MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 13

by @mrsisham12



MATUƘAR INA RAYE
(As Long as I’m Alive)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)

Page 13


Murmushi Ummah ta yi ta manna mata kiss a goshi, sannan ta shafa kanta tare da faɗin,

“Allah ya miki albarka, Mamana.”

Ita ma murmushin ta mayar mata ta amsa da,

“Ameen, Ya Allah. Tun da na farka, akwai abin da kike buƙata ne, Ummah? Ki faɗa min duk abin da kike so in taimaka miki da shi. Ina so yau ki huta, babu abin da za ki yi. Ke dai ki naɗe hannu kawai ki huta a dakinki.”

A wannan karon kam Baba Karami ya rasa mamakin da zai yi akan  Waheeda wacce ke zaune, an ina ta samo wannan uban nutsuwa da maganganu kamar wacce ta haɗiye littafin salon magana. Domin Waheedar da ya sani ba ta da irin wannan nutsuwa da hankali da za ta yi maka magana haka.

Shi kansa Ya Ado, gani kawai yake kamar an sauya masa Waheedarsu.

Ummah kam, in ba murmushi ba, babu abin da take yi tun bayan farkawar Waheeda. A ɗaya ɓangaren kuma, duk lokacin da ta dubi Baba Karami da Ya Ado sai ta ji kamar ta fashe da dariya, ganin yadda suka yi mutuwar tsaye cikin mamaki.

Sam Ummah ba ta hanata ba. Hakan ya sa ta lissafo mata duk abubuwan da za ta yi. Da ta gama sanar da ita kuwa, Waheeda ta fita daga ɗakin ta soma yin duk wasu abubuwan da ta lissafo mata.

Baba Karami da ya kasa haƙuri ne ya zauna kusa da Ummah, yana riƙe da dukkan hannayenta ya ce,

“Ummah, don Allah ki ce min da ta kwanta barci ne aka maƙala mata memory na nutsuwa a cikin kanta.”

Dariya suka yi ita da Ya Ado, kafin ta ce,

“Babu wani abu da aka saka mata. Zuwa anjima za ka fahimci haka.”

Jinjina kai ya yi, domin har yanzu mamakin bai gama sake shi ba.

Sai da ta gyara ko’ina tsaf a cikin gidan, sannan ta yi shara ta tattara duk abin da Ummah ta zayyano mata. Daga nan ta saki murmushi tana ƙoƙarin komawa ciki kenan, Habibu ya shigo gidan da kayan wasansa a cikin leda cike da pieces na takardu. Ai kuwa nan take ya soma barbaza su a cikin gidan.

Nan take murmushin da ke kan fuskarta ya gushe. Cikin ɗaga murya ta furta,

“Kam bala’i! Don ka raina min wayo na gama shan wahalar share gidan nan, sannan ka zo kana zuba min yagaggun takardu a inda na share?”

Habibu ya tsaya yana kallonta kafin ya ankara ta iso gabansa. Ta riƙo shi ta soma zuba masa uban duka a bayansa. Zafin dukan ne ya sa shi ɓare baki ya soma kuka.

“Mugun yaro kawai! Wallahi ɗaya bayan ɗaya sai ka tsince su.”

Ta faɗa tana kuma kafa masa rankwashi a kai.

“Ke, lafiyarki kuwa? Me ya miki da za ki doke shi?”

Cewar Ummah da ta fito tare da Baba Karami.

Turo baki gaba Waheeda ta yi tana kunkuni.

“Ummah, sai da fa na gama share ko’ina tsaf, ya zo yana watsa min kayan datti saboda mugunta.”

Kallon Baba Karami ta yi ta masa alama kamar tana cewa, “Ka ga abinda nake faɗa maka ko?”

Kai kawai ya gyada yana gyara murya.

“Habibu, kwashe abinda ka zubar.”

Ta yi tsammanin zai mata tsawa ya hantare ta kamar yadda ya saba, amma sai ta ga sam ba ita yake ba, domin bai sake ko kallonta ba bayan ya umarci Habibu ya kwashe dattin, sannan ya koma ɗakin Ummah.

Ya Ado kuwa ya ja kujera ya zauna yana faɗin,

“Cin zalinki na da yawa, Waheeda.”

Ummah ta watsa mata mugun kallo.

