GANGANCI

Episode 10

by @zahraroyal

*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR

Page 10


ABDUL POV

Tun daga nesa suka fara masa kirari suna k’od’asa cewa suke.

“Sai da kai d’an Hajiya, ashe Hajiya ta sakar maka naira, muna hango ka ai kaida wasu y’an mata masu class Alajali”

Abdul na murmushi ya ce.

“Bari kawai guys, wata yarinya ce ta tafi da ni Mlm, amma nayi nasarar samo number nata, kai inama da ita za’ai tafiyar nan zuwa k’asar Zarvania da an buga Capacity Alaji”

Dariya suka saki Sagir ya saki yana cewa.

“Idan ka ganta a filin jirgi fa? Saboda na lura suma masu Capacity ne tafiyar tamu kuma kasan ta manya ce, akwai jigaggun y’an gayu da zamu had’e dasu a cikin jirgi”

“Allah ya biya ta bakinka kawai Sagir da ansha shagali”

Suna dariya suka ci gaba da sayayyar kayan da zasuyi tafiyar dashi, duk yawanci k’ananun kaya ne wani wandon ma duk rabinsa a yage yake irin na gayun samarin nan a zamanin da muke ciki, ba wasu kayan arzik’i a ciki dan kowanne Saida ya zab’i kaya sunfi kala goma, dan harda sabon akwatuna suka daya aka fitar masu dashi har cikin Mota da kayansu suna sallama dasu Sagir cewar sai sun had’u a filin jirgi zuwa gobe.

Kamin Abdul ya wuce ya dubi d’ayan Abokinsu mai suna Abduljalal wadda suke kira da Jalal ganinsa duk wani iri tunda suka fara sayayyar ya kasa hakuri ya ce.

“Yaya dai Jalal ya naga duk kayi wani iri ne? Komai dai normal ko?”

“Mtsww kai ka rabu da wannan shi kullum ai kasanshi d’an wa’azi ne, akan wai ba shagali zamuje ba karatu ne ya kaimu mu maida hankali idan munje kaza- da kaza, ni kam na samu na tsallaka k’asa kamar Zarvania ace bazanyi yawo ba bazan baza Capacity ba ina ai hakan bamai yiwuwa bane wallahi”

“Wai Jalal ya kake haka ne? Kamar ba wayayye ba?”

“Idan waye ce irin taku bana buk’atar yinta Abdul, ka duba duk irin kayan da kuka saya babu na arzik’i a ciki, gashi kun kashe kud’i a banza kimanin millions biyu-biyu ina zaku dasu haka? Babu fa kyau irin haka da kuke yi akwai fa masu neman taimako, kuma nasan kuna da kayan da zaku iya tafiyar nan dasu basai kun sai wasu ba”

“Kaga irinta ko? Nifa shi yasa banso zuwa dashi shopping d’in nan ba, dan kawai ya ce shima yana son sayen wasu abubuwa irinsu turare haka sufa kawai ya d’auka, nayi-nayi dashi ya sayi sabbin kaya amma yak’i har ji nayi ka ce kowannenmu ya d’au abunda yake so zaka biya amma bana Jin ya d’auki ko tsinke”

“Kaga Sagir rabu dashi, ra’ayinsa daban namu ma daban, so kowanne yayi abunda yaga zai iya idan mun isa k’asar, ai karatu zamuyi amma saifa mun gama ganin gari gari ya ganmu tukunna koma miye daga baya anzo ayi sa. Yanzu dai gayu sai mun had’u a filin jirgi, ayo shiga ta kece raini do Allah”

Dariya Sagir ya fashe dashi yana d’aga masa hannu yana cewa.

“Ai dole mu tsorata gayu a ranar kaidai Allah ya kaimu kawai”

Kowannensu ya shige motarsa yaja suka bar shopping Mall d’in.


————————— *MONDAY*
“Yanzu Amira da irin wannan kayan zaki shiga k’asar nan? Wato kema kin saje da arnan ko?”

