MARYAMA

Page 62

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

64..


Yau sati na daya a hospital ina jinyar zuciya da ta gangar jikina, amma ko da leke Innarmu da Hamma Jay basu leko ni ba dan ganin halin da na ke ciki, Umaimah ce kawai ke jigila dani cikin wannan kwanakin har na fara samun sauki, tare nake wuni da ita da dare kuma wata da nake kyautata zaton mai aikin gidanta ne take zuwa mu kwana, cikin satin nan ko sau daya ban kawo maganar yadda akayi na gansu a abuja ba itama bata kawo man zancen ba...

Yau ya kasance Saturday, kamar kullum ta shigo dakin da na ke kwance sanye cikin sutura na alfarma doguwar riga mai fadi da babban mayafi tayi kyau har ta gaji. Jikinta yana ta tashin sassanyan kamshi fuskarta wasai wannan fara'a dake makale kan face nata da yake natural tun asali ya kara kawata mata fuskar, cikin jikinta ya fito das dashi gwanin sha'awa, hannunta rike da wannan kyakkyawar yarinyar da hoton fuskarta ya kasa barin idon zuciyata, bayanta wani bodyguard ne rike da babban basket dake dauke da kuloli da flask da sauran tarkacen abinci.

Idanunta a kaina har ta iso gaban gadon taja kujera ta zauna, gyara zaman filin dake bayana nayi wanda shine ya taimaka min jin dadin zaman ina mayar mata martanin murmushin da ta aiko min


"Ya karfin jikin pretty?" ta fada tana kallona.

"Jiki ya yi sauki Umaimah, na gode da kulawar ki gareni, su Innarmu ba za su zo ba ko, suna fushi dani ko? Nasan dole suyi fushi Umai...." katse ni Umaimah ta yi ganin na fara kuka.

"Shhhtt" ta fada tana daura yatsa akan lebenta, "Kuka is not good for your health you know, dan haka ki daina, yakin lafiyar ki muke yi yanzu, idan kina kuka kuma komai tabarbarewa zai yi ohk?" ta karisa tana dage min gira.

Shiru kuwa na yi ina share hawaye na nace, ina mika hannuna "Baby zo?" amma sai yarinyar ta makale kafada tana kara shigewa jikin uwartata wani irin daci na ji a makwogorona amma sai na danne ina murmushin karfin hali

"pretty oya go to mommy, she's your mom also". Cewar Umaimah tana dan zarewa yarinyar idanu.

"She's my momm?" ta tambaya tana kallon uwar a dan tsorace.

"Yes mommyn kice," "

But mommy Daddyna told me that yo...." 

"Shut up! wuce ki gaisheta na ce." 

"Haan Umaimah kar ki tsorata ta mana, yarinya ce ai," na fada muryata tana rawa da kokarin boye halin da nake ciki.

Haurowa saman gadon yarinyar ta yi har kusa dani. 

"Morning Mommy,inji mommyna wai kema mommy na ne" ta fada da murya irin na yara.

Kamata na yi na kwantar da ita bisa kafata dake mike ina shafa lallausan gashin kanta na ce, "Morning dear, nima mommyn kice kina sona" na fada cike da rauni ina tuna nawa cikin, da yanzu nima ina da ya wacce ta fi wannan ma a shekaru...

Kallon mamarta meerah ta yi tace, "Mommy na wai ina sonta?".Gaba dayansu kwashewa suka yi da dariya jin abun da ta fada, Umaimah ta gyada mata kai, hakan yasa meerah fadin, "ehh ina sonki".

"She's very fast and sharp Umaimah".

Murmushi Umaimah ta yi ta ce, "Just like her namesake".

ban samu damar tambayarta ba wayarta dake hannunta kirar iphone 14pro ya fara tsuwwa, tsam ta mike ta fita dan amsa kiran, ni kuma ina cigaba da shafa kan meerah ina mata tambayoyi akan makaranta har ta dawo dakin tana zama da kyar.

"Cikin zolaya na ce, "yau kuma yusuuf din ne ake jin kunyar yin waya dashi a gabana? me yasa baku zo tare ba, ko aiki ne ya rikeshi,?" na watso mata tambayar.

