Episode 9
by @zahraroyal
*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR
Page 9
HAMDA POV
Kallon iyayen kayan da Hamda ta shigo dasu kawai Ummi keyi tana murmushi kamar gonar auduga Harda su sakin bud’a.
Shamsiyya dake zaune akan kujera tana latsa waya ta tab’e baki tana hararar kayan kamin ta ce.
“Yanzu Ummi tsakani da Allah Bilki da Hamda zaki bari su tafi wata uwa duniya su bar k’asar nan kina ji kina gani kuma bazaki hana ba?”
Wani irin kallon baki da hankali Hamda ta jefama Shamsiyya kamin ta ce wani abu Ummi ta rigata cewa.
“Dalla gafara can rufe min bakin nan naki, ke akwai uwar da kike tsinanawa min ne a gidan nan? Ba abunda kika iya ko kin samo y’an kud’in naki ba wajan shaye-shayen banzarki suke k’arewa ba?, sufa kullum sune ke ciyar da gidan nan harda ma ke k’atuwar banza da wofi”
Shamsiyya na b’ata fuska tana zunb’uro baki gaba tana nuna Ummi tana cewa.
“To ni ai gara ni dai bana yawon iskancin ina bada kaina ana bani kud’i, sufa sai sunba wani gardi jikinsu ya mora kamin a d’au kud’in a basu, ko barin k’asar nan da zasuyi na rantse da Allah yawon ta zubar d’insu zasu tafi ba wani abuba amma ke Ummi idonki ya rufe, ai gara ni shaye-shayen kawai nake bana bada jikina ga wani can banza”
Wani shegen mari Hamda ta sakar ma Shamsiyya tana huci, a mugun zabure Shamsiyya itama ta mik’e tsaye tana wani irin jijjga jiki fad’i take murya a sama kamar za’ai yak’i.
“Ni…ni.. kika mara Hamda?”
“Ko zaki rama ne marar kunyar banza. Yo ba gara mu d’in ba keda kike kashe kanki da kanki wajan shan kayan da zasu gusar miki da hankali kina illata jikinki a banza, idan kika sake mutuwar tsaye zakiyi banza”
Wani irin hucin b’acin rai kawai Shamsiyya ke saki tana jinjina kai na zallar b’acin rai.
“Ke rabu da ita Hamda a haka zata k’are da shaye-shaye shashasha kawai”
“Wallahi gara ni sune dai zasu mutu a haka, kuma wannan tafiyar da zasuyi saita koya masu darasin rayuwa”
“Kaii aniyarki tabiki y’ar bak’in ciki, wallahi Ummi hassada ce kawai ke damun Shamsiyya, dafa cewa za’ai ta shirya ayi tafiyar da ita da yanzu ba wannan maganar take ba”
Cewar Bilki data shigo parlon lokacin take fad’ar hakan.
Hannunta itama d’auke da akwati da ledoji Cike da kaya ta aje tana sauke lumfashin gajiya saida ta kai ta zauna kamin taji Ummi na cewa.
“Yo dama mana Bilkisu ai ba abunda ke d’awainiya da yarinyar nan sai bak’in cikin”
“Kuma zata mutu dashi a ranta wallahi”
Cewar Hamda tana kaiwa ta zauna itama akan kujera aka bar Shamsiyya a tsaye b’acin rai kamar ya kasheta na marin da Hamda tayi mata bata rama ba, shin wai ma miya shiga kanta ne da bazata d’auki hannu ta zafga mata marin ba itama? Mima yasa ta kyale ta ne?.
“Kai y’an arzik’i irin albarka, Wai Yaushe ne tafiyar nan taku? Naji Hamda ma ta ce wai k’asa d’aya ashe zaku tafi?”
“Eh wallahi Ummi ranar Monday tafiyar k’arfe biyar na yamma jirginmu zai d’aga”
“Masha Allahu, kuce nanda jibi ma kenan ko?, ke Bilki Sai yau kike dawowa tunda kika fita har saida kikai kwanaki biyu a waje zamu ganki yau?”
“Wallahi Ummi ina can muna sayayyar barin k’asar kin San dole mu sayo kaya na kece raini, ba k’aramin gayu za’a rink’a sha a k’asar Zarvania ba, wowww akwai cin uwar sabada a k’asar Zarvania Allah dai ya kai damo ga harawa kawai”
“Ke dai Bari sis ai inaga shafi na TikTok sun bani da ganin k’asar Zarvania dan ba inda bazanje yawon bud’e ido ba, shi yasa ma na sake waya na sai IPhone 17pro dan na ji dad’in yin videos da pictures masu azabar kyau”
Hamda ta k’are maganar tana wani k’ank’ame jikinta tana jin wani shaukin zuwa k’asar.
“Yo ai nima in gaya miki yanzu d’in da sabuwar waya ta na shigo gidan kin ganta nan a kwali IPhone 17Air ce ne tawa”
Ta k’are maganar tana fiddo kwalin wayar ta mik’ama Hamda dake ta washe baki tana kallon wayar.
“Wai kuna ta maganar kaya da wayoyi ni ina nawa kwason yake”
“Haba dai Ummi ai kema yanzu zanyi miki alert d’in kud’in dana ce miki”
Hamda ta fad’a tana fiddo da tata wayar.
Shamsiyya da aka bari tsaye sai sakin baki kawai tayi tana kallon ikon Allah, wayar da take ta burinta sai d’aya daga ciki amma har yau IPhone 13 ce a hannunta ta jima a hannunta tana ta lallab’awa amma su rana d’aya sun saya wayar million Harda wani abu?.
“Yanzu dai idan kin tura kud’in sai kuma Bilki ke mi zaki tura min?, sana ina tsohuwar wayarki sai ki bawa k’anwarki ko?”
“ Wace k’anwar Ummi?”
“Bafa nason haka Bilki wace k’anwa kuke da ita duk gidan nan shin ba Shamsiyya ba ce?”
“Tab wacce take mana bak’in ciki da samun da muke ita za’a d’au wani abu a bawa?”
Hamda ta idasa maganar tana bankama Shamsiyya wani mugun kallo mai had’e da harara.
“Banfa son rainin wayo Hamda bana son abun hannun naku, ai ko zanyi yawo tsirara akan babu bana buk’atar abun hannunku, abunda aka samo shi daga aikata haram shine har wani abun tutiya ne a nan?”
“Kinji ko Ummi? Ai kima kwantar da hankali Shamsiyya tuni na kyautar da wayar, ke a su waye da zan d’auki abuna na baki? Ai tukun baki kai matsayin ba. Sana kinata wani fad’in haram-haram ke uwar mi kike aikatawar ba sab’on Allah kikeyi ba shaye-shayen har wani abun arzik’i ne?”
“Ai gara ni wallahi sab’on Allahn da nake bai kai naku yawan zunubi ba”
“Kaji banza duk laifi ai sunansa laifi. Kuma dan Allah idan kin haifo daga yau ki daina cin abincin gidan nan, tunda naga ai mune masu nemowar ke cima zaune ce”
Shamsiyya ta zabura tana turo baki tabar masu parlon kamar zata tashi sama, suka bi bayanta da harara su duka…………
Wannan book d’in na kud’i mun kusa k’are Free insha Allah Naira 700 ne idan ya zama Complete kuma ya koma 1k.
Asusun banki 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank
Shaidar biya 👉***