RU'UYAA (The dreams we never lived)

2. ...a mafalkina...🖋️

by @autum17



Free page
      



'' Albishirin ki tuwo " Mama ta furta tare da dakatawa da shafa min ruwan shinkafa a kai tashi zaune nayi ina kallon ta kafin in kalli Asma'u dake riƙe dariyar ta hmm...ban yarda da su biyun ba amma sai nace ''goro'' ina kallon Mama cike da ƙoƙonto, basarwa tayi tace '' Yau tuwon masara za'ayi da daddare!" zaro ido nayi baki sake ina kallon ta kafin kuma fuska ta,ta sauya kamar wadda ruwan sama sukayi ma duka, juyowa nayi na kalli Asma'u ta tuntsire da dariya ji nayi kamar in haukace '' Mama wane irin tuwon masara kuma?" na furta baki na rawa,na tsani tuwon masara a rayuwa gara tuwon dawa sau dubu 

tace '' tuwon masara dai da kika sani da miyar kuka!" dafe zuciya ta nayi kamar mai ciwon zuciya baƙin ciki na turnuƙe ni sosai fuuu na miƙe na shige ɗakin mu dake ɗauke da ledar da taga yaƙin duniya ta gode rabbi na kwanta saman gadon daya girme mu nida Asma'u ina risgar kuka,shekaran jiya da jiya duk wannan mugun abun mukaci shine kuma yanzu ma za'a dafa mana shi... share hawaye na nayi sai kuma na ƙara fashewa da kuka harda dukan gadon 

'' kada ki sabauta mana gado Dan Allah '' inji Asma'u tana cigaba da ayyukan ta...
da daddare bayan sallar isha'i zaune muke cikin duhu kafin Mama ta shigo da fitila a hannun ta ɗayan hannun riƙe da plate ɗin tuwo, ajiyar zuciya na sauke lokacin da ta ajiye plate ɗin tsakiyar mu ta zauna hannu suka zura su biyu suna ci niko na zuba musu ido 

'' bazaki ciba?" Inji Asma'u,Mama ta kalle ni, saida na harare plate ɗin sannan na zura hannu muka cigaba da ci kuma ba ƙarya abincin yayi daɗi sosai daga ƙarshe har da janye plate ɗin nayi na iyarda cinyewa na siɗe taɓe baki mama tayi '' ai na ɗauka da yunwa kike shirin kwana..dama kince cikin ki yayi ƙato...'' idona kamar zasu faɗi hakane fa! 

bana so ciki na yayi ƙato wasu lokuta abincin ma bari nake saboda hakan, daidai nan aka kawo nepa da sauri na miƙe na isa gaban mirror dake maƙale da tsohuwar wardrobe ɗin mu daga gefe kuma ƙaramar TV

tun kafin in ɗaga rigata naga yanda ciki na ya turo kamar me ciki, ihu na fasa Mama dai tayi zugum tana kallona kafin taja tsuki ta fita daga ɗakin daidai Asma'u data tafi wanke hannu ta shigo

jawota nayi da ƙarfi na tsayar da ita gefe bata cemin komai ba sai ma tayani ɗaga rigarta da tayi fuska a tsuke... kallon cikinta nayi gashi nan a ɗame kamar bataci komai ba...waist ɗinta ɗan ƙarami hips ɗinta manya tsabar yanda waist ɗinta yake gani nake kamar idan mutum ya riƙe da ƙarfi karye wa zai yi 

ƙwace rigarta tayi ta wuce ta kunna tv ta zauna bakin gado tana kallo,na kalli kai na a cikin madubi kamar wacce akayi ma albishir da mutuwa kife kaina nayi a saman table ɗin kwalliyar mu ina furta kalmar turancin dana fi sani '' why!" Ina kukan daba hawaye amma ciwon danake ji da gaske ne 

ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tana faɗin '' dama zaki kalli kanki yanda nake kallon ki,ina son yanda kike komai naki tuwo toh ke meyasa ba zaki karɓi kanki ba?" Sharply na juyo ina kallon ta da wani expression a fuska ta '' sauƙin faɗa ne dashi saboda bake kike fuskantar abinda nake fuskanta ba sannan bake kike jin yanda nake ji ba!" nayi maganar ina hararar ta,taɓe baki tayi kafin ta zare ɗan kwalinta gashinta ya fara walwalewa ya zuba har tsakiyar bayanta wani kuma ya zubo ta gaba 

sakin baki nayi ina kallon ta kafin na kalli nawa kan dake ɗauke da kitso all back '' why he!!!!" na sake furtawa ina dukan table ɗin bada ƙarfi ba '' why me ake cewa ba he ba,idan kika ce he kina nufin namiji kenan!" 

