MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 15

by @mrsisham12

MATUƘAR INA RAYE
(As long as I’m alive)

Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp

Page 15

BK ya ci gaba da kallonta na wasu dakiku ba tare da ya ce komai ba. Karo na farko a rayuwarsa ya ji kamar akwai wanda ya fahimci abin da yake ji ba tare da ya yi masa dogon bayani ba.

A hankali ya saki ɗan murmushi, murmushin da tun fitowarsa daga gida ya manta da shi.

Waheeda ta zaro ido.

“Laa… ashe kana iya murmushi?”

BK ya ɗan yi dariyar gefen baki.

“Me yasa kika ce haka?”

Ta ɗan turo baki gaba.

“Tun da na san ka kullum fuskarka kamar ta wanda aka ci wa bashi.”

Yana ɗan langwabar da kansa ya ce, “Shi wanda aka ci bashinsa ba ya murmushi ne?”

“Tabb, ba ya yi mana. Ka ga nima haka na ke yi. Idan aka ce in bayar da bashin kosai ko wani abu, to sai in haɗe fuska in ce bana bayarwa. Mutane sam ba su san mutunci ba, kana ba mutum bashi, sai ya fara zille maka.”

“Uhmmm, lalle kam. Yanzu yaushe za ki koma boko?”

Ta ɓata fuska.

“Ranar Litinin Baba Karami ya ce.”

Yadda take ta surutu babu kakkautawa ya so ya sa shi dariya. Bai ɗauka tana da surutu har haka ba. Ya ɗauka abin da ta fi ƙwarewa a kai shi ne rashin kunya da tsiwa. Amma yau, lokacin da suka ɓata tare a ƙarƙashin bishiya, ya fahimci wani ɓangare na Waheeda wanda in ba ka zauna da ita ba, sam ba za ka fahimce ta ba. Za ka yi ta kallonta a matsayin yarinya mara jin magana da tsiwa, amma yau ta nuna masa kyakkyawan halinta wanda ba kowa ya san da shi ba ta hanyar maganganunta masu kwantar da hankali da ƙarfafa gwiwa tare da rage damuwa.

Maganganunta masu hikima da natsuwa sun tabbatar masa da wannan kalmar Bature da ake faɗi, “don’t judge a book by its cover.” Ya tuna irin baƙin cikin da ya fito da shi daga gida, ya kuma tuna yadda cikin ’yan mintuna kaɗan wannan ƙaramar yarinya ta sauya yanayinsa.

A hankali ya miƙa hannu ya ɗauki ƙaramin dutsen da yake ta jujjuyawa tun dazun.

Ya jefa shi can nesa. Sai ya ɗaga kai ya dubi sararin sama.Numfashi mai nauyi ya sauke.

“Na gode, Waheeda.”

Ta yamutsa fuska.

“Saboda me?”

“Saboda kin sa damuwar da nake ciki ta ragu.”

Ta ɗan yi shiru, sannan ta miƙe tsaye tana ɗaukar allonta.

“Ni ai ban yi komai ba.”

Ta gyara allon a kafaɗarta.

“Na tuna maka ne kawai cewa mutum bai kamata ya daina tafiya ba saboda wani ya ce hanya tana da nisa.”

Kai ya gyada sannan shi ma ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa.

“Shikenan, mun zama abokai?”

Da sauri ta dube shi ta ce, “Ah ah, babu ruwana. Ummanmu ta ce min ba a yin abokai da maza, sai dai ka zama Bestie na.”

Dariya ce ta so kubuce masa jin shirmenta. Ko mene ne bambancin Bestie da aboki, oho.

Ya furta, “To duk abu ɗaya ne ai.”

“Ba abu ɗaya ba ne. Bestie kamar babban yaya ya kasancewa, kuma aboki a wani ɓangaren yana iya zama bangon jingina a duk lokacin da Bestie ɗinsa ta shiga mawuyacin hali, kuma abokin shawara. Shi kuma aboki kawai dai aboki ne, ba shi da wani matsayi.”

