CHAPTER 19
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA TARA
Habib na ta magana ya ji shiru, hakan yasa ya tabbatar da cewa ba lafiya. Ba shiri ya tafi gidan, yana ta sallama, Farida ba ta san yana yi ba. Faɗawa ɗakin Sufyan ya yi, ya tarar da shi a sume, ga wando a gefe. Cikin tashin hankali ya fita ya je ya sanar wa a gidan su Sufyan. Ko da ya je, Abba Shuaibu baya nan, duk sun tafi kasuwa, sai su Momi.
Ba shiri Momi ta nufi gidan Inno da Mama ta sanar musu.
Habib ya koma gidan, ya fito da Sufyan, yana ƙoƙarin fita da shi kenan sai ga Farida ta fito. Cike da mamaki ta bi Habib da kallo, domin duk a tunaninta ba za ta yi tunanin abin zai kai ga haka ba.
“Subhanallah, me ya faru?”
Daidai lokacin shigowar su Mama da Inno kenan.
Inno na kallonsa, hijabi a karkace, ta kau da ido tana taɗewa da hannu ta ce, “Wa iyazubillahi, ya haka tsirara? Ku taimaka a yafa masa wani abu, a suturta hamza mana.”
Da sauri Mama ta janyo ɗankwalin da ke kan Farida ta yafa masa tana, “Maza ki ɗauko mayafi ki zo.”
Farida jiki a sanyaye ta je ta ɗauko hijabi ta zura, ta bi bayansu, zuciyarta na bugawa, tsoronta kar a ce ta yi silar kashe Sufyan.
Suna zuwa asibitin emergency aka karɓe shi, aka duba shi, aka masa allurai, sai da ya ɗau wajen minti ashirin kafin ya farka.
Da Farida suka fara haɗa ido, take ta yi ajiyar zuciya tana hamdala a ranta.
Mama ta ce,”Alhmadu Lillah, Sannu Sufyan.”
Inno ta ce, “Maddallah, ya farka. Sufuyanu, yane? Me ya cije ka a hanzaƙa haka?”
Baki ya mutu, binsu da kallo kawai Sufyan yake, ya gagara faɗin komai, domin har a lokacin yana jin sauran raɗaɗi.
Momi ta karasa daf da shi tana, “Sannu ko.”
Gyaɗa kai kawai ya yi.
Habib ne ya shigo yana faɗin, “Yawwa, ka farka? Yanzu likita ke sanar min da cewa akwai yiwuwar wani abu ne mai dafi ya cije shi a wajen, amma yanzu an yi masa allurar duk wata kariya, ba wata matsala in sha Allahu. daman ya ce in sanar da shi in ka ta tashi” ya karasa maganar yana fita.
Inno ta kalle shi cikin yanayin tausayi ta ce, “Ya Illahil Alamina, kai kuma Sufuyanu, ƙaddararka a hanzaƙarka take. Haka fa lokacin kana yaro, cinnaka ta taɓa maka a wajen, ka dunga tsala mana kuka, sai da aka yi maka allura. Ince ba ka sa ɗankanfan ciki ne?” Ta faɗa tana ƙasa da murya daf da shi.
Sufyan ya kau da kai, don ba ta Inno yake ba, shi kaɗai ya san halin da yake ciki.
Ganin hakan yasa ta taɓe baki tana ƙara ƙasa da murya, “Kar ka damu, dole in shiga Terminus in kwaso maka na gwanjo masu kyau masu kwari da karƙo, daga yau wani abu ba zai ƙara cizar maka hanzaƙa ba, bare su nakasa ka.”
Tana ƙarasa maganar, likita da Habib na shigowa ɗakin.
Ƙara duba shi ya yi, ya masa sannu, sannan ya ba su takardar magungunan da za a ƙara siya, sannan ya ce za su iya tafiya gida yanzu.
Godiya Habib da su Mama suka yi masa, zai fita kenan Inno ta dakatar da shi da faɗin, “Kai ɗan nan, ya ka mana.”
Likitan na dawowa, ta je daf da kunnensa tana faɗin, “Ince dai hanzaƙar Sufuyanu ba ta gama mutuwa ba?”
Dariya ce ta kusan subuce wa likitan, ya daure kafin ya girgiza kai yana, “Aa Baba, kalau, in ya sha magani shikenan.”
