BABAN KAWATA

Chapter 33

by @smauta

Section din daddy abinda kunnenta yaji knn tana shigowa kin karaso muje zugum zugum tabi manar har hanyar dakin gogan taga sun nufa dakin dake kusa da nashi taga kaya baje makil halim wai badai kayan da aka siya dazu bane har sun kawo wannan kayan sunmani yawa wallahi kinga ki rufaman asiri umarnin mai gidanki nidai nake bi,to akai su can dakin naki mana🙄😳kofar ta maida ta rufo ummi nan ne dakin ki bakiga yana kusa dana daddy ba saifa kin saki jikinki nan gidan ki ne nan kuma better place daya kamata ki zauna kina kusa da daddy dan Allah karkiman muzo kawai kizo mu bude kayan nan zan saka maki komai inda ya kamata.......





Cigaba da shirya mata kayan halim tayi saida ta gyare dakin nan tsaf hatta kayan shafa saida ta jera mata su dakin yayi balain kyau ga wani taragon turarukan wuta duk ta siya mata ita dai tana zaune tsoron Allah ne ma ya kamata wai duk shine ya bada kudin wannan hidimar duk wani abu da mace ke bukata saida aka siyo mata shi sun dade a dakin motsi mai ƙarfi bata iyayi saidai taitabin kawar tata da ido..........







To nagama nawa aikin sai ladar ina ice cream din yana fridge a parlour muje to yawwa baki bani number da zan samu su kaka ba duka harda taki,halim ta bude jakarta wayarta ta ciro number daddy ta fara saka mata sannan ta jude sai tata,kinga ashe Prince ya kikkirani aifa ba sabunba😂😂😂kawata kina cikin soyayya kedai bari saifa kuna taroni................






A tare suka fito parlour ba kowa a parlour sai karar AC ice cream dinta halim ta dauka ta bama manar nata to ni zan shige daga ciki kuma karki biyoni kuma ki tashi ki tafi dakin ki idan kuma parlour zaki zauna to ga abinci nan naga sun gama idan zakici kije kici daddy ma lokacin cin abincin shi yayi kinga tafiya ta tunda ke komai saina fada maki yadda akeyi dariya tayi ita kanta maganar halim gskia ne komai fa sai an nunamata ice cream din ta ta bude tana sha hankalinta kwance tama manta dawani cin abincin shi................






Motsin tafiya taji yasa ta dago kanta gyara zamanta tayi akan kujera ko inda take bai kalla ba ya wuce dinning shinkafa da stew ne dan yatsina fuska yayi irin na masu kudin nan bayajin zai iya cin shinkafar nan yanzu kitchen yanufa duk tana kallon shi taga dai komai an kawo a dinning ko yana bukatar wani abu ne tashi tayi tabi bayanshi kamar munafuka ta rangada da sallamar ta bai ansa ta ba yana tsaye gaban gas gefe ta koma ammm dama ga abincin ka nan a dinning ko kana needing wani abu??kamar zai ansa kamar bazai amsa ba yace NO🙂‍↔️..............








Bai kara kulata ba duk sai taji ba dadi custard taga ya dauko da sauri tazo gabanshi ka kawo na hada maka dan Allah kayi hakuri sakar mata robar custard din yayi ya fice a kitchen bata wani bata masa lokaci ba ta fito a tunanin ta zata same shi parlour kashh sai taga akasin hakan,ba tareda da tunanin komai ba tabi hanyar da zata sada ta da section dinsu tafiya take kanta tsaye har kofar dakin knocking tayi daga ciki yace who's there?manar ce come in...................







Yana kan sofa dake dakin tashigo table ta fara kawowa gabanshi sannan ta dora tray din custard gefe ta tsaya kimmm laptop dinshi dake kan cinya ya kashe mika mata yayi da hannu biyu ta karba har inda yake ajiye ta takai mashi duk wani moves nata idonshi nakanta,dan balain custard din ya farasha bai tabajin dadin custard kamar wannan ba,ganin batada niyyar zama yace mata have a seat...............






Nago bai barta ta karasa ba yace meyasa kika fita?kanta ta saddar kasa cikin zafin zuciya ya kalleta look at me jin muryar shi cikin fushi yasa ta kasa dagowa i said look at me a hankali ta dago idonta ta sakashi cikin nashi sannan yace oya answer me banida waya ne kuma bansan ina zan ganka ba kayi hakuri dan Allah bazan kara ba wani sanyi ya tsara shi jin yadda take begging dinshi kuma tayi accepting laifinta.............






Daga yau ko ina nan ko bana nan duk inda zaki saka kafar ki ki fita ki tabbatar kin fadaman kuma ki daina saka karamin gyalen nan irin na dazu idan zaki fita inada kishi kan abinda nakeso karki tunzurani kisa zafin kishi na yasa nayi abinda zanzo nayi nadama manar ina sonki banso ko kuda ya tabaki balle har ki fice a haka kowane kazami na kalleman surar matata kuma halaliya na kinmani adalci kenan????







Wayar hannunta take wasa da ita dan Allah kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba side hug ya bata kamar jira takeyi kuwa tayi luff cikin jikin dattijon taaa😹have you eat?ya katse shurun nasu a'a meyasa bakyason cin abinci wani abu na damunki?a'a ki dinga cin abinci da wuri kafin dare yayi kinji ko kidaina cin abinci late night yanasa katon ciki banaso naganki da katon ciki idan ba na haihuwa ba..........







Kunya ta kamata ta jawo kallabin ta tana rufe fuskar ta baki daina wannan kunya kunyan naki ba ko kwata yayi duk ranar dana kamaki sorry kiddo😉ya kashe mata ido guda da sauri ta tashi ta cigaba da tattare table din hannunta ya rike gudana kikeyi daga na fada gaskiya????





Ta kasa magana kamar wacce za'a cema kyarr ta ruga tray din hannunta ya ajiye ya fuskance ta sosai saboda nayi maganar haihuwa shine zaki gudu?ko nayi tsufa da haihuwa?baki ansa ni ba bakinta kamar zatayi magana amma ta kasa hade jikinshi yayi da nata to KINA SONA?da sauri ta dago suka hada ido dan Allah ka sakeni dariya yayi har yana kyalkyatawa banida ansa kenan😅😅oya kije kici abincin ki idan kin gama kidawo ki tayani haɗa kayana,sai lokacin tace wai dagaske halim zata tafi Maldives?idan kin dawo zamuyi magana..................