Jim ya yi yana nazarin kalamanta da suka kasance masu ba shi mamaki, ya ce, “Shikenan, yanzu mun zama Besties kenan?”

Ta girgiza kai alamar a’a, ta miƙo masa ƙaramar yatsar hannunta ta ce, “Sai mun ƙulla ne za mu zama real Besties.”

Sarke ƙaramar yatsarsa da tata ya yi yana kallonta tana ta murmushi.

Ta ce, “Daga yau mun zama Besties.”

Ya ɗan yi murmushi yana cire yatsarsa ya ce, “Na gode. Ki samu ki shiga gida, kar a fara neman ki.”

A haka suka yi sallama, ta yi tafiyarta har ta shiga gida ba ta juyo ba. Ya sauke numfashi sannan ya shiga gida shi ma, yana jin ransa fes.

Shiru ta yi tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi sosai, tare da kai kofin shayin hannunta baki ta kurɓa kaɗan. Domin har ya fara yin sanyi saboda labarin da take bayarwa ya hana ta maida hankali wajen shan shayin da suka ba ta.

Sani ya ce, “Tirkashi! Lallai akwai ayoyin tambaya masu yawa akan Waheeda. Shin tana komawa boko? Kuma sannan burin mahaifiyarta ya cika a kanta na son ta yi karatu?”

Murmushi ta yi kaɗan ba tare da ta ba shi amsa ba, ta dubi wanda ta kira da Baba dazun ta ce, “Baba, ka ga har shayin ya huce ba tare da na ƙarasa muku labarin ba.”

“Kar ki damu yarinya, yanzu za a ƙara miki wani.”

Sake cika mata kofin aka yi. Ta sha kusan rabin kofin kafin ta ajiye shi a ƙasa tana lumshe idanu.

Baba ya furta, “Yarinya, wannan labari na ki ya sanya ni cikin zurfin tunani. Wato wannan ahalin nasu Waheeda, duk da sun kasance talakawa marasa ƙarfi, amma ba su kashe zuciyarsu ba, sun zaƙe ƙarfe suna rufawa kansu asiri.

“Sannan na lura tabbas akwai wani abu dangane da yarinyar. Zai iya yiwuwa tana da ɓoyayyen baiwa ko kuma dai wani abu na daban. Na ji ta burge ni matuƙa, duk da kasancewarta yarinya fitinanniya, amma akwai basira tare da hikima da ɗan ƙaramin wayo. Akwai haske da yawa a rayuwarta. Za ta kasance yarinya mafi rayuwar jin daɗi a wannan ƙarnin, domin kowa ta san yadda za ta bi ta zauna da shi duk da ƙananan shekarunta. Misali, yadda ta cire wannan matashi a cikin damuwa. Me ma ki ka ce sunansa?”

Ya tambaye ta sunan ɗan ya manta.

Ɗan murmushi ta yi ta amsa da, “BK…”

“Yawwa, shi. Tabbas na ji a jikina akwai wani abu mai kyau tsakanin su. Waheeda za ta matuƙar taimaka masa, musamman a halin ciwon da yake fama da shi da kuma ƙarfafa masa gwiwa. Na san za su samu rayuwa mai kyau, irin wadda suka cancanta, musamman ita yarinyar. Shigowarsa rayuwarta yana da nasaba da za su yi kyakkyawar rayuwa tare da juna.”

Girgiza masa kai ta yi tana jin hawaye na ciko mata idanu.

“Ah ah, Baba. Daga wannan lokacin ne ma komai ya rincaɓe, komai ya tarwatse ya lalace.”

Ci gaban labari……


Tsaye ta yi a kanta tana girgiza kai don ta rasa abin faɗa. Tun dazun da take filin gida ta yi tsammanin Waheeda ta gama shiryawa, ta fito daga banɗaki, ashe ba je wa ma ta yi ba, ta kwanta tana sheƙa bacci.

