MEERAH

02

by @oumfatima33

*MEERAH*

     *OUM FATIMA*

         *02*


        Ajiyar zuciya Momy dake tsaye a ƙofar ɗakin tana sauraronta ta sauke, tana cikin matsananciyar damuwa a kan halin da ƴar tata take ciki kwanakin nan.

   Tunda farko data kawo mata yaron a matsayin zaɓinta sai da ta gargaɗe ta tun kafin abin yayi nisa, saboda ta san halin Mahaifinta sarai. Ba zai taɓa amincewa  da zaɓin nata ba.

   Domin kuwa shi ɗin mutum ne mai matuƙar tsauri da tsats-tsauran ra'ayi, sannan idan ya kafe a kan abu babu mai iya sauya sa daga kan ra'ayinsa. 

   Ajiyar zuciya ta kara saukewa sannan ta murɗa ƙofar a hankali ta shiga da sallama ɗauke a bakinta.

   Cikin sauri na cire wayar daga kunne na ina kife ta a saman gadon da nake zaune, ina faman kif-kifta idanu. Kai tsaye inda nake Momy ta nufo tana kallon yanda duk nabi na tsargu da irin kallon da take min.

    Zama tayi a kusa dani ta riƙo hannayena cikin tausasa wa, ajiyar zuciya ta ƙwace min don na zaci faɗa zata min a kan wayar data kamani ina yi da Nawaz. Bayan Dady ya kafa dokar ko a waya bai yarda na ƙara magana dashi ba bare mu haɗu.

   Ganin tayi shiru tana kallona bata ce komai ba yasa na ɗora kaina a saman kafaɗarta na fashe da kukan da yake tsiƙarina a zuciya. Bata hana ni ba ta barni nayi kuka sosai, sai ma bayana data shiga shafawa cike da rarrashi.

   Sai da na tsagaita da kaina na fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta tayar dani na zauna da kyau. Cikin taushin lafazi irin na Mahaifiyar dake tsananin son ƴarta ta fara magana.

   "Ki natsu da kyau ki saurari abinda zan faɗa maki Ameerah." Natsuwar kuwa nayi kamar yanda ta buƙata na mayar da duka hankalina gare ta.

   "Abinda na saba faɗa maki shi zan mai-maita maki a yanzu ma, kuka baya zama maganin matsala ako da yaushe. Maimakon haka ki miƙa lamarinki ga Allah, ki roƙe shi idan akwai alkairi a cikin tarayyarki da yaron nan ya tanƙwara Mahaifinki ya amince dashi cikin sauƙi. Sabanin haka kuma ya musanya maki da mafi alkair." Ajiyar zuciya ta sauke sannan taci gaba da cewa.

   "Takura kanki da kike yi da  damuwa da ƙunci ba zai sauya komai ba, sai dai ya ƙara jefa ki a damuwa. Sannan kuma nima bana jin daɗin ganin ki a haka ko kaɗan!." Ta ƙare maganar cike da damuwa tana shafa kanta.

    Rungumeta na ƙara yi hawayen tausayin kaina da Momy na sake zubo min, cikin sautin kukan na fara magana.

   "Ya zan yi Momy? Ina tsananin son Nawaz, shima kuma yana tsananin sona. Ba zan taɓa iya rabuwa dashi ba, don Allah Momy kiyi wani abu Dady ya amince da shi, idan aka matsa min rabuwa dashi zaku iya rasa Ni Momy!." Na ƙare maganar cikin kuka ina sake ƙan-ƙame ta.

   Sosai gaban Momy ya faɗi jin kalaman da suka fito daga bakin ƴar tata, daurewa tayi ta danne yanayin da take ciki tace. 

    "Ki kwantar da hankalinki, in sha Allah zan yi bakin ƙoƙarina, amma ina mai baki shawara da ku  sauƙaƙa wa kan ki wannan soyayyar da kika ɗauke ta da zafi haka, kibi komai a hankali ki nemi zaɓin Allah."

    Momy ta faɗa tana jin al'amarin Meerah yana fara bata tsoro. Godiya nayi mata daga haka ta miƙe ta fice a ɗakin, bayan ta sanar dani in shirya in fito muyi lunch.

______________


  Cikin natsuwa da yanayinsa na sanyi yake takawa a gefen titin, Matshi ne da zai iya shekara 28 zuwa 30.  Dogo ne mai matsakaicin jiki, fari tas wanda a kallo ɗaya zaka shaida ya haɗa jini da Fulani.

   Baitukan waƙar da yake son ɗorawa a studio yake raira wa a cikin zuciyarsa har ya ƙarasa zuwa studio ɗin da yake zuwa ya ɗora waƙa a duk lokacin daya yita.

  Ƙofar gilashin ya tura ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, juyowa matashin dake zaune a gaban computer yana faman danna ta yayi.

