MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 14

by @mrsisham12


MATUƘAR INA RAYE
(As Long as I’m Alive)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)

Page 14


BK ya isa gabansu cikin nutsuwarsa, hannayensa na cikin aljihun wandon jeans ɗinsa. Ya tsaya yana kallon Waheeda da Safara’u, waɗanda suka maida hankalinsu kan wayar Zuwaira.

Zannor kuwa ya tsaya a bayansa yana murmushi, ya girgiza kai.

“Dan uwa, wace ce ka shanyewa alawar madara a cikinsu?”

Ya faɗa yana rufe bakinsa da hannu saboda dariyar da ke shirin kubce masa.

BK ya watsa masa harara.

Sai a lokacin Waheeda ta ɗago kai.

Da idanunta suka sauka kan BK, ta yi saurin ɓoye wayar a bayanta. Ta zaro ido na ɗan lokaci, sannan ta haɗe fuska irin ta rashin wasa.

“Uhumm…”

BK ya ɗan ɗaga gira.

“Wayar wa ce?”

Waheeda ta ɗan kalli Zuwaira, sannan ta ce,

“Ta Yaya Zuwaira ce.”

“Ki ba ta.”

Ba musu ta miƙa mata wayar.
Zuwaira ta karɓa tana hararar Waheeda.

“Zan yi maganinku ne akan ɗaukar min waya kuna dannawa.”

Ta faɗa tana ajiye wayar a saman robar da suke zaune.

BK ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya miƙa wa Waheeda.

“Ga kuɗin alawarki.”

Waheeda ta kalli kuɗin, sannan ta kalli BK ta yatsina fuska.

“Ni ban ce ka ba ni kuɗi ba.”

“Amma kin ce Allah ya isa ai.”

Da sauri Zannor ya saki dariya.

“Ai kuwa haka ta faɗa.”

Waheeda ta taɓe baki.

“Ni ai alawata na ce ka biya ni.”

“Shi yasa na kawo kuɗin.”

“Ban son kuɗi.”

Ya kafe ta da shanyayyun idanunsa sannan ya furta,

“Me kike so?”

Ta nuna wani ƙaramin kantin da ke ɗan gaba.

“Alawar madarata da ka sha nake so.”

BK ya juya ya dubi Zannor.

“Mu je.”

Zannor, wanda har yanzu yake dariyar dramarsu, ya girgiza kai.

“Ni de Ina nan,je ka dawo kawai.”

BK bai ce komai ba. Ya fara tafiya shi kaɗai zuwa kantin.

Waheeda ta bi bayansa da ido tana murmushi.

Safara’u ta daki kafaɗarta.

“Ke wai a ina kika san shi? Ƴan sabon gidan nan ne fa, ga su kyawawa. To me ya haɗa ki da shi?”

Waheeda ta ɗan ɗaga kafaɗa.

“Shi ne fa ya ci mun tuwon madarata.”

Safara’u ta rufe baki tana dariya.

“Wallahi ke ba ki da tsoro.”

Zannor, wanda yake tsaye a gefensu, in banda dariya babu abin da yake yi. Sai yanzu yake gasgata abin da BK ya ba shi labari a kanta. Lokaci ɗaya ya ji ta burge shi. Ya jima bai ga yarinya mai irin wannan tsiwar ba.

Can BK ya dawo riƙe da manyan alawar madara guda biyu a cikin packet, tare da wasu ƙananan sweet.

Ya miƙa mata.

“Ga shi.”

Waheeda ta karɓa cikin farin ciki.

“Har guda biyu?”

“Eh.”

Ya amsa a takaice.

Ta yi murmushi har haƙoranta suka bayyana.

“Na gode.”

Sai ta ɗan dakata.

“Allah ya saka da alheri. Ashe dai kana da kirki.”

BK ya gyada kai kawai, bai amsa ta ba.

Yana shirin komawa mota, sai Waheeda ta sake kiransa.

“ BK.”

Ya tsaya ba tare da ya juya ba.

“Na’am?”

“Na yafe maka, ka ji.”

Zannor ya kwashe da wata irin dariya.

“Alhamdulillah! Ka tsira daga wuta balbal.”

Har BK, wanda bai shirya ba, sai da murmushi ya suɓuce masa.

