GANGANCI

Episode 8

by @zahraroyal

*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR

Page 8

“Wai miye kina ta rawar k’afa haka ne?”

“Mtsww ke banza Sajida fitar nan da nayi ce baki ga uban kayan dana kwaso bane?”

Kallon kayan Sajida tayi masu yawan gaske Cike da leda tana kallon yadda Laila ke fito da kayan ciki wasu matsitan kaya ne irin y’an gayu na k’asashen k’etare saidai irin masu fito da tsiraicin nan ne, dan haka da sauri Sajida ta dubi Laila tana nuna kayan ta ce.

“Laila wannan kayan dasu zaki tafi?”

“Ke k’asar Zarvania fa irin ta wayayyun mutane ne, shi yasa duk wadda zai shiga k’asar dole yayo sayayya irin wannan ta kece raini, dan haka kinga rabu dani na fara shirya kayan nan a akwatin da zan tafi dashi”

“Amma Laila wannan kayan ai ba sawar d’an musulmi bane”

“Ahhh Au Allah, ai ko kina da kina aiki Sajida, kinga ko ke abunda zakije yi daban haka nima abunda zai kaini daban. Ke karatu zaki je ni kuma yawon bud’e ido zanje da yin pictures zafafa mu samu na posting a TikTok”

“Duk da haka Laila kar a k’etare abunda Allah ya ce, wannan rawar k’afar dana lura duk wadda za’ai tafiyar nan dashi suke ban tsoro kamar ma na fasa tafiyar, ace tafiya kamar za’aje Saudia an d’auketa kamar mi? An mugun d’ora buri akan zuwa k’asar nan”

Tab’e baki Laila tayi tana kallon Sajida k’asa-k’asa ta ce.

“Dole muyi d’uki da zuwa k’asar da bamu tab’a zuwa ba, haka zalika ba kowanne ke iya biyan kud’in jirgi zuwa k’asar ba, to kuma mun samu sai kawai muk’i nuna murna?”

“Ai abun da kukeyi ne yayi yawa Laila, karfa kuyima Allah shishshigi”

“Wanne irin magana ce kike yi haka? Shishshigi fa kike cewa? To sab’on Allah muke yi?”

“Ai naga shine kuke shirin aiwatar a k’asar da zamuje”

“To wai da kike ta wannan abun kabari daya za’a samu dake ne? Kiyi sha’aninki please muma muyi namu wai da haka ne. Nifa ko badan an riga anyi bokin na Hotel da za’a sauke mu ba da sai na ce bana buk’atar had’a hanya dake ko a k’asar”

“To ai bazamu had’un ba Laila, kawai kusa da kusa ne Hotel d’in, naku ai na masu kud’i ne namu kam ai na dai-dai talaka ne”

Shiru kawai Laila tayi mata jin wayarta na k’ara.

Ganin mai kiran yasa ta bin wayar da ido ba alamar bazata d’auka ba.

Lek’a wayar Sajida tayi tana mamaki ta ce.

“Mama fa ce ke kiranki Laila shine bazaki d’auka ba?”

“Mtswww bazan d’aukan ba”

“Mahaifiyar taki? Kifa sani iyaye ba abun wasa bane”

“Uwarki ce ko tawa uwar?”

“Ahh Allah ya baki hakuri daga maganar gaskiya”

“Rik’e gaskiyar taki Malama. Sana please idan Allah yasa muka je k’asar nan babu ruwanki da duk abunda kikaji ko kika gani akaina bana son sa ido tom”

Rik’e baki kawai Sajida tayi anya Laila kanta d’aya kuwa?.
Wayarta ce ta sake d’aukar ruri saida ta kusa tsinkewa kamin ta d’auka tana turo baki kamar na cikin wayar na ganinta.

“Yanzu fisbilillahi Laila inata kiran wayar taki sai yanzu kikaga damar d’auka dan ubanki?”

Daga cikin wayar aka fad’a.

Laila na d’aure fuska ta ce.

“To wai ni Mama banda damar yin wani abu koda Yaushe ina tare da waya ne?”

“Ke dai kika sani, dama kiranki nayi na ce miki bamu da komai a gidan”

“Ina Hajara ne da bazata nemo wani abun ba itama? Ai naga itama wayon banza take tafiya cikin gari”

Ji tayi an amshe wayar ana cewa cikin tsiwa.

“Ai garani fita nake ina dawowa gidan Ubana, kefa da kike fakewa da wani karatu wadda an kasa gamasa tsawon shekaru babu uwar da kike tsananawa ko a makarantar sai yawon banzar kema”

“Wallahi Hajara zanci kutumar ubanki ni sa’ar wasanki ce?”

Amshe wayar Mama tayi Laila najin Mama tana ce ma Hajara.

“Wai ke mi yasa kuke haka ne?”

“To Mama kiyi mata magana ta daina shiga min harka tom”

Laila dake jin komai ranta a b’ace ta ce.

“Wallahi wallahi Mama idan Hajara bata kiyaye ni ba sai nayi mata abunda bata tunani. Sana zan turo kud’i ke kad’ai zakiyi amfani dasu idan harta tab’a ko asi a ciki ban yafe ba wallahi, itama taje yawon banzar ya bata mana”

Tana k’are maganar ta datse kiran.

Sajida dake jin komai sai tayi tagumi dai su Laila sunfi k’arfin uwarsu sai abunda suke so? Wacce irin rayuwa ce muke ciki to? Dan kawai an rasa Uba sai gida yabi ya lalace? To amma ita ai ta rasa Mahaifin amma tata Mahaifiyar bata bari ta watse haka ba.
Tana jin yadda Laila keta zage-zage tana zagin Hajara k’anwarta kamar ita ce a gabanta, yadda take gunduma ashar kai kace zagi dashi aka haifeta cikin baki kamar wata y’ar maguzawa. Tana yi tana had’a kaya a cikin wani kyakkyawan akwati wadda shima daga shopping d’in aka dawo dashi, dama ita Sajida tuni ta gama had’a nata kayan daba wasu bane, a d’an k’aramin akwati itama sai babbar jakar karatunta school bag duk abunda tasan zata buk’ata a tafiyar ta riga ta had’a, dan yau take shirin barin Hostel d’in zuwa unguwarsu kamin zuwa ranar Monday……….

Wannan book d’in na kud’i mun kusa k’are Free insha Allah Naira 700 ne idan ya zama Complete kuma ya koma 1k.

Asusun banki 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Shaidar biya 👉***