MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 12

by @mrsisham12

MATUƘAR INA RAYE
(As Long As i’m alive)

Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp

Page 12


“Sannunki.”

Nini ta faɗa bayan sun iso inda Waheeda ke zaune, fuskarta ɗauke da murmushin da ya saba ƙawata ta.

Waheeda, wacce ba ta yi tsammanin Nini za ta zo ba, ta ce,

“Ke ma sannunki.”

Tun da ta ga har rana ta fara fitowa ba a zo saye daga gidan ba, ta riga ta cire rai da samun ciniki daga wajensu. Ai ba ta san waɗannan Ajebo bane, ba sa tashi da wuri balle su karya da sassafe.

Mai gadin da ya raka Nini ne ya miƙa mata wani haɗaɗɗen food flask mai matuƙar kyau, kala wine, tare da wasu takardun kuɗi na dubu-dubu a saman.

Sannan ya ce,

“Ki sa ƙosan naira dubu ɗaya a nan. Sauran kuɗin kuma dubu biyar ne. Kullum za a riƙa aiko da ƙosan dubu har sai kuɗin sun ƙare.”

Wayyo daɗi!

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Waheeda. Ji ta yi kamar ta fashe da ihu saboda murna, amma ta daure ta basar… kar su ɗauke ta bakauyiya.

“To.”

Ta karɓa tana saka kuɗin cikin jakarta, sannan ta fara zuba ƙosan cikin kular a tsanake.

Nini kuwa ta zuba mata manyan idanunta tana kallonta, tana yaba kyanta da hasken fatarta mai walƙiya.

Da ta gaji da kallonta sai ta ce,

“Jiya na ce ki jira ni, shi ne kika gudu.”

Waheeda ta ɗago ta dube ta da ƙaramar murmushi a fuskarta, saboda farin cikin cinikin da suka mata.

Ta ce,

“Na yi ta jira, na ji shiru, shi ya sa na tafi kar a fara nema na.”

Nini ta ɗan lumshe ido, ta tsugunna gaban robar tallar.

“Mamie ce ta aiki ni upstairs. Ki yi haƙuri kin ji?”

Waheeda ta girgiza kai alamar ba komai, domin har ta manta da abin da ya faru jiya.

Nini ta sake cewa,

“Yaya Bk ya ce miki wani abu ne, shi ya sa kika gudu?”

Waheeda ta rufe kular sannan ta ɗago tana kallon Nini da ta kura mata ido.

Da ba yanzu ba ma, da ta manta da abin da ya faru jiya. Amma jin ta ambaci sunan da ba ta sani ba ya sa ta tuna fuskar saurayin da ta haɗu da shi.

Ta yatsina fuska.

“Wannan ɗin shi ne yayanku?”

Nini ta gyada kai.

Waheeda ta sake tambaya,

“Kuma yana jin Hausa?”

Nini ta sake gyada kai.

Waheeda ta saki baki.

“Tabdijam! Ai bai yi kama da Bahaushe ba. Ya fi kama da Larabawa ko Turawa irin waɗanda muke gani a wayar Yaya Salma.”

Nini ta yi dariya.

“Kaiii… yana jin Hausa sosai fa. To shi ne ma ya ce in ba ki wannan kuɗin.”

Ta faɗa tana miƙa mata sabuwar takardar naira dubu ɗaya.

Waheeda ta kalli kuɗin, sannan ta kalli Nini cike da alamar tambaya.

“Kuɗin me kuma?”

Ta tambaya tana miƙa wa mai gadi kular.

Nini ta amsa,

“Jiya da kika zo gudu ne kika yar da robar alawar madararki. Shi kuma ya shanye, sai ya ba ni kuɗin nan in kawo miki ki sayi wata.”

Nan take wani irin baƙin ciki ya tokare Waheeda.

Ta ji kamar ta zama tsuntsuwa ta tashi ta shiga gidan ta shake Bk.

Tuwon madarar da ta ɗauka su Rabi ne suka tsinta suka shanye, jiya kafin su kwanta ba irin rashin mutuncin da ba ta zuba musu ba. Har sai da Ummah ta tsawata mata sannan ta yi shiru.

Ashe shi ne ya tsinta! Kuma tsabar rashin kunya ya shanye mata.

