GANGANCI

Episode 2

by @zahraroyal

*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR


*TALLAH TALLAH TALLAH*

LADY'S BEAUTY PALACE 

MACE SAIDA GYARA 

SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
 KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon 

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

 MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE 

ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻

Zumar kiba
Zumar breast 
Zumar hips 
Zumar infection 
Zumar sliming 
Zumar sabon budurci 
Back to virgin 
Abayas 
Atamfa 
Lace
Hijabs 
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su kuma muna bada sari yadda zaki siya Ki samu riba kema 

Location Katsina state 

WhatsApp or call ***
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)


PAGE 2


“Ummi please ki daina dukanta sai kiyi mata illa fa”

Tashi daga kanta Ummi tayi tana huci tana nunata da yatsa ta ce.

“Barni kawai na huce haushin b’ata min parlo da tayi”

Hancin Hamda a toshe take magana tana cewa.

“Ummi ni nayi nan idan ban dawo yau ba sai gobe”

D’aga mata kai Ummi tayi tana dawo da dubanta inda Shamsiyya take har wani bacci ya sureta a wajan ga aman da tai a gefe.

“Wallahi kinma tashi ki gyara wajan dan ba ubanda zai gyara miki shi Mtsww”

Ummi na shigewa bedroom ba jimawa taji ana kwala mata kira.

“Wai miye ne Bilkisu? Yada kira haka kamar wacce na ci bashi?”

“Mtsww haba Ummi dubi parlon nan fa”

“To sai mine? Ga wacce ta b’ata nan idan abunda tasha ya sake ta, ai ta tashi ta gyara shi”

“Yanzu har sai ta tashi kenan za’a gyara? Duk irin warin da parlon nan ya d’auka”

Ta idasa maganar tana toshe hancinta da sauri jin warin aman daya bugo mata.

“Wallahi bazan aikin wahala ba”

“Shi yasa fa bana son dawowa gidan nan na kwana wallahi, inaga komawa zanyi bari na kira Shamsu tunkan yayi nisa dama mun fara magana dashi Akan tafiyar da zaiyi dani kasar wajen nan ZARVANIA”


“Kika ce Zarvania zai tafi dake? K’asar nan da nake gani a Tv mai Kyan gaske ta turawan nan ita kike nufi?”

“Itafa Ummi, ai babu k’asar a ake jin dad’in yawon bud’e ido sai can, sai wadda ya cika ya batse ke iya shiga k’asar nan”

“To ko ita ce Hamda itama zasu tafi da Hon D’anjuma?”

“Wata k’ila, dan naji y’an siyasa da dama zasu shiga k’asar saboda kasuwancin dake tsakaninsu da Dawara d’in da Zarvania”

Ta sake cewa.

“Ummi nayi nan bazan iya tsayawa a parlon nan ba nima zan iya aman wallahi”

“Ke tsaya mana, kawo wani abu Yanzu dai kamin ki koma dan ban San Yaushe kuma zan sake ganinki ba”

“Haba Ummi zanfa dawo tafiyar tamu nan da sati d’aya ce fa”

“Ahh to ki ce duk gaba d’aya ma zakuyi tafiyar kenan?”

“Dasu waye kenan?”

“Hamda mana, naji tana nanda sati d’aya itama”

“Ai kin San a shekara ana shiga k’asar Zarvania baifi sau uku ba, kuma wannan jirgin da zai tashi damu 10 ga wata mai shigowa daga shi babu jirgin da zai sake shiga masu k’asa sai sabuwar shekara, duk wadda zai shiga k’asar to nan da sati d’aya ne kawai yake da damar haka”

Tana maganar har lokacin hancinta a toshe.
Da sauri ta jawo wayarta da wasu kud’i ta mik’ama Ummi da sauri ta amshe tana washe Baki, bata damu ba da fitar data k’arayi ba ta fice daga parlon da hanzari tana kiran waya.

______________________
“Mlm tun d’azu fa yaron nan yake zaune wajan nan, yana son magana da kai ko?”

D’ago idonsa yayi yana zuba mashi ido yadda yayi k’asa da Kansa kamin ya ce.

“Shin wai Zubaida bance bana son maganar nan bane?”

Amma Mlm tsakani da Allah yaron nan gwamnati ce fa ta d’auki nauyin zuwa k’aro karatunsa a k’asar Zarvania d’in nan bafa shi ya ce ka biya masa wani abu bafa, duk wani abun da zaiyi gwamnti ce ta d’auki nauyi, kuma kowa yasan yadda k’asar Zarvania take da kyau ga ilimi da arzik’in da Allah yayi masu koma….”

Tsaida ita yayi tana cewa.

“Ban hanasa zuwa kowacce k’asa k’aro karatu ba, amma k’asar Zarvania dake cike da kafuran Allah ba abunda k’asar nan ake zuwa yi a can sai alfasha, haka kike so na tura yaron nawa kwalli d’aya jal ya lalace?”

“Amma dai kasan Abdul bazai lalace ba ko? Kasan irin tarbiyyar da muka basa fa, dan Allah kawai ka amince masa ka bishi da addu’a tunda dai can gwamnati ta d’auki nauyin zuwan nasa”

Shiru kawai yayi na d’an wani lokaci ya dubi Abdul ya ce.

“Abdul!!”

Ya kira sunansa, da sauri Abdul ya d’ago yana d’an murmushi dan yasan sun gama shawo kansa shida Momyn tasa tunda yaji yadda ya kira sunansa a lokacin.

“Na’am Abbu”

“Badan son raina zan barka kaje k’asar nan k’aro karatu ba, ko jirgin nan dazai shiga k’asar duk y’an siyasa ne da masu zuwa yawon sharholiya daga shi kuma sai wata shekarar, zan barka kaje amma kaji tsoron Allah Abdul, kaji tsoron Allah kar kaga ba idonmu ka ce zaka je ka aikata wani abunda Allah baya so, ka sani shi Ubangiji yana kallonka a duk inda ka shiga”

Murmushi Abdul ya saki wani farin ciki na mamayesa ya farama Abbun nasa godiya.

Bayan Abdul ya fita ya dubi Momy ya ce.

“Kwata-kwata zuciyata bata son tafiyar nan ta Abdul, dan dai keda shi kun takura ne, amma ko nan Dawara ai akwai makarantu ko cikin k’asar nan Marzuna zai iya zab’ar duk school d’in da yake so kowanne gari ni mai biya masa ne”

Momy na murmushi ta dubi Abbu cikin kissa ta ce.

“Ka kwantar da hankalinka please, duka fa shekara biyu ne yaje ya gama karatun ya dawo, kuma ai abun alfahari ne ace a makarantar daya gama duk cikin department nasu shi kad’ai ne yaci nasarar da gwamnati ta d’auki nauyin k’aro karatunsa, ai sai mu gode Allah ko Mlm?”

Jinjina kai kawai Abbu yayi sai yaji duk abincin da yake cima ya fice masa a rai, ya ture abincin kawai. Momy na kallonsa ta wutsiyar ido ta d’an tab’e baki tana maganar zuci (yo idan banda abun Mlm ina kaga kud’in biyama Abdul zuwa k’asar Zarvania ai zuwa k’asar nan sai mai hannu da shuni, k’asar da kowa ke mafarkin zuwa a k’asar nan, d’ana ya samu shine zaka masa bak’in ciki? Ina wallahi ai bazai ma yiwu ba, dole yaro na ya taka inda manyan masu kud’i ke zuwa)
Ta k’are maganar zucin tana jinjina kai…………