Dogon numfashi ta ja kafin ta ce, “Alhamdulillah, Allah ya yi ma albarka, na gode ko.”
Mama ta ce, “Inno, mu fara gaba ko sai su Farida da Habib su fito da shi motar.”
Inno ta gyada kai, “E, kwarai, mu je mu.”
Habib ne ya miƙa masa hannu ya tallafa masa, ya sauka a gadon. Ya kasa haɗa ƙafafuwansa, a wage yake tafiya. Farida ta sheƙe da dariya tana, “Gayu, an ji jiki, an dawo ’yan kaciya, sannu ko.”
Kwafa Sufyan ya yi yana binta da kallon tuhuma. Ta wuce su abinta ta ƙarasa wajen motar, tana buɗewa.
“Yawwa, sannu fa ku tawo a hankali ko?” Ta faɗa tana kunshe dariya.
Ya shiga ya zauna. Ita ma Farida ta shiga, bajewa ta yi a kan seat ɗin, gashi daman ita ba kaɗan ba, har sai da ƙafafun Sufyan suka haɗe ya saki ƙara, “AAAA! Wayyo, wayyo Allah na!”
Ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe ƙafafun.
Farida ta ce, “Subhanallah, sorry, don Allah ban san na matse ka ba, sannu ko.” Ta ƙarasa tana matsawa gefe.
Inno da ke gefen Sufyan ta ce, “Ke dai Faridatu, Allah ya yi miki albarka. Miji ba lafiya, duk kin rude, haka ake so ai. Allah ya ƙara muku so da ƙauna, kuma ya sauke ki lafiya.”
Ana zuwa Terminus, Inno ta ce a sauke ta, za ta yi siyayya. Da ke Plateau Hospital suka je, haka kuwa aka sauke ta, su suka ƙarasa gida.
Suna zuwa Habib ya tallafa wa Sufyan ya shigar da shi. A falo ya baje, ya gwale ƙafafu akan doguwar kujera tamkar sabon ɗan kaciya.
Mama ta kalli Farida ta ce, “Ya kamata ki shiga kitchen ki dama masa ko da kunu, ko sai ya samu ya ɗan sha magungunan.”
Ba musu Farida ta je kitchen ta dafa masa kunu, ta fara kawo masa. Ya karɓa ya sha, sannan ya sha magungunan.
Sai da ya ƙara samun wani barcin kafin su Habib da Mama suka bar gidan.
Ganin dangi ana ta zuwa dubansa ne yasa Farida zama a falon. Sai can yamma ya farka yana yatsina fuska.
Farida ta kalle shi ta kyalkyale da dariya tana, “Ka ga manya masu karyar iskanci, yau ma ai sai ka kirata ta zo ku kwana ko? Sai ta yi jinyarka da kyau?”
Cikin fushi Sufyan ya ce, “Ki zauna cikin shiri, baki ci bulus ba.”
Farida ta yi murmushi, “Ai babu buƙatar wani shiri, kawai a ci gaba da gashi. Yanzu dai ka ji da kanka ɗan kaciya, sannu ko.” Ta tashi tana ɗaga masa gira.
Sufyan har cikin ransa ji yake kamar ya cakumota, ya shaƙeta ga wata irin tsanarta da ya ƙara ji ta turnike masa a ƙirji.
Sai can yamma Sufyan ya shiga ɗakinsa. Ko da ya shiga, lalube ya fara yi ko zai ga abin ya cije shi, amma bai ga komai ba, don hatta gajeren wandon nasa sai da ya laluba.
Inno kuwa da ta sauka a Terminus, wanduna gajeru na maza ta kwasowa Sufyan har kala goma. Da daddare ta ba wa yaron ɗan’uwan Sufyan ya kai wa Farida ta wanke masa kafin ya fara sawa.
Karɓa Farida ta yi, ta je daidai ƙofar ɗakin Sufyan ɗin ta jefa masa, “Ga komutsanka, ɗan kamfenka nan daga Inno.” Ta juya abunta ta koma ɗaki.
Farida na ɗakinta har ta kwanta, sai ga kiran Inno tana, “Yawwa Faridatu, ince dai Sadiq ya kawo saƙon ɗan kamfen Sufuyanu?”