A fusace ta ce,

“Kan uban nan! Shi ne zai sha min abuna ba tare da na ba shi ba? To wallahi ba zan karɓi kwandalarsa ba! Tuwon madara ya sha ai, ba kuɗi ba! Ko ya ba ni alawata, ko in masa wuta bal-bal!”

Mai gadi ya dubi Nini.

“Zo mu tafi.”

Nini kuwa, da ta zuba idanu tana kallon yadda Waheeda ke zazzaga masifa, ta ce cikin sanyin murya,

“To shikenan… zan gaya masa.”

Daga nan suka juya suka tafi.

Ita ma Waheeda ta shiga gida da robarta, domin dama ƙosan duka ta juye musu cinikin dubu ya cika cif.

Tun daga bakin ƙofa ta fara ƙwala kiran sunan Ummah da iya ƙarfinta.

Mama Jamila ce ta daka mata tsawa.

“Kai, Subhanallah! Anya ke ba mahaukaciya ba ce kuwa, sai ka ce ba musulma za ki shigo gida  da ihu kamar wata kafira?”

Turo baki ta yi ta ce, “Ni dai ba kafira ba ce.”

Ta yi shigewarta. Yaya Ado kuwa yana tsaye a bakin ƙofa yana kallonsu. Duk abin da suka faɗa ya ji sarai, amma ya zaɓi ya nuna tamkar hankalinsa ba ya kansu.

“Yaya Ado, albishirinka?”

Ya jawo hannunta zuwa kusa da shi yana amsawa,

“Goro fari ƙal!”

Ta washe haƙoranta farare tas, tana murmushi gwanin sha’awa.

Ta ce,

“Na siyar da kosaina duka, ka ga kuɗin?”

Ta hangame cikin jakarta tana nuna masa kuɗin.

Cikin son biye mata, ya hau tafa mata yana faɗin,

“Congrats! Lallai ke ‘yar sa’a ce. Rana ta farko har kin yi sold out. Inyaa!”

Ta fashe da dariya ta faɗa ɗakin Ummah, amma ta tarar babu kowa. Ta leƙo kanta tana cewa,

“Ya Ado, ina Ummanmu?”

Ya amsa,

“Ta zaga.”

Ta hau gado, ta fito da duk kuɗin cinikin da ta yi ta zuba a kai, tana ware kuɗin da mai gadi ya ba ta a gefe. Daga nan ta fara ƙirga kuɗin cinikin nata.

Sai ta ji Yaya Ado daga bakin ƙofa yana cewa da Ummah,

“Ummah, ’yarki fa ta yi sold out. Waheeda akwai goshin kasuwa.”

Wani irin daɗi ya rufe ta. Kamar ta daka tsalle saboda farin ciki. A duniyar nan, Waheeda tana matuƙar son a yaba mata. Duk lokacin da aka yaba mata sai ta ji kanta na wani irin huruwa kamar zai fashe dan daɗi.

Ummah ta shigo tana cewa,

“Madallah! Shalele, har kin sayar?”

Waheeda ba ta jira Ummah ta iso ba, ta nufe ta da duk kuɗaɗen.

“Eh Ummah, kin ga cinikin?”

Yanayin fuskar Ummah ya sauya lokaci guda da ta karɓi kuɗin. Idonta ya sauka kan wasu sabbin takardun kuɗi na dubu-dubu da suka cure wuri guda.

Hankalinta ya fara tashi. Domin duk kosan da ta saka wa Waheeda, ko dubu biyu bai kai ba. Amma yanzu idanunta na ganin dubu-dubu cure a wuri guda.

Cikin murya mai ɗan rawa ta ce,

“Mamana… wannan kuɗin fa? Wa ya ba ki su?”

Waheeda ta zaro ido tana cewa,

“Ummah, kin san kuɗin su wa ne?”

Ummah ta girgiza kai alamar a’a, cikin matsananciyar ƙaguwa da son jin inda kuɗin suka fito.

Waheeda ta ci gaba da cewa,

“Daga gidan nan mai kyau da aka ƙaura kwanan nan ne. Ina zaune, sai ’yar gidan da mai gadinsu suka zo suka sayi kosai na dubu ɗaya. Daga nan sai mai gadin ya ba ni dubu biyar, ya ce kullum za a riƙa aika musu da kosai na dubu ɗaya har kuɗin su ƙare.”

Wani irin kwanciyar hankali ya mamaye zuciyarta. Fuskarta ta nuna alamun samun natsuwa, sannan wani sassanyan murmushi ya kwanta a gefen labbanta.