Take fara'ar dake kan fuskan Umaimah ya dauke cak ta fara wuki wuki da idanu kamar marar gaskiya gabanta na dukan tara tara,wani irin dunkulewa abun da ke cikinta ya yi hakan yasa ta yi saurin daura hannunta bisa cikin tana shafawa a hankali ba tare da ta kalleni ba.

Ganin bata ce komai ba yasa ni jan bakina nima nayi shiru ina cigaba da shafa kan yarinyar dake kwance bisa kafata, shigowar nurse ne ya katse mana shirun inda ta duddubani sannan tace inci wani abu lokacin shan magani ya yi.

Da sauri kamar jira take dama ta mike tana fadin "bari in hada miki breakfast din gashi na taho miki dashi amma kin rike ni da surutu,"dan bowl mai fadi ta dauko ta zuba min peppe soup na kayan ciki ta sa spoon a ciki ta ce tana miko min, "ki fara da abu mai dan ruwa ruwa idan kinsha maganin sai kici abinci".

Hannu biyu na karba ina jinjina kaunar Umaimah gareni a zuciyata, a hankali na fara shan parpesun yayinda nake jinshi tamkar madaci a bakina dan rashin apetite, amma haka nake daurewa dan kar in bata kunya ganin yadda take dawainiya dani.

"Baby ta so ki sha pepe soup" na fada ina taba kan meerah dake kwance jikina har lokacin bata tashi ba.

Dagowa ta yi cike da yarinta ta ce, "Mommyna ta bani a gida, kuma sunana ba baby ba, bari kiji sunana"

ta fara lankwasa yatsarta karami.

"Hoo talkative, ba na hanaki yawan magana ba, uhmm?"   

Mommyna baby take kirana fa kuma ba haka sunana ba".

"Barta ta fadamin mana Umaimah" oya fadamin sunanki my baby".

"Kinga Innarmu da Baffanmu Suna kirana Namirah, kema kina da Inna da baffa irin nawa?" 

Gyada mata kai na yi da sauri ina rufe idanuna jin wani abu ya tokare min makoshi.

Daddyna kuma yana kirana Meerah, Anty Fati da Anty Salima da Mommyna kuma suna kirana Pretty, kema kina da anty da mommy,?"

Ta kuma tambayata, wani irin zillo kirjina ya yi jin sunayen da ta ambata, kafin ince komai ta cigaba da fadin, "A school namu da tahfeez kuma ana kirana.

MARYAMA JABEER ALHUSSAIN."...

Wani irin tari ne ya sarkafe wuyata sakamakon hadiyar da nayiwa abun da ke bakina cikin gaggawa sai dai cikin rashin sa'a ya kauce hanya hakan yasa shi shigewa ta cikin ramin hancina, tari na dinga yi idanuna suka kwalalo waje suka kada jajur a take ta dalilin yajin dake cikin parpesun.

"Subhanallah sannu pretty sannu" cewar Umaimah da tayi mutuwar zaune, da kyar ta yunkura ta mike ta dauko ruwan gora ta buda tana sanya min a bakina, ruwan nasha kadan ina maida numfashi sama sama, "Sorry" ta kuma fada jikinta a sanyaye.

"Sorry second Mommy, ki daina kuka" cewar Namirah tana kai hannunta saman fuskata da goge min hawayen dake ambaliya da ban san ma ina kuka ba saida takai hannunta fuskar tawa, ".

A dai dai lokacinne kuma wani daddadan kamshi da ya gauraye da wani kamshin da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata ya bakunci kofofin hancina, A tare muka dago dukkanmu muka sauke idanunmu kan masu shigowa, idanuna ne ya sarke cikin nashi, yana sanye cikin milk colour shadda getzner sai maiko take da daukar ido, kallo daya zaka fahimci ba kananan kudi kayan suka lamushe ba, dinkin riga tazarce da wando sai bakar hula zanna bukar dake kanshi, kana kafafunshi sanye cikin takalma half cover na maza shima baki, hannunshi daure da agogo kirar rolex baki, sai zabba dake yatsunshi guda biyu, ya yi kyau matuka ya yi wani fresh dashi haskenshi irin na buzaye ya fita tas fuskar nan sol har wani naso yake yi, babu wannan daudar da kodewar na rana, idan ba asalin sani ka masa ba, a kallo daya bazaka ce wannan Jabeer kafinta nan ne ba, yana tsaye kikam a bakin kofar ya harde hannayenshi a kirji, bayanshi ya dan jingina da bango ya nade kafa daya ya taka jikin bangon dashi, duk a cikin second biyar na mishi wannan kallon, da sauri na janye idanu na ina mayarwa kan Daada da suka shigo tare wacce ta sanya kuka mai karfi tana kama kafata har da su fyace majina 

Cikin kukan ta ce, "Ni dama nasan addu'oin da muke yi bazai fadi kasa a banza ba, Allah maji rokon bayinsa ga shi nan ya jeho mana ke rana tsaka.

