RIKICIN DUNIYA

CHAPTER 1

by @meenatyandoma

*TEAM WOW THREE ELEGANT WRITER'S*

*RIKICIN DUNIYA...*

©️ Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

CHAPTER 1

DUTSIN-MA
Isa Kaita College

Dandazon ɗalibai ne tsaye a bakin hanya suna jiran abin hawa. Wasu da dama mashin suke hayewa ganin har yammaci na kokarin doso su.
"Mtsww! Wannan lecture ya ɓata mana lokaci, nan da kwana biyu fa za a fara exam Amma ki duba ki gani yadda ya rike mu da wata text dinsa ta banza, mu da yi ko kar muyi uwarsa daya ubansa daya dole ne mu haye" Nadiya ta karasa maganar tamkar mai shirin fashewa da kuka.
Dariya Wasila ta ɓaɓɓake da ita, sai da ta yi mai isarta kafin ta tsagaita.
"Dilla! Malama me ye haka? Kin dai sani na tsani dariya me ya sa kike yin abin da kika san na tsana?"

"Maida wukar Allah ya huci ziciyarki. Ni fa abin da ke bani dariya game da ke shine yadda kike hakikancewa irin kokarinmu ke bamu nasarar da muke yi, ko dai kin manta ne" Wasila ta karasa maganar tare da ɗaga mata gira. 
A tare suka tuntsure da dariya.
"Kin tuna mini, ya kamata muyi sauri mu samu abin hawa mu fara zuwa wurin Malam bawa kinsan yadda muke NCE 3 Yayi mana aiki mai kyau kada wahalarmu ta tafi a banza"
Cewar Nadiya

"Aa fa ki daina cewa wahalarmu, kada dai kudinmu su tafi a banza" rufe bakinta ke da wuya Napep ta tsaya a gabansu.
"Maƙera zaka kai mu amma, zaka fara biyawa da mu ta wani wuri za mu amshi sako, daga nan sai ka sauke mu gida tunda duk unguwa daya ce"
Ciniki suka yi ba tare da neman ragi suka fada motar.
Kasancewar gidan Malam Bawa duk a cikin makera ne, ba su bata lokaci ba suka fada gida.
Dattijo ne wanda zai kai shekaru 70 a duniya. Zaune ya ke saman fatar kura Dakin zagaye da bakin kyalle.
Baki Nadiya ta bude da nufin yi masa magana, hannun daya ɗaya mata ya sakata yin shuru.
"Indai maganar jarabawar ku ce ku dauka kunci. Magana ta biyu kuma ina sawun takunsa da da na ce ki kawo?"
Shuru Nadiya ta yi gabanta na tsananta faɗuwa. 
"Zuwa gobe in Shaa Allah za a kawo, matsala aka samu ya yi tafiya yau ya dawo" ku je ku dawo tare da kudin aikin.
Tsakar gidan suka fito. Ya'ya da iyaye ne kwantsam yadda kasan gidan marayu.
Da gudu-gudu Nadiya ta fice tana mayar da numfashi da kyar.
"Ɗan wake kafi harawa. Naga dai gidan Malam bawa wata kilama ya fi gidan iyayemmu, tunda shi o banza za a yi ci uku a rana. Mu fa da kyar ake yin biyu"
"Ki gyara kalaman ki. Gidanku dai za ki ce, amma ni kin sani tun bayan shigowar Kasim cikin rayuwata komai ya sauya ko ba ki ga alama ba?"
Duk da Wasila ta ji zafin maganganun da Nadiya ta yaɓa mata haka ta hadiye su, tare da kirkiro murmushin da ita daya ta san ma'anarsa.
"Kawata! Ai ke kam sai godiya. Saboda Allah ya kashe ya baki, ba ke ba ni kaina da nake matsayin kanwarki ai ina dangwalar arziki."
Murmushin kasaita Nadiya ta yi tare da kara daga kafada.
"Fadi da ihu ki kara da wayyo Allah. Amaryar attajiri Kasim nan da lokaci kankani. Na tsani talaka na tsani talauci duk da a cikinsa aka haifa ni, alkawari na yi ko ta wane hali sai na auri attajiri kuma ganin idonki dai kin gani" ta karasa maganar ta shige napep.
Tayarwa ya yi, Nadiya aka fara saukewa kasancewar tafi kusa da gidan Malam Bawa. Ita ta fito da kudi ta biya kasancewar ba lungun su daya da Wasila ba gaba aka yi da ita.
Yamutsa fuska tayi kwatankwacin wadda ta ga kashi, sakamakon hango saukakken kyauren gidansu data jima da biyan kudi amma shuru Inna ta taushe kudin ta hana a gyara.
Ɓacin rai bayyane a fuskarta ta karasa cikin gidan da iya kallonta tsakar gidan babu shafen siminti
Babu sallama bare gaisuwar ta fara mita.
"Yanzu Inna fisabilillahi abin da kika yi kin kyauta?"
Washe baki Inna dake durkushe gaban murhu tana hura wuta ta yi saurin miƙewa.
"SHALELE! Banga dawowarki ba, sauri nake In gama dafa abin cin nan kada ki dawo ga karatu ga yunwa. Laifin me kuma nayi?" 
Turo baki ta yi cikin Shagwaba ta ci gaba da magana.
"Ina kudin da na bayar na ce a kira Idi mai walda?"
"Kai! Tsohon zance ai na aika a kira shi aiki ne yayi masa yawa, ya ce da ya rage zai zo har gida da kayan aiki ya gyara mana"