Kallon jikinta Amira tayi sanye take da wando da riga wandon fari yayi mugun matse ta rigar bak’a ce sai wani gyale data yafa a saman kanta sai wata riga y’ar sama wacce take a bud’e mai mab’alli saita d’ora wata hula a saman kanta wacce take kamar fesinkaf, kware shigar tayi mugun mata kyau Sai dai bata dace da y’ay’an musulmai ba.

“Umma k’asar nan fa da zamuje babu ruwan kowa da kowa, koma fa irin sa idon nan fa Umma basayi, ko ace wai kayo shiga ka fito bamai kallonka Umma koda sirara zakai yawo”

“Ai kinji basu san ciwon kansu bane kawai”

Zatai magana wayarta tayi k’ara ta saki akwatin dake rik’e hannunta tana fiddo a cikin aljihun ta.

“Sohia kun iso ne?”

Daga cikin wayar ta ce.

“Muna k’ofar gidanku, ke muke jira kin San biyar dai-dai jirginmu ke tashi, gashi naga k’arfe hud’u harda minti sha biyar, kiyi da jiki fa ki fito, dan har filin jirgin nake so muyi pictures”

Da to ta amsa tana kashe wayar da zumud’in tafiya ta dubi Umma dake tsaye ta matsa tana rungume Ummar tana ce mata.

“Umma sai mun dawo”

Umma ta kira sunan Amirar murya a sanyaye tana cewa.

“Allah ya k’addarar saduwarmu Amira ya k’areki a duk inda kike”

Cak Amirar ta tsaya duk sai taji jikinta yayi sanyi da kyar ta iya takawa zata bar gidan taji muryar Sa’a na cewa.

“Aunty Amira zaki dawo? Yaushe zaki dawo? Karki tafi Aunty dan Allah ki zauna”

Wani irin yammmm taji a jikinta har wasu ruwan hawaye-hawaye sun fara taruwa a cikin idonta, kai saita fara Jin wata irin fargabar fita daga cikin gidan.

Kiran wayarta ne da aka sake yasa ta dawowa cikin hayyacinta ganin Sophia ce ga lokaci na sake ja yasa bata Juyowa bare su Umma su sake ja jikinta yayi sanyi, Sai dai tana taka k’afarta ta fita daga cikin gidan taji wata irin muguwar bugawar zuciya wacce tasa ta dakatawa a zabure tana dafe saitin zuciyarta ido a rufe, tafi minti biyar a haka kamin da kyar ta taka har zuwa wajan Motar dasu Sophia ke ciki.

“Kina lafiya kuwa Amira? Yana ganki haka?”

Samira ta fad’a tana d’an dafa kafad’ar Amirar.

“Ba komai kawai dai ina jin wani iri da tafiyar da zanyi nabarsu Umma”

“Mtswww karkisa nayi miki dariya fa? Ni wallahi su Momcy da murna da farin ciki muka rabu ba wani abunda naji ni kam”

Cewar Samira tana gaban Mota anci uban wanka kusan shigarsu duk iri d’aya ce.

 Sophia ta amshe da cewa.

“To ni ai Mama har wani zallen murna take da tafiyar da zanyi fa k’asar waje, ba wadda baiji tafiyar nan tawa ba a bakin Mama tsabar d’okin zan fita k’asar waje, Abba ne kawai baya so, dan da kyar saida aka kai ruwa rana kamin mu samu ya amince”

Shiru kawai Amira tayi dirver ya tayar suka fara tafiya zuwa Airport tana jin yadda suke ta fad’ar irin yadda iyayensu ke son tafiyar, amma ita a wajan tata uwar ba haka bane, ko shi yasa take jin tafiyar ta fara sirai mata duk ta zama wata iri, dan har lokacin bata daina jin bugawar zuciyar da take ji, ga gabanta dake yankewa yana fad’uwa jikinta na dad’a yin sanyi kamar mai shirin kamuwa da rashin lafiya………..

*To fa😪🤔 a nan na kawo k’arshen Free yaya zata kaya ne a k’asar Zarvania? Shin wai mi zai faru? Yaya zaka k’are ne?. Harfa yanzu bamu kamo zaren labarin bama, kaidai kawai karka sake a barka a baya*

Naira 700 ne idan ya zama complete document 1k ne
Asusun banki 👉8130479973

Shaidar biya👉***