ɗago idona na nayi ina hararar ta'' to kun alijabe turatu uwar turai '' (queen Elizabeth)

'' bafa kun alijabe ba elizabe...'' kafin ta iyar na ɗauki powder na jefe ta dashi ya same ta a goshi '' idan ina turanci kada ki ƙara gyara min!" shafa wurin dana jefeta tayi tare da faɗin '' mugunta dai ba kyau!" kafin ta mayar da hankali tana kallon Chinese drama ɗin da ake yi

nima zuwa nayi na zauna kusa da ita muna kallo tare idan aka nuno wata ko wani mai gashi inyita santi,riƙo hannu na tayi ta ɗaura saman gashin ta ta kwantar da kanta saman cinyata '' ɗan shafa min kaina kinji!" tayi maganar a sheɗanan ce, kamar in ture kanta amma saboda yanda nake son gashi na kasa cike da jin haushi na dinga jan gashin muna kallo tare 

'' Tuwo xoki kwaso kayan da Asma'u ta shanya ruwa za'ayi!" Mama ta faɗa tana tattara kayan dake tsakar gida ta kai kitchen '' ga ninan tafe'' na bata amsa amma banida niyar tashi '' yaushe hadari ya taru? nasan yanzu zasuyi gaba da wutar su...'' Asma'u ta faɗa tana tashi daga jiki na,da takaici nace '' dan Allah kada kiyima mutane baki'' sannan na fita naje kwaso uniform 

Muna shigowa cikin ɗakin aka fara ruwa da mugun ƙarfi tule ma Asma'u kayan nayi a jiki ina faɗin'' ki lunke'' fara ninke kayan tayi na zauna kusa da ita mama a gefe muna kallo bayan na banko murya saboda ƙarfin ruwan baya bari aji magana...dama kuma dai ba turanci nake ji ba kawai kyaun mutanen da yanda suke tashi da kuma kayansu da gashin suke burgeni 

'' Tuwo rufe mana ƙofa feshi ake!" '' toh mama!" nayi amsa Batareda na tashi ba idona yaƙi barin TV'n duka mama ta kawo min nayi saurin tashi naje na rufe ƙofar ina turo baki dai dai ankawo wurin akshon (action) Asma'u tace '' ace kawai sai a ɗauke wuta?"

'' ta Allah ba taki b..'' kafin in iyar yan nepa sun warce wutar su, faɗuwa wurin nayi ina shure shure ina birgima ɗauke ƙafafunta Asma'u tayi tana sheƙa dariya '' mama kin gani yarinyar nan baƙin bakine da ita wallahi!" nayi miƙe na hawo gado

matsawa Asma'u tayi sanin tsaf zan kaimata duka cikin duhu mama tace '' kai banson shashanci fa!" tsawar da aka saki yasa muka ƙanƙameta,fitila ta lalubo ta kunna ta kalli Asma'u '' ke tashi kije ki ajiye kayan nan a closet!" kwasar kayan tayi tasa mana a wardrobe 

tsakiyar gadon na kwanta mama da Asma'u a gefe da gefe na bargo suka jawo kowa ya lulluɓe banda ni don na tabbar da wuri zan fara jin zafi ruwan suka ƙara ƙarfi 
sauka Asma'u tayi ta kashe tv da wuta ta dawo ta kwanta 

'' Mama Saida safe,tuwo sai da safe!" ''Allah ya bamu alkhair'' mama ta amsa '' Ameen '' mu biyu muka faɗa....

Bayan mun yi sallar asuba Asma'u ta shiga aiki kamar dai matar novel ta gaske tayi wannan tayi wancan,nidai na tsuguna bakin ƙofar ɗaki ina binta da kallo harda tagumi mama kuma tana kitchen tana haɗa kunu...kunu kawai mafa babu ƙosai...kai! zuciya ta kamar zata kama da wuta.. ɗauke idona nayi daga kallon su na koma tunanin mafalkin da nayi wai a cikin mafarkin,wani farin mutum mai baƙin gashi wanda bama ɗan Nigeria bane yake faɗa min yana sona...Ni Abeedahtuwo 😳 
harda sunan shi ya faɗa min amma dai na manta sunan dan shima bana yan Nigeria bane...dogon tsuki naja..in bacin da kwashe kwashen mafalki nida ko airport ban taɓa zuwa ba...ban masan hanyar ba ta ina zan haɗu da bature?

Kuma na tabbatar yana ganina zai juya yace anyi kuskure niba wannan na sani ba... 🙄! amma fa kalaman shi ɗin sun ratsa zuciya ta..duk da suma na manta su,wata rana nima dai insha Allah zan gano masoyina na gaskiya ..irin mazan novel ɗin nan masu tsananin kyau... murmushi mai kyau nayi harda rufe fuska ta kamar mai jin kunya...

