BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 3

by @maidambu41

Chapter 3


     Shiru ta yi kamar bata wurin asali ma wani irin ɗauke wuta ta yi tana jin yadda Maamah ta ƙara maimaita mata tambayar.

"Kun dai-dai ta da Mahmoud?" Maamah ta juya tana kallon yadda ta shiga ruɗani. 

  Wani lokaci kamar me cutar autism. "Allah ya kyauta, ni ba shiga tsakaninki da zuciyarki zan yi ba, sannan duk abin da kike gani to ki sani ba abu me sauƙi ba ne. 

Zuri'arku ce haka, shi wanda yake ta nuna miki kulawa da ƙaunar bai zama dole iyayensa su ƙyale shi ya aure ki ba. Idan ma su ɗin sun amince sauran dangi da kakarku tana nan akan kome.

  Mahmoud kuwa ko bana raye ba zai wulaƙanta ki ba, ni ba zan ce ga yadda zaki yi ba, ko ga yadda zaki ji ba amma ki sani duk wani abin da zai shiga rayuwarki yana da kyau ki sani dole ki guje shi mutuƙar hakan zai cutar da rayuwarki, ni dai Allah ya ga zuciyata bana son ki sakankance wani ya cusguna miki yadda zai saka ki da na sani a rayuwa. 

  Da ina da zaɓi, ko mayar da hannun agogo baya to da na zauna da shi ko da ace zaku zama ajalinsa. To amma ita ƙaddara ba ruwanta, ƙaramin kuskure za ka aikata amma zai yi ta bibiyar rayuwarka har zuwa tsawon zamani.

  Wani lokaci samun abin da kake so mai sauƙi ne a wurinka, amma rayuwa da shi yafi kome azaba, gemu da gemu suka ƙulla, amma a yau ina raye ne madadinku kada ƙaddara da tsautsayin da tsantsin da ya kwashe ni ya kwashe ki." Wannan shi ne kalaman da Maamah ta yi mata magana da shi, wanda duk mai hankali idan ya ji yasan me take nufi. Bata hanata ba, amma tana tuna mata kada ta zura zuciyarta.


  Fita ta yi daga kitchen ɗin ta barta tsaye a gaban sink. Dawowa ta yi ta ƙara mata da cewa "Tun da ya auro matarsa kin sake ganin wani tashin hankali da fadan da Hajiya take ban da yau? Kimanin shekaru biyu kenan daga ita sai ɗanta kin ji wani abu ya faru ban da yau? Ba zan gaya miki komai ba, amma ina son na ƙara tuna miki su danginki abin da yake nasu suke so, musamman ke, ni ban hanaki haƙƙin ki ba, amma ina tsoron kada ƙaddara wanda ya riga fata ya tafi dake nahiyar da baki da daraja.

Mahmoud bai da uwa sai mu, ni ƙanwar mahaifinsa ce, idan kika nutsu aka haɗa wannan abin to har abada babu wanda zai miki gori, a nan kuwa akwai kuraye da ƙayoyi a hanyar da kika ɗauka." Daga haka ta juya ta batta a tsaye tan bin ta kallo zuciyarta ɗauke da wani saƙo mai nauyi, tunda har Maamah ta iya fadar haka akwai abin da ta hango. 


      Amma shin zata haƙura da ya Almu ne? Zata hakura da abin da take so ne? Almu mahaifiyar shi da mahaifinsa sun san komai sun san me yake tsakaninsu. Sannan hasashe Maamah take yi domin Ya Almu ba zai mata yadda take zargi ba. 

  Hawayen da ya zubo mata ne ya fahimtar da ita nisan da ta yi hakan yasa ta yi maza ta share da bayan hannunta. Ta fito a hankali tana tafiya Habibi yana bin ta, a baya a baya har zuwa ɗakinsu ta zauna can ƙuryar gadon hawaye mai zafi yake zuba daga idanunta. 


  Har dare bata fito ba, abincin dare ma bata ci ba. Tana ɗakin a zaune aka kawo mata abin da Abba Babba ya kawo daga waje, shi ma bata ci ba ta ajiyewa Faɗime domin tasan zata zo tambayarta ta cinye ne. Ba ita ba 'yan uwanta baki ɗaya bata iya hana su komai, duk abin da suka gani suka ce suna so bata iya hana su. Ga jakan tsarabar da tazo musu da shi har yanzu bata buɗe ba. 