“Amma ke kam an yi ja’irar yarinya. Kin sani sarai yau Monday kuma tare da yayanku za ku je makarantar nan, shi ne ki ke kwance ko? Yayi kyau, Allah ya kawo shi ya tashe ki ta hanyar da za ki fi tashi.”

Da sauri ta miƙe zaune tana rarraba idanu jin sunan Baba Ƙarami. Tun tsayuwar Ummah a kanta ta farka daga baccin da take yi, amma ko buɗe idanu ta ƙi, sai da ta ji sunan dodonta.

Ta shagwabe fuska. “Ayyah Umma, ai bacci barawo ne fa, ya saceni. Yanzu zan shirya.”

Ci kanki, Ummah ba ta ce mata ba, sai akwatin da ta buɗe ta fito da kaya a cikin baƙar leda. “In kin gadama ki saka kafin Allah ya ba shi ikon shigowa.”

Ledar ta buɗe. Nan ta ga sabbin uniform ne a ciki da Ummah ta ba Salma ta ɗinko mata, ga kuma sabbin sandals ɗin roba a ciki. Tana tura baki gaba ta saka kayan. Tana ƙoƙarin sanya hijab ne Ummah ta zuba wa kirjinta ido ta furta

“Cire rigar nan, ki fara sa singlet.”

Don ta lura da yadda kirjinta suka fara tasowa suna girma, fito mata da wata sabuwar vest ta yi ta miƙa mata ta sanya, kana ta mayar da rigar ta.

Ta saki murmushi. “Masha Allah, kin yi kyau sosai, Mamana.”

Sai a sannan ta saki murmushi ta zo ta rungume Ummah.

“Ina sonki, Ummanaa.”

“Nima ina sonki. Yau kin cika shekara sha huɗu. Allah Ya ƙara miki shekaru masu albarka, Ya tsawaita rayuwarki cikin ƙoshin lafiya da imani. Allah Ya kiyaye ki daga dukkan sharri, Ya cika rayuwarki da farin ciki, nasara da kwanciyar hankali. Ya ƙara miki ilimi, hikima da kyawawan halaye. Ya sa kowace sabuwar shekara ta rayuwarki ta kasance mafi alheri fiye da wadda ta gabata.”

“Ameen, Ummanaa.”

Ta ɗagota a jikinta tana kallon fuskarta.

“To zauna anan, bari in kawo miki kayan karyawanki. Shayi na dafa miki, sai biredi . Nasan kina son shayi da biredi ko?”

Kai ta gyada mata kawai tana ta kallanta, tana kallon yadda mahaifiyarsu take ta faɗi-tashi a kansu don kawai rayuwarsu ta yi kyau. Wannan ya sa Waheeda ba ta da wani buri da ya wuce in ta girma ta yi kuɗi ta siyawa Ummansu danƙareren gida, ta zuba mata ’yan aiki a ciki.

Ba a daɗe da fitarta ba ta dawo, hannunta riƙe da kayan shayin da ta faɗa. Tana cikin karyawa ta ji muryan Baba Ƙarami suna magana, shi da Salma. Cikin sauri ta ƙarasa karyawar da take ta miƙe ta fito a ɗakin.

“Ina kwana, Baba Ƙarami.”

Dago kai ya yi ya ɗan kalle ta. Gani ya yi tayi wani kyau na musamman yau, uniform ɗin ya mata kyau sosai. Amsa mata ya yi yana faɗin

“Mu je ko?”

Sallama suka musu sannan suka fice daga gidan.


Zaune suke a cikin falon duk sun yi shiru cikin taƙaitaccen jimami, domin tun da Zannor ya sanar da su abin da yake faruwa, suka bukaci ganinsa don ji daga nasa bangaren.

