RIKON KA'KA

RIKON KAKA

by @rukyelmuaz

Rukayyat

(Rukyelmuaz)

RIKON KAKA 

 YOTA

Free page



Page 4




Tafiya  takeyi a hankali ta isa bakin ƙofar gidan. Ganin baƙar motar da taga anyi parking a ƙofar gidan ne ya tabbatar ma ta tabbas maganar Haisu gaskiya ce ga kuma glass ɗin motar a buɗe wannan ya bata tabbacin sarkin isa da izza ne a ciki.

Da ƙarfi tayi magana ta ce.  "To sarkin isa me gidan da babu cefa ne jirana kake saina fito na kamo hannunka na shigo da kai????????

Magana ya ji kamar da ga sama wanda hakan yasa shi lumshe manyan idanun shi  Golden Hazel Eyes. Wanda ya ke ƙarama fuskar shi kyau da kwarjini a idon duk wani mutum da zai haɗa ido dashi wanda ke saurin rikita zuciyar mata da yawa akan shi maganar da yaji ne yasa shi sakin wani kyakkyawan murmushi wanda ya yi sanadiyar bayyanar lotsawar kumatun shi dimple ɗin shi na duka gefe biyun ya lutsa kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar da cewa yaji daɗin wannan sautin muryar da yaji domin duk da rigima irin ta wannan Kakar tasu suna jinta a ransu fiye da tunani.

Ƙofar motar ya buɗe a hankali kamar wanda akama dole  kallon inda sautin maganar ya fito ya yi tare da sakin wani kyakkyawan murmushi da ya ƙara  fito da asalin kyau fuskar shi complete Masha Allah.


"Wannan ƙasar ta ƙofar gidanki nike tsoron ta ɓata min kaya kinga farin kaya ne kuma wannan ƙurar za ta iya sa ni tari ya yi maganar yana kashe ma Kaka ido ɗaya.

Buɗe baki tayi cikin mamaki ta ce..

 "Yo kai yanzu in ka mutu ba'a ƙasar za'a rufe ka ba zaka min iyayi irin naka. "Zaka shigo ne ko sai na zo da kaina na ɓata gayun naka tukunna???

 Ta ƙare maganar tana dariya shima a ɓarayin shi dariya ya ke wacce in ba ka lura ba baza ka ce wannan dariya yake ba.

Magana ya yi cikin yanayin tsokana ya ce " Kai kina son in janye miki (subsidy)ne cikin ya na yin rashina gane mai kalmar take nufi ta ce.

"Meye wani sabudi zaka shigo ne ko kuma in bar ka a wajen in koma gida"????? 

"Ha ha ha ha kyal, kyal".  Ya yi dariyar da saida fararen Haƙoranshi suka bayyana.

Wanda shi kaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki a duk lokacin da ya shigo garin Batsari yaga wannan rigimarmiyar  tsohuwar wacce ta rage musu kamar tsoka ɗaya a miya


Dariya mai sauti ya saki ya ce. "Ohhhhhhh na manta ke fa ba aikin gwamnati kike ba bazaki san girman abinda yake ƙoƙarin faruwa da ke ba".

Ya ƙare maganar ya sakin wata dariyar ƙasa ƙasa don yasan yanzu zatayi zuciya domin in akwai abinda tafi tsana shine jira.

Juyawa ta yi zata koma cikin gida ganin hakan ya sa Julaibib saurin ce wa." Jirani kafin ki ce na yi miki rowar samun tabarrakin kyakkyawan matashin saurayi kamar ni wanda a lokacin ku ba bu irin shi". Ya ƙare maganar ya na fitowa a hankali kamar wanda akama dole daga cikin motar  key ya sa ya kulle motan. Sannan ya fara takawa a hankali cikin natsuwa zuwa ga inda kaka ta ke.

Yanayin yanda yake tafiya kawai zai tabbatar maka cewa wannan akwai Izza da Isa tafiya ya ke yanda ka san yana tsoron ta ka ƙasa don kada ya faɗa ƙarƙashin ta ko don kada ƙurar gurin ta, ta ɓa mishi kaya.

