GANGANCI

Episode 7

by @zahraroyal

*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR

Page 7

ABDULLAH POV

Zaune yake rik’e da waya hannunsa yana waya sai dariyar shak’iyanci yake yana cewa.

“Ai na gaya maka friend da kyar Man d’in can ya barni sai da aka kai ruwa rana ya barni zanyi tafiyar nan”

Daga cikin wayar aka saki wata dariya yana cewa.

“Ai na sani da wahala dama a barka, amma tunda an barka ai na maka murna aboki”

“Bari kawai Sagir ai da Mlm ya kwafsa min wallahi”

Sun dad’e suna waya kamin daga k’arshe Sagir dake cikin wayar ya ce.

“Mufa yanzu haka mun fito shopping na barin k’asar Kasan dole mu shiga k’asar Zarvania da kaya masu capacity ta yadda zamu kashe pictures masu azabar kyau mu posta a duniya tasan mun shiga k’asar Zarvania”

“Amma shine dan bak’in ciki tsakani Allah Sagir ko a sanar dani”

“Hhhh ai mun san da wahala kace zaka je wani shopping”

“A’a wallahi Momy zata barni, kawai Ku jira ni wane shopping kuka ce?”

“Muna a D’anjuma Dawara shopping Center Mall”

“Kai naga sunayen da suka fito fa na tafiyar nan namu jirgin da zai tashi damu harda sunan mai shopping Mall d’in nan fa”

“Ai rik’ak’k’en d’an siyasa ne zai iya biya ma mutum fiye da biyar zuwa k’asar nan fa”

“Kuma ai yaran manyan ne mufa gwamnti ce fa ta d’auki nauyinmu”

“Kai ka manta kawai nawa ce Million hamsin? Ko ni na biya maka zuwa k’asar Zarvania”

Abdul na dariya ya ce.

“Ku jira ni kawai ina zuwa yanzu”

Ya kashe wayar yana tashi da sauri ya d’auki wayarsa yana fita zuwa parlo.

Ganin Momy ita d’aya yasa Abdul sakin murmushi ya kai ya zauna kusa da ita yana marairaice fuska ya ce.

“Momy kin san tafiyar nan ta masu Capacity ce ko?”

Jinjina kai Momy tayi tana cewa.

“To shine mi ka fad’a kanka tsaye kawai, mi kake so yanzu?”

“Dama Momy abokaina ne wadda zamuyi tafiyar dasu zasu je shopping na kayan sawa da wasu abubuwan shine nazo ki bani wani abu nima nad’anyi sayayya”

“Shine zaka tsaya kuma wani kauce-kauce, bari Abbun naka ya dawo zan amsar maka ATM nashi kaje kayo duk sayayyar da kake so”

“Noo Momy Abbu kin san fa da kyar ya amince min tafiya k’asar nan, yanzu idan kikaje masa da maganar nan zai iya fassara abun ta wata sigar fa”

“Ehh kuma haka, bari naje bedroom na d’akko maka nawa ATM d’in, amma kai naka ba kud’i ne a ciki?”

“Momy duk fa naira dubu d’ari biyu ce a ciki, ko kala biyu kaya bazasu saya min ba”

“Dole dai nayi ma Abbun naka magana ya tura maka wasu kud’i saboda idan kaje ai kana buk’atar kud’i”

“Hakane Momy kin san dai yadda zaki lallab’a minshi”

“Karka damu ba abunda zai faru”

Ta fad’a tana mik’ewa ta haye sama, jim kad’an saiga ta ta dawo d’auke da ATM ta mik’a masa.

“A dawo lafiya akwai million biyar a ciki Kar ayi b’anar kud’in dai Abdul”

“Insha Allah Momy bai wuce na kashe million biyu ba”

Jinjina kai tayi, shi kuma ya tashi ya fice yana fita harabar gidan ya hau Motarsa ya bar cikin gidan.

Yana tafiya cikin Mota yana cin wak’a yana bin wak’ar harya iso Shopping Mall d’in.
Yana Parking kenan yaga wasu Motoci Guda biyu tsala-tsala sunyi parking suma a dai-dai inda yayi.

Kallon Motocin yake har lokacin Dana ciki suka fito.

Ba wacce ta tafi da imaninsa irin mai sanye da Hijab d’in nan dan sauran matan biyu dake biye da ita basu kaita kyau ba.

Irin kallon da yake masu yasa Amra tsarguwa tana juyowa kuwa idonta ya sauka akan nashi idon. Lokaci d’aya itama Abdul d’in kyansa da ajinsa suka tafi da ita, amma saita wani maze tana jefa masa harara tana turo baki.

Abunda tayi ne yasa Abdullah sakin murmushi kad’an baiyi k’asa a gwiwa ba yabi bayansu ganin sun fara masa nisa.

Bai sha wahalar tunkararsu ba dan kuwa yana masu sallama su Rooma suka amsa masa suna tsayawa amma banda Amra dan gaba tayi tana b’ata fuska harda hararar su Asy da suka tsaya.

Ganinsu Rooma wayayyu ne dandanan suka saba dashi wajan magana yana ce masu shifa k’awarsu mai Hijab yake so ya za’ai?.

Murmushi Rooma ta saki tana cewa karya damu zata shawo masa kanta.
Badan komai Rooma ta sakar masa fuska saidan ganinsa shima ba raini dan kallo daya suka masa, suka gane shima akwai naira a tattare dashi, dan bamai iya zuwa shopping irin wannan sai masu hannu da kumbar susa.

Bai bar inda suke ba saida Rooma ta bashi number Amra, shi kam Abdul tsabar jin dad’i saida yayi ma Rooma kyautar kud’i yayi mata transfer ta dubu d’ari biyar wadda yasata rud’ewa a wajan jiki na rawa ta nufi Amra kamar bakinta zai tsage ita da Asy………