RU'UYAA (The dreams we never lived)
3. ...na amsa tambaya a karon farko...🖋️
by @autum17
Fitowa nayi saye da farin hijabi na jakata ta ledar biki pink color riƙe da hannu na,ɗayan hannun kuma riƙe da jakar goyo mai zanen cartoon ɗin nan pirozin da farin hijab na miƙa ma Asma'u, ta samu jakar ne lokacin da sukayi wani spelling bee tayo na ɗaya
sandals ɗina baƙaƙe dake kitchen na ɗauko na cire slippers ɗin dake ƙafafuna na saka,itama na dauko mata nata brown na bata '' yau kuma mutanen na kai kenan?" ta tambaya tana ajiye cup ɗin data sha kunu ciki
'' ke kika sani!" na bata amsa takalmin kafarta ta cire tasa sandals ta saka hijabinta sannan muka tsaya gaban Mama dake ta kallon mu '' Mama mun tafi!" ƙullin zanenta ta kwance ta miƙo muna ɗari biyu '' Allah ya kiyaye '' Ameen na amsa ina yin gaba bayan na karɓe kuɗin '' bazata bani ba fa'' ta kai karata
'' tuwo kiba Asma'u ɗari ki ɗauki ɗari!" juya idona nayi sannan nace '' toh ''
biyo bayana Asma'u tayi, har ƙofa Mama ta rako mu tana faɗin '' banda biye biye,banda hawa bishiyar mangoro,kuyi addu'a kafin ku fita!" '' toh Mama '' muka amsa muna mata bye bye.kullum Mama sai tayi wannan maganar amma kuma kun sani babu yanda za'ayi mutum na secondary ace baiyi biye biye ba.. sannan wannan bishiyar mangoron bata da nisa da gidan mu kuma mafiyawanci nan muke haɗuwa da yan makarantar mu..
har yanzu da ya kasance karfe bakwai da rabi gari bai iyarda wartsake wa ba,kamar akwai hadari hadari don rana bata fito ba...
dai dai bishiyar mangwaro muka kawo '' riƙe min!" na miƙa mata jakata amsa tayi nikuma na shiga tattare wando na, na hawo bishiyar na fara tsinko mana mangoro
ina jefowa Asma'u na kamawa...
can sai ga wasu yan mata kusan su biyar saye da irin uniforms ɗin mu sun iso wurin haka na dinga katso ma kowa da kowa...sai ga ƙananan yara wasu almajirai wasu yan makaranta suma sun taru kowa ma so yake
ja Asma'u tayi ta tsaya gefe tana kallo dan tasan yau muda barin wurin sai wani ikon Allah
wani mutumi ya iso wurin da tsumagiyar shi yayi cikin yaran aiko kowa ƙafa me naci ban baki ba, tuntuni yake magana amma mun ƙiji
Ganin baba Iliya yana korar Mutane yasa na maƙe saman bishiya idan na sauko ya haɗa dani ban shirya ba…. ‘’ ki sauko ki tafi makaranta!” Baba iliya ya faɗa yana kallona ‘’ toh idan na sauko zaka buge ni?” Na tambaya a shagwaɓe
''ABEEDATU Allah ya shirye ki! Sauko bazan buge ki ba" a hankali na riƙe wani reshe daga bishiyar ‘’’ wiiiiyyyyy!” Na furta ina dariya tare da shilla ƙafafuna ina lilo cike da nishaɗi ‘’’ au..wasa ma kika tsaya yi ko?” Ya tambaya yana riƙe baki
‘’ yanzu zan sauko!” Na faɗa tare da sakin reshen na diro.. kuma fa tsaye nayi ban faɗi ba!...na kalli Baba iliya ina murmushi nace ‘’ nima nayi irin na yan chana…’’
Taɓe baki yayi yace ‘’’ tunda baki kare ba ai anci sa'a!” Sai na turo baki tare da yin gaba ina bubbuga ƙafafuna ƙasa
‘’ Allah ya shirye ki!” Ya sake faɗa…
ina kawo wa wata kwana naga su Asma'u zaune su shida suna jirana,suna ganina suka kwashe da dariya nima sai na taya su...'' ya dake ki? Ameena ta tambaya girgiza kaina nayi
'' ina zai dake ta ta zama mage da daddare ta hanashi bacci!" inji Aleeyah,juya idona nayi abinda ya zame min ɗabi'a idan Abinda mutum ke faɗa baida muhimmanci ko kuma abin situpit(stupid )ne
