SOYAYYAR ZUCI

Chapter 22&23

by @deeyamerh10

đź’–đź’– SOYAYYAR ZUCIđź’–đź’–
    (Love and Romantic story)
                 Written 
                         By
                 Deeyamerh
07070647236
Page 23&24
Da wuri ya tashi domin yana so ya shiga asibiti da wuri domin yana so yaje bikin abokinsa dan yayi alkwari da bazai jeba zai tsaya wajan mafara lfyarsa.domin kuwa shi ne abu mafi muhimmanci da yake so fara kafin ya bar gari idan so samu ne ma yau su dawo tare da ita ya dangawa hajjiya ita a cikin abubuwan da ya tsara a ranar kenan. Bayan ya gama karya, ya ɗan zauna yana hira da Hajjiya, tare da addu’o’in samun nasara da alheri a rayuwarsa . Sai a lokacin ya tambaya hajjiyar“ wai Ina ’yan matan gidan?”
Hajjiya ta ɗan yi shiru kafin tace, “Wallahi tun da suka tafi gidan Saheeba suka ƙi dawowa. Ni fa na fi zargin dawowarka gidan ce tasa yarana guduna.”
Ya É—aga gira, yana kallonta.
“Ni kuma, Hajjiya, me na yi musu da za su gudu daga na dawo”
“Hmmm…” Ta ja numfashi. “Ai kana sa ƙafa ka bar gidan. To fa, ba mai zuwa makaranta nake fada maka ba, ko wacce ta makale a ɗaki wai bacci. Idan ka ji shigowarka sai ka ji shewarsu. Damansan na ce zan faɗa maka. Amma fa kar ka ce ni na faɗa maka, ah!”
Dariya ya yi, amma wannan karon dariyar ba ta daÉ—e ba. Sai ya girgiza kai, yana jin haushin halin yaranan wato yawage bakin aljihu wato suki zuwa ko.
“ murmushi yayi sannan yace wato Hajjiya, an haɗa baki da ke an yi laifi yanzu Kin ga ba sa nan, kin faɗa. To ki da ’yan matanki ku ci gaba da shirya min abin da zan ji idan na je can.”
Ya ɗauki wayarsa ya kira Saheeba. Tunda ita ce ƙanwarsa, sai ya sa wayar a hands-free.
“Hello, Yaya. Barka da safiya.”
“Yawwa, barka. Ya kuke? Ya su Asham?”
“Suna lafiya, Yaya. Ya Hajjiya ta?”
“Tana lafiya. Yawwa, ke ina yaran suke?”
Saheeba ta ɗan yi shiru. Tun da suka miƙa mata wayarta, suka ce mata Big Boss ne yake kira, duk suka zo suka zauna gabanta, kowacce da fuskar tausayi.
Cikin nutsuwa tace, “Gasu a gabana.”
“Dukansu?”
"Eh, dukansu.”
“Ki sa wayar a handsfree"
Saheeba ta kalli ’yan matan. Nan take suka fara kallon juna, babu wacce ta iya kwankwaran mutse cikinsu.
Big boss nasaka suna jinka
Daga cikin wayar suka ji muryarsa mai cike da faÉ—a
"Nabawa ko wacce mins 10 na ganku a gida wllh wllh kuka dara haka ko wacce ta kuka da kanta".
Ai ba wacce ta tsaya nemi komawa É—aki, domin É—auko jakar kayan da suka zo da ita, ko wacce wayarta ta dauka fita da gudu. Don ko maganar da Saheeba take yi masu basu tsaya saurara ba. Su dai fatansu su kai gida kafin cikin mintuna goma É—in da ya ce, tunda basuda nisa da gidan nasu.
Har da gudu suke haɗawa, kowa yana ƙoƙarin ganin sun isa gida da wuri. Inda Allah Ya taimake su, safiya ce, ba kowa a hanyar sai masu zuwa training ke wucewa jefe-jefe, wasu da gudu, wasu kuma a hankali.
Su kuwa ba su damu da komai ba sauri suke har da har dewar kafafu,ji suke kamar su bude ido su gansu a gida dan Big Boss ba sauki wllh zuciyarsu cike da zullumui suka kwankwasa get din gidan.
Da sauri Getman din gidan yazo ya bude lekowa yayi yagansu da sauri ba su hanyar wucewa.
Ai suna shiga farfajiyar gidan suka manna a guje,suna zaune a parlon sai ji sukai sun fada da gudu ba inda sukai burki sai gaban Big Boss hannuwa biyu su ka hada gurin bashi hakuri"Dan Allah Big Boss kayi hakuri bazamu kara ba.
 Danna wayar da yake har sai da yaga abinda zaiyi Sannan ya kalle su daya bayan daya,da sauri suka sunkuyar da kansu kafin ya bude baki yace"kun gama makaranta ne?da zaku tafi wani wajan ku zauna?ko kun gaji da karatun ne ko wacce ta fito mijin Aure nayi mata?"
Girgizar kai suke kamar wasu ka dangaru,tsawa ya daka musu"zaki bude baki kuyi mun magana ne ko zaku tsaya kuma bani single word ne ?
A'a big boss kayi kahauri mun san samu mis semester shine muka je muyi 1week sai mu dawo kafin ranar mu koma.
Hajjiya ya kalla Domin Indai haka ne zata fada,ai tana jin haka tace "Oh Ni Amina ashe haka sukace mun da zasu tafi".
Kallonta yayi da ido kawai domin lamarin hajjiya sai ita.
Kawani tsare Ni da wasu idanu kan kana kallona banace mantawa nayi ba to yanzu na tuna ba Shikenan ba.
Sai yanzu suka gane ashe hajjiya ce ta hado musu komai.
