin asirin da munafukai ke aikatawa a jikkunanmu).
Wani wawan birki ya ja yana huci gami da fizgo ta da karfi ta fado jikinshi, kamar kashi ne ya zube mishi a jiki haka ya hankadata ta koma baya ta bugu da jikin marfin motar, wani irin azaba ne ya ziyarci keyarta nan ta fara ganinshi dishi dishi da bakinshi dake motsi da sauri sauri alamar masifa yake yi har idanunshi suna kankancewa, sai dai ko kalma daya banaji daga gareshi.
"Ya Allah, am I daft?" Na tambayi kaina ina dafe keyata dake cigaba da sani hajijiya daga zaune, kodai na kurumce ne? na kuma tambayar kaina babu mai bani amsa wasu hawaye masu dumin gaske ke rige rigen sauka saman face nawa.
Zuwa lokacin Qaseem ya fara tantamar da gaske yarinyar akwai kwankwamai a kanta duk yadda akayi, dan ya lura cewa batajin abun da yake fada ne ba wai ganganci ne ba,wani sashi na zuciyarshi na son tausaya mata, but wannan sashi da ya tsaneta din yafi rinjaye dan har wani ji yake kamar ya shaketa ya huta.
Da mugun speed ya ja motar yana danna horn da karfi watchman ya zo ya bude musu gate. Ko gama parking baiyi ba ya bude motar ya fito sannan ya zaga ta bangarenta ya damki hannunta gami da janyo ta da karfi ya nufi entrance na gidan.
Cikin rawar jiki Sameera dake gyara wajen cin abinci da akayi diramar dazu ta saki sweeper dake hannunta da gudu ta nufi bakin window jin shigowar mijin nata, arba da tayi dashi janye da Maryama yasata dafe kirji a lokaci guda gabanta na faduwa, "wannan wacce iriyar masiface haka? Duk wuyan da tasha yarinyar nan bata tafi ba?".
Shigowar Qaseem yana kwala mata kira ne yasata matsawa daga jikin window din tana karasowa gabanshi...
"Sameera ta tabbata yarinyar nan aljanu gareta, kina ina harta fice daga gidan nan baki dakatar da ita ba? Yanzu ba dan Allah ya takaita min wahala ba, har na iso bakin eatry da zan mana takeaway na laluba naga ban fito da atm dina ba, babu shiri na juyo, a nan tsakiyar titin anguwar nan na tsince ta tana ta zabga gudu", duk maganar da yake yi ko kalma daya Maryama bata ji ba.
"Honey, dama ka bani ajiyar ta ne da zaka tuhume ni akan fitarta? Gaskiya wannan ba adalci bane, tun yaushe nake fada maka akwai damuwa akan yarinyar nan amma kaki aminta ga shi dai yanzu ka gani kallon idonka, don haka sai ka dau mataki.
Zaro ido na yi dan tabbas na ji abun da matar ta fada, amma mai yasa idan shi yayi magana bana ji? bani da mai bani wannan amsar dan haka na ci gaba da kukana.
"Dole ne ma in dau mataki, dan tabbas zata kara yunkurin guduwa, idan ta gudu kuma ban kyautawa modibbo ba, ban rike amanar da ya yi ta jadadda min in rike ba.
Dan haka yanzu zan daureta zuwa gobe in nemo mai ruqiya a fara yi mata, ko ya ki ka gani?".
"Dauri?" cewar Sameera tana zaro idanu kamar taga abun tsoro, sai kuma ta fashe da dariya, tace.
"Karka damu honey, ba sai ka nemo mai ruqiya ba nima na iya ruqiyar ai zan kona su yadda ya kamata har sai sun bar jikinta kai dai ka bani dama kawai," cewar Sameera murmushin mugunta kwance bisa fuskarta.
"Kiyi duk abun da ya kamata na baki dama".
That's my honey, sai ka samo mana ma'ul khal,da man habbatussauda ,da kuma zaitun, inajin dasu ake amfani."
Baice komai ba ya shige abun shi dan wani irin sarawa kanshi ke mishi, tun da ya hadu da yarinyar hankalinshi bai kwanta ba bai samu nutsuwa ba har yanzu.