Ya Mutallab ne ya miƙe tsaye ya soma kai-kawo a cikin falon cike da takaici ya furta

“Yanzu shikenan kana ji kana gani za ka rabu da mafarkin ka? Wai tsaya ma, kai kam menene abin da yake damunka, Muhammad? Mamie fa ita ta tsuguna ta haife ka, me ya sa ba za ka buɗe baki ka faɗa mata abin da kake so da wanda ba ka so ba? Wannan fa rayuwarka ce, kuma dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa. Idan ka bari ya suɓuce maka, ba na tunanin kuma za ka iya samun wata.”

Ya Abdul-Samad da Ya Jalal suka jinjina kai na amincewa da zancen Ya Mutallab dari bisa dari.

BK wanda tun shigowarsa falon bai ce komai ba, yana zaune ne a kan kujera yana kallon ƙasa. Maganganun Ya Mutallab suna ratsa masa zuciya ɗaya bayan ɗaya, amma bai samu ƙarfin buɗe bakinsa ba.

Ya ɗaga idanunsa a hankali ya kalle su ukun.

“Ba wai bana son faɗa mata ba ne.”

Ya Mutallab ya tsaya cak, ya juyo ya kalle shi.

“To, me kake jira?”

Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya.

“Ban san yadda zan faɗa mata ba.”

“Me za ka ce mata da har ya zama abu mai wuya haka?” Ya Abdul-Samad ya tambaya cikin sanyin murya.

BK ya ɗan karkatar da kansa.

“Ba ni da ƙarfin guiwar yin hakan ne. Ba zan iya jayayya da Mamie ba, bana son ɓacin ranta. Duk abin da take yi tana yi ne saboda lafiyata.”

Ya Mutallab ya matso kusa da shi ya zauna a kujerar da ke gefensa.

“Ka saurare ni, Muhammad. Ba wai muna son mu matsa maka ba ne. Amma ka san abin da nake gani? Kana barin tsoron ka ne ya mallaki rayuwarka. Ka san abin da kake so, ka san abin da ba ka so, amma saboda tsoron ɓata wa Mamie rai sai ka yarda ta zaɓa maka rayuwar da kai ba ka zaɓa ba.”

Muhammad ya haɗe hannayensa.

“Amma ita ɗin mahaifiyata ce, Ya Mutallab. Ba za ta taɓa yin abin da zai cutar da ni ba. Ta sadaukar da abubuwa da yawa saboda ni da kuma lafiyata. Shi ya sa nake jin kamar duk abin da zan yi zai zama kamar na ci amanarta.”

Dafe kai duka suka yi, sun rasa ta ina za su bullowa al’amarinsa. Sun rasa yaushe ne zai tsaya wa kansa da mafarkansa.

Ya Abdul-Samad ya girgiza kai.

“Ba cin amana ba ne ka faɗa mata gaskiyar abin da ke cikin zuciyarka. Cin amana shi ne ka yi shiru ka yarda da abin da ba ka so, sannan daga baya ka fara zargin ta da lalata maka rayuwa.”

Muhammad ya ɗaga kai ya kalle shi.

“Na riga na yanke hukuncin yin resigning kawai.”

Ya Jalal cikin ɗaga murya ya furta

“What! Kana da hankali kuwa?”

Mai Martaba, da yake saukowa daga stairs sanye da farar jallabiya, ne ya saki murmushi ya ce

“Ya  kuke so ku takurawa yaron nan ne? Ya riga ya faɗa muku hukuncin da ya yanke. Why can’t you support him in that?”

Riƙe kai Ya Jalal ya yi kafin ya iya faɗin

“Abbah , anya wannan yaron naka lafiyarsa ƙalau kuwa? Ya kamata a duba kwakwalwarsa a ga ko ta samu matsala. Ni ban taɓa ganin inda mutum bai da ra’ayin kansa ba, sai dai a dinga tsara masa rayuwa ba.”

Ya faɗa yana miƙewa da nufin barin wajen, don ya rasa me zai kuma cewa.

