Page 59
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela
59
____________________________________
BAYAN SHEKARU BIYAR.
____________________________________
Kowa ka gani a wajen yana ta harkokinsa na yau da kullum, kamar yadda suka shigo wajen sun san babu su babu fita sai ranar da ransu ya bar gangar jikinsu, hakan yasa kowa ke morar lokacin sa a sashen gidan kurkukun na wadanda akayiwa daurin rai da rai, amma banda ita. Kullum anan kasan bishiyar take zama hadi da sanya kanta tsakanin cinyoyin ta tayi ta kuka har sai lokacin sallah ko cin abinci yayi ko kuma idan za'a sanya su wani aikin, Babu mai kulata kasancewar kowa ta kanshi yake yi a gidan.
Kimanin shekaru biyar ke nan amma Maryama ta kasa sabawa da wannan rayuwar, kullum a sabuwar rayuwa take ganinsa sabo fil.
Yau ma kamar kullum tana zaune bakin bishiyar, kan ta cushe tsakanin cinyoyinta, sanye da riga da wando ruwan bula mai duhu, bayan rigar dauke da lamba dari tara da goma sha daya (911) tun tana kuka da hawaye yanzu sai dai idan ta tsungunnar da kai ta yi ta ajiyar zuciya kawai gaba daya ta sauya ta fita a kamanninta na Maryama ta zama wani abu daban.
___________________________________
Wasu jibga jibgan motoci ne kirar range rover, marcedes da makamantan su bakake wuluk masu bakin tinted, baka ganin komai na cikinsu sai walkiyar da suke yi kamar zasu kashe idanun mai kallonsu. sun kai su shida suke ta sharara gudu akan babban titin tsakiyar birnin Abuja kai kace su kadai ne bisa kwaltar sai dai duk da cunkoson da titin ke dashi na ababen hawa kasancewar yau ta kasance monday tushen aiki kuma lokaci ne na tafiya aikin misalin karfe takwas na safiya, hakan bai hana motocin dake bisa hanyar basu waje ba suna shigewa a guje.
*FEDERAL MINISTRY OF JUSTICE*
A katafaren shalkwatar ma'aikatar shari'a ta kasa dake Abuja motocin suka yada zango. Babban ma'aikata ne da girmanshi ya wuce kwatance. da hanzari kofofin motar suka bude, suka fara firfitowa sanye da bakaken suit da kuma bakaken glasses da ko kwayar idonsu baka gani, a kallon farko zaka fahimci bodyguards ne, su kusan goma sha biyu, babban cikinsu ne ya nufi motar dake tsakiya wacce ta fi sauran haduwa da sauri ya bude bayan motar yana matsawa gefe hadi da qamewa waje daya yana sarawa na cikin motar tun bai fito ba.
Kafafunshi dake sanye cikin takalmar cover bakake kirar italy ya fara fitarwa, farare ne sol a ciccike har wani naso suke yi kamar an watsa musu ruwa, kafin sannu a hankali gangar jikinsa ya bayyana.
Kakkyawan matashi ne ajin farko fari kal mai cike da haiba da kwarjini yana da tsaho sosai, akalla zai kai kimanin shekaru talatin da biyar. yana. Sanye da Suit blue-black colour wanda ya fitar da kwarjini da haibar Shi, sai agogon hublot dake daure tsintsiyar hannunsa cikin zafin nama mai cike da mazantaka irin na masu ji da lokacinsu yake takawa bodyguards din gaba daya suka mishi kawanya baka hango shi sosai sai tsawon wuyarshi kawai ta baya.
Elevator suka shiga ya sauke su a fifth floor, woww iya haduwa wannan waje ya hadu.
Wani Office mai girma da tsaruwa dan akalla zai kai gidan wani talakan, a gefen office din da kuma samanshi anyi rubutu da manyan baki mai kalar gold a jikin wasu billboard masu kyau da daukar hankali,
(Ofishin babban lauyan gwamnatin kasa)
Office din ya nufa bodyguards din kuma suna kamewa a nan bakin kofar fuskarsu mur babu rahama ko kadan, jira kawai suke kace kule suce casss. Da sauri sakatariyar dake zaune cikin office din ta ta mike.