Farida ta amsa da, “E Inno, har ya tafi ma.”
Inno ta ce, “Yawwa, ki maza ki wanke masa cikin daren nan, ga su nan wadatattu ne guda goma, yana sawa domin kaucewar husumar wani dafin. Kar ku yi wasa fa. Ke kuma, ya cikin naki? Dazu hankali tashe, ba kwance ba ko lura ban ba.”
Farida ta ce, “Lafiya lau.”
“Ba zan ce lafiya lau ba, ba ki ga wani canji ba? Ko motsi bai yi? Kodayake ai ciki sai ya kai wata shida yake fara motsi, lokacin da za ki fara zuwa awo asibiti ko?” Cewar Inno.
Farida ta ce, “Inno, wallahi ban sani ba.”
Inno ta ce, “To, to, na manta ai da ke na fari ne, ba komai kika sani ba. To, ki tabbatar dai kina shan rubutun nan da sauran magungunan, kuma ki shafa a cikin.”
Farida ta amsa to, don jin jawaban Inno take kamar kaya ta zaku ta kashe wayar.
Inno na katse wayar ta taɓe baki tana, “Oh, yaran zamani sai rawar kai kawai, amma ba a iya komai ba.”
Sufyan sai da kwana biyu bai je School ba, sai dai Farida ta je ta dawo ta same shi, ana yi wa juna kallon-kallon.
Yamma misalin ƙarfe shida, Habib ya zo wajensa, suka zauna a ɗakin ƙofar gidan suna shan iska suna hira. Wayar Sufyan ta fara ƙara, kallon wayar ya yi ya saki tsaki ya ajiye ta gefe.
Habib ya ce, “Ya dai Sufy? Ba kiranka ake ba?”
Sufyan ya ce, “Falila ce fa, wai za ta zo, ita ba ta san halin da nake ciki ba.”
Cikin sigar zolaya Habib ya ce, “Ba ta san kana nan kana jinya ba, wato ita fa Farida ta san kan tsiya, ita gaba ɗaya a wandonka take kare lamuranta. In ba a yi wasa ba, sai ta nakasa ka fa.”
Sufyan ya girgiza kai yana, “Bara in gama warewa, za ta san na fita sanin salon mugunta.” Ya ƙarasa maganar yana kwafa.
Daidai lokacin da Farida ta dawo kenan daga School din zata shiga.
Habib na kallonta ya ce, “Yawwa, na manta fa, dole gobe ka daure ka shiga School don mutuniyar taka ta ba da presentation, kuma duk wanda ya yi missing akwai kura. Group ɗinmu ɗaya, mun gama tsara komai da waɗanda za su yi, kai kawai attending za ka yi, tunda ba ka da lafiya.”
Sufyan ya ce, “Ban gane akwai kura ba, ka san fa ni duk bana lamuran nan, lokacin exams kawai nake zuwa wajen lecturers mu gama.”
Habib ya ce, “Ai su daban, ita daban, shi yasa na ce kawai ka daure ka zo ɗin.”
Sufyan ya girgiza kai, “Shikenan, Allah ya kaimu.”
Washegari da sassafe Farida ta tafi School, don tana da wasu classes ɗin kafin na su Sufyan. Shi kuwa sai wajen 1 ya shirya ya tafi, saboda sai 2 ne suke da ita.
Suna zaune dukansu a filin School, students da yawa ta ko ina, duk sun fito. Masu sallah na yi, masu cin abinci na yi. A gabansu daman Farida ta wuce Computer Lab.
Sufyan na ganinta, ya je daidai gadar kwalbet ɗin da dole sai ta bi. Ya sa kwali, sannan ya zuba ƙasa a saman kwalin yadda ba za a gane ba. Kuma gadar daman tana daidai tsakiyar inda ɗalibai suke, gaba da baya. Kuma daman gashi ta kasan gadar ruwan datti ne makil, Ya janyo Habib, suka tsaya kan gadar suna hira, yadda dole sai ta bi ta can ɗin.
Da sauri ta tawo kenan, ba ta ko kallon gabanta, sai jin kanta ta yi, “Tim!” Sai da wani irin sauti ya fita, da duk ’yan wajen idanunsu suka yo kanta.
Ji ta yi kanta na wani irin juyawa, tana ganin dishi-dishi…
I