“Masha Allah. Allah Ya miki albarka, Autata. Ki kwanta ki yi barci, ki samu ki huta.”

Hakan kuwa aka yi. Ko fita daga ɗakin ba ta sake yi ba, ta miƙa kan gadon Ummah. Ba a ɗauki wani lokaci ba, barci ya yi awon gaba da ita.

A yayin da Ummah ke tattara wasu kayan amfanin gida da ba a ɗage ba, domin da gangan ake take musu a fasa mata su, alhali yanzu kayan aikin gida sun yi tsada. ita kaɗai ce a tsakar gida. Habibu kuwa yana ta wasa a ƙofar Mamansa, yayin da Ya Ado ya shige ɗakin Mama Sadiya.

“Wato Ado, duk abin da zan gaya maka a banza ko? Me ya sa ba ka kishin uwarka ne? Wannan matar ba ƙaramar annamimiya ba ce, ita da ‘ya’yanta. Amma ka kasa gane hakan. Kullum kana manne da su kamar ita ce ta haife ka. Wannan ai tozarta ni kake yi. Tun kuna yara nake iya ƙoƙarina wajen raba ka da wannan shegen yaron mai bala’in jiji da kai, amma kai ba ka san inda ake maka ciwo ba. Shi ma ka liƙe masa. Duk irin abin da matar nan da ‘ya’yanta suke mini a gidan kana gani.”

Ya Ado, wanda tun farkon maganarta yake kallonta, ya dafe goshinsa yana girgiza kai. Daga bisani ya ce,

“Mama, Sadam ɗan uwana ne, jinina ne. Duk abin da za ki faɗa min a kansa ba zai taɓa canza abin da ke raina ba. Tun tasowarmu bai taɓa nuna min wani bambanci na ɗan ubanci ba. To me ya sa ni zan nuna masa? Gaskiya ki yi haƙuri, ba zan iya hakan ba.”

Ya gama maganar yana ƙoƙarin miƙewa.

Mama Sadiya ta watsa masa wani mugun kallo tare da cewa,

“Koma ka zauna, dan ubanka!”

Ya koma ya zauna yana murmushi, ganin yadda take hararar sa.

“Yanzu Ado, ni  mahaifiyarka da na ɗauki cikinka har wata tara, na sha wahalar da ba a lissafawa. Ashe yanzu da ka zama mutum za ka fara bijire mini?”

Ya Ado ya buɗe baki yana kallonta. Ya fahimci tana ƙoƙarin sauya akalar maganar.

Ya sauke numfashi a hankali, sannan ya dubeta.

“Mama, bari in tambaye ki. Tsakaninki da Allah, a duk tsawon zaman da kuka yi da Ummah, ta taɓa yi miki wani abin da bai dace ba? Ta taɓa cutar da ke? Ko ta taɓa yi miki rashin kunya? Ko kallon banza ma ta taɓa yi miki? Ki faɗa mini. Idan kuma za ki ɓoye, ki tuna Allah Yana kallon ki.”

Mama Sadiya ta yi rau da idanu. Ta san idan ta ce eh, ƙarya za ta yi. Domin tun kusan shekara ashirin da biyar da Baffah ya auro Ummah, ba ta taɓa yi musu ko kallon da bai dace ba, balle ta rama baƙaƙen maganganun da suke jefa mata.

Da ya ga ta yi shiru, sai ya ce,

“Kin ga ba za ki iya amsawa ba, ko? Domin ku ne kuke cutar da ita da kuma ‘ya’yanta. Wallahi Mama, ku ji tsoron Allah. Ku guji ranar da Allah Zai kama ku da haƙƙin baiwar Allah nan.

Ni dai na fita haƙƙinki a matsayina na ɗanki. Na faɗa miki gaskiya. Allah Ya ba ki ikon aiki da ita. Amma idan kika bari kishinki ya kai ki inda zai halaka ki, ni babu ruwana.”

Cikin baƙin ciki da borin kunya ta fashe da kuka, tana nuna kanta da yatsa.

“Yanzu Ado, ni kake yi wa waɗannan maganganun? Yaushe ma ka yi wannan girman? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Ummah na ci gaba da aikinta a tsakar gida, sai ta ji kamar sheshsheƙar kuka na fitowa daga ɗakinta.

Cak ta tsaya, tana ƙoƙarin tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji.