     Shigowar su a tare bai saka ta buɗe ido ba, hasali ma ci gaba da kwanciyarta ta yi tana jinsu. Kunna wutar ɗakin Khamilah ta yi ta ga Habibi a gefenta shi ma ya kwanta.

  Zama a bakin gadon Khamilah ta yi, Mairoh ta zauna a gefen nasu da yake ɗakin gadajen biyu ne ɗaya a kusa da ɗaya. Haka Faɗime tana zuwa ta zauna a side bed ɗin da yake gefen gadon da Naanah Asma'u take suka zuba mata ido. "Didih tun ɗazun muke son shigowa amma Maamah ta haɗa mu da aiki, ki yi hakuri." 


   Murmushi ta yi tana gyara kwanciyarta ta ce musu. "Ba komai!" Ta juya musu baya tana jan mayafin kwanciyarta. 

  "Didih muna tare da ke fa, muna bayan ki. Muna sonki da Ya Almu kin ji!" Cewar Khamilah.

"Eh muna son ki da Ya Almu har azumi nake miki Allah ya tabbatar da soyayyarku!" 


     Bata ce uffan ba, sai can ta ce musu "Ku kwanta, Khamilah za ki tafi makaranta ke da Faɗime, Mairoh kwanta zamu tashi da aiki gobe jibi idan Allah ya kai mu za'a tashi da azumi." 

Daga haka ta sauko daga gadon ta shiga ban ɗaki ta yi alwalar sallar isha'i, tana zuwa bata kula su ba ta fara sallah, kamar yadda tace su kwanta haka suka kwanta ta rufe su da mayafinsu bayan ta idar sannan ta kwanta. Dare ya yi sosai amma idanunta a bushe babu alamar bacci a cikin su.

  Tashi ta yi ta shiga ban ɗaki ta yi alwala ta sake fitowa ta fara sallar nafilla. Kafin ta fara jin bacci. Zata kwanta wayarta ta fara kuka. A hankali ta kai hannu kasan pillow ta ɗauka. *Rai* number Ya Alamu ta fito ɓaro-ɓaro a jiki. Take jawaye ya cika mata idanu kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka tare da mannawa a kunnenta. 

             "Mmmh!" Ya furta mata a sanyayye, tana jin hayaniyar mutane a kusa da shi. 

Toshe bakinta ta yi alamar kuka ne ya kwace mata. "Mmmh!" Nan ma shiru ta yi, a karo na uku ya ce mata. "Mmh ki min magana!" Jan hanci ta yi tare da sake wani sirrintaccen kuka ta ce mishi "Hmmh!"

"Kuka kuma Mmmhhhhhh!" Yadda ya karasa da wani siga yasa ta sake sabon kuka zuciyarta tana wani irin harbawa.

   "Uhmm baki yarda da ni ba ne?" Shasheƙar kuka ta sake wanda ya fi na baya ma ƙarfi. A yadda take kukan ban da Mairoh da take saman Khamilah babu wanda yasan tana kuka sosai. Sai dai kukan irin wanda yake tafiya da nutsuwa da kuma touched duk wanda yake gefen me yin sa.

   Bata san dalilin Maamah na yin haka ba, duk da sun fahimci Maamah bata son Didih ta fuskanci same destiny ɗin da ta fuskanta ne, amma ai maganar gaskiya Ya Almu ya dace da Didih, yana da ilimi yana da abin yi, sannan asalima bai da matsala da family kowa son shi yake. To me yasa Maama take ganin kamar abin da ya faru da ita zai faru da Didin su? Wannan shi ne tambayar da bata da amsarta. 

  Duk da sun taso sun ga irin wahalar da Mahaifiyarsu take sha da dangin Mahaifinsu Amma basu san akwai wani abu da ya fi haka muni ba, koda yake ita ƙiyayya haka take. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ji Didin ta daina kuka. 

      Murmushin farinciki ne ya ƙwace mata, ta ƙara juyowa tana kallon yadda Didin take zaune a tsakiyar gadon, ga Habibi a kan cinyarta. Alamar waya take amma babu yadda zaka ɗauka magana take a can ƙasa makoshinta.


   A nan kuwa wai magana take a shagwaɓe, ƙura mata ido ta yi kamar mayya a cikin daren nan, har bacci ya lullubeta, hakan yasa bata san lokacin da Didih ta gyara mata kwanciya ta rufe mata kafarta ba. 


        Da asuba sai da Abba Babba ya buga musu kofa, kafin ya wuce masallaci, dama a cikinsu Faɗime ce mai nauyin bacci don har suka yi sallah tana kwance. Sai da suka idar Naanah Asma'u ta tashe ta tana lallaɓata dama haka take mata, idan Khamilah ko Mairoh ɗayansu ya zo tashinta to maketa suke da gaske har sai ta farka da kuka. 