“Ko ita haka ake mata, oho. Ke kam, anya ba Bauchi zan kai ki ba kuwa, ko bakina ya huta?”

Ya Ado ya sanya dariya.

“Allah Ummah, idan kika mayar da ita Bauchi, wallahi sai ta fi yanzu sangarcewa. Gara ki bar mana ita, mu riƙa managing ɗinta a haka.”

Ɗan murmushi Ummah ta yi.

“Ado, kai dai ba ka da dama, gaskiya.”

Ta kunce bakin zaninta ta fito da murtala ta ba Habibu, tana rarrashinsa kan bugun da Waheeda ta yi masa. Aikuwa cikin murna ya karɓa ya fita gidan da gudu.

Ajiyar zuciya Ummah ta sauke tana gode wa Allah da ya sa Mama Jamila ba ta nan lokacin da abin ya faru, domin da tana nan ne da tuni ta tada hankalin kowa a gidan. Ita kuwa uwar guntsin, Mama Sadiya, tana ɗakinta duk wainar da ake soyawa ba ta leƙo ba.

“Ummah…”

Baba Karami ya kwalla mata kira.

Sai da ta kalli ƙofar ɗakin kafin ta girgiza kai ta amsa.

“Ya aka yi, Baba?”

“Dan turo min Heedat.”

Lokaci zuwa lokaci haka suke kiranta, amma ba koyaushe ba. Salma da Zuwaira sukan fi kiranta da Heedat, Ya Ado kuma Autar Ummah yake kiranta. Baba Karami kuwa dama ba kasafai yake kiranta da wannan sunan ba, saboda halin rashin jinta, sai dai idan ya yi daɗin rai.

Ummah ta dubi Waheeda.

“Ba ki ji ana kiranki ba ne?”

Waheeda ta turo baki tana mulmula baki, alamar akwai abin da take son faɗa.

“Ummah, duka na fa zai yi.”

Ba tare da Ummah ta ɗago ta kalleta ba, ta ce,

“Haka kuka yi da shi? Ke me yasa ba kya kyautatawa mutane zato ne?”

Waheeda ta sunkuya gabanta, ta buga tagumi tana kallon Ummah. A maimakon ta je inda ake kiranta, sai ta ce,

“Ummah, wai me yasa Baba Karami ba ya sona ne? A duk gidan nan shi ne ya fi tsanata.”

A tare Ya Ado da Ummah suka ɗago suka kalleta, jin abin da ta faɗa.

Ummah ta ajiye lariyar hannunta da take tankade garin tuwon abincin dare.

Cikin kulawa ta ce,

“Kar in sake jin kin faɗi haka da bakinki. Shi ɗan uwanki ne, ciki ɗaya kuka fito. Duk da yana tsawata miki idan kika yi laifi, hakan ba yana nufin baya son ki ba ne. Wani lokaci mutum yana nuna soyayya ne ta hanyar gyara halin wanda yake ƙauna.”

Waheeda ta yi shiru tana wasa da yatsunta, kafin ta ɗan ɗago kai ta dubi Ummah.

“Amma Ummah… ni dai kullum idan na yi abu, shi kaɗai yake fara min faɗa.”

Murmushi Ummah ta yi, ta shafa kumatunta.

“Saboda ya fi son ya ga kin zama mace ta gari. Ki daina kallon faɗarsa a matsayin ƙiyayya.”

Baba Karami, wanda yake tsaye bakin ƙofa, ya yi gyaran murya.

“Heedat… zo nan.”

A hankali ta miƙe tana kallon Ummah kamar mai neman izini.

Ummah ta yi mata alama da kai.

“Je mana.”

Da sanyin jiki ta taka zuwa inda yake tsaye. Da ta isa gabansa, sai ta sunkuyar da kanta.

“Na’am, Baba Karami…”

Ya ɗan yi shiru yana kallonta. A karo na farko tun da ta tashi yau, ya lura da yadda take magana cikin natsuwa.

“Heedat.”

“Na’am.”

“Na ga aikin gidan da kika yi. Kin share ko’ina, kuma gidan ya yi kyau sosai.”

Ta ɗan ɗago kai cikin mamaki. Tabbas, yau ne karo na farko da Baba Karami yake mata magana cikin sanyin murya, har yana yaba mata. Tsakaninta da shi, duka da hantara kawai ta sani, shi ya sa ta fi shaƙuwa da Ya Ado, domin ko tsawa bai taɓa yi mata ba.