Saida na fada musu cewa hannu a ka sanya miki, jifa ne, amma suka ki, idan ba jifa ba jama'a duk wanda ya fita duniya ai da kumari yake dawowa da arziki, amma dubeki takwara kinje kin dawo a lalace, a firgice kamar guzurin mayu, duk kin fige Allah na tuba ka yafeni kamar mai kanjamau wannan duk sharrin jifa ne, kuma ina nan ina bincike duk wadda na samu da hannu wajen aikata miki haka sai anjimu da shi a duniya.

Taune lips Jabeer ya yi da karfi kamar zai huda su, sannan ya fara takawa zuwa gabansu. Ta gefen ido nake kallonshi duk takun da yai sai zuciyata ta buga.


Difff na tsaida numfashina lokacin da ya iso daf da gadon, tsunkuyawa ya yi ya bawa cikin dake gaban Umaimah wani kyakkyawan kiss ya shafa cikin sannan ya tunkaro inda nake, cakkk numfashin nawa ya dauke time da sunkuyo kaina har muna shakar numfashin juna, kyawawan hannayenshi ya sanya gami da daga Meerah dake kwance jikina ya mike yana yatsina fuska kamar wanda ya ga abun kyama.

Kusan suma Umaimah ta yi a wajen tsabar kunya ji tayi kamar kasa ya tsage ta shige ciki...""Daddyna yaushe kazo?" meerah ta fada tana taba kwantaccen sajenshi da ya kawatu da gyara sai daukar ido ya ke yi, lumshe ido ya yi kana ya bude yana shafa kanshi da hannu daya kamar kullum ya ce. 

"Na dade a nan ai my princess na zo daukar ki da Mommy da little ne mu koma gida,".

"Yauwa Daddyna I love you". Ta fada hadi da bashi kiss a goshi kasancewar yana rike da ita, shima peck din ya mata a kumatu yace, "And I love you too princess".

"Tashi muje gida ki huta haka nan madam," ya fada cike da command yana kallon Umaimah da kafarta suka fara hayewa suntum kamar filawa ya ji yeast, dama haka yake mata matukar ta jima a zaune.

Samun kanta ta yi da kasa yi mashi musu, ta mika mishi hannunta ya kama ta mike da kyar ba ta yadda sun hada ido da Maryama ba tace, "Pretty zan dawo anjima, make sure kin sha drugs na ki plsss". Daga haka suka fara tafiya yana rike da hannunta daya hannun kuma yana rungume da Meerah.

"Ahh, kaga ja'iri, a gabana kake irin wannan abu haka Jabeeru, tukunna ma ina ce yar uwarka ka zo dubawa bata da lafiya? Amma ka buge da jan hannun matarka zaka tafi ko ya jiki baka ce mata ba, ita kuwa tsabar jaraba irin taku ta yayan yau ta wani bika zuqai zuqai kamar talo talo, to me zaka mata da wannan uwar cikin dake tsaye gabanta kamar kwarya?" cewar daada tana kankance idanu.

Juyowa Jabeer yayi with smile on his face, ya ce, "Wannan tsohuwa akwai kinibibin tsiya, matata fa ki ka ce dan na dauketa ai banyi laifi ba, da kike tambayar mai zan mata kuma, wannan ba hurumin ki bane. Kin san dai ba'a shiga tsakanin mata da miji," ya fada yana kara matso Umaimah dake jin kamar ta nutse a wajen jikinshi, kafafunta har rawa suke yi.

"Ohhh ni Maryamu wannan duniya ina zaki damu?, to ita yar uwar taka da ba ka mata sannu da jiki bafa,?"..

"Daada ni banga mutum ba, dan haka duk sadda kika gama abun da ya kawoki driver yana jiranki waje,"daga haka suka fice daga dakin.

