01
by @oumfatima33
🌹🌹🌹🌹🌹
MEERAH
🌹🌹🌹🌹🌹
NA
KANSA'U BELLO
(OUM FATIMA)
[1/9/2026/8:00pm]
PGE 01
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHEEM
SOYAYYA!
Kalmar soyayya taƙaitacciyar kalma ce guda ɗaya mai ɗauke da haruffa bakwai, sai dai a zahiri girmanta ya wuce duk yanda mai tunani ya kai ga tunaninsa a game da ita.
Idan zuciyoyi biyu suka amince da junansu basa duba kyau, matsayi, nasaba, ko mulki. Idan zuciya ta kamu da soyayya ta kan makance ta yanda bata duba ko wane irin bambanci dake tsakaninta da abinda take so.
Soyayya ta kan shiga cikin zuciya ba tare da neman izinin mamallakin zuciyar ba, hakan ne yasa mai yinta kan kasa cire ta da daga zuciya komin tsanani, barazana, matsi da takurar da zai fuskanta.
Kar na kai mu da nisa kai tsaye mu shiga cikin labarin, domin kuwa tsayawa fayyace mecece soyayya da abinda take nufi zai iya ɗaukar dogon lokaci Ba tare da mun ƙar-ƙare ba.
Don haka Gara mu Bibiyi MEERAH don jin irin gwagwarmayar da tayi a soyayya, da irin ƙalubalen data fuskanta. Faɗuwa da nasarar data samu.....
>>>>>>>>>>
"Matuƙar nine Mahaifinki kuma kin yarda da hakan to ki manta ta da wannan yaron a rayuwarki. Domin kuwa ko bayan raina ban amince ya amsa sunan Miji a gare ki ba. Babu ke babu shi har abada, ke ɗin ba mahaɗinsa bace. Bai dace dake ba, bai kai matsayin da zai shigo cikin zuri'ar Mamman Gwangwazo a matsayin suruki ba. Ya fiye maki tun wuri ki cire shi a cikin zuciyarki ki sama wa kanki wanda ya dace da matsayinki!."
Razanannun kalaman Dady a gare ni suka shiga yi min amsa kuwwa a cikin kunnawana suna razana zuciyata da tsananin tsoron abinda zai iya faruwa da SOYAYYATA.
Kalaman da tunda ya furta su a gareni suka rabani da duk wata natsuwa da nake aciki, kalaman da suka min shamaki da duk wani farin ciki da wal-wala da aka sanni da ita a baya.
Kalaman da suka sauya ni daga asalin MEERAH dana kasance mai fara'a surutu da walwala ako da yaushe. Kalaman da suka zame min tamkar makamin daya datse zaren duk wani fata da burin da nake dashi a soyayyata da mutumin dana bashi zuciyata, nake burin na rayu dashi har numfashina na ƙarshe.
Kalaman da suka saka na fara zargin anya wannan shine Mahaifina dake tsananin sona, wanda shine mutum na farko da yake fara cika min duk wani buri da nake dashi. Mahaifina da duk abinda na buƙata matuƙar a kwaishi a wannan duniyar zai mallaka min shi domin farin cikina.
Sai gashi a wannan karon shi da kansa ya saka almakashi ya datse zaren farin cikin nawa, ya sanya min tsoro da fargabar da nake jin zan iya zaucewa ako wane irin lokaci....
Kiran daya shigo cikin wayata da daddaɗan sautin waƙar MEERAH dana saka a matsayin ring tone ɗina ya dawo dani cikin duniyar da a zahiri ne nake a cikinta, amma a baɗini ruhina ya jima da barin gan-gar jikina, yayi nisa a cikin duniyar tunanin da a yanzu a zama abokin rayuwata ako da yaushe.
Duk da halin da nake ciki bai hana kyakykyawan murmushi ya bayyana a saman fuskata ba, hakan kuma ya faru ne sakamakon arba da sunan dake kaÉ—awa a saman screen É—in wayata.
NAWAZ shine sunan dake kaÉ—awa da alamar zuciya a gaban sunan, wanda ke nuni da cewa shi É—in zuciyata ne baki É—aya. Cike da zumuÉ—i na É—aga kiran na sanya wayar a kunnena.
"Masoyi!." Na furta cikin muryar da kuka yaci ƙarfinta, yayinda hawaye masu zafi ke gudu a saman fuskata.
Ajiyar zuciya wanda na kira da masoyi ya sauke sannan shima yace.
"Masoyiya!" Da karyayyiyar muryar dake bayyana rauninsa a kaina, kuka mai ƙarfi na fashe masa dashi ina jin zuciyata tana raya min ba zan taɓa iya rayuwa da wanin Nawaz ba a wannan duniyar.
Cikin kwantar da murya ya shiga rarrashina da kwantar min da hankali.
"Ki daina kuka kin ji masoyiya, ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abinda zai raba mu. Muyi haƙuri muci gaba da addu'a, in sha Allah zamu mallaki juna, ina ji a jikina cewar ba zan koma ga Mahaliccina ba har sai na amsa sunan mijin AMEERAH ABBAS MAMMAN GWANGWAZO." Nawaz ya ƙare maganar cike da ƙwarin gwuiwa da son kwantar min da hankali.
Ajiyar zuciya na sauke a hankali ina share hawaye na nace.
"Baka san waye Dadyna ba masoyi, mutum ne mai kafiya wanda idan ya yanke hukunci babu mai iya sauya masa ra'ayi. Kuma sannan duk wani wanda nake da sauran ƙwarin gwuiwar zai iya taimaka min duk sun goyi bayan Dady ne. Ina matuƙar jin tsoro masoyi!" Na ƙare maganar ina tuna yanda muka yi da Yaya Sultan lokacin dana kira shi na roƙe shi a kan ya taimaka min ya yiwa Dady magana ya amince da zaɓi na.
"In sha Allah komai zai wuce, soyayyarmu ba zata taɓa tafiya a banza ba. Kar kiji tsoro kinji zuciyar NAWAZ." Ya furta cikin kwantar da murya sosai. Ci gaba yayi da rarrashina har sai da na samu natsuwa.
Bai barni haka ba sai da ya raira min daɗaɗan baitukan da a yanzu ya tsara su domin faranta min, ai kuwa yaci nasara domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci na manta da damuwata na fara sakin murmushin dake taso wa daga cikin zuciyata, shauƙin ƙaunarsa na ƙara mamaye ni. Irin mamayar da bana jin zan iya rabuwa dashi koda za'a yanka naman jikina ne.......
Barkanmu da wannan lokacin, ga sabuwar tafiyar MEERAH ta fara daga yau. Ina fata zaku amshe sa da hannu biyu kamar yanda kuka saba amsar labaran da nake kawo maku. Ku bani ƙwarin gwuiwa ta hanyar yin comments da shere, na gode.
Oum Fatima
***