A hankali ta furta,

“Na gode.”

“Amma…”

Ya dakata na ɗan lokaci.

“Ba daidai ba ne ki daki Habibu saboda ya zuba miki datti a inda kika share. Ki tuna, ƙaninki ne.”

Ta cije laɓɓanta cikin nadama.

“Yi haƙuri, Baba Karami. Ba zan sake ba.”

“To, shikenan.”

Ya juya zai shiga ɗaki, sai kuma ya tsaya.

Ya furta,

“Jiya da safe Principal ɗinku ya kirani a waya. Ya sanar da ni cewa za ki koma makaranta ranar Monday, saboda za ki zana jarabawa tare da ɗaliban JSS 3.”

Nan take ta ɓata rai. Sam labarin bai mata daɗi ba. Tana cikin rayuwarta mai daɗi, sai ga maganar komawa makaranta.

Ummah ta miƙe ta ƙarasa kusa da Baba Karami, ta tsaya jikinta a sanyaye.

“Baba, ya aka yi ba ka sanar da ni ba? Yanzu ya ake ciki? Na san dole akwai kuɗaɗen da za su buƙata, tunda ka san makarantar kuɗi ce.”

“Wannan kar ki damu, Ummah. An gama komai. Zuwa ta zana jarabawa kawai ya rage. Kuɗin exam da sauran buƙatu dubu arba’in ne. Na samu na haɗa dubu ashirin da biyar, Ado kuma ya bayar da dubu goma sha biyar, kuɗin ya cika cif. Tun jiya da yamma na tura musu.”

Ummah ta rasa farin cikin za ta yi ko akasin haka. Ta san a kwanakin nan Baba Karami yana fama da rashin kasuwa. Ga dawainiyar gida, ga kuma halin matsin rayuwa. Amma duk da haka ya biya wa Waheeda kuɗin jarabawarta. Shi ma Ya Ado ba wani kasuwa sosai yake yi ba, amma ya cika sauran kuɗin ba tare da gardama ba.

Cikin damuwa ta ce,

“Amma da kun sanar da ni, da na nemo kuɗin. Na san ba wani daɗin kasuwa kuke ji ba a yanzu.”

Ya Ado ya ce,

“Kar ki damu, Ummah. Waheeda ta cancanci haka. Tana da basira da ƙwaƙwalwa. In sha Allah za mu yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin ta yi karatu mai zurfi.”

Waheeda kuwa tana jin duk abin da suke faɗa. Ta taɓe baki cikin takaici. Haushi ya cika zuciyarta har tana jin kamar ta fashe da ihu.

Ummah ta yi musu godiya sosai, sannan ta ce,

“In sha Allah gobe zan aiki Salma ta yanko mata uniform, tunda jibi ne Monday.”

Daga nan ta juya ta kalli Waheeda, wadda ta cika tana batsewa.

“Mamana, kin ga yadda ’yan uwanki suke ƙoƙari a kanki ko? To, dan Allah ki yi abin da ya dace. Kar ki ba su kunya, kin ji ko?”

Ta ƙaƙalo murmushin dole ta ce,

“To, Ummah. Na gode, Baba Karami. Na gode, Ya Ado. Allah ya ba ni hanyar faranta muku rai.”

Ɗan murmushi Baba Karami ya yi. Har yanzu mamakin sauyin da ya gani tattare da ita bai gushe ba. Bai sake cewa komai ba, ya juya ya koma ɗakin da ya fito.

“Ummah, me za a yi ne? Na ga za ki tankaɗe gari.”

Ummah ta ɗago kai ta ce,

“Tuwo da miyar kuka zan yi, Ado. Kai kam na san ba cimarka ba ce.”

Ya Ado ya yi dariya.

“Gaskiya kam, an bar muku kayan ku. Mutumiyar ma na san ba kaunar tuwon nan take ba. Zo, ki je ki siyo mana Indomie mu dafa.”

Ya miƙa mata kuɗi.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta karɓa ta nufi shago. Ba a jima ba kuwa sai ga ta ta dawo riƙe da baƙar leda cike da kayan da ta saya.

Shi da ita suka haɗu suka dafa Indomien, Ummah kuwa tana ta musu dariya. Bayan sun gama, Ya Ado ya zuba musu a kwano, ya shiga ɗakin Ummah domin su ci tare da ita da Baba Karami, duk da yake Ummah ba cika cin irin wannan abinci take yi ba.