Yana wucewa Sameera ta juyo tana ganina da idanunta dake sani jin kamar in saki zawo a wajen duk sadda ta kalleni dasu tace, "Kin san mai yasa bazan bari ya daure ki ba da kawo mai ruqiya? Nasan baki sani ba, to nayi haka ne domin kaina, dan kar a bata min aikina. ke kuma tunda taurin kai ya hanaki tafiya hakan ya tabbatar min aikin bautar kike bukata, so lets go yanzu zaki fara gaba daya abubuwan da na irga maki a gidan nan.
_____________________________________
Hakan ce kuwa ta kasance, a kullum ta Allah rayuwata kara shiga garari take, na zama ni da baiwa bamu da bambanci kamar dai yadda ta fada tun fari. tun ina kuka yanzu hawaye na sun bushe saidai kukan zuci, a duk sadda na kai goshina kasa da nufin neman gafarar ubangijina, sai inji kunya ta kamani sai in rasa mai kuma zan rokeshi bayan gaba daya ni'imar rayuwar da ya yi mini a baya amma na butulce mishi, haka zan dago kaina ina mai dana sani da inama zan maida hannun agogon rayuwata baya kamar shekaru biyu da rabi da suka shude.
Duk ma'aikatan gidan ta sallamesu. ni nake hatta da wankin motoci idan bai fita ba kuma in sake,tun ban iya ba har na kware bana manta day one da na fara wanke motocin bansan yadda akeyi ba dan haka na dinga kwara musu ruwa ashe na jika cikin motar sharkaf ranar ba karamar duka naci ba a hannun Sameera
Shikuwa qaseem ya zama tamkar mutum mutumi baida wani katabus a gidan sai abun da matar ta fada.
Dan haka dan wanzuwata da rashin wanzuwata duk daya a wajenshi duk abubuwan da take min bai cewa ko kala. Ta inda na samu sauki dai shine gane ganen da na daina yi, amma har gobe a gaban Qaseem ni kurma ce, duk maganar da zai min bana taba ji amma idan wasu sukai magana na kan ji radau.
Duk na rame na kwanjale na fita a kamannina kamar ba wannan maryamar mai ji da kyau ba, kamar ba wannan Maryamar wacce ta fi karfin auren talaka ba, kamar kamar kamar....
Yau na tashi da matsanancin ciwon mara na wata wata da ya saba yimin, ciwon ciki da mara ga amai da kuma gudawa duk wata haka nake fama, ni kadai duk sadda ya zo min nakan yi kuka da tunawa da hamma Jabeer irin yadda yake shiga tashin hankali duk sadda nake fama da cramps irin yadda yake tsananin bani kulawa har sai na warware, share hawayen idanuna nayi a karo na barkatai ina amsa kiran da Sameera ke kwalo min daga falo.
Da gaggawa na mike ina jin jiri na kwasata ga cikina dake kartawa na fito kafin tazo ta karasani a dakin.
A falo na sameta ita da bakuwa da zuwa lokacin na fahimci yayarta ce datake kira anty falmata tana yawan zuwa gidan, kallon sama da kasa suka min dukkansu kafun tace, "me kika je kika kunshe a daki bayan kinsan baki gama aiyukan ki ba?, "cewar sameera.
Cikin sanyin murya na ce, "Kiyi hakuri banajin dadi ne shiyasa"
"Wuce ki kawo wa anty na ruwa da drink, kiyi warming snacks dake cikin frizer din nan a microwave ki hado dashi."
"Da to " na amsa na wuce kitchen din ina jan kafa da kyar dan halin da nake ciki...Sai a lokacin Falmata da tun da Maryama ta shigo pakon idonta ke kanta kyam ko gaisuwar da take mata bata amsa ba ta juyo tana kallon sameera tace, "Ke Sameera anya kuwa bama kitso da kwarkwata kuwa?"
"Kamar yaya kitso da kwarkwata anty? ban fahimci hausar ba ki fahimtar dani dan Allah".
"Ina nufin kin tabbata Alqaseemu baya kebewa da yarinyar nan? Anya baya bin dare yaje ya biya bukatarsa ba tare da saninki ba?".
A zabure Sameera ta mike tana dafe kirji gabanta yana dukan tara tara tace, "Na shiga uku ni sameera, Allah karka jarrabce ni da abun da bazan iya dauka ba, me kika gani anty? dan Allah sanar dani kar zuciyata ta buga. sanar dani kar in karasa ta tun yanzu".
Cewar sameera tuni hawaye ya balle a idanunta.
