Chapter 32
by @smauta
Balain kunyar shi takeji shiko ko a jikinshi tafiya yayi dakin shi yabarta nan dan shi mutum ne mai karantar halin mutane yagane sarai tana bukatar space kamar jira takeyi kuwa yashige itama tayi dakin halim da tsiya tsiya ta tasheta kuwa wai me akayi ne kikeman wannan tadin to ki tashi mana ni kadai a gidan ba abokin lbr nan suka bata lokaci sunata firar makarantar su har bayan azahar sannan manar ta ankara ba wanka bare sallah,manar ta riga halim shiga wanka hakan yaba halim damar fitowa parlour ta nemi abinda zata saka a cikinta..............
Kicibus tayi da daddy shima ya fito da sauri taje ta rungume shi daddy ina wuni,shafa kanta yayi yanajin son diyar tashi daya tilo kintashi lfy?have you eat?a'a yanzu na fito ummi ce ta tasheni ma nibanyi niyyar tashi ba,har cikin ranshi yaji wani irin matsanancin dadi jin halim ta kira manar da ummi rayuwar turawa yasaba da diyar sa baya ɓoye mata komai nashi haka itama.............
Tea yake zuba mata sannan yace ki kira tailor dinki ta kawoma manar kaya sai ku zaba wane takeso komai da komai batada kaya sosai a gidan nan kallon daddy tayi eh babu ammm daddy dama inaso muyi mgn samun wuri yayi suka zauna a tare menene,inaso zan koma school exams dina nan da 8 days ne,jimmmm yayi kina bukatar wani abu??
Ehh daddy banida kudi da kudin ne nayi booking flight na zuwana da komawa sai tayi shiru, Flight din naki yaushe ne jibi ne 7pm manar tasani?a'a karki kuskura ki fada mata school zaki koma kinaji na ko amma daddy meyasa bazataji dadin zaman gidan nan ba idan bakyana kuma bazan barta ta koma china ba inaso semester ya kare zatayi transfer tadawo nan Abuja........
Ya zance mata knn zakije wata kasar yin wani abu daga baya kina iya fada mata gaskiya cigaba da bata lbrn matsalar data taso mashi a Lagos yayi,kaiii daddy ya kamata kaje da kanka mutanen nan bawani kirki ne dasu yeah i know my daughter gobe 7am zanbi Flight idan nagama naga zan iya dawowa gobe zan dawo idan ba zan dawo ba kuma sai nan da 3days, lokacin daddy na tafi ka dawo goben dai,idan nagama zan dawo nima banso a barta ita kadai a gidan nan,ina rokon wata alfarma daya dan Allah daddy ka siya mata waya kuma tanason ta dinga magana dasu kaka itama...............
Duk abinda take needing daga yanzu zuwa lokacin da zaki tafi ki saka mata order danaje officer zansa treasurer ya saka maki kudi ki kula da kanki a duk inda kika samu kanki koda bana tare dake ki tuna Allah a ko ina yake ki rike tarbiyyar dana baki karki zama kece sanadin kuka na a duniya kinsan fadi tashin danayi akanki,ko da wannan inaso ki tuna idan kin tuna sai ki duba wace makoma zan koma idan wani abu kika bari ya faru dake ki rike Allah dakuma addu'a a ko ina kike muna tare dake..............
Sai taji wani farin ciki ya lullube ta koba komai ta mori mahaifi rungume juna sukayi idanunta cike da kwalla yasan kukan me takeyi,ki tashi kije wurin ummin ki zanje officer idan abubuwan da zanyi covering dayawa bye,koda ta shigo dakin sallah manar keyi itama wankan tashiga ta fito saida suka dawo parlour tace albishirin ki,da sauri tace gori fari kallllll daddy yace a siya maki waya da kayan da kike bukata zo kigani dame dame kike bukata na kayan sawa tailor dina tanada kaya ready-made zata kawo maki...................
Kusa da halim ta zauna tsoron Allah ya kamata ganin tsaruwar kayan kai halim wannan kayan ai sun tsada hahahahaa wayyo inama nice daddy yaba wannan damar ummi kinsan wa kike aure kuwa daddy fa kudi ba matsala bace wurin shi ki zaba nidai kasa daukar kayan tayi halim tashiga picking kayan ba abinda bata daukar mata ba kaya kala kala kayan bacci kuwa har saida suka kusan fada dan gaba ɗaya wasu ƴan iskan kaya take zabar mata bana kirki a ciki,sunfi two hours ana selecting kayan...................
Muyi sallah laasar saimu fita kiyo sabon simcard nifa jibi tafiya zanyi ummi ina zakije kuma???? Maldives ta bata ansa kai tsaye me zakiyi acan kinsan ina cemaki inason fara business daddy ya bani kudi zanje in duba abubuwan da zan iya saidawa ana nan abuja har na siya ticket dama shiru nayi ban fada maki ba naga hankalin ki ba'a kwance yake ba yanzu duk tafiya zakuyi ku barni??????wayance mata halim tayi ahhh daddy yana nan fa a'a lagos zai tafi gobe murmushi tayi lagos indai daddy ne zaki ganshi ya dawo a goben danma lagos nan kusa idan kinajin yunwa ki ƙarancin abinci bari nayi sallah saimu fita ko kin ki ko kinso kuma wlh iPhone zan siya maki nasanki kin tsani iPhone 😂😂😂😂😂
Daga inda sukayo simcard shagon waya suka wuce iPhone 18 ta siya mata kafff Nigeria nan shagon kadai ya fara kawota a abuja,itadai manar ba abinda takeyi sai aikin kallo har bayan isha sannan suka dawo gidan halim ke driving manar na rike da wayar tana duba cikinta settings takeyi abinda zata iya akan wayar koda suka iso gida a tare suka shigo da gogan,gaban manar ya fadi ganin ya fito daga mota hakanan taji kamar bata kyauta ba fitar da tayi ba tareda izinin shi ba...............
A tare suka fito tana rike da ledar ice cream dinsu ita kawai yake kallo halim tace daddy sannu da zuwa ciki ta wuce tabar su nan kasa gaba tayi bare tayi baya a hankali ta tako har gaban shi ina wuni dan Allah kayi hakuri na manta ban fada maka zamu fita ba munje siyan waya ne zata miko masa wayar kawai yace shiga ciki...........