Episode 4
by @zahraroyal
*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR
*TALLAH TALLAH TALLAH*
LADY'S BEAUTY PALACE
MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su kuma muna bada sari yadda zaki siya Ki samu riba kema
Location Katsina state
WhatsApp or call ***
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)
PAGE 4
AMIRA POV
Jin yadda ake buga mata k’ofar d’aki yasa ta d’an motsawa tana b’ata fuska.
A hankali ta shiga bud’e idonta da sukai mata nauyi, tana bud’ewa tana sake bud’e su.
Jin muryar Umma ke buga mata k’ofar d’akin tana cewa.
“Wai Amira hala ma bakiyi sallar asuba ba? Kika kwanta har sha biyu kina baccin asara”
Mik’ewa tayi zaune tana b’ata fuska sosai har lokacin fuskarta ba walwala sosai da alama ita ba gwanar murmushi ba ce bare dariya.
“Kina jina fa na sani”
“Ummahh nafa tashi”
Ta fad’a tana sakkowa daga bisa gadon.
A hankali ta nufi k’ofa ta bud’e ganin Umma tsaye yasa ta sake cewa.
“Umma ki tafi mana na tashi fa”
Jinjina kai Umma tayi tana kallon y’ar tata yadda duk ta zama kamar wata firgitacciya wacce bata cikin yaccinta.
Waje ta fito d’auke da makilin da burash a hannunta ta dube k’aramar k’anwarta dake zaune tana cin koko da k’osai ta kwab’e baki tana cewa.
“Ke Sa’a bari na fito ki sayo min kwai da indomi”
“To k’osan fa baza kici ba Aunty Amira?”
“Ki had’a ki cinye Sa’a”
Ta k’are maganar tana shigewa band’aki.
Bayan ta idar da sallar ta Sa’a ta kawo mata indomin data sayo mata tana ci wayarta tayi k’ara alamar kira.
D’aukar wayar tayi tana duba mai kiran, d’an murmushi ta saki tana d’auka ta kara a kunne.
“Insha Allah Honorable Sirika dani zaka je tafiyar nan wannan lokacin”
Tana k’are fad’ar hakan ta sauke wayar.
Sai dai tana saukewa wani kiran ya shigo, d’an tsaki ta saki tana ganin Sophia ce mai kiran yasa ta d’auka tana cewa.
“K’awas yaya dai? Komai ya saitu a nan?”
Daga cikin wayar Sophia ta ce.
“Inafa Amira tun jiya muke ta fama da Abba yak’i ma amincewa dan jiya kamar zai kaimin duka fa akan zuwa k’asar Zarvania, Umma ce ta kwace ni”
“Hhhhh ni kinga dama da banda uba ko Umma bana jin zata iya hanani tafiyar nan tama sani, idan nasa abu a gaba Sai nayi sa”
“To nima kina tunanin danya ce bazanje shine zan bari ku tafi ba tare dani ba? Ai wallahi nake gaya miki ko satar hanya Sai nayi mun keta hazo idan na dawo an saita komai”
“Ki dai bari su yarda”
“Bafa zai yarda ba, dan inaga ma gidanku zan kwaso kayana jibi na dawo kamin zuwan tafiyar tamu naga ta kama ranar Monday zamu tashi ko?”
“Haka yake, yanzu dai ina wani abu ne sai kin jini”
Tana k’are maganar bata bari taji mi zata ce ba ta kwashe wayar.
Saida ta gama cin abincinta tas kamin ta mik’e tsaye tana nufar d’akin Umma.
Ganin shugowar Amira yasa Umma gyara zamanta dake zaune a k’asa.
Zama Amira tayi kusa da ita tana d’an kwantowa jikin Ummar haka kawai taji wata fargabar sanar da ita tafiyar.
Amma abun kamar tsafi sai taji wani kwarin gwiwa nazo mata dan bata san lokacin data fara cewa.
“Umma nan da ranar Monday zamu tafi k’asar Zarvania nida sauran k’awayena”
Gani tayi Umma ta zabura tana d’ago da Amira daga jikinta dubanta take sosai kamin da kyar ta samu bakinta ya furta.
“Amira kinsan wacce k’asa kike cewa kuwa?”
“Na sani Umma!!”
“K’asar data fi kowacce k’asa tsadar jirgi k’asar data fi kowacce kyau a zamanin nan, sana k’asar data fi kowacce k’asa shaid’anci, kuma shaid’ancin da shashanci zaku je kenan?”
“Umma!! Kawai fa yawon shak’atawa zamuje fa”
Girgiza kai Umma ta shigayi tana kallon Amira Cike da takaici.
“Duk d’aya dai Amira, da zaki ji magana da baki je…..”
Da sauri Amira ta rufe ma Umma baki kamar wacce aka tsikara ta ce.
“A’ah Umma kawai kimun addu’ar dawowa lafiya, domin inaji a jikina bazan iya fasa tafiyar nan ba, saboda shiga k’asar Zarvania sai mai rabo mai k’umbar susa, duk wadda sukayi nasara keta hazo suka shiga k’asar Zarvania a Dawara ana masu kallon jiga-jigan masu kud’i ko y’an siyasa”
“Jiga-jigan y’an iska dai Amira, sana wai ma tsaya waye zai biya maku mak’udan kud’ad’en zuwa k’asar Zarvania?”
“Umma kina abu sai kace baki san wace Amira ba? Dama kin dad’e da sanin burina d’aya na zuwa k’asar nan fa”
Zuciyar Umma na tsinkewa da tafiyar ta dubi Amira ta ce.
“Baki jin komai a cikin tafiyar k’asar nan?”
Da mamaki Amira ke kallon Umma a hankali ta mik’e tsaye tana kallon k’ofa ta ce.
“Umma zan fita yanzu sai zuwa anjima zan dawo”
Bata iya cewa komai ba har Amirar a fice daga d’akin. Ubangiji ne tasan ya jarrabeta da Amira bazatai mata baki ba, kullum addu’a take Allah ya shirya mata ita, amma wannan tafiyar tunda sukai maganar zuciyarta ke tsinkewa, da Amira najin maganarta bazatai wannan tafiyar ba………….