Ya girgiza kai kaɗan.

“Thank you.”

Waheeda ta ɗaga alawar hannunta.

“Amma kar ka sake cin tuwon madarata ba tare da izini ba.”

“Ba zan sake ba.”

“Promise?”

“Promise.”

Ta yi dariyar jin daɗi tana kallonsa har ya shiga mota.

Motar na barin layin, Salma ta fito daga gida, dama ta shiga ƙaro musu yaji ne. Nan take Zuwaira ta soma ba ta labarin duk abin da ya faru.

Salma ta riƙe haɓa tana kallon Waheeda, wacce ta fara cin alawarta cikin annashuwa.

“Ke Waheeda, ina raba ki da shiga sabgar masu kuɗin nan. Aradu ba mutunci ne da su ba. Kin ga mu talakawa ne, ya kamata mu kulla alaƙa da mutanen da suke daidai da mu, ba waɗanda suka mana fintinkau ba.”

“Wayyo Allah na! Na shiga uku da ke, Yaya Salma.”

Waheeda ta faɗa da ɗan ihun takaici.

Sannan ta ci gaba da cewa,

“Tuwon madarata fa ya shanye min, shine yanzu ya siya min wata alawar.”

Salma ta girgiza kai tana murmushi.

“Hmmm… Heedatu kenan.”

Shi kaɗai ta faɗa, sannan ta ci gaba da soyar suyar da take yi.

Da lokacin tashinsu ya yi, suka shiga gida.


Washegari kuwa ya kasance ranar Lahadi.

Ba su fita talla ba, domin kosan da suka yi a gida an saye. A ranakun Lahadi ba sa yin kayan sana’a da yawa, sai dai adadin da za a saya a gida, domin su ma su samu lokacin hutawa.

Ummah ta zuba kosan na naira dubu ɗaya a cikin leda, sannan ta miƙa wa Waheeda.

“Je ki kai kosan nan gidan Mai Dawah, sannan ki dawo. Kar ki tsaya shirme da shiririta, na san ki sarai.”

Waheeda, wacce ta shirya tsaf cikin uniform ɗin Islamiyyarta, ta ajiye allonta, ta karɓi ledar, sannan ta fita.

Da ta isa ƙofar gidan Mai Dawah, ta yi knocking sau biyu zuwa uku.

Mai gadi ne ya buɗe ƙaramar ƙofar.

Da ya ganta, ya saki murmushi, sannan ya matsa mata gefe ta shiga, tana gaishe shi.

“Lafiya lau, yarinya. Ki shiga ta ƙofar falon nan.”

Ya faɗa yana nuna mata entrance ɗin falon da hannu.

Bugu biyu ta yi a ƙofar, aka buɗe.

Nini ta gani tsaye a gabanta tana sakar mata murmushin farin cikin ganinta.

“Kawata! Ke ce? Shigo mana.”

Ta faɗa cikin zumuɗi.

Waheeda ta girgiza kai sannan ta ce,

“A’a, sauri nake yi. Bana son in makara a Islamiyya.”

Nini ta riƙo hannunta tana jan ta ciki.

“Kar ki damu mana, ai ba za ki yi late ba.”

Ba ta jira amsarta ba, ta ja ta suka shiga falon. Da shigarsu ciki, Waheeda ta tsaya cak.Idanunta suka fara yawo cikin falon. Komai na gidan ya matuƙar burgeta. Kujeru masu tsada ne suka kawata falon, ga katafaren television da ya mamaye wani ɓangaren bango, sai ƙamshin air freshener da ya cika ko’ina.

A zuciyarta ta ce,

“Wayyo Allah… Ashe haka gidajen masu kuɗi suke.”

“Wa ya zo, Nini?”

Muryar Mamie ta fito daga kitchen.

Nini, wacce har yanzu ke riƙe da hannun Waheeda, ta ɗaga murya tana cewa,

“Kawata ce ta zo, Mamie. Zo ki ganta.”

Ba a wani ɗauki lokaci ba Mamie ta fito tana goge hannunta da dry towel.

Tun daga nesa take ƙare wa Waheeda kallo, daga kayan jikinta har zuwa ledar kosan da take riƙe da ita.
Da ta iso kusa da su, Nini ta sake cewa cikin farin ciki,

“Mamie, kin ga kawata?”

