Page 61
💫MARYAMA💫
61....
"Plsss karki sanyawa ranki damuwa Innarmu,I have only you in this Dunya, kuma kinji abun da likita ya fada a kan condition da kike ciki".
Hawayen da ya cika mata idanu tayi kokarin Mayarwa dan ta karfafa mishi guiwa ta ce, "Kaima kar ka tayar da hankalin ka duk abun da kaji ya faru, ka zama mai biyayya na tabbata Baffanku bazai taba aikata abun da zai cutar da kai ba, duk abun da kaji ka yi kokari zuciyarka ta dauka, ka zama namiji mai iya hadiyar zaki da madaci, sanyi da zafi, ka ji ko"
Ba don ya fahimci inda maganganunta suka dosa ba ya gyada mata kai kawai da fadin "Insha Allah Innarmu," Allah ya maka albarka,idan Baffanku ya dawo zai nemeka" ta fada tana shafa sumar kanshi.
Su Basira da tawagarsu suna fita ko minti biyar ba'ayi ba, mahaifiyar Siyama ta shigo gidan a fujajan kamar an hankado ta, tun a tsakar gida ta fara bala'i da tofin ala tsine akan Innarmu.
"Ina kuke dangin jaraba bakin haure mayu masu lashe kurwar mutane? ku zo ku fitar min yata in ba haka ba za'ayi yakin duniya na uku. kurwar yata kurrr wllhi namanta daci ne dashi, a fito min da yata nace"
Ta fada cike da hargagi da daga murya, hayaniyar da ta shigo dashi ne ya dakatar da Innarmu daga shiga madafa da tayi niyyar yi. Hakama Jabeer ya dakata daga shiga dakinshi da ya nufa.
"Baiwar Allah lafiya zaki shigo har gida kina jifanmu da munanan kalamai haka? kinsan wannan ba karamar jifa'i bane ko?" cewar Inna da tashin hankali ya gaza boyuwa a fuskarta.
"Lafiya,? Ai babu zancen lafiya kuma tunda kin lashe min kurw..."
Dakatawa ta yi da maganar sakamakon gyaran murya da Baffa ya yi yana shigowa, Jabeer kam mutuwar tsaye ya yi jin furucin da ke fita daga bakin matar.
"Dijah me ke faruwa ne haka,?" Baffa ya jeho mata tambayar, "Ranka ya dade nima ban fahimci inda ta dosa ba, ta dai shigo kawai ta fara jifata da jafa'i kala kala ba tare da nasan abun da na aikata ba,"
"Baiwar Allah lafiya dai?" ya tambaye ta.
"Inafa lafiya tsoho, wannan munafukar matar ta cinye min yata, dama an dade ana rade radin cewa mayyace amma bamu yadda ba sai yanzu, ni tunda na ga Siyama ta kulla kawance da wannan yar taku kodaddiya mai kama da sulalliyar karas na san babu lafiya, kwatsam aka nemi Siyama aka rasata sama ko kasa, munyi neman duniya babu ita babu dalilinta, munje wajen malami ya mana istikhara shine fa ya gano cewa mayyar matar nan ne ta lamushe min 'ya ta ta 'yar kuma ta sadaukar da ita wa dodonsu na mayu dan munafurci kuma shi ne ake ta kumbiya kumbiya, to wllhi a fitar min 'yata ko mu kwashi yan kallo tare da ku, na baku awa ashirin da hudu in ba haka ba..." Daga haka ta juya ta fita.
Ba Inna da Jabeer da suka sandare a tsaye ba, hatta Baffa ji yayi kafafunsa suna rawa, kanshi yana sarawa.
A hankali Inna ta fara tafiya kasa kasa yayinda take ganin wasu irin giragizai suna ta shawagi a sama, a hankali bakinta ya furta "Maryama!"
lokacin da ta kai kasa, sai kuma da karfi ta ce, "Maryamaaaaa" idan ka ganta a lokacin zaka iya rantsuwa cewa kanta ya kwance.