Janyo hannunta falmata tayi tana fadin, "Tsiyata dake kenan gajen hakuri, dalla malama zauna, ayi maganar fahimtar juna, "Ke bakiga yadda yarinyar ta zama wani iri ba, gashi kirjinta sun cicciko kamar mai juna biy...
"Bata karasa ba Sameera tayi wani irin mikewa a firgice, karya ne anty, karya ne wallahi, babu wacce ta isa in hada miji da ita, babu wacce ta isa in hada shimfida da ita, haka babu wacce ta isa ta haihu da Qaseem sai ni kad...." itama maganar tata yankewa yayi sakamakon fitowa da nayi a guje daga kitchen din da nufin shiga daki na dan wani amai da ya taso min na al'adata, saidai ban samu kaiwa dakin ba na durkushe bayan kujerun dake palon na fara kwarara amai kamar zan amayar da kayan cikina.
Wani irin jiri ne ya fara diban Sameera yayin da anty falmata ta mike tayi saurin rikota ganin zata kai kasa, kamar mahaukaciya ta fizge ta nufi wani fruit basket dake zaune kan dining table ta dauko wukar dake ajiye a ciki ta nufi Maryama gadan gadan kamar wata zakanya. Ganin maganar anty Falmata ya tabbata lallai Qaseem ya ci amanarta ya yaudareta... Ya kwanta da wata mace ba ita ba har ma ya dirka mata ciki, ita kuma bai mata cikin ba tsawon shekaru goma suna tare.
Dam damm kirjina ya bada sauti ganin tayo kaina hannunta rike da wuka ga idanunta na tsiyayar da hawaye abun da ban taba gani ba tsawon watannin da mukayi tare da ita. Mikewa na yi jiri na debana na fara yin baya baya ina girgiza kaina ganin babu inda zan bi dan tseratar da raina, fuskarta babu alamun rahama ta ke matsoni yayin da hawaye ke ci gaba da wanke mata fuskar lumshe idanu nayi lokacin da na zo gaf da kofar fita palon ina jingina a jiki da addu'ar Allah yasa hakan shi ne karshen wahalata, tamke ido Sameera tayi da karfi ganin ta iso ta ta kawo mata wani wawan suka da wukan a tare anty Falmata da Maryama da kuma Qaseem suka saki wani irin kara mai firgitarwa, shigowarshi ke nan gidan yana bude kofa ya hango abun da Sameera ke kokarin aikatawa cikin zafin nama ya cafko Maryama da kokarin maida ita gefe, sai saukar wuka yaji a gefen cikinsa.
Karan da sukayi yasa Sameera bude idanunta da karfi, da wani irin zabura itama ta fada kan Qaseem da suka fadi gefe guda da Maryama gefen cikinsa na bulbular da jini, duk wani abu da ke aiki a jikin Maryama tsayawa yayi cakkk kamar daukewar ruwa a karon farko ta ambaci sunanshi da karfin gaske"Qaseeeeeeemmmm".
Qaseeeemmm" Sameera ma ta ambata, damko hannun Maryama dake gefenshi yayi ya rike da karfin gaske wani irin jini yana biyowa ta bakinshi, a hankali bakinshi ya motsa babu wadda yaji abun da ya fada kanshi ya fadi gefe.."Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un maryama ta ambata yayinda ta daura hannunta saman wukar dake jikin cikinshi da nufin zarewa dan ji tayi zuciyarta ta bushe kamassss babu kuma wani sauran tashin hankalin da ya rage bata gani ba a duniya.
A hankali sameera ta mike ta fara kallon kowa bibbiyu, palon ya fara hajijiya da ita cikin kasa da minti daya ta fadi kasa a hankali ta furta Honeyyyy.
Daga nan numfashinta ya dauke.
Kallon kallo aka fara tsakanin Maryama da a lokacin in za'a tambayeta sunanta tabbas baza ta tuna ba, da falmata wacce tayo kan yar'uwarta da gudu.
Wani irin tunani ne ya fadowa Falmata da hanzari ta saki kan Sameera jikinta yana rawa ta mike gami da daukar jakanta ta shige dakin samerar, wayarta ta lalubo ta fara neman layin yan sanda na emergency.
Maryama na zaune jikin Qaseem har lokacin hannunta daya damke cikin nashi, daya hannun kuma rike da wukar da ke makale a cikinshi har lokacin tana zaune kawai kamar mutum mutumi, komai dake cikin kanta ya goge sai wanda ya sani ne kawai zai fahimci cewa suman zaune tayi.