Da sauri BK ya riƙo hannunsa cikin yanayi na sanyi irin na sa ya furta

“Please, kar ka tafi.”

Komawa ya yi ya zauna ba tare da ya ce komai ba. Mai Martaba ya zauna a kujerar gefen BK yana dafa kafadarsa.

“Ina tare da kai a duk hukuncin da ka yanke a rayuwa. Kuma a duk halin da za ka shiga, kar ka manta kana da Kawu da ’yan uwa da suke sonka.”

Lumshe idanunsa ya yi tare da faɗin

“Na gode, Uncle.”

Mai Martaba ya ɗan saki murmushi.

“Ina goyon bayanka. Komai zai faru, kar ka taɓa juya wa Mamie ka baya matuƙar a kanka take yin komai, ba wai dan cutarwa ko saɓawa addini ba. Ka bi ta sau da ƙafa, akwai lada a tare da hakan. Yayyunka ba za su gane ba, ba su tashi da mahaifiyarsu ba. Ni na san akwai lokacin da komai zai zo ƙarshe da za ka tsaya wa kanka da kanka. Kawai lokacin ne bai yi ba. Amma yanzu ka ɗan jira kaɗan, kar ka yi gaggawar tura musu resignation letter.”

Jinjina kai ya yi yana gode masa, don ya matuƙar jin daɗin kalamansa.

Yau ce ranarta ta farko a makarantar a matsayin sabuwar malama. Tana zaune a ajin da take koyarwa JSS 2 aka tura wani ɗalibi ya kirata daga ofishin principal.

Bayan ta je ta amsa kiran ne ta ɗauki hanyar komawa ajinta. Nan ta bi ta hall ɗin da aka yi jarabawa, idanunta ne suka sauka kan yarinya a cikin hall ɗin, ta kifa kanta a benci ita kaɗai a ciki babu kowa.

Da sauri ta shiga ciki tana tsayawa a kanta tare da dafa kafadarta.

“Lafiya kuwa? Me yake damunki? Tashi ki zauna.”

Da ƙyar Waheeda ta iya ɗaga kai ta kalle ta sannan ta zauna da kyau tana share hawayenta.

“Masha Allah,” ta furta a ranta lokacin da idanunta suka mata arba da kyakkyawar fuskar Waheeda.

A fili ta furta

“Me ya same ki?”

Waheeda wacce kamar za ta sa kuka ce

“Tun dazun ƙasan cikina yake min ciwo sosai.”

Ɗan nazari ta yi kafin ta ce

“Sannu kin ji. Dama yana yi miki ne?”

Ta girgiza mata kai alamar a’a. Wannan ne karon farko.

“Tashi tsaye mu ga.”

Ba tare da tunanin komai ba ta miƙe a hankali. A tare idanunsu suka sauka kan jinin da ya bata inda take zaune.

Wani irin zaro ido Waheeda ta yi ta toshe bakinta da tafukan hannu, kawai ta sa kuka tana faɗin

“Wayyo na shiga uku! Na zauna akan ƙusa ya yanka min mazaunaina!”

Sosai ta ba ta dariya, amma sai ta danne don ta san a wannan lokacin tana buƙatar a kwantar mata da hankali ne, ba a sa ta a gaba ana dariya ba.

Zama ta yi a gefenta ta soma ce mata

“Kar ki yi kuka. Ba fa ciwo kika ji ba, girma ne ya zo miki. Ko wace mace tana ganin wannan duk wata. Wannan ba fa damuwa ba ce, kin ji? Kyawawa kuka ba ya musu kyau. Yanzu faɗa min, menene sunanki kuma ina ne gidan ku?”

Dakatar da kukan da take yi ta yi. Jin ba ciwo ta ji ba sai a sannan ta ke tuna karatun malamin Islamiyyarsu da yake musu na cewa kowace mace tana al’ada. Amma da yake lokacin ba ta fahimta ba, sai a yanzu da ta ji maganar da ta yi mata. Tana share hawaye ta ce:

“Ni sunana Waheeda S. Baffah, gidanmu ba yi da nisa da makarantar nan.”