Tsaye take a bakin hanya sanye cikin doguwar hijabi mai launin toka har ƙasa. Hannunta riƙe da katuwar akwati, daga gani tana jiran abin hawa.

Wayarta ce ta fara ringing. Ta ciro ta daga cikin handbag ɗinta ta ɗaga bayan ta yi sallama.

Shiru ta yi tana sauraron wanda ke magana ta ɗayan ɓangaren wayar.

Daga bisani ta lumshe kumburarrun idanunta a hankali. Kallon idanun nata kaɗai ya isa ya nuna ta sha kuka, domin sun yi jajir.

“Anty, ku yi haƙuri… ku yi haƙuri dan Allah. Ba wai don ba ku isa da ni ba ne, ku ne komai nawa a duniyar nan. Amma ba zan iya aikata abin da Baba yake so ba. Ba zan iya auren wanda yake so in aura ba.

In na auri Hamza, tabbas na tarwatsa rayuwata ne da hannuna. Hamza fa mashayi ne, sannan mazinaci ne. Wannan kaɗai bai isa Baba ya hana shi neman aurena ba? Amma saboda son kuɗi ya rufe masa ido. Duk wannan bai dame shi ba, bai damu da irin rayuwar da zan shiga ba bayan mun yi aure.

Da na ce ba zan aure shi ba, sai Baba ya ce idan har ba zan aure shi ba, to tabbas sai na bar masa gida. Ba ni da wani zaɓi da ya wuce haka. Da ace mahaifiyata tana raye, da ban fuskanci irin wannan musgunawar ba. Amma na bar wa Allah komai. Na bar musu gidan, Anty. Zan je in kama ɗaki da kuɗin da ke hannuna, sannan zan nemi aiki. Kuma na miki alƙawari, zan riƙe kaina. Ba zan taɓa zubar da tarbiyyar da Mama ta ba ni ba.”

Da ta gama faɗin haka ta katse kiran, sannan ta kashe wayar gaba ɗaya.

Nan take ta fashe da kuka tana rufe fuskarta da hijabinta, gudun kada mutanen da ke wucewa su fahimci halin da take ciki.

Bayan ta ɗan samu ta lafa, ta tari wani mai abin hawa ta faɗa masa sunan unguwar da zai kai ta.

A bakin gate ta samu Abbaty yana jiranta. Kuɗinsa ta tura masa ta transfer, sannan suka shiga cikin gidan.

Gida ne babba mai sassa da dama, kowanne sashe yana zaman kansa.

Bangaren da ta kama ya buɗe suka shiga. Ɗan ƙaramin self-contained ne, falo, bedroom ɗaya, sai toilet da ke cikin falon. Kitchen kuwa babu.

Sai dai ɗakin yana da gado da katifa, wardrobe mai kyau, haka kuma a falon akwai furniture masu sauƙin kuɗi amma masu kyau da tsabta. Ta ga ya dace da kuɗin da ta biya.

Abbaty ya miƙa mata key ɗin.

“To Husna, ga key ɗinki. Duk abin da kike buƙata sai ki sanar da ni. Sannan dan Allah a kula da tsaftar gidan. Asalin masu gidan suna ƙasar waje, ba za su ji daɗi ba su dawo su tarar gidan da suka bari a hannuna ya lalace.”

Husna ta amsa cikin sanyin jiki.

“In sha Allah zan kula da bangarena. Na gode sosai.”

“Babu komai. Na barki lafiya.”

Ya juya zai fita, har ya kai bakin ƙofa sai ya ji ta kira sunansa.

“Abbaty…”

Ya tsaya ya juyo yana kallonta.

Cikin sanyin murya ta ce,

“Na san ka yi min ƙoƙari sosai, amma ina da wata alfarma guda ɗaya.”

Ya ce,

“Faɗi, kar ki damu.”

Sai da ta ɗan yi shiru kafin ta ce,

“Akwai inda za ka taimaka min in samu aiki?”

Ya tsaya yana kallonta cike da tausayinta. Ya san duk abin da take fuskanta, domin makwabtansu ne tun tana gidan mahaifinta.

Ya ce,

“Ba dai kin zo da takardunki ba? Idan har za ki iya koyarwa, akwai wata makaranta da za su iya ba ki aiki da yardar Allah.”