Mamie ta saki ɗan murmushi kaɗan sannan ta ce,

“Ita ce wacce suke siyar da kosai ko?”

Ta ƙarasa maganar tana mayar da idonta kan ledar kosan da ke hannun Waheeda, wacce har yanzu zafinta bai sauka ba.

Waheeda ta ɗago kai, idanunta suka haɗu da na Mamie.

Nan take zuciyarta ta buga da ƙarfi, amma ta yi saurin daidaita kanta.

Cikin ladabi ta ce,

“Ina kwana… Wai ga shi, in ji Ummah.”

Mamie ta karɓi ledar tana taɓawa.

“Sannu da ƙoƙari. Kosan ku yana da daɗi sosai. Menene sunanki?”

Kafin Waheeda ta samu damar amsawa, Nini ta riga   ta magana ta ce,

“Sunanta Waheedat, Mamie.”

Mamie ta watsa mata ɗan harara.

“Ke aka tambaya ne?”

Nini ta fashe da dariya tana rufe bakinta.

Mamie kuwa ta juya ta koma kitchen, daga inda suke tsaye suna jiyo tana mita wa masu aikin gidan.

Nini ta murmusa ta ce,

“Kar ki damu fa, haka Mamie ɗinmu take.”

Waheeda ba ta ce komai ba. Ta juya za ta tafi, amma Nini ta yi saurin bin bayanta tana ta yi mata hira.

Da suka fito daga falon, suka yi karo da BK da Zannor, kowannensu riƙe da ƙwallo, jikinsu sharkaf da zufa.

Kallo ɗaya kawai za ka musu ka fahimci daga buga ƙwallo suka dawo.

Nini ta yi murmushi ta ce,

“Ya BK, ga Waheedat.”

BK ya zuba mata ido yana kallonta.

Ita kuwa ko kallonsu ba ta yi ba. Hankalinta ma ba ya kansu.

Zannor ya yi dariya ya ce,

“Hajiya Waheeda, yau ke ce a gidanmu?”

Sai a lokacin ta ɗago ta dube su.

Ba yabo, ba fallasa ta ce,

“Eh, ni ce.”

Ganin suna tsaye a gabanta ne ya sa ta matsa gefe za ta wuce.

Tana wucewa ta ce cikin muryar da za su jiyo ta

“Kun wani tare wa mutane hanya. Jikinku sai hamami yake.”

Ta wuce abinta.

Daga BK har Zannor, bayanta suka bi da kallo har ta isa bakin gate.

Zannor ya soma sunsuna jikinsa yana dariya.

“Wallahi BK, wai da gaske muna wari ne?”

BK kuwa girgiza kai kawai ya yi yana jinjina halinta.

“Jiya kamar ba ita ba… Yau kuma ga shi rashin kunyarta ya dawo.” Ya faɗa hakan a ransa

Zannor ya dafa kafaɗarsa yana dariya.

“Bro… Anya wannan budurwar taka ba ta da aljanu ?”

BK ya watsa masa wani kallon da ya sa ya yi shiru.

Sannan cikin sanyin murya ya ce, “Kai kana da hankali kuwa?”

Zannor ya ɗaga masa gira ɗaya yana murmushi.

“Nobody knows tomorrow.”

Ya kuma watsa mai hararan da ta fi na ɗazun “Don’t be stupid tomorrow is Monday.” 

Dariya Zannor ya kwashe da shi

BK bai sake cewa komai ba. Girgiza kai kawai ya yi ya shige ciki.

A falon suka tarar da Mamie da Nini tsaye, alamar kamar tana jiransu ne.

Da BK ya ƙaraso, Mamie ta nufi gabansa, ta riƙe hannayensa cikin kulawa.

“BK, kai kam ba ka nemawa kanka hutu sam. Maza je ka yi wanka, sannan ka dawo mu yi breakfast.”

“Okay.”

Shi kaɗai ya faɗa, sannan ya hau stairs.

Zannor na shirin binsa, Mamie ta dakatar da shi.

“Minti ɗaya, Zannor.”

Ya tsaya yana kallonta.