A lokacin ne kuma karar jiniyar yan sanda ya karade illahirin unguwar inda suka cika tsakar gidan Qaseem, jiki na rawa Falmata ta fito a daidai lokacin kuma sufetan yan sanda da sauran jami'an suka shigo,.
"Officer gata nan, ita ce wannan" cewar falmata dake nuna Maryama da har lokacin bata a hayyacinta da yatsa, idanunshi ne ya sauka kan hannunta dake rike da wuka akan cikin Qaseem sai daya hannun dake rike cikin nashi, a ilimin shi na aikin tsaro take ya gano cewa jinine ya hau kanta shi ya sa ta zama haka, wato dai ita ta KASHESHI.
"Call the ambulance" cewar sufetan yana kallon sauran ma'aikatan, daya daga ciki ne ya fitar da wayoyinsu irin na yan sanda ya kai kusa da bakinshi ya sanar da General hospital suna bukatar ambulance a gida mai lamba...Dake anguwar......Abuja.
Babu bata lokaci ambulance ya iso sai a lokacin wani ya matso kusa da Maryama ya sanya farin hankici ya zare hannunta gami da zaro wukar dake jikin Qaseem wani dake gefe ya bude mishi wata farar leda mai bakin zip ya jefa wukar a ciki raba hannunsu dake makale akayi sannan aka kwashi Gawar Qaseem da Sameera da har lokacin babu wadda ya tabbatar ko tana raye aka wuce da su cikin ambulance din. jami'an suka fara zagaye gidan daki daki suna bincike irin nasu, wata yar sanda mace ce ta zo gaban Maryama ta tsugunna gami da daga mata handcuff ta ce, "You are under arrest for the suspect of murdered.
Daga haka ta makala mata handcuff din tana mikar da ita tsaye. Amma duk yadda akaso ta tsaya kasawa Maryama tayi sai kafafunta dake rawa da kirjinta dake luguden daka, kuma ko digon hawaye babu a fuskarta hoton fuskar Qaseem ke ta mata a yawo a allon zuciya.
Gefe da gefenta yan sanda mata biyu suka kama, tana ji tana gani aka fito da ita zuwa lokacin makwafta sun cika tsakar gidan, a gaban gomman mutane aka cusa ta cikin motar nan ta shiga ba biya fita da Allah ya isa, garkame gidan akayi da kwado bayan Anty falmata da mai gadi duk sun shiga motar yan sandan, can headquarter aka wuce da Maryama sashen binciken manyan laifuka aka tsareta a can tsabar tashin hankali sai da Maryama taji kamar gaba daya duniyar aka daura mata aka, dan tunda take bata taba ganin waje makamancin wannan ba.
Kwana biyu tana tsare a can a lokacin babu abun da ya rage a jikinta sai idanunta, cikin kwana biyu aka cike kara aka mika gaban kotu.
A bangaren Sameera kuwa tun ranar ta farfado sai dai bata uhm bata uhmuhm, ba karamin dadi hakan yayiwa Anty falmata ba, dan zai taimaka wajen yin nasarar yar'uwar tata a kotu.
Qaseem kuwa tuni aka kaishi gidanshi na gaskiya bayan su modibbo sun zo daga yola.
Babban lauya mai zaman kanshi Falmata ta daukarwa sameera, ba karamin kudi ta kashe ba dan winning case din, itama Maryama an bata lauyan gwamnati sai dai ko da yazo don yi mata interview babu abun da ya samu daga wajenta har ya gaji ya tafi sai idanu kawai take binshi da.
____________________________________
Yau ake zaman shari'arsu, sosai kotun tayi cikar kwari kasancewar bayan nasu shari'ar akwai wani shariya da za'a gabatar.
Kowa ya hallara manya da yara kasancewar labarin ya yadu a duniya na matar da ta kashe mijinta kamar yadda ake ta yayatawa.
Maryama tana tsaye cikin dan akurkin da ake ajiye masu bada shaida da wadanda ake tuhuma. bayan zaman alkali sai kowa ya nutsu kotun tayi tsiitt baka jin komai sai karar kadawar fankoki, lauyan mai kara ne ya mike ya fara gabatar da kanshi.