Ta saki murmushi.

“Ni kuma sunana Husna, sabuwar malama. Yanzu kin ga ba zai yiwu ki koma gida haka ba. Ga rigar sanyi na, ki saka sai mu je gidana ki gyara jikinki. Amma gidana yana da nisa sosai da makarantar nan”

“To, ke ɗin aina kike?”

“Kina tsoro ne kar in siyar da ke?” Husna ta faɗa cikin raha.

Kasancewar an kusa tashi yasa ba ta samu matsala wajen karɓan uzuri ba a ofishin principal. Bayan sun fito ne ta tara musu napep suka tafi gidan da take. Tun da suka zo Waheeda sai kalle-kalle take.

Tun da suka zo gidan, Waheeda ta yi shiru. Ba irin shirun da mutum yake yi saboda rashin abin faɗa ba ne, akwai wani irin yanayi a tare da ita da ya sa Husna ta kasa cire idanunta daga kanta.

Husna ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga, ta ɗauko mata wasu kayan da za ta saka da pad da sabbin pants sannan ta dawo.

Zama ta yi cikin nutsuwa ta yadda Waheeda za ta fahimce ta. Ta faɗa mata yadda za ta gyara jikinta ta kuma saka pad ɗin.

Waheeda ta karɓa tana kallon kayan.

“Zan iya amfani da banɗakinki?”

Husna ta saki murmushi tana kallon yarinyar, don tana tuna mata kanwarta da ta rasu, ta ce

“Eh mana, shi ya sa na kawo ki.”

Ta nuna mata inda toilet yake kafin ta koma falon.

Bayan ’yan mintuna Waheeda ta fito. Ta zauna a gefen kujera tana kallon ƙasa, hannayenta a haɗe.

“Maza karɓi ki sha.”

Husna da ta zauna ta faɗa tana miƙa mata kofi mai ɗauke da tea a ciki.

Bayan ta karɓa ta soma sha ne ta ji Husna na tambayarta

“Waheeda, kin taɓa zuwa gidan Malaman ku haka kafin yau?”

Girgiza mata ta yi tana faɗin

“Ah ah, yau ne karon farko.”

“To me ya sa kika biyo ni, ba kya tsoron zan iya cutar da ke?”

Tsura mata manyan idanunta ta yi kafin ta hau saman kujeran tana daura hannunta a saman kirjin Husna, daidai saitin zuciyarta. Ta dawo da idanunta kan kirjinta tana kallo.

Duk da ba ta san abin da take shirin yi ba, amma ta kasa dakatar da ita, sai dai zuba mata idanu da ta yi tana son ganin abin da take shirin yi.

Waheeda ta dago ta dubenta ta sakar mata murmushi.

“Malama, zuciyarki ba za ta iya cutar da ko da ƙaramin dabba ba, balle mutum. Fara ce ƙal, kuma tana ɗauke da kyakkyawar niyya. Babu komai a tattare da ita sai jini da ya lullube ta.”

Da mamaki haɗe da tsoro take kallonta. Ta yi saurin ture hannunta daga kirjinta.

“Ta yaya aka yi duk kika san wannan? Ta yaya kike iya ganin zuciyar mutum da iya idanunki biyu, ko dai mayya ce ke?”

Cewar Husna, don al’amarinta ya girgiza ta. Waheeda da jikinta ya yi sanyi ne ta koma mazauninta tana girgiza kai.

“Malama, nima ban sani ba. Ban san abin da yake faruwa da ni ba yau ɗin nan. Haka kawai nake jin wani baƙon yanayi a tare da ni. Ban sani ba ko idan mutum yana ganin zuciyar mutane maye ne.”