hira mukeyi har muka isa makaranta daidai an gama assembly class muka wuce,nida su Aleeyah ajin mu ɗaya SS3D Asma'u kuma science take... Muna shiga mathematics na shigowa ji nayi kamar in fasa ihu,bani son makaranta amma kuma naƙi jinin mathematics da malamin da kuma mai koyar da subject ɗin
'' Gooooood mooooooining sir!" muka gaidar dashi, kallon mu yayi cike da jin haushi kafin ya bamu izinin zama batareda ya amsa gaisuwar muba '' ku fito da mathematics note book ɗin ku,ku buɗe zuwa inda muka tsaya!" yayi maganar yana jinginar da zabgegiyar bulalar shi
kusan rabi da kwata na aji sai rarrabar ido muke kuma nima ina cikin su... a inda nake zaune daga baya dan back bencher ce duk wuya duk runtsi babu Ni a gaba
aji ya ɗau surutu tsawa ya daka mana tare da faɗin '' ba surutu nace kuyi ba ku nunamin littafin ku..'' kafin ya gama wayarshi tayi ringing
kallon kallo muka shiga yi wasu na shewa wayanda keda note kenan,wasu sun fara sun shiga uku wasu kuma suna faɗin in ma kashe su za'a yi saidai akashe su...wasu har sunfara kuka suna yarfar da hannu,oh...ashe ban faɗa muku cewa makarantar mu makarantar mata bace? makarantar mata ce toh
nidai daga inda nake zaune babu abinda ya dame ni nama ga nawar azo ayi dukan kowa yakama gabanshi bawai dan inason duka bane sai dai saboda bani kaɗai za'a daka ba, sannan wani irin daɗi nake ji ajiki na me haɗe da tsoro...
'' Operation show me your note!" wata mai suna Hameeda ta faɗa tana sheƙewa da dariya itama fa bawai dan tanada note ɗin ba,ga hadari daya taru aji yayi duhu da haske
da sauri muka fara yan dabaru masu ƙananan jakunkuna suka rage littafan su,sai su tusa jakar a bayan su idan malami na duka bazasu ji zafi ba..nima dai haka nayi
Bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da discipline master Wanda kafiri ne sunan shima gunta..amma tunda mu Hausawa ne kuma yan makaranta Mr Mugunta muke kiran shi, musamman ni...da muguwar fuskar shi da akoda yaushe murtuke take da kuma buɗaɗdiyar muryar shi yace '' idan kasan baka da note ka fito '' sai ga rabi da ƙwatar aji sun fito wasu harda hawayen su
zan iya rantsewa naga lokacin da ya lashe bakinshi tsabar mugunta kafin yayo cikin mu bulala biyar biyar,duk inda ya samu zunta ma mutum ita yake, hankali na ya tashi amma kuma wannan daɗin ƙara ratsani yake
musamman wasu idan aka dake su naga yanda suke faɗuwa ƙasa suna billiƙe billiƙe kamar tanar da aka zuba ma gishiri abun dariya yake bani wasu harda yar drama '' wayyo Mallam tsaya kar ka karye Ni....na bani na shiga uku.... wallahi Ni kaɗai mamata take dani.....dan Allah kayi haƙuri...mamata ki taimake ni.....'' haka dai
lokacin da aka kawo kaina ba ƙarya nima bulalar ta shige ni wallahi ba ƙarya amma sai na dake
lokacin da yagama zane mu wasu harda kukan su,shiko sai huci yake harda zufa yana cigaba da murmushi
Bayan ya tafi kowa ya koma seat ɗinshi aka fara wani banzan ni nama manta sunan topic ɗin amma dai nasan akwai logic ciki...oh na tuna logarithm...har da wani graph Wai sai mu gano wata banzar X da Y can...har yayi ya gama wallahi komai ban gane ba
yana fita aji ya kacame da surutu '' kai amma mutumin nan anyi tsinanne... wallahi bulalar da yayi min babu wadda ta shige ni sai ta ƙarshe dan ga ɗuwawu ya zunta min ita da ƙyar nake iya zama!" inji A'ishah class Captain,muka kwashe da dariya suma wasu sai ƙara tsine ma mr mugunta suke
wani Malami ne ya leƙo '' wane subject kuke dashi yanzu?"
