Wutar ƙaiƙayi

Chapter 1

by @sadiyaabdulrazak954



PAGE 1

 
 
   Kawo wutar nefa ya haddasawa jikina karɓar baƙon yanayi, na sanyin iskar fankar da ta fara falfala gudu, hakan ne ya ƙwato ni daga hannun ɓarawon da ya shammace ni ya tafi da ni, duk kuwa da burin yaƙin da na yi da shi, firgigit na yi juyi a kan makeken gadona, zuciyata cike da fatan na ga angona kwance a gefena, burina bai cika ba, don kuwa wayam na ga makwancin nashi, 'Salman bai dawo ba kenan?' Na yi tambayar a zuciyata, tsam na sakko daga gadon, na je bakin windona wanda yake ta waje, na buɗe na yaye labulen, barikin namu ya yi tsit idan ka cire haushin karnuka da yake tashi, duk da ba baƙon abu ba ne amma yakan ba ni tsoro, hasken fitulun sola nake kallo wanda ya haske gidajen maƙota, wanda wannan bai ƙara mini komai ba sai ƙuncin zuciya, sakamakon tuna duk mazajensu suna gida tare da su, ko kuma suna da masaniya a kan ƙwaƙƙwaran dalilin rashin kwanansu a gida, saɓanin nawa mijin, na rufe windo na juyo na sauke idona a kan agogon ɗakin, ƙarfe biyu da minti talatin ya nuna, na tuna wayar da muka yi da Salman misalin ƙarfe tara da rabi, inda yake tabbatar mini yana hanyar dawowa gida kar na yi bacci, sai zuciyata ta ɗarsa mini ba lafiya ba, saboda haka na ɗauki wayata na kira lambar shi, ta kusa tsinkewa aka ɗauka sai dai an yi shiru, cike da shagwaɓa na ce"Hello".

"Wace ce?" Muryar mace ta saka ni wartsakewa na canza murya daga ta sangarta zuwa ta mace mai zafin kishi, na ce"Matarsa ce! Ke wace ce? Me ya kawo wayar mijina hannunki? Kuma yana ina?"

Ƙitt! Ta kashe wayar ba tare da ta ba ni amsa ɗaya ba, zuciyata ta ɗarsa mini zargin shi, sai dai fa ina kokonto, na sake kira na ji wayar a kashe, ba ni da zaɓin da ya wuce na kwanta, da safe idan ya dawo sai na ji hanzarinsa, juyi na yi ta yi baccin ya gagari idona, har sai da na yi sallar asuba sannan ya ɗauke ni, shi ma mai cike da rashin nutsuwa, don zuciyata sai azalzala take yi.

 Cikin bacci na ji ana buga ƙofar gidan, na tashi na kalli agogo ƙarfe bakwai da rabi, na je na buɗe, na yi tozali da kyakkyawar fuskar mijina, sai na ɓata rai na juya ba tare da na yi masa kallo na biyu ba, cak ya ɗauke ni yana dariya, ina ta zillewa da nufin sakkowa bai ba ni dama ba har sai da ya dire ni a kujerar falo, yana cewa "Jiya na kwana da kewar amaryata".

Ganin na ƙi sakin fuska, shi ma sai ya canza na shi yanayin zuwa na damuwa ko kuma dai mamaki ya ce"Abar ƙauna lafiya, na ga kamar kina fushi da ni?"

Hawaye suka zubo mini, na ce"A ina ka kwana jiya? Wace ce ta ɗaga wayarka cikin dare?"

Da farko ya yi alamun mamaki, cikin sakanni ya fuzge ta hanyar canza fuska zuwa dariya sannan ya ce"Yanzu saboda wannan kike fushi da ni?"

Na yi shiru ina jiran amsar tambayata.

"Ki ba ni amsa, saboda wannan ne?" Ya faɗa yana ƙoƙarin janyo ni jikinsa, sai na fizge.

Shi ma ya saita kansa ya ce"Wallahi Zinatu aikin kwana na yi jiya, ita kuma wacce ta ɗaga wayata ƴar sanda ce abokiyar aikina, kin san ba da shirin kwana na tafi ba, to ban tafi da caza ba, shi ne na ba ta wayar ta jona mini, ni ba ta ma faɗa mini kin kira ba".

Na sauke numfashi don har zuciyata na yarda da shi, cikin shagwaɓa na ce"Amma me yasa ba ka faɗa mini za ka yi aikin kwana ba, sai ka ce mini ga ka nan a hanya?"

Ya ce"Saboda ba na so ki ji tsoro idan kika san za ki kwana ke ɗaya, ki yi haƙuri da yanayin aikin namu, za ki saba a hankali kin ji?"