Wani kyakkyawan murmushi ya sakarma Kaka wanda ya sa ta washe baki ita ma duk wani farin ciki ya gama rufeta.

 kallonshi ta ke a hankali da ga sama har ƙasa inda a zuciyarta take ce wa. Yaran zamani duk kun ɗauki iyayi kunsa a zuciya tun kuna jarirai kuke tsarface _tsarface har girmanku.

Maganar shi ce ta katseta da ga maganar zuciyar da take.

"Mu shiga cikin gida ko Amaryata ban saya wannan kwalliyar ba duk da na ga kin ƙara kyau"

Ko dai duk don nazo ne yasa haske na da kyauna suka zo gareki kika samu tabarraki.

Ya ƙare maganar yana riƙe hannunta suka shiga cikin gida.

Shigarsu ta yi dai_dai da fitowar Haisu da ga kitchen riƙe da man gyaɗa da barkono a hannunta da sauri ta mayar da hannunta bayanta.

Duk ta tsorata da ganin Julaibib da kaka zuciyarta ta shiga bugawa a hankali kamar wacce wani mugun abu ke shirin faruwa da ita.


Ganin yanda ta ke raba idanu yasa Kaka ta ce. "Hasatu me ye kike ɓoyewa?? Da sauri ta girgiza kai alamar A'a babu komi.

Ganin yanda take ƙara ɓoye hannun a bayanta ya tabbatar da cewa wani laifin ta aikata.

"Me kike ɓoyewa aka tambaya kika tsaya kina kallon muta ne kamar wacce akayi ma albishir da mutuwa Julaibib ya yi maganar kamar wanda yasan abinda ta aikata,


Buɗe baki tayi da niyyar zatayi magana amma kafin ta ce wani abu sallamar da akayi ya sa dukansu waigawa.



"Assalamualaikum". Aka ƙara cewa a karo na biyu hakan yasa Kaka saurin amsawa amma da mamaki wa zata gani. 

Matar da ko a masallacin juma'a suka haɗu basa gaisawa ko shiri da juna matar da duk inda ta zauna ɓata mata suna dana jikarta take yi matar da in akace wa tafi tsana a duniya zata iya nuna Kaka tace wannan nafi tsana.

Iya Mai Ƙosai ta maimaita a cikin zuciyarta.

Kallo ɗaya zakama fuskar Iya dake tafe Tukur na bin ta, a baya za ka gane cewar wannan tafiyar ba ta lafiya ba ce wanda hakan kaɗai sai da yasa gaban Kaka faɗuwa. Ba komi yasa gabanta  faɗuwaba face ganin kwalba uwar rubutun sharri tare da su wacce ta kasance jaɓa sa baki a bar miki wato Delu Mai Ɗan Wake.

Kallo ɗaya zakama Iya Mai Ƙosai ka san wannan dai a lokacin su an taɓa bariki bakin ya yi baƙi saboda shan sigari ga wani hujin hancinta da ya yi ƙato dashi ƙafafu duk sigari ta gama ƙone su.

Julaibib ya gaishe su cikin natsuwa Delu Mai Ɗan Wake ce kawai ta amsa gaisuwar ta shi amma Iya Mai Ƙosai komi ba ta ce ba.Face kallon banza da harara da take watsama dukan su ukkun da tazo ta iske a tsaye tsakar gidan.

Kallon Tukur da ke tsaye a bayanta tayi ta ce.

  " Zaka fito ne ko kuwa sakaran banza da wofi wanda yaba abun kunya baya tunda maza ka rako duniya gwara a baka zani da kallabi ka ɗaura domin babu ragon namiji sai ɗandaudu niko a sani kai ba shi ba ne." 

 Iya Mai Ƙosai ta ƙare maganar ta na janyo hannun Tukur ya dawo gaban ta ya tsaya.

Julaibib ya ce " Inna lafiya kuwa me ya faru??????         

    Iya Mai Ƙosai cikin isa da gadara ta ya tsina baki irin na tsofaffin ƴan barikin ta kalli Haisu dake tsaye tana turo baki tana zare ido kamar wadda tayima sarki ƙarya domin duk tsoro ya gama rufeta don ta san yau za ta sha faɗa gurin wannan basamuden mugun wanda ke zaluntar ta  Iya Mai Ƙosai ce ta katse ma ta tunanin da ta ke ta ce..     