'' I.R. S'' suka amsa tare gyaɗa kai yayi yana faɗin '' ku fito da littafin ku kafin yazo!" muka amsa da '' Yes sir '' amma babu wanda yayi hakan
'' Macijin sari ka noƙe muke dashi fa!" Muneeba ta faɗa tana kallona, wannan sunan nice dakai na na raɗa masa shi me yasa? mutumin tsohon munafuki ne kuma na tsane shi...tantagaryar ɗan iska ne,na rantse ba sau ɗaya ina ganin shi a hotel ɗin danake aiki ba da yan mata daban daban suna iskancin su
amma idan yazo gaban mu sai yayi tayi kamar na Allah yana jawo ayoyin Alkur'ani da hadisi yana fassarawa, yan mata da yawa harda ni ada yana burge su..sai da na gano waye shi Sannan nagane cewa kuskure ne...yan mata da yawa suna matuƙar macewa akan mutumin nan musamman saboda kyakkyawa ne gaskiya,ga ilimin addini ɗalibai sun yarda dashi basu kaɗai ba harda iyayen su,na rasa dalilin dayasa mutane irinshi ke ɓoyewa bayan addini suna cin amanar ɗalibai da iyayen su da kuma addini duka...
ina tsaka da tunani ya shigo ajin yan mata suka fara gyare gyare, yanda ya tsuke fuska zakayi tsammanin mutumin kirki ne...naji daɗi sosai da Asma'u ta rabu dashi,nasan lokacin dayake magana da ita da zummar yana sonta sai ya dinga kiranta office ɗin shi... Allah yasa na gano hakan da wuri na kuma taka musu burki na rabasu kuma tayi min alƙawarin bazata sake ba,bansan ya zanyi ba idan wani abu ya faru da ita wani banza ballagazan namiji ya lalata rayuwar ta... lokacin harda zuge ta yake akan ni ina kishi da ita ne don tafini komai...abun ya baƙantamin rai sosai
ya sani nima kuma nasani nidashi maƙiya ne na har abada bazamu taɓa shiryawa ba!
'' me kike tunani?" naji muryarshi kusa dani dab da kunne na,da sauri na juya na kafe shi da idona da launin suke ƙara rinewa idan na tsani mutum,idan kuma inason mutum idona har wani ƙyalli suke idan nayi fushi ko kuma bana son in nuna emotions idona size ɗinsu ragewa yake
kallon shi nake cike da tsanar data kasa ɓoyuwa a idona '' meye damuwarka?" na mayar mashi da tambayar
haɗiye fushin shi yayi tare da faɗin ki maida hankali,komawa yayi gaban allo kowane sakan biyar sai ya kalle ni har yayi ya gama bance komai ba..yan matan ajinmu kuwa sai biloshing suke...bafa haka kalmar take ba amma aidai kungane ko?
Bayan ya fita sai ga Civic ta shigo,nifa bana maida hankali idan ana karatu dan ba ganewa nake ba,amma yau topic ɗin da aka koyar damu yaja hankali na sosai,da farko waje nake kallo kamar koda yaushe ina tsarawa acikin raina yanda zanyi kyau idan inada wannan da wancan idan fuska ta babu pimples idan... idan...
'' Our topic for today is SELF ESTEEM!!". Muryar malamar ta dawo dani daga tunani na, duk da bansan mai hakan ke nufi ba jinayi ina so insan ma'anar hakan yasa na mayarda hankali
'' wa zai faɗa min me ake nufi da SELF ESTEEM?" ta tambaya tana kallon mu, mutane dayawa sun ɗaga hannu amma babu wanda ya cinki ansar da kyau..nuna ni tayi tareda faɗin '' meye ma'anar SELF ESTEEM?" kallon mutane nake ido waje kamar yanda suke kallo na,sun sani na sani bansan amsar ba,wasu har sun fara dariya, yawu na haɗiye kafin na miƙe ina kallon malamar da itama nitake kallo batareda tunani ba nace '' sef istim na nufin sanin darajar kai da kuma samun ƙwarin guiwa a duk abinda mutum yake...kamar dai ace yaƙini.. mutum yazama mai yaƙini akan kanshi!" na amsa da ina ina,ina shafa kunne na inda ake sa ɗan kunne idona ƙasa..duk sanda nake jin tsoro kaɗan haka nake
ji nayi yan aji suna dariya,banji ba daɗi ba don abune dana saba dashi malamar ta kalle ni tareda ƙara faɗin '' shine amsar ki?" ta tambaya,gyaɗa kaina nayi alamar eh
'' CLAP FOR HER!!!" ta faɗa da ƙarfi,sai kawai suka faramin tafi sakin baki nayi kafin na zauna na kasa yarda wai yau ni ake tafa mawa abinda bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru goma sha bakwai na rayuwa ta, suma yan ajin mu sunyi mamaki don dai sun sani niɗin daƙiƙiya ce lambar ƙarshe ban taɓa daga hannu don amsa tambaya ba ban kuma taɓa amsawa daidai ba koda kuwa amsar a bayyane yake
bayan wani lokaci malamar ta fara bayani da turanci
- Self-esteem: It's how you feel about yourself, your worth, and your abilities. It's your internal evaluation of yourself.( self esteem shine yanda kake ji game da kanka da kuma yanda, amfanin ka,da kuma abunda zaka iya yi... yanda kake ji azuciyar ka dakuma yanda kake ɗaukar kanka... Sai kuma akwai low self esteem da high self esteem
- Low self-esteem: You're kinda down on yourself, doubt your abilities, and might feel unworthy or not good enough. 😔( Shine tsaurarawa Kai, kokonton abinda zaka iyayi da wanda bazaka iya ba, sannan kake ji kamar baka cancanta ba ko bakada amfani ko baka kai ba....