Da sauri ta ce,

“Zan iya. Na gode sosai. Allah ya saka da alheri.”

“Ameen.”

Ya amsa sannan ya fita.

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta cire doguwar hijabinta ta ajiye, sannan ta zauna kan kujera tana tuna abin da ya faru yau a gidansu, abin da sam bai yi mata daɗi ba.

Hawaye suka cika idanunta.

A raunane ta ce,

“Tun da kika bar wannan duniya, rayuwata ta shiga cikin wahala, Mama. Na yi kewarki sosai. Rayuwar nan ta daina min daɗi. Baba kansa kawai ya damu, sauran ’yan uwana kuma suna goyon bayansa.”

Ta ci gaba da magana ita kaɗai, cikin tsananin damuwar da babu mai fahimtar girman abin da take ji sai ita kaɗai.

AlMustapha Mai Dawah House

Safa da marwa Sima take yi a katafaren ɗakinta. Tana sanye da kayan bacci masu matuƙar jan hankali, hannunta kuma riƙe da wayarta tana jujjuya ta. Daga dukkan alamu akwai kiran da take jira ya shigo.

Ai kuwa tana wannan zagayen, wayarta ta soma ƙara.

Da hannu mai ɗan rawa ta ɗaga ta manna a kunnenta.

“Hello, kawata.”

Shi ne abin da ta faɗa tana zaunawa a gefen gadonta.

Ta ci gaba da magana cikin ɗokin ba da labari.

“Ya salam, ke kin gan shi kuwa? Muhammad namiji ne yadda ba kya zato. Wallahi, duk lokacin da na ɗaura ido na a kansa, sai na ji wata irin wutar sha’awarsa ta taso min. Gaba ɗaya kasa riƙe kaina nake yi. Ba ni da wani buri da ya wuce in kasance tare da shi. Domin ke ma daga gani ba sai an faɗa miki ba, ɗan zai fi uban sa a shimfiɗa. Matsalar kawai, ya na da tsare gida sosai. Wallahi ko kamannina bana tunanin  ya sani , saboda ko kallo ban ishe shi ba.”

Ta ƙarasa maganar da ɗan damuwa a fuskarta.

Sai ta yi shiru tana sauraron abin da kawarta ke faɗa daga ɗayan ɓangaren wayar.

Can kuma sai wani makirin murmushi ya bayyana a fuskarta.

“Shi ya sa nake son ki. Dama na san za ki nemo min mafita. Ni yanzu duk wani plan ɗina na yadda zan kwashe dukiyar wannan tsohon zai biyo baya ne, bayan na biya buƙata da BK. Domin ya tafi da imanina.”

Ta ƙarasa maganar tana dariyar mugunta.

A haka suka yi sallama, sannan ta kashe wayar.

Wayar ta ajiye a gefenta tana jin daɗi, domin kawarta ta yi mata alƙawarin zuwa gidan domin kawo mata hanyar da za ta cimma burinta.

A ɓangaren Mamie kuwa, suna zaune a falo suna kallon series. Daddy kuma yana zaune a gefe, gabansa cike da files masu yawa yana duba aikinsa. Nini kuwa Zanaya ke yi mata assignment, kasancewar ranar Monday za ta koma makaranta.

Saukowa BK da Zannor suka yi cikin shirin fita. Suna sanye da ƙananan kaya masu irin brand ɗaya, sai dai kala ce kawai ta bambanta. Duk wanda ya gan su zai fahimci ’yan biyu ne, domin tsayinsu ɗaya ne, haka ma zubin jikinsu. Sai dai ba sa tsananin kama, they are not identical twins.

Zannor, wanda ya haɗe fuska, ya sunkuya ya manna wa Nini kiss a kai sannan ya ce,

“Mamie, mu za mu fita. Sai mun dawo.”

Mamie ta ɗan ɗago ta kalle su gaba ɗaya, sannan ta ɗauki remote ta rage ƙarar TV.

“Ina za ka je haka, Zannor?”

Zannor da ya san abin da take shirin faɗa ne ya ce,

“Ba ni kaɗai zan fita ba, ni da ɗan uwana ne.”

“Ohh… ashe haka ka ce.”

Ta faɗa tana duban BK, wanda ke danna wayarsa cikin natsuwa. Bai sa musu baki ba, kuma ba alamar zai yi, sai dai idan an saka shi cikin zancen.