"Maryama a sanadin haihuwarki yau an kirani da Mayya mai cin mutane, a sanadin haihuwarki yau ance da ni mai dodon tsa..."
Shiiittt"cewar baffa yana rufe mata baki da hannunshi, cikin taku mai cike da karfin Hali Jabeer ya matso kusa garesu ya durkusa hadi da kama hannunta duka biyu.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Jabeeru wannan wacce iriyar masifa ke bibiyata, wannan wacce irin masifa ce na shiga uku na lalace, haihuwar ta ba tai min rana ba."ta fada tana tsiyayar da hawaye masu tsananin ciwo.
"Innarmu karki fadi haka, ki daina yi mata kuka, hawayenki tashin hankali da masifa ne a gareta" cewar Umaimah da babu wanda ya kula da fitowarta sai muryarta suka ji tana sharewa Inna hawaye.
Dago Inna Jabeer ya yi, dan baffa gaba daya ya rasa garkuwar jikinsa shima, daki ya wuce da ita har kan gadonta ta zauna tana cigaba da gunjin kuka, tsugunnawa ya yi gabanta ya kama kafafunta duka biyu ya rike ya ce, "Innarmu ki daina kuka,ki dinga nanata wannan addu'ar a ranki.
(La ilaha ilallahul Azeemul Haleem. La ilaha ilallahu Rabbul Arshil Azeem. La ilaha ilallahu Rabbus Samawati, Wa Rabbul Ardhii, Wa Rabbul Arshil Kareem.)...
Ki yawaita karanta shi yana gusar da damuwa da bacin rai da izinin Allah.
Ba Inna da ya sanarwa ba hatta Baffa da Umaimah da suka biyosu take suka kama addu'ar dan duk dinsu suna cikin kunci da damuwar.
Bayan komai ya lafa ne da daddare dukkansu suna zaune dakin Innarmu, Baffa yana zaune bakin gado, Inna kuma tana kwance bisa gadon jikinta ne ya tasar mata, Jabeer yana zaune bisa durowan gado, kanshi a kasa banda sarawa babu abun da kan nashi ke yi tunda Baffa ya sanar mishi maganar auren da aka daura mishi da Umaimah, ya rasa a wanne ma'auni zai aje batun, and yasan jayayya da duk wani hukunci da Inna ko Baffa suka aiwatar a kanshi shine abun da yake rokon Allah da kar ya bashi ikonyi.
Umaimah da Fati da Salima duk suna zaune kasa, Itama banda rawa babu abun da zuciyarta ke yi wai Hamma Jay din pretty shine mijinta, kai ina wannan ba mai yiwuwa bane, sai dai kuma bazata taba komawa gidansu ba, nan wajen Inna zata zauna, but Jabeer a matsayin mijinta shima ba abune mai yiwuwa ba.
Baffa ne ya cigaba da magana, "Kamar yadda na fara fada dazu, dukkaninmu kowa ya kimtsa abun da yake bukata nan da kwana biyu zamu koma nijar dan bazan cigaba da zama a nan in zuba ido ana ciwa iyalai na mutunci ba, bazan cigaba da zama ina gani ana wulakanta mu ba dan haka na yanke shawara nanda kwana biyu zamu wuce mu koma tushenmu muma, zan yi magana da daada, kema Umaimah kiyi hakuri da yadda kaddarar ki tazo miki, kin taso a birni, ga shi yanzu zamu tafi kauye dake inda baki taba zuwa ba."
