Episode 3
by @zahraroyal
*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR
*TALLAH TALLAH TALLAH*
LADY'S BEAUTY PALACE
MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su kuma muna bada sari yadda zaki siya Ki samu riba kema
Location Katsina state
WhatsApp or call ***
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)
PAGE 3
Zama tayi Tana dubansa yana latsa Computer kamar ma bai san ta shigo d’akin ba, Cike da takaicinsa dana y’arsa ta ce.
“Daddyn Amra!!”
Bai d’ago ba ya amsa da.
“Uhmm”
“Dan Allah ka aje aikin nan magana fa zamuyi”
D’agowa yayi yana zubo mata ido, ganin yanayinta yasa shi zare gilas d’in dake manne a idonsa yana sauke lumfashi kad’an kamin ya ce.
“Uhm ina jinki?”
“Yanzu Amra taje min da wata magana”
Murmushi ya saki kad’an dama yasan zata zo Indai akan maganar tafiyar Amra ne k’asar Zarvania.
“Kana murmushi Daddyn Amra, bakai magana ba, kaine ka barta ko kuwa dai shirme ne irin nata?”
“Kema kin san babu inda Amra take zuwa har sai na amince okay? To yanzu ma ni ne na sahale mata tafiya sati mai zuwa, dan har visa ta fito na sai mata teket na tafiya k’asar”
Sosai ta zuba masa ido da zallar mamakin wannan sangarci da yake nuna ma Amra d’in.
“Bazai yiwu bafa Daddyn Amra”
“Miye bazai yiwu ba?”
“A’ah ya za’ai ace budurwa kamar Amra a barta tafiya wata k’asa can daban wacce take Cike da arna turawa wadda k’asar nan ba abunfa ake cikinta sai zuwan yawon shashanci da sunan shak’awata, shine kai zaka bar y’arka d’aya da Ubangiji ya baka tafiya k’asa irin Zarvania haba, kuma ma wai tafiyar ita d’aya?”
“Ko zaki shirya ki bita ne? Kema kinyo wayon bud’e ido ai”
Da sauri ta girgirza kai tana cewa.
“Allah ya kyauta min zuwa irin wannan k’asar koda yawo ne kuwa, ko itama Amrar duk nacinta wallahi bazata je ba”
“Ki daina wallahi, Y’ata babu abunda zata nema a waje na ta rasa, dan kawai yau rana d’aya tana so ta d’an matsa daga inda muke taje ta shak’ata shine zai zama laifi?”
“Y’a macece fa?”
“Akwai k’asar data tab’a zuwa?”
“Shi yasa ai yanzu ma Bana so taje ko ina”
“Bazai yiwu ba”
“Kasan Allah idan har ni ce na haifi Amra bazata je k’asar nan ba”
Ta fad’a tana tashi tsaye.
Murmushi ya saki kad’an ya ce.
“Nida ke zanga wadda yafi iko da ita”
Binsa kawai take da kallo, Akan tafiyar nan duk yabi ya sauya mata, itafa badan wani abu take gudun tafiyar Amra k’asar Zarvania d’in nan ba, haka kawai yadda taji Amra d’in na fad’in tafiyar da za’ai tare da manyan k’asar da duk wani yaro d’an gata sai taji tafiyar bata kwanta mata ba.
Bar masa bedroom d’in tayi kai tsaye ta nufi bedroom d’in Amra da har ta kwanta lokacin dan dare ya farayi.
A hankali ta tura k’ofar ta shiga sai taga ashe ba bacci take ba, tana zaune saman gado tana kallo a Computer.
Ganin Mom tata a d’akin yasa ta d’an b’ata fuska tasan Yanzu zata fara mata fad’an mi yasa batai bacci ba?.
“Amra dama baki kwanta ba?”
Ta k’are maganar tana zama bakin bed d’in kusa da Amra.
Amra na sosa gashinta daya sakko mata har gadon baya ta ce.
“Mom Yanzu fa zan kwanta kika shigo kuma”
“Ina so muyi magana ne Amra”
Amra na b’ata fuska kad’an ta ce.
“Mommm ki bari safe mana”
“Ke bana son shanshanci fa, yanzu zamuyi maganar, ko dan kinga ana lallab’aki ne?”
Mom tayi maganar tana kallon yanayin Amrar dake turo baki.
“To ni Mom bacci?”
“Saida kika ganni baccin yazo ko yar rainin wayo?”
Amra ta fara mutsu-mutsu da k’afa tana turo baki na zallar shagwab’a dan daka kalleta zaka san dama shagwab’abbiya ce ta gidan gaba.
“Akan zuwanki k’asar Zarvaniar nan ne Amra, so nake kije ki ce ma Daddynki kin fasa tafiyar nan”
A d’an zabure Amra ke duban Mom tama kasa magana ganin hakan yasa Mom cewa.
“Ko baki ji abunda na ce bane?”
“Momm naji zamuyi magana da safe”
“Yanzu zaki bani amsa”
Runtse ido kawai Amra tayi tana Jin Mom yau tayi mugun takura mata, itafa bata jin zata iya fasa tafiyar nan gaskiya, amma gudun maganar Mom yasa ta bud’e baki ta ce.
“Shikenan”
“Kina nufin kin hakura?”
Da kyar ta iya d’aga mata kai. Mom ta saki wata ajiyar zuciya duk da dai tasan halin Amra idan tafiyar riga ta saka abu a ranta da wahala fa ta fasa tafiyar, dan haka saita zuba mata ido tana son gano idan da gaske take maganar.
Ganin kallon da Mom d’in ke mata tayi saurin cewa.
“Momm Allah!!!”
“Dakata nafa son halinki dana Mahaifinki idan kuka so abu kamar uwa taso d’anta”
“Dan Allah Momm bacci!!”
Cewar Amra tana komawa ta zame ta kwanta.
Tashi Mom tayi tana kallon Amra dake kwance taja abun rufa ta rufe har kanta dan kawai Mom d’in tabarta haka nan.
“Allah ya kai ranmu goben dole ma a fasa tafiyar nan idan har na isa dake wallahi”
Ta k’are maganar tana juyawa ta fice, tana fita Amra ta mik’e zaune tana b’ata fuska had’e da turo baki a fili ta ce.
“Momm ai gani can a k’asar Zarvania, ina bazan bari su Asy suyi tafiya irin wannan ace babu ni ba, gobe ma zan kira Rooma nayi mata albishir nima an biya min kud’in jirgi dan haka next week dani za’a shiga k’asar Zarvaniaaaa”
Ta k’are maganar da d’an ihu tana wani k’ank’ame jikinta shauk’in tafiyar na rufe ta………..