Barka da zuwa yallabai"
Ta fada tana kamewa itama, ko gefen da take bai kalla ba ya wuce cikin ofishin mai kama da aljannar duniya dan haduwa, a gefe guda na office din ya yi nasarar lakume kujeru saiti biyu launin ja da ruwan madara tamkar palo, sai curtains masu ban sha"'awa dake makale jikin ko wanne window suma kalan kujerun, kana turkey center carpet mai girman gaske shimfide a kasan tiles din da center table mai kyawun gaske dake zaune bisa sai babbar plasma tv 100 inches da sauran abun bukata na palo, daura dashi kuma akwai wani dogon teburi wanda akayiwa shape na kwai da kujeru a jejjere a bayanshi wanda ba za su gaza sittin ba ko wanne kujera yana dauke da abun magana da wajen ajiye takardu ko papers a gabanshi, hakan na nuna an tanadi wajen ne dan gabatar da meeting da ya danganci ofishin kawai.
A can gefe guda kuma wajene dake dauke da abubuwan da ya danganci office irinsu office chairs desk, da sauransu. Sai bangon wajan mai dauke da shelf cike taf da tarin awards masu bada mamaki.
Direct kan office chair na shi ya zauna, abun da ya bani mamaki gami da daurewar kai ke nan dan a tunani na wajen mahaifinshi ya zo tunda mun saba ganin irin wadannan manyan mukaman na gwamnati tsofaffine suka yi kaka gida a kai a kasata matashi bai isa ya durfafi wajen ba duk da matasan sune kaso mafi yawa a cikin kasar.
Amma zaman shi bisa kujerar ofishin ya tabbatar da cewa shine mamallakin wannan kujera mai tarin albarka da cigaban ko wanne kasa matukar aka samu shugabancin shari'a adalai, tabbas kasa zata cigaba.
Da sassarfa sakatariyarsa ta shigo dauke da files files ta zube su gabanshi ta na kaiwa duqe kasa, "Ranka ya dade an gama fixing time na meeting naku da sauran excos, karfe tara za'a fara, wadannan kuma sako ne daga hukumar EFCC, wannan kuma ta fada tana daga wani file din, daga hukumar NDLEA ya zo sai sakonnin da aka turo ta email daga police headquarter dake Kano idan ka huta zan turo maka su, sai kuma meeting da zaku shiga around 11 da mai girma attorney general shugaban alkalai na kasa (alkalin alkalai). Ta fada tana duba jadawalin a cikin tab dake hannunta.
Tunda ta fara magana ya hade yatsun hannunshi dake daure bisa desk na gabanshi yana jinta amma ko tari bai ba har ta gama ta fice bai ce mata kala ba, in da sabo ta saba da halin shi na shariya, amma abun da bai sani ba, wannan miskilancin kara mishi kyau da kwarjini na musamman yake yi.
Ita dai tunda ta fara aiki a karkashinsa watanni kadan da suka shige yake burgeta, sai dai ta san wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.
Bubbuda files din ya fara yana dubawa domin fara aiki a kansu, wanda ya ja shi lokaci har quarter to ten.hakan ya sa ya sassautawa aikin dan shirin fara taro mai muhimmanci da za su yi, wani kararrawa ya taba dake zaune bisa teburin gabanshi. cikin kasa da minti goma mutane suka fara shigowa office din, kan kace me, wannan teburin ya cika makil da mutum sittin ciff ciki har da mamallakin ofishin.
Wasu ma'aikata ne suka shigo dauke da abubuwan motsa baki kowa aka ajiye mishi bottle water da soft drink sai wani karamin bowl mai dauke da sweets masu dadi a ciki, kowa an ajiye mishi a gabanshi.
Bayan bude taron da addu'a bangaren musulmai, bangaren kirista ma suka gabatar da addu'ar su sannan suka fara gabatar da abun da ya tarasu.
Mai magana da yawun antony janar ne Brr, Ahmad Tijjani Isa, ya mike yana gyara zaman necktie dinsa ya ce, "Muna yiwa kowa barka da halartar wannan taro mai muhimmanci, kamar yadda muka sani mai girma babban lauyan gwamnati ya saba gudanar da irin wadannan taruka masu dumbin tarihi wanda a ciki ake kaddamar da aiyukka dake amfanar al'umma ta ko wanne bangare na kasar nan.
Yauma mun taru ne don muyi bita akan koke koken da muka samu na cikowar da gidan yarinmu suke fama dasu wanda hakan ke haifar da cututtuka masu illah ga fursunoninmu duk matsayar da muka zartar mai girma babban lauyan gwamnati zai je ga attorney general domain ayiwa matsayar duba na karshe.
Tunda mai magana da yawunsa ya fara magana ya harde hannunsa yana bin fuskokin mutanen da kallo, dukkansu tsoffine yawanci sun haura shekaru hamsin zuwa sittin, lallai ya kamata a irin wannan lokaci ace suna hutawa ne a gida abar masu jini a jika suyiwa kasa hidima murmushi mai fadi yayi lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.