 " Ku tambayi wannan ja'irar yarinyar me ido a tsakiyar kai yarinya sai ka ce rainon sheɗanu ke wannan Inaga ƴar Allah bani ko wani iri ne ina so.


Ran shi ya ɓaci akan furucin da tazo har gida tana yi Wani kallo ya ɗa go ido ya watsa ma Iya Mai Ƙosai wanda ba ita da ta yi maganar ba hatta Tukur dake gaban ta kallon da Julaibeeb ya yi saida ya sa shi ja da baya. 


Jin maganar da Iya Mai Ƙosai ta yi ne ya sa Kaka saurin  kallon Haisu da ke tsaye ta na raba ido hannunta har yau ya na bayanta taƙi fitowa da shi don kar aga abinda ta ɗauka.

Haisu ba yar Allah bani ba ce idan akwai abinda ta yi kamata ya yi ki faɗa bawai ki fara ai banta ta ba.


Cikin kwaɗayi da son jin abin da ya faru Kaka ta kalli Haisu ta ce "Me kuma ki ka yi???????

 Hankalin Haisu kwata kwata ba gurin ya ke ba domin ita tunaninta ɗaya ta ya zata samu hanyar guduwa agurin taje ta kaima Atika kayan da ta ɗauƙo in ya so in ta dawo sai ayi duk abinda  za'ayi.

Saida Julaibib ya da ka ma ta tsawa ya ce.   

"Wai ba magana ake yi ba"

 Tsawar da ya yi ne ya dawo da ita da ga tunanin barin gurin da ta ke wanda ya kusa sanadin tsayawar dodon kunnanta daga aiki da sauri ta turo ƙaramin bakinta ta ce " Tsokanata ya fa ra shine na ra ma" Kalmar ce Julaibib yake sake mai'maitawa a bakin shi "Tsokanarki ya yi kamar wannan shine zai tsoka ne ki" Julaibib ya ƙare maganar yana nu na Tukur da idon shi duk ya yi ja saboda murzawa ga ƙaramin kumburin da fuskar shi ta yi.

Delu Mai Ɗan Wake ta yi caraf ta amshi maganar ta ce " In banda neman rigima ta wannan yarinyar ina ita ina faɗa da namiji ai shi namiji uba ne ko ba a gidanku yake ba shi garkuwa ne ta ƙare maganar ta na kallon Haisu.

Kaka ta ce duk ba wannan ba  Delu tunda kin rako su yanzu a samu wani ya yi min bayanin abinda ta aikata.

 Tukur ya yi saurin fara magana ya ce. " Daga naje siyan gyaɗa gurin Mairo shine kuɗi na basu kai ba na ce ga abinda ke hannuna zan kawo ma Mairo cikon kuɗin, "Shine fa suka fara zagina ita wannan harda ce wa.....Ni ɗan iska ne ina tare yara a shagon chaji ina ɗaga musu riga sannan ina taɓa musu Nono" shine don na ce zan kaita ƙara gurin kakarta kafin in juya ta watsamin jar miya a fuskata.


Kaka da Julaibib lokaci ɗaya suka kalli Haisu dake tsaye guri ɗaya har lokacin da sauri ta fa ra girgiza kai alamar karya ya ke ta ce.

"Ƙarya kake in kai ɗan iska ne kawai ka fito fili ka faɗama Mai Ƙosai ce wa iskanci ka ke a shagon chajin naka bawai kazo zakamin sharri ba". Haisu ta faɗa tana ƙare mishi kallon banza.


Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Iya Mai Ƙosai ta buga salati ke yarinya ƙazafi zakima jikana wannan wace irin shegiyar yarinya ce" Ta ƙare maganar tana nuna Haisu da Hannu.

Julaibib ya ɗan waiga kamar wanda akama dole ya kalli fuskar Tukur yaga yanda idon ya yi ja ya ce.

 “Eyes are not something to joke about have you been to the hospital????? Tukur kallon Julaibib kawai yake don shi fa iya hospital kawai ya fahimta a maganar shi.