“Wai me yasa ka raina ni ne? Sau nawa zan gaya maka ka daina ja min yaro zuwa buga ƙwallo? Me yasa ba ka tausayin condition ɗinsa?”

Zannor ya sauke numfashi.

“Mamie, babu abin da ya haɗa ciwon BK da wasan ƙwallon kafa. Sai dai idan neman excuse kike yi na hana shi cika burinsa. Wallahi ban san dalilin da yasa kullum kuke juya masa rayuwa ba, kuna fakewa da ciwonsa kuna tauye masa haƙƙinsa.”

Kafin ya gama rufe baki, Mamie ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari mai ƙarfi.

Paa!

Ta nuna shi da yatsa.

“Ka soma wuce gona da iri, Zannor. Wallahi zan yi maganinka. mara mutunci kawai.”

Ya shafa kumatunsa a hankali.

Sai ya ɗaga idanunsa da suka ɗan yi ja ya kalleta.

“Ko sau nawa za ki mare ni, ba zan taɓa daina faɗa miki gaskiya ba. BK ba ƙaramin yaro ba ne yanzu. Ku bar shi ya yi abin da yake so, kamar yadda kowa yake yi.”

Mamie ta sake ɗaga hannu za ta ƙara marin sa.

“Ya isa haka, Hiyana.”

Dukansu suka juya suka kalli sama.

Daddy ne tsaye a bakin stairs. Ashe tun ɗazu yana kallonsu ba tare da sun ankara da shi ba.

A hankali ya sauko ƙasa, idanunsa na yawo a kansu.

Da ya iso gabansu, ya dubi Zannor.

“Me yasa kake son ɓata wa Mamie ku rai? Me yasa ba za ka yi koyi da ɗan uwanka ba? Yana yin komai ne domin ya faranta mata rai. Why can’t you do the same?”

Zannor bai kauce masa ba.

“Saboda ni na san abin da nake so da wanda bana so.”

Yana gama faɗin haka ya juya ya haura sama.

Mamie ta juya wajen Daddy cikin damuwa.

“Almustapha, ka ga wai ni Zannor yake maida wa magana? Ni yake ganin ina cutar da ɗan da na haifa? Yana ganin ina tauye wa Muhammad haƙƙinsa, alhalin kare shi nake yi.”

Daddy ya jawo ta jikinsa yana lallashinta.

“Ki yi haƙuri. Zannor har yanzu akwai sauran yarinta a tattare da shi.”

“Ko ma mene ne kuwa, wallahi ba zan taɓa amincewa da abin da zai cutar da lafiyar ɗana ba. Ka yi masa magana tun kafin in nuna masa fushina.”

Daddy ya shafa bayanta.

“Duk ba za ta kai ga haka ba, in sha Allah.”

Zannor da ya haura sama bai nufi part ɗinsa ba.

Kai tsaye ɗakin BK ya nufa.

Da ya shiga, ya tarar da BK zaune a gaban system ɗinsa, idanunsa ƙafe a kan screen ɗin, wani irin haske na farin ciki na bayyana a fuskarsa.

Jin motsi a bayansa ya sa BK ya ɗago.

Da ya ga Zannor ne, nan take ya miƙe cikin sauri ya nufeshi.

Ya rungume shi gam, yana buga bayansa cikin murna, bai ma lura da yanayin fuskar Zannor ba.

Zannor ma ya mayar masa da rungumar, amma zuciyarsa cike take da tambayoyi.

Me ya sa BK yake cikin wannan farin cikin?

A tausashe BK ya furta,

“Bro… sun yi accepting ɗina.”

Ya ɗan ja numfashi, murmushi ya ƙara faɗaɗa a fuskarsa.

“Kungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG sun yi signing ɗina. Yanzu na ga sun turo min saƙo ta email.”

Kalaman BK suka soki zuciyar Zannor.

Ya jima bai ga ɗan uwansa cikin irin wannan farin ciki ba. Sai dai a lokaci guda, wani irin tausayinsa ya lulluɓe shi. Domin ya san wannan farin cikin…
Ba zai daɗe ba.

Saboda ya san Mamie ba za ta taɓa amincewa BK ya bi wannan burin nasa ba.

A hankali ya ɗan matsa baya ya kamo kafaɗun BK.