Dan kam mijin novel da nake tunanin samu sai dai a mafalki ko a littafin...shine yasa wasu lokutan nake share awa da awanni ina hasashen yanda rayuwa ta zata kasance idan na samu irin wannan soyayyar...inyi ta tsara abinda zuciya ta tayarda bazai taɓa faruwa dani ba..amma kuma ina da damar ƙirƙirar tawa duniyar a cikin ƙwaƙwalwa ta inda nice sarauniya...bani da wani aibu... sannan duk wani abunda nake burin samu akwai shi a can...



 '' Mama yaudai shinkafa zakiyi ko?" na tambaya daga inda nake '' infa tuwo zan yi bazaki ciba?" 

'' kai mama dan girman Rabbi karki kiɓa mana wannan mugun abun!!" nayi maganar cikin magiya ina haɗa hannayena,bata ce komai ba

miƙewa nayi '' kada ki kuskura kizo nan babu takalma tunda ke bakijin ƙyanƙyamin taka wuri mai damshi!" 

takalmina na saka sannan nazo na tsaya daga gefe ina ƙara roƙonta kada tayi mana tuwon masara '' naji!" ta furta batareda ta kalle Ni ba

'' thanks You Mama!"

'' Tuwo bafa Thanks You ake cewa ba,thank you...idan kince thanks...ma yayi amma kada kice thanks da ƙara s daga ƙarshe kuma kice You a gaba mai makin exam zai faɗar dake!''

juya idona nayi kamar in kaima yarinyar can duka amma dai.  

ƙarasowa tayi ta ɗauki bokiti ta juye ruwan data tafasa ta wuce bayen mu na kara, ɗaki ta shiga ta ɗauko zanin ta sannan ta shige wanka kamar wadda ke canja fata saida muka gama kari sannan ta fito '' ai na ɗauka farar mace zamu gani bayan kin fito!" batareda ta kalleni ba tace '' toh ai saiki ajiye yanzu '' sannan ta shige ɗaki nan ma ta daɗe kafin ta fito cikin uniforms ɗin makarantar mu brown ɗin wando farar riga da hijabi kayan sun bala'in amsarta har suka fitar da shape ɗinta daya ke nan kamar irin na yar cartoon ɗin nan mema ne sunanta...uhm.. yawwa olsa ta cikin pirozin (frozen) haka shape ɗin Asma'u yake ƙirjinta cike kamar na yar cartoon ɗin nan,hakama hips ɗinta... gashinta ta taje kafin ta kitse shi kamar yanda olsa ɗin take kitse nata don makarantar mu idan tayi parking za'a ce acuci maza ne

sannan ta shafawa idonta da shape ɗinsu yake kamar na ƙwai kwalli wani irin sihirtaccen kyau tayi ta ɗauko lip gloss tashafawa pink lips ɗinta da suke ƙanana kuma acike masu shape kamar na M daga sama,hancinta kamar pencil... ba ƙaramin kyau tayi ba wallahi 

'' wannan kallo haka kada a cinye ni nidai!" juya idona nayi "kinyi kama da akuyar da aka yima kwalliya '' na furta kafin na iyar da shanye kunu na na miƙe,nima ruwan na juye na shiga na ɗauki zane nima na shiga bayen 

zuwa tayi ta ɗauki kunun ta tana sha Mama tace '' shi zuwa makarantar har sai anyi kwalliya?" ƙasa da idon ta Asma'u tayi zuciyar ta na dukan uku uku jin idanun Mama na yawo akanta...

Bayan minti goma na fito nima na shiga ɗaki na shirya cikin uniforms ɗina,naɗan riƙe rigata ta baya in gani ko akwai shape Babu abinda idona suka gani sai tulelen ciki da shafaffen ƙirji da ɗuwawu hips ɗin ma babu taɓe baki nayi kafin na kalli baƙin gashi na daya ke nan da mugun tauri tun kafin ma mutum ya taɓa..ya wani coge taƙi ma ya kwanta duk da anyi kitson 

sannan na kalli wuyana....yana da ramuka sannan da wani V shape a tsakiya sannan babu layi layin nan smooth yake,fuska ta cike da pimples musamman goshi na da haɓata da kuma kumatuna,hancina irin na Asma'u ne abu guda da muke dashi iri ɗaya 

Sai kuma na kalli girata kamar an aske hakama lashes ɗina wasu sunfi wasu tsawo suma dai kamar gashin kaina,daga ƙarshe na kalli ƙwayar idona da suke ash... mutane dayawa suna faɗin wai insa kontat glasses abun yake ko kanta leshi (contact lenses) amma naƙi...na farko ba muda kuɗi na biyu inason kalar idona...don yana tsorata mutane 

idanuna manya ne sosai shape ɗinsu kamar na mage, sun dace dani sosai...



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️