Na gyaɗa masa kai alamar na ji.

Ya ce"Yunwa nake ji fa, me zan samu?"

Na ce"Daga bacci na tasha, ban yi komai ba, bari na ɗora".

"Yi sauri ki dafa mai sauƙi, don wajen aiki zan koma". 

Na juyo na kalle shi da mamaki, na ce"Ka yi aikin kwana kuma sannan ka sake komawa da sassafe? Dama haka aikin yake, ba ku da lokacin bacci kenan, ba ku da na matanku?"

Ya ce"Ba haka ba ne, za ki gane a hankali, yanzu dai je ki yi abunki, ba na son ki saba zama da yunwa".

"Hmm!" Kawai na ce, na fita zuwa kitchen, cikin zuciyata ina tunanin ta yadda zan iya rayuwa da yanayin aikin nan na shi, indomi da shayi na dafa a gurguje, daf da zan ƙarasa falon kunnuwana suka jiyo mini sautin muryarsa ƙasa-ƙasa yana cewa"Ni dai na faɗa miki kada ki sake yi mini haka". Ina shiga yanayin shi ya nuna alamun rashin gaskiya, don ya ɗan zabura ya sauke wayar daga kunnensa da sauri, sannan ya kalle ni ya saki murmushi, kamar na tambaye shi da wacce ya yi waya, sai dai na fasa, na bar shi a ƙila abokiyar aiki ce. 

Muna gama karyawa ya yi wanka a gurguje, sai dai abin da ya ba ni mamaki, bai wuce ganin ya tada sallah ba, bayan ya idar, na kalle shi ina wasa da turaren dake riƙe a hannuna na ce"Salman sallar me ka yi?"

Ya ce"Ta asuba mana, wallahi makara na yi, ina sauri na zo na ganki shi yasa ban tsaya na yi a can ba, sai kuma na sha'afa da na dawo gidan".

Gabana ya faɗi, ina kallon shi, tsoro sai ya shiga zuciyata, shin wane irin miji na aura ne? 

"Zo maza ki fesa mini, kada na yi latti". Maganarsa ta katse mini tunani, na fesa masa turare a unifom ɗinsa wanda suke yi wa farar fatarsa kyau sosai, na yi guntun murmushi na ce"Ban da kallon ƴan mata".

Ya yi dariya ya ce"To ni ina ma zan gansu? Sai dai idan ma su laifi ne aka kawo su, ko kuma ma su zuwa wajen ƴan'uwansu ko?"

Na gyaɗa masa kai alamar hakane, na ce"Me zan dafa maka da rana?"

Ya ce"Sai fa dare zan dawo, amma da wuri, ki dafa duk abin da kike so, zan aiko Sabi'u ya kawo miki cefane".

Na ce"To, sai ka dawo, Allah Ya tsare, Ya ba da nasarar aiki".

Ya amsa da amin, na raka shi har zaure, ina kallo ya shiga motarsa ya ja ya tafi, sannan na rufe gidan na koma.

Na hau gyara gidan, na gama komai, na yi wanka na yi adona, sai na saka tabarma na zauna a tsakar gidan na yi shiru, ina kewar gida sosai, gidanmu babban gida ne na family mai cike da mutane maza da mata, manya da yara, gida mai cike da farinciki a yi ta raha ana dariya, yanzu kuma ƙaddarar aure ta saka ga ni zaune ni kaɗai babu abokin fira, sati biyu kenan da aurena, wancen satin ƴan gidanmu sun yi ayari sun zo ganin ɗaki, a nan suka wuni muna ta nishaɗi, daga nan kuma sai dai tsilli-tsilli na waɗanda ba su zo ba, sukan zo su ga ɗaki su tafi, ɗakuna biyu ne a gidan wadatattu kowanne windo biyu gare shi ta gaba da ta baya, sai kitchen shi ma mai girma, har da windonsa ta waje da banɗaki shi ma mai biyu ne, ga kuma filin tsakar gida babba, sai zaure mai sanyi, don wataran nakan zauna a nan ina kallon tsirarun masu wucewa, idan na rasa abun yi, sau ɗaya na taɓa shiga maƙota duk muka gaisa, su ma duk sun shigo, sai yaransu da kullum sai sun shigo, na gane suna sona, don na kasance mai son mutane da yawan kyauta.