“Congratulations, Bro.”

BK ya saki tsadadden murmushi.

“Thank you.”

Ya juya ya ɗauko laptop ɗinsa, ya buɗe email ɗin sannan ya miƙa wa Zannor.

“Duba ka gani.”

Zannor ya karɓa ya fara karantawa.

Dear Muhammad Almustapha… We are pleased to inform you…

Sai ya lumshe ido na ɗan lokaci, ya ɗaga kansa yana kallon BK.

“Gaskiya Bro… wannan babban mataki ne.”

BK ya sauke ajiyar zuciya.

“Tun jiya ban iya bacci ba saboda ina jiran amsarsu.”

“Yaushe suka turo?”

“Yanzu… mintuna kaɗan da suka wuce.”

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu.

BK ya zauna gefen gado yana kallon laptop ɗin da ke hannunsa.

“Ban yi tsammanin za su yi accepting ɗina da wuri haka ba. Tun farko video ɗina kawai na tura musu, suka buɗe amma ba su ce komai ba. Sai jiya na sake tura musu wani.”

Zannor ya zauna kusa da shi yana murmushi.

“Saboda sun san idan suka rasa ka, ba lallai su sake samun player mai irin talent ɗinka ba. You’re so talented, Brother.”

BK ya yi murmushi, amma bai ce komai ba.

Can Zannor ya ɗan gyara zama.

“Amma ka sanar da Mamie?”

Nan take yanayin fuskar BK ya sauya.

A hankali ya rufe laptop ɗin.

“Kai ne mutum na farko da ya sani. Amma zan sanar da ita… idan ta amince.”

Zannor ya zuba masa ido na ɗan lokaci kafin ya ce,

“Idan kuma ba ta amince ba fa?”

BK ya sauke numfashi.

“Zan yi addu’a Allah Ya sa ta amince. Domin wannan shi ne babban mafarkina… zama shahararren ɗan ƙwallon ƙafa.”

Zannor ya dafa kafaɗarsa.

“Allah Ya sa haka. Mu je mu yi wanka, sai mu je mu yi breakfast. Bayan haka ka sanar da ita. Dan Allah wannan karon ka tsaya kan matsayinka. Ka nuna musu cewa wannan mafarki ne da ka jima kana rayuwa da shi.”

BK ya gyada kai. Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya miƙe ya shiga toilet. Shi ma Zannor ya fita zuwa sashensa.

Zaune suke a dining table suna karya breakfast cikin nutsuwa. Kowa ya yi wanka ya sauya kaya.
Bayan sun gama ne BK ya ɗaga kai ya kalli Zannor.

Shi ma Zannor ya zuba masa ido, sannan ya ɗan gyada masa kai alamar,

“Yanzu ne lokacin.”

BK ya sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya.

A hankali ya ɗago ya kalli Mamie.

“Mamie…”

Ta ɗago kanta tana kallonsa.

“Na’am, Muhammad?”

Ya haɗiye yawu kafin ya ce,

“Nan da two weeks zan koma U.S.A.”

Dukkaninsu suka tsaya cak suka zuba masa ido. Mamie ta ɗan karkatar da kanta cikin kulawa.

“Wani abu ne na gaggawa ya taso BK?”

Ba tare da wata-wata ba ya amsa,

“Eh. Abin da na daɗe ina jira ne ya samu. Kungiyar kwallon kafa ta PSG ce ta yi accepting ɗina, sannan sun buƙaci na je domin yin medical, signing contract da kuma cika sauran ka’idojin da suka dace.”

Mamie ta ɗora haɓarta bisa tafin hannunta.

Idanunta suka sauka kan fuskarsa cike da tsantsar ƙaunar ɗanta da damuwar da ta saba ɓoyewa.

Ta ɗan yi shiru kafin ta furta cikin sanyin murya,

“Muhammad…”

Ya ɗago ya dubeta, amma bai amsa ba.

Ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da cewa,

“Ba zan iya amincewa da wannan tafiyar ba.”

Shiru ya mamaye dining ɗin.

BK ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.

Tun kafin ta yi magana ya riga ya yi hasashen wannan amsar. Sai dai jin ta fito daga bakinta ya fi masa ciwo fiye da yadda ya zata.

