Chapter 2
*RIKICIN DUNIYA...*
*TEAM WOW THREE ELEGANT WRITER’S*
©️ Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
CHAPTER 2
…Ba su suka karasa gidan Boka Bakurmi ba sai da aka gama isha'i. Kasancewar akwai hasken Nepa, saboda ko kudin da zasu hau Napep babu.
"Kin tabbatar sawun takun kafar Nadiya ne kika dauko?"
Boka Bakurmi ya fada cikin kakkausar murya.
"Eh ita ce, yau din nan da muka je makaranta na debota"
Karamin faranti ya dauko tare da baje ƙasar. Ya dauki mintuna biyar kafin ya ɗago ya kalle su.
"Akwai matsala! "
Wasila da Umma kallon juna suka yi a rikice.
"Bakurmi! Matsala kuma? Rana ta farko da na ji ka ambaci matsala a cikin aikin ka. Sanar da mu wace matsala ce wannan?"
"Aiki ba zai cika ba sai ta kawo sawun kafar shi saurayin"
"Umma na shiga uku! Ina zan samo sawun Kasim?"
"Ke ar! Har kika samo sawun Aminiyar ki bare na Kasim"
Dariya Bakurmi ya kece da ita. "Za ki kawo sawun ƙafarsa ko kuma mu tsayar da aiki?"
"Aa wallahi zan kawo..."
Uwar tsawar da ya daka mata ce ta sakata hadiye sauran maganar da ke bakinta.
"Karo na karshe da zan gargadeki a kan ki daina Kira mini sunan Allah a wurin nan, kin san Allah me ya kawo ki wurinmu?"
"Tuba take yarinya ce bata san dawan garin ba, ina nema mata gafara ba zata sake ba"
Umma ta karasa maganar jikinta na kyarma. Saboda yau ce rana ta farko da ta ga Bakurmi ya yi irin wannan hasalar.
"Ku ɓaci mini da Gani"
Minti ɗaya ba su kara ba suka fito da gudu.
"Umma! Bakurmi ya tsorata ni, anya kuwa zamu iya?"
"Ke dai anyi sakarar banza, haka kike da saurin sarewa kamar ba ni na haifeki ba."
"to Umma ni ya zanyi da kawo ƙasar nan? Kin san fa sau biyu kadai Nadiya ta hadani da shi, wallahi ba zata bari mu hadu ba domin bata haɗashi da kowa ba"
Wasila ta karasa maganar cikin murya mai nuna Karaya.
"Ina kasar da kika ce mini za ku kaiwa Malam Bawa?"
"Umma ita ma fa bata samo ba yau ta ce mni zai zo, tafiya ya yi"
"To kinga kin samu hanya idan ta debo kasar ke ma sai ki ɗibi taki a bare da ta sani ba"
"Har naji hankalina ya kwanta, ina hango mu cikin daula yadda zamu mike kafa"
Dariya Umma ta yi jin abin da Wasila ta fada.
" 'yar nema a tunaninka a bazan muke shan wannan baƙar tafiyar nan da kafarmu. Hatta bokon da na tilasta mahaifinku ya sakaki duk da zafin talauci da muke fama da shi, niyyata ita ce ki hadu da wani mai kudi ya kwashe mini ke. Sai kuma aka yi sa a Nadiya ita ce wadda ta yi gamo da Katar. Ba tare da sanin ke ta samowa saurayi ba"
"Hmm! Har so make in ga idanun munafuka a lokacin da ta gane wanda take so shi ne wanda zan aura"
"ke! Wa ya ce miki zata sani kafin aure? Idan kika bari ta gane kafin ya aure ke da auren shi har gaban abada"
A gigice ta dafe ƙirji.
"Umma da gaske ba zai aureni ba?"
A kufule Umma ta watsa mata harara.
"Oh da duk bayanin da Bakurmi ya yi ba ki riƙe ba? To ki bude kunnuwanki da kyau ki ji Ni, hatta ubanki sai komai ya daidaita sannan zan bari ya sani. Don haka bakin ki ƙanan ƙafarki"
"Ai dole na ba sai kin jaddada mini BA" a gajiye suka karasa gida ga ciwon jiki ga na ƙafa...
Gidansu Nadiya
"Ance ana sallama da Nadiya"
Karamin yaro dan kimanin shekara biyar ya fada.
"In ji wa?"
Inna da ke cikin daki ta fada tare da fitowa tsakar gida.
"Cewa ya yi Kasim ne"
Rufe bakin yaron ke da wuya, Nadiya ta fito cikin shirinta sai faman zabga uban kamshi take yi"
"Yawwa Shalele. Kiyi sauri ki fita tun kafin mahaifinku ya dawo ya taras da ke a wurin nan"
Turo baki ta yi.