Sannan lauyan wacce ake kara shima ya gabatar da kanshi. maga takarda ne ya mike ya karantowa Maryama laifin da ake tuhumar ta dashi na kisan mijinta Alqaseem modibbo, shiru kotun ya kara dauka lokacin da Alkali ke tambayar Maryama "shin kin amince?" shiru bata ce komai ba, dan duk abun da ake yi a wajen sai take ganinshi kamar a irin serial fim dinnan na india.
Lauyan mai kara ne ya fito zuwa gaban Maryama ya kara tambayarta "Malama Maryama, shin ko zaki iya fada mana dalilinki na kashe mijinki Alqaseem Modibbo?" rumtse idanu nayi da karfi a karon farko.
Lauyan dake kare wanda ake kara ne ya mike da hanzari yana gyara hular gashin dake kanshi ya ce, "Objection my lord,akwai alamun tursasawa da kuma tozartarwa a harshen lauyan dake kara brr musa kallah,"..."Barrister musa kallah, a kiyaye, cewar alkali"
Rusunar da kai musa kallah yayi da fadin, "Za'a kiyaye ya mai shariya". Ya kara juyawa kan Maryama saidai duk tambayar da yai mata babu amsa, hakan yasa ya juyo yace
"Ya mai shariya ina da hujjojina masu karfi da zan nunawa kotu na cewa lallai Maryam Alhassan itace ta kashe mijinta Alqaseem, nafarko, wani farar leda ya dauko dake dauke da tambarin yatsun Maryama wanda aka samu kan wukar da aka kashe Qaseem dashi, magatakarda ne ya karba hannunshi rike da hankici shima ya mikawa alkali.
Kkallon tsanaki alkali yayi wa abun sannan ya gyada kai, na biyu shine mai gadin gidan, malam garba in kana kusa bismillah,
Koda ya fito shima yana kallon alkali yayi rantsuwa da cewa zai fadi gaskiya, saidai sabanin tunanin Maryama karya ya ringa sharawa na cewa dama kullum cikin fada suke....
Objection my lor....." cewar lauyan mai kare Maryama da ya mike zai kalubalanci garba mai gadi, amma sai Maryama ta dakatar dasu ta hanyar toshe kunnuwanta da karfi.
A karon farko tun bayan mutuwar Qaseem tayi magana da karfin gaske har dakin na amsa kuwwa tace
"Duk ku dakata, duk na hutar daku. kowa ya koma gida ni..nice na kashe shi. ni na kashe shi da hannuna."
Ta fada tana daga hannayenta duka biyu.
Sai kuma ta sassauta murya ni na kashe shi da hannuna. nima ku kashe ni ko zan huta da wannan duniyar mai cike da tashin hankali.
Ta fada tana sakin wani marayan kuka a karon farko.
Kotun ne ya barke da hayaniya har saida alkali ya buga gudumanshi sau uku sannan aka nutsu, farin gilashinsa ya zare ya goge sannan ya mayar yace
"Malama Maryam shin kin amince ke kika kashe shi?".
"Ehh ni na kashe shi ya mai shariya, ni na kashe shi da wuka na soke shi a gefen cikinsa nima dan Allah ku kashe ni."
Nisawa alkali yayi kafun yace, "Bisa saukakawa kotu bincike da Malama Maryama Alhassan tayi, kotu bisa adalcinta ta mata hukuncin daurin rai da rai sabanin hukuncin kisa nan take da za'ai mata matukar an sameta da laifin. Gudumar dake gabanshi ya buga sau uku yana mikewa.
"Court jama'a suka fada,."
A hankali maganar alkalin ke maimata kanshi a cikin kwakwalwata.
"An yanke mata hukuncin daurin rai da rai" Maryama is sentences for death" Innalillahi wa'inna ilahiraji'un na fada a hankali.
Hoton Hamma jabeer ya bakunci idanun zuciyata da muryarshi...
"Maryama ina sonki, zan ci gaba da sonki har karshen numfashina, plsss don't betray me no matter how situation goes, Maryama ki soni koda kaso daya cikin wanda nake miki, Maryama son ki ne jarabtata kuma na tabbata shine ajalina, i luve yoh Pretty.
Another picture Innarmu, Maryama kiyi hakuri da rayuwa a duk yadda tazo miki, ba baki nake miki ba, amma matukar kika guji jabeeru bazaki taba samun makancinsa ba, ita duniya cike take da darasi kala kala Maryama, tabbas idan bakiyi sharar masallaci ba za ki yi ta kasuwa.
Another pictur