Daddy ya ɗago kai ya kalleta, amma bai ce komai ba.

Mamie ta ci gaba cikin sanyin murya,

“Ka san condition ɗinka fiye da kowa. Ba ƙaramin abu ba ne. Kana iya kasancewa lafiya yau, gobe kuma komai ya sauya. A irin wannan yanayin, ba zan iya barinka ka yi tafiya zuwa wata ƙasa kai kaɗai ba saboda wasan ƙwallon ƙafa. Gaskiya Muhammad… ba zan iya ba.”

BK ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya da tun ɗazu yake ƙoƙarin ɓoyewa.

Sai ya ɗan sunkuyar da kai.

A hankali ya furta,

“To shikenan, Mamie. Allah Ya sa haka shi ne mafi alheri.”

Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ƙara da cewa,

“Bari in ɗan fita waje… akwai kira da zan amsa.”

Ya miƙe tsaye.

Ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ɓoye damuwar da ta cika zuciyarsa, tare da hana hawayen da suka cika idanunsa zubowa.

Da ƙyar ya juya ya fice daga dining ɗin, tafiyarsa cike da sanyin jiki.

Mamie ta miƙe da sauri da niyyar binsa.

Sai dai Zanaya ta dakatar da ita.

“Please, Mamie… kar ki bi bayansa.”

Mamie ta tsaya tana kallonta.

Zanaya ta ci gaba da cewa,

“A yanzu yana buƙatar ya kasance shi kaɗai. Yana buƙatar ya yi jinyar kalamanki da kansa.”

Mamie ta sauke ajiyar zuciya.

A hankali ta koma ta zauna.

Zanaya ta ɗan girgiza kai kafin ta ce,

“Ina tsoron ranar da Ya BK zai fara juya miki baya… kamar yadda ke ma kullum kike juya masa baya a duk lokacin da ya zo da burinsa.”

Ba ta jira amsa ba.

Ta juya ta nufi sashensu.

Zannor kuwa, wanda tun farkon maganar bai ce uffan ba, ya miƙe a hankali shi ma ya fice daga dining ɗin.

A falon yanzu sai Mamie, Daddy da Sima suka rage.

Sima kuwa ko kallonsu ba ta yi ba. Hankalinta gaba ɗaya yana kan wayarta, tana ta danna screen ɗinta tare da taɓe baki, alamar dai wannan rikicin bai shafe ta ba.

Nini kuma tun ɗazu ta bi bayan Zanaya, ita ma ta bar wurin cikin yanayin damuwa.


Zaune yake a ƙarƙashin katuwar bishiyar layinsu, bayansa jingine da jikin bishiyar, idanunsa sun kafe wuri ɗaya. Hannunsa na riƙe da ƙaramin dutse yana juyawa a tafin hannunsa ba tare da ya san me yake yi ba. Zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai, ba saboda Mamie ta hana shi cika burinsa ba, sai don ya san ba zai taɓa cimma burinsa ba har abada matuƙar yana son faranta mata rai. Yana ji yana gani, mafarkin da ya jima yana yi na ƙoƙarin suɓuce masa.

A daidai lokacin ne Waheeda ta dawo daga Islamiyya.

Allonta na hannunta, tana tafiya a hankali tana rerawa karatun da malaminsu ya ƙara musu.

Lokacin da ta ƙaraso bakin bishiyar sai ta hango shi zaune. Mamaki ya kamata, tana tambayar kanta, “Shi kuma me ya kawo shi ƙarƙashin bishiya ya zauna?”

Cikin natsuwa ta ƙarasa bakin bishiyar ta tsaya tana kallonsa, tana nazarin yanayinsa. Cikin ’yan dakiku kaɗan ta fahimci yana cikin damuwa.

Ba tare da ta ce komai ba ta zauna gefensa tana ajiye allonta a ƙasa. Shiru ya ratsa tsakaninsu. Ba wai bai san da zuwanta ba ne, sai dai ba ya cikin yanayin biyewa surutunta da tsiwarta.

Suna zaune cikin shiru, babu wanda ya kula ɗan uwansa. Ta ɗauki ƙaramin kara ta fara zana layi a cikin yashi.