"Shi Baba ya na da matsala. Shi da ya kamata ya yi farin ciki da samun siriki mai kudi irin wannan amma sai faman wasu bincike-bincike marasa amfani ya ke yi"
"Rabu da shi duk abun shi sai kin auri Kasim. Ina fatan kin shafa turaren da Malam Bawa ya baki"
"Eh shi ne fa ke ta faman kamshin nan"
"Maza ki tafi yar albarka Ubangiji ya yi miki albarka kinji"
Da tafiyar kasaita ta karasa gaban Kasim da ke cikin mota ya fito da kafafuwansa waje.
"Barka da Fitowa tauraruwata."
"Barkanmu dai Kasim. Yi hakuri na Barka kai daya ko, Inna ce ta sakani wani aiki"
"Ayya bakomai tunda Inna aka yi ma aiki ai magana ta kare. Dama cewa nayi dole In shigo garin nan saboda ke, domin nayi kewarki ga kuma tafiya da muka yi ban samu nazo ba. Ungo wannan"
Hannunta har kyarma ya ke yi ganin dalleliyar waya cikin kwalinta iPhone 12.
Wani irin ihu Nadiya ta yi ta ma rasa me zata ce.
"Baby na gode! Ubangiji ya biya ka wallahi na kasa rufe baki saboda murna"
"Bakomai tunda kika so ni ai kin gama mini komai. Jira nake ku gama exam in turo iyayena, saboda bikinmu bada nisa nake so a saka shi ba"
Hira suna yi sosai har mahaifinta ya dawo ya shige gida.
Ganin haka ya saka tayi bankwana da shi a kan zai kwana nan dutsinma gobe ya wuce Katsina.
Sai da ta tabbatar da ya jima da barinwurin sannan ta fito ta ɗibisawun shi kusan rabin farar leda.
Da ihun farin ciki ta fada gidan.
"Inna! Innarmu fito-fito dawa tayi nama"
Inna da Jamila a tare suka fito a hanzarce.
"Me nake gani haka?"
Cewar Inna tana kara jujjuya dalleliyar wayar.
"Tsaraba mana daga Kasim. Kalli ki gani wannan kudin hada su ya haɗa mini inyi hidimar gama makaranta. Sannan wayar nan ba a dade da kaddamar da ita ba"
"Ayyiririii! Haihuwa tayi rana"
Inna ta rangaɗa gudar da Tayi sanadiyyar fitowar Malam Amadu wato mahaifin Nadiya.
"Asibi! Ke ce kike rangaɗa wannan gudar har haka? Bani wayar nan tunda na fahimci ku dai karamar kwalwa garemu."
Galala tayi tana kallonsa.
"Ban gane in baka waya ba, to me zaka yi da ita?"
"Zan mayar wa da yaron can kayansa ce har sai ya turo iyayensa sannan duk abinda zai bata sai ta amsa"
"Ni wallahi babu wanda zai rabani da wayata, ba a siyarmin a Gida ba an kawo kuma a hanani amsa"
Nadiya ta karasa maganar cike da rashin kunya.
"Aunty Baban kike fadawa haka?"
Jamila tayi maganar fuskarta cike da mamaki.
"Ta je ta fada bakar munafuka mai irin halin ubanta, wadda bata kishin yar uwarta. Ni gaskiya amadu abin da kake yi baka duba mana. Ya Allah Ya aiko yaro ya zo ya ji kanmu kana yin wani abu kamar kana haddasa. Gaskiya ba za a mayar ba kome zaka yi kaje kayi"
Murmushin takaici Malam Amadu ya yi. "Asibi yau Ni kike fadar ina haddasa da Nadiya ko. Ba damuwa Ni har gobe ina alfahari cewa Ni mai gadin primary ne, ku kuma tunda kun daurawa kanku rayuwar karya da kwadayi kuje ba baki nayi maku ba Allah ya kyauta”
Ya karasa maganar a fusace ya fita.
"Munji dai! Umma ta gaida assha, Ke kuma na dawo gareki"
Inna ta matse kunnen Jamila.
"Duk abin da nake fada miki ta bayan kunne ki ya ke bi ko?"
"Inna ba zata gane wannan Yaren ba, kamata ya yi ta ji a jikinta"
Nadiya na rufe baki suka hau jibgar Jamila tamkar Allah ya aiko su.
Da kyar makofta suka kwace ta.
Bayan gari ya waye da wuri Nadiya ta shirya ta fice kai tsaye gidansu Wasila ta nufa sakamakon suna da aji da shafen nan.
Sai da ta bari sun fito daga gidan ta yi wuce ta fiddo wayar ta ɗora a hannuwan Wasila.
"Me nake gani haka? iPhone 12 "
cikin gadara Nadiya ta furta "kwarai kuwa"
Wata iriyar kyarma ce ta kwacewa Wasila tuni wayar ta subuce a hannunta ta yo kasa...
Meenat A. 'Yandoma
***
***