   Parlourn suka fito kowacce ta kama aikin da tasan nata ne, musamman Naanah Asma'u da ta kama aikin abin karyawa, Mairoh tana haɗa wanke-wanke, tana fama da aikinta. Sai ga Tente Hasiya ta fito da wanke-wanke ta jibga mata.


Bata kulata ba ta cigaba da aikinta can ta ce mata. "Ke ni ba sa'arki ba ce waccan mai suffar bayan tukunyar ce sa'a ta kuma gidan Alhaji Muhammad Mustapha Ladan nawa ne, ni ce Uwar Baba karami." 

           Wani matsiyacin kallo Mairoh ta mata tana ci gaba da wanke-wakensu.

Sosai abin ya tsayawa Tente Hasiya a rai. "Umma!" Wani kyakkyawan yaro da bai wuce shekaru biyu ba ya kira sunan Tente Hasiya. Juyawa ta yi tana cewa "Shalele haihuwar namiji sai Macen da Allah yaso ta da arziƙi, na ci tumunin takaba ya kwashe dukiya mai yawan gaske." 


"Duk saurin unguwar zoma ta jira a haihu dai ko?" Inji Mairoh tana dariya. 


A fusace ta juyo Mairoh ta ɗauki muciyar da take wankewa ta ce mata. "Wallahi sai na fasa miki kai na gaya miki!" Ta fada tana juya muciyar da kai. 

"Rakiya ce sa'ata!" Murmushin tsokana Mairoh ta yi mata ta ce mata. "Ina fa ta zama sa'arki kina sa'ar Babbar yarta ta fari sai dai 'ya ta ɗauke ki." 

"Ƙarya kike miji ɗaya muka kwana da shi." 


"To matar dattijo, ai mace idan ta isa ta auri matashin wanda zai nuna ta a matsayin matarsa ta nunawa ƙawayenta mijinta, ba mijin wata ba me aka yi aka yi mijin wata. Kin dai samu sauran Maamah! " 


  "Maryama!" Abbansu ya kira sunanta daga ɗaki.

"Anya ba aure kike so ba?" 

Ɗib ta ɗauke wuta bata ƙara magana ba, haka ita Tente Hasiya ta yi ta faɗa da zage-zage. 


  Sai da Maamah da Naanah Asma'u suka gama abin karyawa. Sannan ta dauki na Hajiya Innah a basket tafi da shi, tsoron bin lungu yasa ta wuce ta babbar kofar shiga gidan Hajiya Innah. Abinda ya guda a can shi ta samu d'ago kai tayi suka yi ido hudu da shi da sauri tayi kasa da kanta. Jikinta har rawa yake hatta basket ɗin hannunta rawa yake. Kamar kasa ya bude ta shige yana zaune a kan plastic chair, yana karanta Alkur'ani, yana ganinta ya tamke fuska, yadda kafarta yake hardewa yasa take tafiya kamar wacce ake turata. Hatta basket ɗin rawa yake yana jin sautin ƙarar plat na basket ɗin, bai kulata ba har ta wuce. 


     Tana shiga ta samu Hajiya Innah tana can uwar ɗakinta, kitchen ta shiga ta samu kaca-kaca. Gyara zaman inda aka tara kayan da aka yi amfani da shi ta yi sannan ta ajiye basket ɗin ta ɗauki tsintsiya ta share kitchen ɗin. tana gama sharewa ta gyara tare da ɗaurawa Hajiya Innah shayi irin nasu na Tuareg. Ta ɗauko wata 'yar buta ta zuba shayin da yake wani azababben ƙamshi. Ta jera a tire ta zuba doya da ƙwai da tazo da shi. Sannan ta zuba farfesu a wani bowl. Ta juya zata fita kenan suka yi wani irin karo da shi.


   Butar shayin ya tuntsira ya zube a saman cikinsa. Wani irin tsoro ne ya rufe ta, ta juya da sauri tana me ajiye tiren. Wucewa ya yi ya ɗauki abin da zai ɗauka ba tare da ya kalli yadda jikinta yake wani azabar rawa ba. Har ya gotta ta gabanta ya ɗan dawo kaɗan. Ai kuwa ta sake fitsari tsoro. Allah ya mishi baiwar kunne kallonta ya yi yadda take matse fitsarin, "ki ka sake na dawo na ga fitsarin nan ko!" Ya saka kai har ya fita fa, bai juyo ba ya ce mata. 