Da kukan ya sake ƙaruwa, ta gane na Waheeda ne.

A firgice ta miƙe tana kwala sunanta, kafin ta nufi ɗakin da sauri.

Kiran nata ya sa Ya Ado da Baba Karami wanda shigowarsa gidan kenan suka ruga zuwa ɗakin.

Waheeda suka tarar kwance a kan gado, jikinta ya miƙe ya sandare. Gaba ɗaya jikinta ya jike sharkaf da zufa, har fuskarta. Kuka take yi cikin barci, hawaye na zubo daga idanunta suna diga kan pillow.

Yanayin ya matuƙar ɗaga musu hankali.

Ba tare da ɓata lokaci ba, Ummah ta hau gadon ta fara jijjiga ta tana kiran sunanta. Amma ko motsi ba ta yi. Sai ma kukanta da ya ƙara tsananta a cikin mafarkin.

Baba Karami ma ya zauna a gefen gadon. Ya ɗago kanta ya ɗora a cinyarsa, sannan ya fara tofa mata addu’o’i, domin yanayinta ya yi masa kama da wanda aljanu suka firgita.

Sama da mintuna goma suka shafe a haka, amma har yanzu ba ta farka ba.

Ummah kuwa, ta kasa ko da addu’a. Hawaye ne kawai ke ta zuba daga idanunta.

Ya Ado ya dafa kafaɗarta yana rarrashinta, shi ma zuciyarsa ta yi sanyi ƙwarai, yana kallon kyakkyawar fuskar Waheeda cike da tausayinta.

Ummah ta kama hannayenta tana matse su cikin nata.

“Waheeda!”

Ta kira sunanta da ƙarfi.

A wani irin mugun razane Waheeda ta farka. Ta miƙe zaune jikinta na rawa. Kallo ɗaya za ka yi mata ka san tsoro ya gama mamaye zuciyarta.

Da ta ga Ummah tana kuka a gabanta, sai ta rungume ta ita ma ta fashe da kuka.

“Ummah… tsoro nake ji. Ba zan ƙara barcin rana ba.”

Ummah ta shafa bayanta cikin tausayi.

“Ki yi haƙuri, Autata. Laifina ne. Ba zan ƙara sa ki barcin rana ba.”

A tare Baba Karami da Ya Ado suka sauke ajiyar zuciya, suna jin wani irin sauƙi ya ratsa su.

Ya Ado ya dubi Baba Karami.

“Na ɗauka ta dena irin wannan barci,tsoro ya ke bani wallahi?”

Ya girgiza kai cikin damuwa.

“Ni ma na yi mamaki. Rabon da ta yi irin haka tun shekara bakwai da suka wuce. Dole zan nemo Mallum mu yi magana.”

Ummah tana rungume da Waheeda, tana shafa bayanta. Lokaci zuwa lokaci tana share hawayen da ke zubo mata.

“Na ɗauka ta daina ne. Shi ya sa na ce ta koma ta yi barci. Gaba ɗaya laifina ne.”

Baba Karami ya girgiza kai.

“Dan Allah, Ummah, ki daina faɗar haka. Wannan ba laifinki ba ne ko kaɗan.”

Waheeda ta ɗago kanta daga jikin Ummah. A wannan karon, idanunta cike suke da wani irin natsuwa mai ban mamaki.

Ta ɗora tafin hannunta a fuskar Ummah, ta share mata hawaye a hankali.

“Me ya sa za ki ɗora wa kanki laifi, Ummah? Ke fa uwa ce. Uwa ba ta taɓa nufin cutar da ɗanta ba. Don haka kada ki sake ɗora wa kanki abin da ba laifinki ba ne. Ba zan ji daɗi ba idan na sake jin kina zargin kanki.”

Gaba ɗayansu suka yi shiru.

Ya Ado da Baba Karami suka kalli juna cikin tsantsar mamaki.

Ba wai maganar da ta yi ce ta ba su mamaki ba…

Salon da ta yi maganar ne.

Ta yi ta cikin nutsuwa, da hikima irin ta manya, ba irin yarinya mai shekara goma sha huɗu ba. Kamar dai ba Waheeda ce ke magana ba, wani ne ya aro bakinta yana zuba kalmomi masu nauyi da hikima. Wannan ya sa jikinsu ya yi sanyi, zuciyoyinsu kuma suka cika da tambayoyi marasa amsa.

follow me for more interested chapters 🥰😍