  Ƙarfe sha ɗaya Sabi'u ya kawo mini cefane, shi yaron Salman ne, ta wani ɓangaren ma zan iya cewa abokinsa, sun shaƙu sosai, wanda bai sani ba ma sai ya ce ƴan'uwan juna ne, tun kafin auren ƴan gidanmu babu wanda bai san Sabi'u ba, saboda yawan aiko shi da Salman yake yi, ko ma ya zo haka kawai a yi fira da ƴan gida bakiɗaya. A mutunce muka gaisa, yana zolayata kamar yadda ya saba, ya ba ni cefane ya tafi, na duba na ga kayan miya ne mai yawa da kaji, na hau gyara su, na soya na ajiye, don ban yi niyyar yin girki ba sai na dare, golden morn kawai na sha, na cigaba da harkokina.

 Dab da magriba na kammala komai, na ci kwalliyata, na bulbula humra, don Allah Ya yi ni da son ƙamshi, shi kan shi ya fahimci hakan, shi yasa ya zubo mini turaruka masu yawan gaske a kayan lefe. 

Ina cikin sallar magriba ya shigo, ya cire kaya ya fita don shiga wanka. Ina idar da sallah wayarsa da ya ajiye a kan mudubi ta fara kawo haske alamar kira ya shigo, na tashi kamar ni aka kira na leƙa wayar _'Yar shilata_ Sunan da yake yawo a screen ɗin kenan, gabana ya faɗi, na ɗauki wayar da sauri na ɗaga.

"Ofisa ya ne, za ka shigo na yi maka booking?" Ƙirjina ya ba da sautin dam, a razane na ce"Tanadin uban me za ki yi masa? Wace ce ke?"

"Uwarki ce, kuma tanadin uwar uwarki zan yi masa!" Ta faɗa kai tsaye, sannan ta katse kiran.

Zuciya ta ciyo ni, saura kaɗan na doka wayar da ƙasa, yana shigowa ɗakin jikina ya hau karkarwa murya na rawa na ce"Wace ce ƴar shilarka!?"

Ya warci wayar hannuna yana haɗe gira ya ce"Me yasa kika ɗaukar mini waya!?"

A fusace na ce"Na ɗauka ɗin! Wace ce ita?"

Sai ya sauke ajiyar zuciya, ya zauna a bakin gadon, ya janyo hannuna, na fizge ina yi masa muzurai, ya sanyaya murya ya ce"Zinatu ki nutsu don Allah, ki kwantar da hankalinki, kin fa san wane ne mijinki, kin san yanayin aikina kuma, dole zan yi mu'amula da abokan aiki da kuma ma su laifi, tun da kin ga dai...".

Na ce"Dakata Salman! Maganar aiki ba ta taso ba, ka yi saving lambarta da taka, kuma har tana cewa za ta yi maka tanadi, sannan ta zagi uwata, me zai saka abokiyar aiki ta yi wannan?"

Ya sosa kai, duk alamun rashin gaskiya sun bayyana a tare da shi ya ce"Ba za ki gane ba Zinatu..."

"Ka ganar da ni!" Na katse shi, ina zazzare ido kamar zan hau bori.

Ya ce"To kin san shi sha'anin aiki irin namu, ita wannan tabbas ba mutuniyar kirki ba ce, wata karuwa ce ake ta nemanta ta gagari jami'an tsaro, akwai cases ɗinta da yawa a hannuna, ana zarginta da bawa karuwai masauki, yi wa mazan banza kawalci, da kuma safarar ƙwayoyi, to sabodw salon dabara ta aiki na so na fara shiga jikinta domin na kamata da ƙwaƙƙwarar hujja, wannan tanadin da kika ji tana faɗa na ƙwaya ne, don na ce mata zan je na siya, shiyasa take so ta ji tabbas ɗin zuwan nawa".

Na ce"Idan haka ne akan me za ka yi saving lambarta da wannan sunan?"

Ya ce"Wallahi ba ni na yi na, wanda ya turo mini lambar wani saurayinta ne, ta whatsApp ya turo min, ni kuma sai ban damu da gyara sunan ba, tun da na ga da na kammala aikin zan goge ta".

Na ce"A kan me za ta zage ni?"

Ya ce"To ai wannan ba abun mamaki ba ne, kin san irin matan nan ƴan tasha, zagi ba komai ba ne a wajensu".

Na ce"Hakane!" 

Zuciyata sai ta rabu gida biyu, wani sashe yana faɗa mini na gasgata, ɗayan sashen kuma ya dage da ba ni hujjojin ƙaryata zancen, ban yarda wani sashe ɗaya ya yi rinjaye ba, na tsaya a tsakiya ne, amma na saka a raina tabbas sai na binciki wayar Salman, don akwai buƙatar hakan.


***