"Amma Inna kamar baki kula Anti bata yi sallama ba ko?"
Jamila kanwar Sajida ta fada.
Wata uwar ashar Sajida ta danna.
"Inna na rantse da Allah ki shiga tsakani na da wannan munafukar yarinyar, In ba haka ba sai na yi abin da zata jima bata manta da ni ba"
“yi shuru Nadiya! Yanzu zan yi ma tufkar hanci. Ke Jamila! Me na fada miki game da irin wannan abin da kuke yi ma yayarki? Idan kika kara irin haka sai na saka ta haɗa miki jini da majinah a cikin gidan nan. Maza ki bata hakuri" 
"Yi hakuri Allah ya huci zuciyarki, ban fada da wata manufa ba"
Tsoki Nadiya ta yi tare da shigewa dakinsu.
"Ke kuma na dawo gareki. Yanzu ke Nadiya ba ita ce cinmu da shanmu a cikin gidan nan ba? To bude kunnuwanki da kyau, hatta jarin awarar da na samu nake yi miki kina mana suya a kofar gida ita ta bayar. Uban naki ma da nake boyewa mawa ina ce masa kaf hidimar da muke yi da ribar a ce to ita ta bayar ko kuma in ce saurayinta."
Duk da Jamila ba zata wuce shekara 23 ba amma. Murmushi ta yi irin na manya.
"Amma Inna me ye amfanin boyewa Baba da muke yi?"

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! ke dai wannan yarinya anyi yar banza, wadda bata gaji arziki ba. Ni zaki wulakanta ni za ki kwancewa za ni a kasuwa? So kike yadda kike ba zuciya yan samarin ma ba ki kulasu bare ki samo mana wani abu ita ma burinki ta zama haka? Ba damuwa ni kike wulakantawa wadda ta tsugunne ta haifeki" 
Fashewa Inna ta yi da kuka domin ta san ta haka ne kadai zata tsira daga abin da Jamila ke kokarin aikatawa. 
Rikicewa ta yi ta aje waken suyar da take gyarawa da sauri tayi kan Inna.
"Dan girman Allah Inna kiyi hakuri. Wallahi ban fada da wata manufa ba, malamin mu na islamiyya ya ce hawayen mahaifa masifa ne a wurin yayansu"

"To idan kina so in huce ba ruwanki da Sanar da Mahaifinku abin da kika sani"
"Na amince ba zan fada ba, kiyi hakuri ki yafe mini”

"Shi kenan ba damuwa dauki waken markaden ki kai na yafe miki."
Da Sauri Jamila ta bar gidan har tana tuntube...

GIDANSU WASILA
Mai Napep na sauke ta a fusace ta fada gidan ko sallama babu. Kusa da Umma da ke gyaran garin rogon da zata jiƙa masu su sha ta zauna tana huci.
Murmushi Umma ta yi. "Nadiya ce ko?"
"Hmm! Umma wallahi yau Sajida ta wulakanta ni wulakanicin da bazan taba mantawa da shi ba. A gaban mai Napep ta ci mutumci na, ji nake kamar na zama ajalin Nadiya wallahi na tsane ta"
"Ta yaro kyau take bata karko. Ki daina fadar zaki zama ajalinta kada ki fada daidai da bakin yan Amin. Saurayin da take miki gadara tana wulakanta ki saboda shi da shi za muyi amfani mu nuna mata iyakarta.”
Da sauri ta kalli Umma.
"Da gaske kike?"
"Kwarai kuwa na taba yi miki wasa ne, ina abinda na sakaki nemowa?"
Ta karasa maganar tana mika mata hannu.
Jikkar ta ta bude ta fito da ƙasar data kulle cikin farar leda.
"Kin kawo abin da zai tarwatsa rayuwar Nadiya, yanzu ki shiga kiyi wanka ki fito kisha garin nan mu karasa wurin Boka bakurmi.
Bata bata lokaci ba duk da duhun magriba daya fara haka suka nufi wurin bokan rayukansu cike da farin ciki...

Meenat A. 'Yandoma
***



***