Kamar yadda Baffa ya fada hakan ce ta kasance suka tattara duk abun da suke bukata cikin kwana biyu, wani dare da bazasu taba mantawa da shi ba, daren da bazai taba gogewa cikin taswirar kwakwalensu ba, ana gobe da asuba zasu wuce Nijar, baffa na dakinshi, Inna da Umaimah suna dakin Innar, Salima da Fati kuwa suna Dakinsu yayinda Jabeer ma ke nashi dakin. Dare ya tsala sosai wajajen karfe sha biyu suka fara jiyo hayaniyar mutane mafi akasari muryoyin maza ne matasa irin yan a mutu din nan, "Ku cinnawa gidan wuta MAYU ne dangin jaraba a kona gidan a kona gidan"...Shine kawai maganar dake tashi daga waje, a firgice duk suka mike dan babu wanda ya yi bacci dama a cikinsu sai yaran fati da salima,.
Baffa ne ya fara fitowa daga dakinshi cikin sanda ya matso tagar Inna, yace, "Dijah wannan ne abin da na yi gudun yasa na ce zamu tafi nijar, gashi kuma mai afkuwa ta riga da ta afku, nasan yaran nan sarai basu da kirki ko kadan, maza ku fito mu gwada ficewa ta baya ko za'a dace, dan babu abin da hukuma zasu iya mana," da sauri sauri yake maganar yana jin yadda suka fara jifan gidan da duwatsu wasu kuma suna buga kofar da nufin ballewa.
A rikice Jabeer ya fito daga dakinshi, ganin Baffa jikin window yace, "Baffa yaran nan ne fa yan...."
"Jabeeru yi shiru maza fito mu gwada fita ta baya," da gudu jabeer ya dauko wani dogon tsani ya kai ta baya yana dawowa su Inna suna fitowa tace, "Jabeeru mun shiga uku, kaga abun da ya same mu ko?.. "Dijah wannan ba lokacin magana bane, yi hanzari ki kamata ku haura ta kan wancan tsanin".. Ya fada yana nuna tsanin, "Baffansu ku fara sauka bari in dauko yaran nan, yanzu haka basu san abun da ke faruwa ba, idan sun fara bacci kam..."
Maza Dijah ku tsallaka zamu fito dasu, ba don ran Innarmu ya so ba ta kama hannun Umaimah da jikinta ke ta mazari suka hau tsanin hadi da dirga ta baya, hakan kuwa ya yi daidai da ballewar kofar da yaran ke ta faman bugu, suka shigo babu iyaka suna fadin "Mayu ne, mayu ne, mayu ne" abun mamaki kuwa babu wanda ya fito daga cikin gidansa da nufin taimakonsu, kowa yana makale a gida yana gudun ranshi.
Zaro ido Baffa ya yi lokacin da yaga sun fara cinnawa gidan wuta, a haukace ya shiga dakin su Salima ya same su makale da juna sai faman rawar jiki suke yi kafin ya kamo su aka harbo wani kwalba mai dauke da wuta a ciki, bauuu haka ya tashi a dakin, ihu yaran suka fara da kiran Innarmu Baffanmu, Hamma Jabeer kuzo ku taimakemu.
Su inna da suka dirqa ta baya wani irin wawan firgita suka yi har cikin kunnenta ta jiyo maganar yaran nata suna kiranta tazo ta taimake su hakan ya sa ta juya da gudu zata zagaya ta gaban gidan da nufin shiga dan taimakon yayan ta, da sauri Umaimah ta rikota ta ce, "Innarmu dan Allah kar ki je, Baffa zai fitar dasu da Hamma jay dan Allah, Jabeer yana dakinshi sai faman harhada Important takardunshi yake yajiyo ihun Yaran suna kiran sunanshi, wani irin hantsilowa ya yi daga gaban dirowar da yake hada takardun ya cusa iya wanda ya dauka cikin rigarshi ya fito, saidai ganin gidan gaba daya yana ci da wuta ya kara rikita shi, ga wani irin tururi dake busoshi, gefe kuma ga kukan su Fati da kuma tarin Baffa da yake jiyowa sama sama, gabas da yamma na gidan ci yake da wuta kamar ana zuba mishi petur.......