Gyara zama yayi yana shafa sumar kanshi da ya sha gyara as usuall ya gyara abun maganar ya ce cikin daidaitacciyar murya.
"Gidajen yari suna bukatan gyara, sun yi cikowar da har hakan ke haddasa cutuka irin na amai da gudawa a tsakanin fursunonin, dan haka mun yanke shawara bisa adalci irin na wannan kujera zamu sake karkade files wasu daga cikin masu laifi sassauci inda zamu nemi amincewar gwamnati ya yafe musu suma su samu yancin walwala kasancewar da yawa cikinsu sahun barawo suka taka, wasu kuwa sharri akayi musu.
Already mun turawa shugaban kasa takardar kokenmu.
Daga gidajen gyaran hali ma samu list daga shugabanninsu na wadanda ya kamata a sassautawa bisa lura da canzawar dabi'unsu ko kuma halayyarsu, nan da awa daya zan yi ganawar sirri da ministan Shari'a a kan hakan."
Tafi gaba daya suka sanya kowa ya nuna farin ciki da aminta da maganar da yayi a zahiri, amma a badini Allah ne kadai ya san karatun kurma. Daga haka taron ya tashi bayan kowa yayi jawabinsa na yadda yake ganin ya kamata aiyukan su gudana..
____________________________________
Wanene Artoney General Of Justice?
Shine ministan shari'a na kasa,kuma shine babban lauyan gwamnati, bayan shugaban kasa shi kadai ke da ikon yiwa fursuna afuwa, idan ya ce, an yiwa wane afuwa to babu mai canzawa duk wani manya manyan cases musamman irin na kisa, gaba daya a karkashinshi suke.....A karon farko ga dai matashi a kan irin wannan babban mukami ko waye shi???
_______________________________________
Kamar yadda suka tsara yau suka fara rangadin gidajen gyaran hali domin duba wadan da za'ai wa afuwa, sai dai akasin da aka samu antony janar ba zai samu damar zuwa ba saboda wasu dalilai dan haka mukarrabansa da mai magana da yawunsa suka tafi zagayen.
Cikin ikon ubangiji Maryama da itama ke fama da amai da zawo wanda ya zamar musu kamar annoba, sunanta ya fito cikin wadanda akai wa afuwa, tsabar farin ciki a take kafafunta da suka zama tamkar musillan rake suka fara rawa, yayinda da dama daga cikin mutanen wajen suka fara ihun murna da jin dadi wasu na rawa wasu na kuka, amma Maryama a hankali ta ji ta kai kasa sai kuma ta juya gabas ta sanya goshinta kasa tayi sujjada wasu hawaye masu zafi suna kwaranyo mata godiya sosai da kirari tayiwa ubangijinta, lokacin da ta dago dayawan mutanen wajen sun fara wucewa bangarensu dan tattare abun da yake mallakinsu, amma Maryama cikin nutsuwa ta taka gaban wadannan mutane da take ganinsu a matsayin silar ta ta cigaba da neman iyayenta.
Jami'an dake gadinsu ne suka yi kokarin tsaida ita daga isowa gabansu, amma brr, Ahmad Tijjani ya dakatar da su ta hanyar yi musu nuni da cewa su barta.
Duke ta kai gabansu zata fara magana kawai sai ta fashe da kuka, cikin kuka tace.
"Na gode na gode na gode, ina rokon ubangijin Annabi Musa da Haruna ya yaye muku duk wani damuwar dake tattare da rayuwarku kamar yadda kukayi silar fitar tawa damuwar.
Dakatar da ita ya yi ta hanyar fadin, "Allah zaki yiwa godiya yan mata. sannan wannan"
Ya fada yana fitar da wani kyakkyawan kati daga aljihunsa ya mika mata, wata rana zaki iya kiran wayarsa ki gode masa dan shine sanadi, hannu yana rawa Maryama ta karbi katin yayinda ta ji karfin gudun zuciyarta ya karu.
A ranar aka sallamesu kowa kuma an bashi wasu kudi da zai kaishi har garinsu ko gidansu, gabas da yamma kudu da arewa Maryama ta duba babu wanda ta sani babu inda ta sani kuma babu wanda ya santa,a hankali ta sa hannu ta tsaida wani taxi da addu'ar Allah yasa shi kam ya tsaya dan wannan na hudu kenan amma da zarar sun ga yanayin jikinta sai su wuce abinsu.
"Ina zuwa mama?" cewar mai taxi din yana kallonta sama da kasa. Haka kawai ta samu kanta da mika mishi katin dake hannunta wasu hawaye suna zubo mata, katin ya kalla sannan ya kalleta ya kuma kallo ya kalleta kusan sau biyar sannan ya kada kai ya ce "muje."