Cikin nutsuwa da sassanyar murya, tamkar ba ita ba, ta ce,

“Ka san me yake sa bishiya take girma ta zama babba?”

BK da ke fama da damuwar da ta mamaye zuciyarsa bai amsa ba.

Ta ci gaba.

“Saboda ta na tsayawa duk lokacin da iska mai ƙarfi ta zo.”

Sai a lokacin ya ɗan juya kansa ya kalleta.

Har yanzu idanunta na kan yashin da take zana wa.

Ita ma ta ɗan kalle shi kafin ta ce,

“Da zarar bishiya ta ce tana tsoron iska, to ba za ta taɓa yin inuwa ba.”

Ya yi shiru yana ci gaba da kallonta.

Ta ɗan yi murmushi ganin har yanzu idanunsa na kanta.

“Ni ba wani karatu na yi sosai ba, hasalima na tsani makaranta. Amma rayuwa ta koya min wani abu.”

Ta ɗauke idanunta daga kansa tana ci gaba da zanenta.

“Mutum idan yana gudun abin da yake so saboda yana son faranta wa wani rai, to tabbas wata rana zai tsinci kansa yana rayuwar da ba tasa ba.”

Wani irin faɗuwar gaba BK ya ji. Kalamanta sun bugi zuciyarsa kai tsaye.

Ta ci gaba da maganarta, hankalinta kwance.

“Ka san meye?”

Yana kallon kyakkyawar fuskarta ya girgiza kai alamar bai sani ba.

Ta ce,

“To akwai lokacin da Ummah ta ce sam ba zan yi talla ba. Ita ta fi so in tafi boko ba kakkautawa. Ban nuna mata bana so ba, haka na yi mata biyayya har hankalinta ya kwanta. Amma daga baya, saboda in cika burina na fara talla, sai da na yi sanadiyyar da aka kore ni a makaranta aka bani hutun makonni.”

BK da yake kallonta cike da mamaki ya ce,

“To me yasa?”

Ta ɗaga kafaɗarta.

“Saboda in cika burina. Ba ga shi yanzu ina talla ba? Idan ina son abu, ina bin duk wata hanyar da ta dace domin in same shi.”

Ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama saurarenta ya furta,

“Ba komai yake da sauƙi ba.”

“Ah ah.”

Ta faɗa da sauri.

“Sai dai idan mutum ba ya ƙoƙarin cimma burinsa. A lokacin ne zai ga komai yana da wuya.”

BK ya sunkuyar da kansa. A hankali ya ce,

“Ba kowa ne yake da ikon tsayawa kan abin da yake so ba.”

Waheeda ta yi murmushi mai jan hankali wanda ya ƙara mata kyau.

“Ni ma ba ni da iko.”

Ya ɗago ya kalleta.

Ta nuna ƙirjinta.

“Amma ina da zuciya.”

Sai ta matso daf da shi ta ɗora hannunta kan ƙirjinsa cikin rashin wata damuwa irin ta yarinta.

“Kai ma kana da ita.”

Ta ci gaba da cewa,

“Mutane za su iya hana ka tafiya, za su iya hana ka magana, za su iya hana ka abubuwa da yawa… amma kar ka bari su hana ka cimma burinka.”

BK ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta. Yarinya ce ƙarama a gabansa, amma kalamanta suna da nauyin da ko manya da yawa ba sa iya furtawa.

A hankali ya tambayeta,

“Wa ya koya miki irin waɗannan maganganun?”

Waheeda ta yi murmushi mai cike da natsuwa. Ta koma gefe ta ɗauki allonta ta rungume a ƙirjinta.

“Idan rayuwa ta yi ta dukan mutum, ko yana so ko baya so, tana koya masa abubuwan da babu su a cikin littafi.”

BK ya yi shiru yana kallonta. A karo na farko tun bayan fitowarsa daga gida, ya ji wata irin nutsuwa da ƙarfin guiwa suna fara shiga cikin zuciyarsa. Ya kasa yarda cewa wannan ƙaramar yarinyar ce ta faɗa masa kalaman da suka kwantar masa da hankali. Yana kallonta ne cikin mamaki, yana tambayar kansa daga ina take samun irin wannan hikima duk da ƙuruciyarta.

Follow me for more interested chapters 😍🥰🤌🏻