Domin shima duk uwar ɗarin ce bawai zuwa school ɗin ya ke ba in ma ya je ta katanga yake guduwa  ganin bai fahimci abinda ya ce ba ne yasa Julaibib ya sake maimaita masa. " Ka je, Asibiti ne????

Da sauri Tukur ya girgiza kai alamar "A'a"  Julaibeeb ya sauke wa ta a jiyar zuciya wanda na kusa dashi ma zai iya jin sautin domin haniyar da aka fa ra ya sa kan shi ma ya fa ra ciwo kwata kwata ya ƙosa su bar gidan.

A hankali Kaka ta ce too munji na ka bayanin amma ai ba'a yanke hukunci da ɓarayi ɗaya don haka itama Haisu a barta tayi magana. Da sauri Haisu ta buɗe baki ta ce.


"Kaka wallahi....." Julaibeeb ya yi mata wani kallo da dole yasa ta haɗiye maganar da zatayi


"Wallahi kika yi wa ta magana a gurin nan saina zaneki ". Ya faɗa yana kallon ta ya juya ya kalli Iya Mai Ƙosai ya ce.


"Please Hajiya kiyi haƙuri yanzu bari inje in kaishi, Asibiti don a duba idon nashi amma don Allah kuyi haƙuri.

Insha Allah ni da kaina zan ja ma ta kunne hakan bazai sake faruba kaima kaja girmanka kaji.

Kaka  da sauri ta ce kai ko aida ka bari itama munji ta bakinta Julaibib ya ce.       "A'a anyi musu laifi inda ta makanta shi fa??.Ya yi maganar a kasalance

Kaka ta kalli Iya Mai Ƙosai ta ce "tooo kuma haka ne don Allah kiyi haƙuri yaran yanzu ne sai dai addu'a". Amma kuma ai Haisu ba mahaukaciya ba ce da zata fa ra tsokanar shi shima yanzu saiya bata haƙuri ko???

"Nooo kawai suyi haƙuri shine abinda ya iya furta wa.    Julaibib sake kallon su  ya ce , "Kiyi haƙuri Hajiya bari yanzu in kaishi Asibiti"


Da sauri Tukur ya ce "Ai zan iya zuwa da kaina mai gida ko kuma Iya ta rakani da kanta.

Julaibib ya fahimci me Tukur yake nufi yakan yasa ya fiddo wallet ɗinshi dake aljihun Rigar shi ya ciro kuɗi ba ta re da ya duba ba ya bashi.   

  "Kaje Asibiti fa kar kayi wasa da idonka!      


Julaibib ya bashi kuɗin tareda yi mishi kashedi 

Iya Mai Ƙosai ta ce, "Angode yaron kirki mai hankali amma a ja ma ta kunne sosai.

Julaibib ya amsa da "shikenan"

 Domin duk wannan tsayuwar a takure ya ke yinta maganar duk damun shi takeyi duk ya kosa su fita ya je ya kwanta.


Godiya Iya Mai Ƙosai takeyi taƙi tafiya har saida Tukur ya ja hannunta suka fita. Fitar su keda wahala Delu ta ce " Sai a bani kaso na tunda ansamu abun arziki"

Wani kallo Iya Mai Ƙosai ta watsa ma ta, ta ce

 "Wai me ya sa bakida imani ne yanzu ko tausayin yaron bakiyi to Asibiti aka ce ya je kuma can zai tafi a duba idon shi.

Delu ce ta rike baki kamar wa ta sakara ta na bin iya me Ƙosai da kallo sai kuma ta sauke a jiyar zuciya ta ce " Au ni za'a wa sa tare ci ban,ban to ai gobe ma rana ce"

Ta ƙare maganar tana jan koɗaɗen hijabinta ta ƙara gaba. 

Iya Mai Ƙosai ta kama hannun Tukur suka wuce. 

Julaibib ya kalli Haisu ya ce " 


Wuce ki koma cikin gida ai sai kin fita sannan zaki jawo fitinar ko to bazaki fita ko nan da ƙofar gida ba in ko ki ka fita ki tabbatar saina zaneki."

Babu gardama ta juya ta shiga ɗaki kaka da Julaibib suka bita a baya ɗaki su ka shiga Kaka ta zauna kan kujera tana kallon bakin ƙofa.