Hakan ya sa ta ce,

“BK, ina ne inda ɗan uwanka zai ja ka da wannan daren ?”

Ya dakata da danna wayar, ya ɗago cikin sanyinsa ya ce,

“Alawa ta ce ta ƙare, shi ne Zannor ya ce zai kai ni in siya.”

Zannor da ya zuba masa ido ya girgiza kai, ya buɗe baki zai yi magana, amma Mamie ta tare shi.

“Amma kai kana son bin sa? Ka san kana buƙatar hutu. Dare lokacin hutawarka ne.”

BK ya dubi Zannor, wanda ke jiran amsar da zai ba Mamie. Sai ya kau da idonsa gefe ya ce,

“Ah ah, Mamie. Zan zauna a gida. Dama shi ya takura sai mun tafi.”

Mamie ta saki murmushi.

“Very good. To zo mu zauna, ka bar shi ya je ya siya ya dawo a duk lokacin da ya ga dama.”

Zannor ya riƙe goshinsa. Ya rasa abin faɗa, yana jin kamar ya kurma ihu. A ransa yake mamakin irin gidan da yake rayuwa.

Daddy, wanda tun farkon hirar bai ce komai ba, ya ɗago kai ya ce,

“BK, ku tafi. Amma kar ku yi dare.”

“To, Daddy.”

Sosai Zannor ya ji daɗin maganar Daddy, domin ya san duk dokar da Mamie ta kafa, idan Daddy ya yi magana ta rushe.

Suna shirin tafiya, sai Nini ta kira,

“Ya BK!”

Shi da Zannor suka juyo.

“Na’am, Nini.”

Ta miƙe ta ƙaraso gabansa.

“In kun je, kar ka manta ka siya mata alawar madarar da ka shanye.”

Cikin sanyinsa ya ce,

“Ban ba ki kuɗi ki ba ta ba?”

Ta waro ido cikin shagwaɓa.

“Tab! Wallahi ta ƙi karɓa. Ta ce ai tuwon madararta ka sha, ba kuɗi ba. Shi ya sa ta ƙi karɓar kuɗin. Wai idan ba ka biyata ba, Allah ya isa, ba ta yafe ba… kuma wuta balbal.”

BK ya runtse ido cikin nadamar shan tuwon madarar.
Yanzu hankalin kowa na falon ya koma kan hirarsu.

Mamie, da ta kasa haƙuri, ta ce,

“Wait… alawar wacece ya sha har take masa Allah ya isa? Faɗa min, Nini.”

“Mamie, sabuwar kawata ce. Wacce muka siya kosai a wajensu.”

Mamie ta girgiza kai.

“Ikon Allah. Matsalar ‘ya’yan talaka kenan, zaƙewa. In ba haka ba, ina ita ina jawa Muhammad BK Allah ya isa?”

Ba tare da ya shirya ba, BK ya ji maganar ta ɗan taɓa masa zuciya. Ba shi kaɗai ba, har Daddy da Zannor ba su ji daɗin kalmar da ta yi a kan ƙaramar yarinyar ba.

Daddy ya gyara zamansa yana murmushi.

“Lalle BK, ka haɗu da rigimammiya kuwa. Ka ga ta kanka. To kar ku manta da alawarta idan kun fita, in ba haka ba, wuta balbal ɗinta ta bi ka.”

Zannor da Zanaya suka yi dariya.

BK kuwa ya yi ɗan murmushin gefen baki.

“In sha Allah, Daddy.”



Bayan sun shiga mota, mai gadi ya wangale musu gate suka fita.

Hasken motar ya haska Waheeda da Safara’u, suna zaune kamar yadda suka saba gurin kayan sana’arsu na dare.

Su biyu sun ƙwace wayar Zuwaira suna ta dannawa, ita kuwa tana ta mita tana cewa su ajiye mata wayarta, amma ko kulata ba su yi ba.

BK ya dubi wajen, sannan ya ce,

“Ka ɗan yi parking a gefensu kaɗan, Zannor.”

Ba tare da tambaya ba, Zannor ya ja motar ya yi parking, sannan ya kashe engine.

BK ya buɗe ƙofar motar ya fito, ya nufi inda suke zaune.

Zannor kuwa ya bi bayansa.

Follow me for more interested chapters 😍🥰