Jikinta ne ya yi sanyi. Ta ji ba ta kyauta ba na saurin jifanta da kalmar mayya da ta yi lokaci guda, amma ba laifinta ba ne. Ko wani ne, abin da zai zo masa a zuciya kenan. Ta yaya za a ce tana iya ganin zuciya haka siddan?

“Ba haka nake nufi ba, kawai na tsorata ne. Amma dama tun baya kina ganin haka? Sannan kina iya ganin kayan cikin mutum?”

Girgiza mata kai ta yi.

“Yau na fara gani, sannan iya zuciya kaɗai nake iya gani.”

Ajiyar zuciya ta sauke tana gode wa Allah jin ta ce iya zuciya take iya gani. Haka nan ta ji ta samu sauƙi. Ta ɗan yi shiru tana kallon Waheeda wadda ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen rigarta.

Husna ta ɗan yi shiru, idanunta suna kan Waheeda kamar wadda take son gano wani abu a tare da ita.

“To kafin yau, kin taɓa jin irin wannan yanayin da kika ce kina ji?”

Waheeda ta ɗan yi tunani kafin ta girgiza kai.

“A’a. Sai yau da cikina ya fara ciwo. Tun dazun nake jin wani abu kamar… kamar ba ni kaɗai ce nake gani ba. Wani irin zugi idanuna suke min.”

Husna ta daɗe tana kallonta.

“Me kike nufi?”

Waheeda ta ɗaga kafaɗunta.

“Ni ma ban sani ba. Wani lokacin idan na kalli mutum sai na ji kamar akwai wani abu a jikinsa da idona yake son gani. Amma ban san me yake ba sai da kika bari na taɓa ki.”

Husna ta sauke idanunta zuwa hannun Waheeda.

“Hakan na nufin sai kin taɓa mutum?”

Kai ta gyada.

“Eh.”

“Duk lokacin da kika taɓa mutum, kina iya ganin irin abin da kika gani a tare da ni?”

“A’a. Yau ne kawai na gane hakan.”

Husna ta sake yin shiru.

Ba ta san abin da za ta ce ba. Abin da yarinyar ta faɗa ya fi ƙarfin abin da za ta iya ɗauka da wasa. Amma kallon Waheeda ya sa ta fahimci cewa ba ƙarya take yi ba. Idanun yarinyar cike suke da tsoro da ruɗani, kamar ita kanta tana neman wanda zai gaya mata abin da yake faruwa da ita.

“Waheeda.”

“Na’am?”

“Ki yi min alƙawari ba za ki sake gwada wannan a kan wani ba.”

Waheeda da take jin cikinta na ɗan murɗawa ne ta dube ta ta kau da kai.

“To, amma me ya sa?”

“Saboda ba ki san abin da za ki gani ba. Kuma ba ki san yadda mutumin zai ɗauki abin da kika faɗa masa ba.”

Waheeda ta ɗan yi tunani sannan ta gyada kai.

“Shikenan.”

“Ba za ki taɓa kowa ba saboda kawai kina son ganin zuciyarsa.”

“A’a.”

Husna ta yi murmushi kaɗan.

“Madalla.”

Shiru ne ya gifta tsakaninsu kafin Waheeda ta katse shurun ta hanyar faɗin

“Malama, babu kowa a gidan ne? Tun da muka zo ban ga kowa ba. Ina ’yan’uwanki?”

Murmushi ta yi tana ɗauke idanunta a kanta ta ce

“Ni kaɗai nake rayuwa a gidan nan.”

“Ke kaɗai kuma? To me ya sa? Kina da aure ne? Ina mijinki?”

Dafe kai ta yi.

“Wayyo Allah! Wai dama haka kika kware a iya tambayoyi?”

Tura baki ta yi tana kurɓan shayin a hankali.

“Ni fa kawai so nake na sani. Na ga babu wanda ya leko tun shigowar mu.”

Follow me for more interesting chapters 🥰😍🤌🏻