Episode 5
by @zahraroyal
*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR
*TALLAH TALLAH TALLAH*
LADY'S BEAUTY PALACE
MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su kuma muna bada sari yadda zaki siya Ki samu riba kema
Location Katsina state
WhatsApp or call ***
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)
PAGE 5
Ta dube ta sosai tana rik’e hannunta ta ce.
“Laila bana so kina irin wannan rayuwar kwata-kwata, karatu kikazo fa bai kamata kina cin amanar iyayanki ba”
Laila ta watsa mata wani kallo kamin ta tab’e baki ta ce.
“Sha kurumunki ma Sajida nima dani za’ai tafiyar nan k’asar Zarvania”
“What waye ya biya miki kud’in shiga k’asar nan?”
“Ahh sannu y’ar b’akin ciki, zan bari ne kuyi tafiyar babu ni a ciki? Baccin naji labarin duk wani wadda yake ji da kansa a k’asar nan dashi za’ai wannan tafiyar, ni Laila kuma sai nayi sake ayi babu ni ko?”
“Amma ni ai kin San school d’in nan ce ta wakilta ni zuwa domin k’aro sani akan abunda ya shifi department namu ko saboda irin kwazona da k’ok’ari aka zab’eni, amma ke fa miye abunda zakiyo a k’asar?”
“Ke kinga kinfa fara bani haushi”
“Amma Laila mi zakiyo a k’asar Zarvania idan kinje, waye ya d’auki nauyin kaiki k’asar nan?, a k’iyasi fa kusan millions hamsin ake biyan kud’in zuwa k’asar nan fa”
“Ina ruwanki, ai kin san dai bazan rasa mai biya min kud’in jirgi ba ko? Ko baki ganni bane Sajida?”
Sajida ta kalli Laila da kyau tana girgiza kanta eh tabbas Laila d’in irin matan nan ne masu diri masu saurin jan hankalin Maza gare su da surar da Allah ya zuba masu, amma Kyan fuska Laila bata dashi, dan Sajida ta fita kyau nesa ba kusa ba, bama za’a had’asu ba.
Katse mata tunani tayi da cewa.
“Kema da zaki waye ai da kin taka k’asashe wadda suka fi Zarvania nisa da tsadar zuwa da Kyan nan naki, dan nasan idan banda maganar school ta d’auki nauyinki idan danginki za’a had’a baza su iya fitar da kud’in da zaki je k’asar Zarvania ba”
“Hmm mima zai kaini k’asar da kullum y’an siyasarmu dama mutanan cikinta ke zuwa yawon iskancinsu suna shek’e ayarsu a can, mi zai kaini wannan k’asar ai Sai Abu irin wannan da babban dalili kuma”
“Hhhh waye bazai so zuwa k’asar Zarvania ba Sajida? K’asar data fi kowacce kyau a k’asashen duniya idan kika cire Saudia to ita ce ta d’aya”
“Laila ki kira gida su san da tafiyar nan, ni haka nan ma nake jin tafiyar bata wani kwanta min bama kamar kar naje”
“Kinga kinyi ma kanki kuwa. Gida ne dai bazasu san naje ba har na dawo”
Sajida zatai magana wayarta tayi k’ara d’aukar kiran tayi tana cewa.
“Shegiya Hamda, Sai Yanzu nake jinki yaya maganar shirye-shiryen tafiyarmu”
“Shine ai na shigo school d’in taku na d’aukeki muje shopping na tafiyar nan, kin San Monday ne tafiyar fa”
“Ina zan manta k’awas, nima bari yanzu na kira Alhaji Sammani kin san dashi ne zamu keta hazo”
“Shegiyar kaya nasan ai shine zai iya biya miki shiga k’asar nan, ai dole wani abun sai da y’an Siyasa b’arayin gwamnati. Nima shopping mall d’in mutunan zafa muje”
“Yo ke k’awata idan basu ba waye zai wani iya cire Million hamsin biyan kud’in jirgi? Ai sai su sai kuma masu kud’in nan ko y’an kasuwarmu”
“Kinga Yanzu dai Laila kiyi-kiyi ki fito mu wuce tare muke da Anas fa”
“Ahh ina kika baro Hon D’anjuma d’in?”
“Ai shi amfaninsa dama sai mun bar k’asar, kedai ki same ni a harabar school muna nan”
Ta k’are maganar tana kashe wayar.
Tashi Laila tayi tana yafa gyalen Abayar dake jikinta tana duban Sajida ta ce.
“Ni sai na dawo”
“Yanzu fa k’arfe sha biyu na dare shine kuma zaki fita a lokacin nan?”
“Mtswww kin cika damuwa wallahi Sajida, ki rink’a kauda kai a abunda ba ruwanki ciki please”
Ta fad’a tana ficewa daga room d’in naso.
Tagumi kawai Sajida tayi tana jin ba dad’i da tafiyar nan kwata-kwata duk kwanan duniya sai taji tafiyar na sake sire mata a zuciya, danko d’okin zuwa k’asar da take gani a Tv da jin labarin had’uwarta da irin tsadar kud’in jirgi da ake biya wajan zuwa k’asar bata jin wani farin ciki bare jin dad’in itama zata kafa tarihin shiga k’asar.
Ta sauke ajiyar zuciya tana tuno Umminta duk duniya ita kad’ai ta rage mata yanzu idan ta tafi waye zai kula da ita?. Duk da tasan Ummin irin matan nan ne masu neman na kai, dan yanzu haka tana sana’ar abinci dan dashi ma take d’aukar nauyin karatun Sajidar har sana’ar kiwon Kifi da Kaji take shi yasa ba abunda zata nema Ummin batai mata ba.
Yanzu ma Ummin ce ta k’arfafa mata gwiwar tafiya k’asar nan da ta ce bazata je su wakilta wata ko wani a school d’in………