Murmushi yayi yace hajjiya ta kenan ai daga gani wllh Alhaji yasha fa da lamarinki.
Dariya duk sukayi hajjiya tace"ai haka yake ce mun Akuke sarkin rigima Allah ya jikan mahaifa ku,shiyasa nake muki addu'ar Allah yasa yadda naji dadi a soyayya da gidan miji yasa kusami abokin zama masu irin halinsa".
Ameen ya allah mikewa yayi yace hajjiya bari zan shiga hospital daganan zan wuce Kano bakin abokina idan nake naga jikin nata inshallah xansa Dr Maryam kawuta insha.
To Allah yasa ma big boss tasamu llfy wllh Muna so muganta ko dan labarin ta da muke ji a gunka.
"Tom Allah dai yasa kada kudameta da rashin idan ji".
Ficewa yayi daga parlon,kallon Hajiya sukai dariya tasa tace "eh fa kun tafi gun yar uwarku Ni kun barni a gida kamar wata marainiya".
"Yanzu hajjjiya da yabamu gwala gwala fa"?
Bama zai baku ba Auta shiyasa na zauna ai duk abinda zaiyi akan idona.
Tunda yafita sai da ya tsaya siyayya Sannan ya dau hanyar Daama Specialist Hospital babban asibity ne da ke cikin garin JEMETA cikin toki na hankali ya har ya isa cikin Asibiti.
Asibity ne me kyau kagana gani kasan an kwashe kufi domin gina shi,tun daga waje zalajie shi yana kamshi sabanin wani asibituci da zakaga ji na karni da wari.
Packing yayi a wajan ashe motoci Sannan yataka ya shiga cikin repection,duk inda ya wuce gaisuwa kawai ake masa domin a ko ina ya iya mu'amala da mutane gashi bashi da wulakanci Amma ya rike girmansa dan duk wanda ya kawo masa raini cikin aikinsa yana iya juyewa zuwa daya fuskartashi.shiysa duk wani ma'aikaci yake kame kansa tun suna rawar kai wajan cewa suna sonshi har ya koma kowa ya hakura domin zuciyar ta partner life ce.
Da wanna tunani har yashiga dakin mai number 0011 yana shiga wani murmushi ya subu ce masa domin ganin majinyar ce zaune bakin gado masu kula da ita suna tafama wajan bata magani Amma taki karba.
Sallamarsa da taji a kunnanta yasa tai saurin jiyowa ai kuwa tana a rangama dashi ta sakar masa laulausar murmushin ta,Da hannunta tayi masa alamar da yazo.
A hankali ya taka inda take,gaisuwa yayi mata kamar ta kurame ita amsa sa tayi game da nuna masa a gogo wai ya dade.
Kunnwansa ya rike alamun ban hakuri,domin wllh yana tananin yadda zai fada mata zai tafiya amma haka zai fada mata ya zaiyi.
Karbar magani da abincin take wanda tun dazu masu kula da ita ke fama.sosai taci ta koshi sainan ya janyo kujera ya zauna kafin daga bisani yace mata"mama wata tafiyace ta kamani wacce dole sai naje,shi nace dana barki a nan da na kaiki ki zauna da hajjiyata wanne kike so?"tambayarta yayi domin yina fuskarta ya gane bataji dadin hakan ba.
Amma ga mamakinsa sai tayi murmushi gami da nuna masa da hannu alamun ya kaita gun mahaifiyar tasa.
Sosai yaji dadin zabin da tayi,ai kafin kace me an hada komai nata an kai masa mota.a hankali suka jero duk da har cikin ransa yana jin nauyinta sosai kamar wacce surukar sa haka matarn take masa abubuwa irin na surukinta.
Komai Dr Maryam yace tasa masa a mota sosai yake ganin Mutunci domin shi kansa ya yadda da irin don da Maryam yateke masa Amma yasani ko da ya aure baya jin zai iya adalci a cikin zuciyarsa shiyasa duk abinda yake yana gani Amma sai ya nuna mata shi baima san me take ba,har hajjiya ta sama yana kuka akan yasa ya sota ko da hajjiya tayi masa magana sai yace mata,Indai baso take ranar lahira ya tashi da shanyewar barin jiki ba to tayi hakuri,dole hajjiya ta kyale domin duk abinda Sha'ayan ya kafe to fa yana da dalilinsa.
Wa wannan tuanni suka isa gidansu,sosai hajjiya taji tausayin wa majinya ciyar domin ba wata babbance sosai,kallo daya hajiiya tayi mata tasan asiri ke dauwainiya da ita domin me ciwan hauka ai yafita daban da na asiri.
Sosai sisters Sha'ayan sukai murna da zuwan bakowa,sosai abin ya bashi mamaki dan tunda sukazo tazauna a gefen Hajjiya bata sake yadda tayi masa magana sai hajiiya abin har mamaki yasu yabashi domin tace wa hajjiya zata sha ruwa shi kuwa komai sai dai tanuna masa.sosai yaji dadi yadda sukai mata inda yayi musu sallama sai KANO TABO TUNBIN GIWA KO DA MEKAZO AMFIKA.
Bari mu kowa cikin labarin mu...........
Kowa ya gyara zama yanzu labarin ya fara .........