"Uban me na yi miki kike wannan rawar jikin?"

 Nutsuwa ne ya shigeta lokaci guda. Ya wuce abinsa yana tsaki. 


  Da sauri ta fita daga gidan ta nufi lungun nan, ai kuwa ta same shi a wurin yana zuƙar taba har da busawa a iska. Juyawa ta yi zata koma ɗaya kofar. 

 "Zo nan!" Ya faɗa da wata kakkaura murya, ai fashe wa ta yi da kuka ta juya. 

  Izuwa yanzu ran shi ya gama ɓaci yarinyar nan ta bala'in raina shi. Shiru ya yi ya ƙara zuƙe sugarin ya kalleta ya ga yadda take tsaye a wurin kamar an dasata. Takawa ya yi gabanta ya daki kwanjinta sai zata yi kara ya ce mata. 

 "Shiii!" A hankali ya bangajeta ya wuce, har zai fita a lungu ya ce.

  "Au kuka kike?"  

 Da sauri ta miƙe tare da barin wurin. Ba kowa a tsakar gida ballantana parlourn, ta shiga ɗakin ta samu Mairoh ban daki ta shiga tana me cire kayan jikinta, ta wanke jikin sannan ta fito ɗaure da towel din Khamilah, saka kaya ta yi da sauri tana komai a ɗan hanzari, ta ɗauki wata tsumar zanin  da suke goge ɗakinsu, ta koma ta babban ƙofar. Ai kuwa a tsakar gidan ta same shi yana ɗaga karfe, ba riga a jikinsa. Bata yarda ta kalle shi ba, saboda kada ya ganta ya ci mutuncinta. 


      Kitchen ɗin ta shiga ta saka ruwa sannan ta goge shi Tsaf, ta dawo parlourn ta goge. Tana cikin gyara kayan parlourn ya shigo da takalmi har Parlourn, ya je tsakiyar parlourn ya zauna. Daidai fitowar Hajiya Innah tana faɗin. "Yau dai Asma'u kin kashe ni da yunwa, ni da Rakiyah take kawo min abinci tun shida na safe. Allah ya kyauta wannan Mijinki ya shiga uku!" Bata ce mata komai ba ta nufi kitchen ɗin ta daura wani ruwan shayin, sannan ta kawo mata doya da ƙwai da ya huce. 

 "Uban kowa a zuba maka ne?" Kallon doyar da ita Naanah Asma'u ya yi cikin wani irin ƙyanƙyami ya taɓe baki yana kauda kai.

  Idanun Hajiya ne ya sauka akan cikin shi zuwa saman kirjinsa inda ya yi jajur. "Innalillahi wainnalihir rajoun Uban kowa garin Yaya ka kone? Uban kowa a ina ka kone?" Miƙar da kafar shi yayi da takalmi akan Centre table din da yake parlourn yana kallon wayar shi. "Uban kowa?"

  "Hajiya" ya fada a wata irin murya can cikin kirjinsa. 

"Innalillahi wainnalihir rajoun! Tashi muje asibiti ai ba zama?"

  Naanah Asma'u tana kitchen duk tsoro ya gama cikata kada ya gayawa Hajiya ita ce ta ƙona shi.

  "Tashi mu tafi mana kana wasa da kuna ne yana lahani fa!" 

Banza ya yi da Hajiya ta yi ta surutunta. 

  Ƙarshe ya ce mata. "Ki ce ta share min ɗakina!" Ya fada yana barin Parlourn. 

 "Ke Asma'u wuce ki gyara mishi ɗakinsa!" 

  A dan ruɗe ta ce mata. "Hajiya Ya Almu ya hana ni!" 


    Ashe yana bakin ƙofar bai tafi ba. Dawowa parlourn ya yi ya kalleta daga sama har ƙasa ya fita daga parlourn. 

  "Bana son munafunci ki wuce ki gyara masa." 

  Kamar ta yi kuka haka take ji. Wucewa ta yi ɗakunan maza matasan gidan yana can baya, da ɗan tazara da cikin gidan. Ta haɗiye yawun ya kai sau goma. Har ta isa ƙofar ɗakinsa. Da yake dauke da wasu takalma na yan gayu irinsa. Da sallama ta shiga parlourn, ba kowa sanyayye ta shiga tare da ɗaga labulen parlourn ta shiga gyarawa kafin ta fara share parlourn tana gamawa ta wuce inda ɗakinsa yake zuciyarta na wani tsalle kamar ta fasa amma tasan masifar da zai faru sai ta gwammaci yaƙin duniya da wannan tashin hankalin. Cikin ɗakin ta shiga bakinta da addu'a, yana tsaye da wani gajeren wando. Hannunsa auduga ce da wata yar almakashi. Ta mirror ɗin da yake gaban shi suka yi ido hudu. Sai lokacin ta hango yadda farar fatanshi ta cika da ruwa alamar ya tashi. 