- High self-esteem: You feel confident, capable, and worthy. You like who you are and trust your abilities. 💪 ( high self esteem,kanajin ƙwarin guiwa, zaka iya, ka cancanta...kana son kanka kamar yanda Allah yayi ka,baka neman wani ya yabe ka ko ya soka sannan kayarda da abinda zaka iyayi...
misalin low self esteem=
😔
- Constantly comparing themselves to others ( haɗa kanka da Wasu)
- Saying "I'm not good enough" or "I'm a failure" ( cewa ni ban isa ba kuma ban kai ba ta hanyar raina kai)
- Avoiding challenges or new experiences due to fear of failure ( gujewa ƙalubale da sabon abu gudun kada a faɗi)
- Needing constant validation from peers ( buƙatar mutane su yabe ka ko abokai)
- Negative self-talk or self-criticism (Maganar da bata dace ba ko mara daɗi wa karan kanka)
- Difficulty accepting compliments or praise ( wahalar yarda idan an yabe mutum)
- Feeling like they're not worthy of love or respect ( ji kamar basu cancanci a girmama su ba ko a sosu..) tunda malamar tafara magana na nitsu bani kaɗai ba ma harda sauran yan aji... bamu taɓa bada hankali ga wani subject ko topic ba kamar yanda muka bada a wannan topic
nake ji araina kenan bani kaɗai bace mai wannan sef istim ɗin? ke nan low self esteem ɗin kesa ina kushe halitta ta kuma ina haɗa kaina da Asma'u,low self esteem kesa inason in cire pimples daga fuskata sannan in zama me kyau don a yabe Ni? badon hakan shine abunda nake so daga ƙasan zuciya taba!
tunani na ya katse lokacin da naji Malamar na faɗin '' nasan dayawa daga cikin ku abinda ke damun ku kenan,akwai abubuwa dayawa da zaku iya yi amma saboda kuna gudun kada a kushe ku ko kada ku faɗi sai ku ƙiyi...da yawa daga cikin ku kuna kallon kanku kamar munana ko idan jikin ku bai girma ba, dan baki da ƙaton ƙirji ko ƙaton ɗuwawu ko girman hips ko idan kina da wannan masu girma da suka girmi shekarunki sai ki dinga jin kunya.. kina gudun abinda mutane zasu ce...ya zama rayuwar ki gaba ɗaya ke burin ki ki burge mutane ko dai ki tsira daga maganganun su....idan har kina ji yanda kike bakya son kanki a haka,kina ji yanda mutane suke so ki kasance haka kema kike so ki kasance to kina da low self esteem!"
tayi shiru tana kallon mu kamar tana ƙoƙarin gano idan mun fahimce ta tacigaba da faɗin '' ku kalle Ni,ku kalli fuskata duk pimples, shekaruna ashirin da bakwai amma wasun ku sunfini girman ƙirji da ɗuwawu da hips.. kin gane ni idan ina tafiya ina nuƙu nuƙu?"
'' a'a'' muka bata amsa muna ƙara kallon ta da kyau yau nima naga wadda ta girme ni kuma take a shafe kamar ni hakan ba ƙaramin ɗaukaka sef istim ɗina yayi ba tacigaba da faɗin '' wasun ku suna tafiya suna nuƙu nuƙu cikin hijabi badan suna jin kunyar Allah ba sai dai saboda suna gudun maganganun mutane...ku dena kunyar yanda Allah ya halicce ku,kuso kanku yanda kuke... babu wata wacce tafi ki,you're beautiful a yanda kike bakya buƙatar saiwani ya faɗa maki... love your self! abinda wani yake tunani game dake ba damuwarki bane,abu me muhimmanci ya kika ɗauki kanki? kina da HIGH SELF ESTEEM OR LOW SELF ESTEEM shine kawai" ta ƙarashe maganar tana kwasar littafan ta
miƙewa nayi tsaye na fara mata tafi haka ma sauran yan aji suka bini juyowa tayi ta kalle mu tana murmushi muma muna dariya '' muna sonki sosai malam Hafsah '' muka faɗa kusan atare dariya tayi tana mana bye bye tace'' nima ina son ku '' sannan ta fita.....
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️