   Murmushi ya wadata a saman fuskarsa ganin aminin nasa, cikin yanayi irin na abokan dake da shaƙuwa sosai Jabir da ake kira da JB ya miƙe ya bawa abokin nasa hannun yana masa kirarin daya saba masa idan sun haɗu.

    "NAWAZ BAFFA! Yaro mai zamani, matashin mawaƙi mai baiwa da basira. Da yardar Allah gobenka sai ta gir-giza maƙiyanka, kaga angon AMEERAH ABBAS MAMMAN GWANGWAZO. Ko za'a mutu sai ka amsa wannan sunan da yardar mai sama!." Ya ƙare maganar yana bashi hannu.

   Tattausan murmushi ya kufce daga fuskar Nawaz, don duk duniya idan akwai sunan da za'a ambata ya sanya dariya a fuskarsa to MEERAH ce. Bai san iya adadin soyayyar da yake mata ba a rayuwarsa.

   Yana mata wata irin makauniyar soyayyar da yake jin duk duniya babu wanda yake mata irinta, shifa gani yake ko iyayen da suka haife ta basu kai shi sonta ba. Mahaifiyarsa ta sha faɗa masa cewa yabi a hankali, don wannan soyayyar da yake yiwa yarinyar nana tana bata tsoro.

   "To yane, me muka samu? Na san ba za'a rasa wata zazzafar waƙar da zata tashi kanmu ba." JB ya faɗa yana nuna masa wurin zama, murmushinsa mai sanyi ya masa yace.

   "Ƙwarai kuwa, kai ma ka san in dai ina da Meerah a rayuwa bana rasa baitukan rairara wa ai." 

   "Kace yau akwai tashin kai?." Cewar JB yana murmushi.

   "A sosai ma kuwa, don yanzu ina waya da ita baitukan suka zo min. Kuma ta karɓe su da shaukin da ya saka naji ba zan iya kai wa gobe ba sai ɗora ta yau ɗin nan, saboda haka wannan ma tata ce." Nawaz ya faɗa yana tuna yanda take murmushi cike da shauƙi lokacin da yake rera mata waƙar.

   "To muje a kafta kawai." Cewar JB yana zuwa gaban Computer ya fara ƙoƙarin haɗa kidan da zai dace da waƙar.

   Kai tsaye Nawaz ya shiga inda aka killace don ɗora waƙar, abin sauraren kiɗa ya saka a kunnensa sannan ya tsaya a gaban mic ya lumshe ido ya fara rero dadaɗan baitukan da a lokacin da yake waya da ita suka zo kansa.

  Yayin JB ke nasa aiki, na ɗora kiɗan daya dace da karin waƙar.

   Wata baiwa da Allah ya yiwa Nawaz ita ce, baya rubuta waƙa. Da zarar tazo masa a kansa zai shiga rairawa kuma ta zauna a ƙwaƙwalwarsa daram.

   Mituna uku ya kwashe yana rera waƙar mai ɗauke da daɗaɗa kuma tausasan kalamomin soyayya ga masoyiyarsa Meerah. Wacce duk wani masoyi da yaji ta sai ta tsuma masa zuciya.

    Lokacin da ya sauke head phone ɗin dake kunnensa alamar ya kammala tafi da ihun mutanen dake wurin ya kaure dashi, JB kuwa kasa jurewa yayi sai da ya taso ya rungumi abokinsa cike da farin ciki yana yaba masa.

   Allah ya horewa Nawaz baiwar iya tsara waƙa, da kuma muryar rera ta. Nan gaba kaɗan idan ya ƙara samun gogewa ba ƙaramar ɗaukaka zai samu ba.

   "Ka tashi kai mutumina, Allah ya ƙara basira." JB ya faɗa yana bashi hannu suka yi musabiha.  Godiya ya masa fuskarsa ɗauke da murmushi. Sauran mutanen wurin ma hannu suka riƙa bashi suna taya sa murna, amsa ya riƙa yi cike da fara'a yana musu godiya.

   Daga haka ya samu wuri ya zauna yana kallon yanda JB ke aikin editing ɗin waƙar daya kammala kafin a sake ta, ya jima a studio ɗin kafin yayi ma JB sallama ya tafi akan idan ya kammala komai zai tura masa.

   Kai tsaye gidansu ya nufa dake Ɗorayi, matsakaicin gida ne irin na masu rufin asiri. Domin kuwa shi ɗin bai fito daga gidan masu dukiya ba.

  Mahaifinsa Malam Habibu da ake kira da Baffa ɗan sanda ne mai ritaya, Mahaifiyarsa Hauwa'u da suke kira Umma kuwa Malamar makaranta ce ita ɗin ma dai tayi ritayar. Saboda haka ɗan fensho da suke karɓa dashi dai suke rufa wa kansu asiri.

   Sai kuma shi da yake taimaka musu da ɗauke wasu nauye-nauyen, kasancewarsa babba a cikin su bakwai da iyayensu suka haifa, akwai ƙannensa mata guda uku sai maza biyu wanda sune ƙanana.......