A bakin wani MANSION ya tsaya cikin gatse ya ce, "ga inda kika ce a kawoki sannan a daure a dinga wanka hajiya tsamin yayi yawa".
Ya fada yana mika mata katin, amsa tayi ba tare da ta ce mishi komai ba hannunta yana rawa ta mika mishi duka kudin da aka bata a prison ta juya ta nufi gidan kirjinta na tsananta bugu.
Kallon up and down sojan dake bakin gate din ya mata ya ce, "Daga ina, almajirai basa zuwa nan, ko an fada maka ana raba sadaka ne?"
Hawayenta ta cigaba da sharewa kamar an like bakinta da superglue ta mika mishi katin hannunta, zaro idanu yayi yace, "Waya baka wannan" cikin gidan ta nuna da yatsarta, jijjiga kai kawai ya yi yace, "Ka tabbata"gyada kai Maryama tayi yace biyoni.
Ko wanne taku daya ta yi tana jin yadda kafarta ke kara yin nauyi wajen dagowa ta biyu tsabar yadda kirjinta ke bugu kuma saida ta sanya hannunta ta danne wajen don tsoron kar ya fado kasa. Duk haduwar wannan gida sai ta samu kanta da kin gidan dan ta tabbata irin Sameera ne ake samu suna rayuwa a ciki.
Wani daddan kamshi ne ya bakunci hancinta sa wani irin sanyi ya buso ta lokacin da wannan soja ya zuge kofar glass na shiga ainahin gidan yana matsa mata, duk da gudun da kirjinta ke yi, hakan bai hanata shahadar shiga ciki ba dan ji ta ke yi kamar ana ingizata ga shiga cikin.....
Wani irin cafka taji an mata ta gaba saura kadan ta zube a kasa, cikin zakin murya irin na yara masu dan banzan surutu a kace, "Anty mai chaculate ki boye ni Mommy zata min bulala. ki boye ni plssss zata zane ni na mata barnar cookies a palon Daddy.
Saura kadan Maryama ta zube a kasa dan ko kadan jikinta babu karfi, faduwan da ta kusa yi yasata ganin fuskar yarinyar.
Fara ce sol har wani yellow take yi tsabar haske, kyakkyawa ce na bugawa a jarida shafin farko. A kalla zata yi shekaru hudu a duniya, tana sanye da wando skin tied blue da riga ja na shan iska, kanta babu kitso amma an raba gashin biyu an daure mata da jan band, sai sandal na yara jajaye a kafarta idan ka ganta tamkar yar tsana haka take dan kyau.
Wani irin bugawa zuciyar Maryama ya kuma yi a karo na barkatai jin wani Murya yana fadin, "Duk inda kika shige fa gwara ki fito Pretty, idan na kama ki double punishment zaki samu,"
A rikice ta dago kanta dan ganin ko dai kunnenta ke mata gizo, amma sai ta karayin wani mugun ganin sakamakon wani kofa da aka bude wata mata ta fito daga dakin tana fadin wai me ya samu MEERAH ta ...Maganar ta ce ta makale a makoshi, da gudu yarinyar ta saki Maryama ta wuce bayan matar.
"Granny ki boye ni Mommy zata min bulala". Gaba dayansu uku mutuwar tsaye suka yi yayin da jikin Maryama ya kara daukar rawa kar kar kar kar har tana jijjiguwa a wajen, "I..Inn..Innar...muu" ta fizge na karshen da karfi tana kallon matar da hanzari kuma ta juya ta ce, U.Ma...M..Um. Umaimahh.
Babu wanda ya samu zarafin cewa wani abu, suka jiyo muryarshi yana saukowa daga sama
"Assemblyn me ake ne a palon haka ba'a neme ni b.." shima ta shi maganar ta makale yayin da zuciyarsu ya harba a tare har yana rumtse ido ya bude da sauri...
Wani irin hajijiya ne ya fara rinjayar Maryama da zuwa lokacin gangar jikinta yafi karfin kafafunta kana ta gama fita a hayyacinta cikin janyo magana da karfi dan tuni iska ya daina kaiwa ga huhunta tace, Ha.m ma...Jayyyyy" daga haka ta fadi kasa wanwar idanunta suka kafe, kara Umaimah ta kwala tana sakin sauran cookies din da Meerah ta bata a kasa ta nufi Maryama da gudu, wani irin damka innarmu ta mata cikin sanyin murya ta ce, "Umaimah ina zaki?"..