  Ai ji ta yi zuciyarta kamar zai fito daga kirjinta. Tasan Ya Adam tunda ta ƙona shi sai ya rama, shi a cin bashinsa ya yafe ka yi kaɗan baka isa ka isa ma ba. 


      Gadon ɗakin ta karkade sannan ta fara shara, tsoro ya hanata isa gare shi sai satar kallon shi take shi ma yana gamawa ya wuce banɗakin haka ta gama aikin cikin ɗakin sannan ta yi sauri zata fito sai ga shi ya fito daure da towel.

 Jikinta ya fara rawa musamman hannunta. Saka hannu ya yi ya rufe ƙofar. Ya ci gaba da abin da yake ɗaukar bandeji ya ɗaure wurin bayan ya saka magani. Ita fa sai yanzu take tunawa ashe yana da degree da master a bangaren kiwon lafiya. Ya taɓa aikin asibiti kafin ya watsar ya kama gaban shi babu wanda zai ce ga aikin da Ya Adam yake domin bai da wani ƙwaƙwaran aiki. Kodayake Abba ƙarami yana da kuɗi sosai. 


Banɗakin ta shiga ya wanke har ta gama zata fito ya shigo da wani abin shakar iska, ya kunna mata wani hayaki. Yasan tana da asthma. Ya ja kofar ya rufe tayi ta buga kofar tana tari. "Don Allah ka buɗe, don Allah ka yi haƙuri ba zan ƙara ba. Wallahi ba da gayya na ƙonaka ba, don Allah ka buɗe mini kofa Ya Adam don darajar Ummanka da take kabari ka yi hakuri ba zan kara ba." 

    *Au dama tasan duk irin wannan kalaman?* Tsaki ya yi ya gama shiryawa sannan ya buɗe ƙofar ya same ta yashe a toilet ɗin ta faɗi a can tare da dunƙulewa. Murmushin mugunta ya yi yana jin wata nutsuwa na shigan shi. A hankali ya janyo ta har zuwa parlourn. Ya watsar da ita kamar bai damu da ita halin da take ciki ba, ya koma ɗakin ya gama abin da yake sannan ya fito dauke da wata bag ya buɗe bag din sabon kwalin inhela ne buɗewa ya yi ya ɗaura mata bakinta ya matsa mata. Wani numfashi ta ja tare da lumshe idanunta. Ta miƙe tare da fita ya barta a nan tsakar parlourn yashe. 


     Bacci ne ya ɗauke ta shi kuwa fita ya yi ya bar gidan baki ɗaya bai da matsala da gidan. Can gidan Mahaifinsa ya nufa inda ya samu ƙanwar babansa autarsu da 'Yarta mai suna Mufidah. Sai wani iyayi take tana wani yauƙi. Wucewa parlourn mahaifinsa ya yi ya samu ƙaninsa Fu'ad yana zaune ƙasa, shima zama ya yi a can nesa da Fu'ad yana kallon Mahaifinsa da yake ta waya. Sai da ya gama wayar sannan ya zuba mishi ido. 

  "Adam Ladan!" Kallon Uban yabyi kafin ya ɗauke kai yana me gyara zamansa ya miƙar da dogayen cinyoyinsa yana cewa. "Na'am Abba ƙarami." Shiru parlourn ya yi can Kanwar Babansa ta ce masa. "Uban kowa maganar aure ne fa, yasa aka kira ka." 

  Cikin wani irin kallon renin hankali ya juya ga mahaifinsa yana cewa "Ina zaune ne akan wani?" 

  Cikin lallaɓawa Mahaifinsa ya ce masa "Ko ɗaya Uba kowa! Kawai ta ga dacewar hakan ne yasa ta maka maganar aure. Sannan ai yanzu kana neman kusan shekaru!" 


Miƙewa ya yi yana me zuba hannu a aljihun wandonsa ya ce masa "Bana buƙatar wata mace  a rayuwata. Ina son na zauna da kaina na ga zan iya da halina ko na kawo wata da zata iya min!"



©️Mai Dambu