Wani irin ihu Maryama ta fashe dashi tana jin kirjinta na mata zafi a take kanta ya fara sarawa.


"No,Ya Allah No...Ya Rabb..Dont let it be, Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un." kawai Maryama ke maimatawa tana kuka kamar ranta zai fita, duk yadda taso ganin ta hana kanta kukan kasawa tayi dole ta barshi ya fita kawai, Umaimah, Hamma Jay, Ya Rabb no plssss."

Tagumi Daada ta yi tace, Dole ki koka yan nan, muma nan haka muka koka miki da faruwar wagga lamarin amma ai idan bera ta iya sata, ko shakka babu daddawa ma da warinta...

Dan haka yi kuka ki godewa Allah, tukunna ma ina kika shiga haka kika dawo mana a fige kamar kazar mayu? Na yi zaton zaki dawo kin zama hamshakiyar attajira, amma sai ki dawo ko zanin daurawa babu a duwawunki?".

Rungume Daada na yi ina kara sakin sabon kuka mai karya zuciyar mai sauraro.

  _____________________________________

Da karfi yake taune lips nashi na kasa kamar zai huda su har suka fito harabar hospital din, magana ne fal ran Umaimah amma bata ce komai ba sabida securitys dake take musu baya, gaban motar da aka bude musu ya sanya Meerah a ciki sannan da kanshi ya budewa Umaimah bayan motar ya ce, "Zaki iya shiga ko in daga ki,?" dariya kawai ta yi ta shiga da jin wani irin sanyi a ranta. Tabbas duk macen da ta samu irin hamma jay a matsayin miji, babu shakka ta huta a nan duniya. Zagawa ya yi ta daya bangaren inda aka bude mishi ya shiga sannan driver ya shiga suka bar hospital din, kan Umaimah ya kama ya daura bisa kafadarshi yana shafa kan a hankali, ya yinda ya kwanta da nashi kan jikin headrest na motar.

"Me ya sa ka yiwa Daada hakan,? Mei yasa ba kayi wa pretty ya jiki ba?".

Muryarta ta doki kunnenshi. Lumshe ido ya kuma yi, murya kasa kasa ya ce, "Wayyo ni, duk kun sani a gaba wai ban yi ya jiki ba, nifa gado kawai na gani a dakin, kin taba ganin mutum mai hankali ya yiwa gado sannu da jiki?".

"Ohk duk bamu da hankali ke nan ni da Daada?"  

"Ohhh rufa min asiri sweet heart, ni na isa in fadi haka".

"To me ya sa ka dauko ni maimakon ka barni sai dare". 

Sunkuyo da kanshi ya yi daidai fuskarta ya hura mata iskar bakinshi mai dauke da kamshin strawberry mint a kan face nata ya mata light french kiss saman lip a hankali ya ce, "Dan ina son in kara yi miki wani ciki ne, kinga sai ki haifar min twins ko?".

Da sauri ta rufe idanunta jin wani irin abu yana yawo a jininta, daga haka bata kara magana ba dan gabadaya ya rufe mata bakin, rufe idanunta tayi tana kara kwantar da kanta mai kyau jikin shoulder dinshi, a nashi bangaren shima Jabeer, mayar da kanshi ya yi yana rufe idanunshi, ko da muka iso gida ma, da taimakonshi Umaimah ta fito daga motar dan sosai kafarta suka kumbura. ya daga Meerah da ta makalkalesa tana zuba mashi surutu.

"Ohhh my talkative, baki ga Mommy bata da lafiya bane," zaro ido yarinyar ta yi ta ce, "Sorry Mommyna, little ne take naushinki?". Duk dariya suka sanya, dan Jabeer ya riga da ya sabar musu sau tari sai ya kafa kunnenshi jikin cikin Umaimah wai suna magana da little, haka yake bata lokaci akan cikin nan shida diyar tashi ita kuma tayi ta biye musu.

A palon kasa ya tsaya ya ce yana kallon meerah, "Gudu kije wajen Innarmu ki ce mata mun dawo kuma kafar mommy yana ciwo zata huta,". Da gudu ta shige dakin dake mallakin Inna cikin dakuna shida dake kasan wanda in sun zo gidan daga gidansu suke sauka a ciki, yanzuma dan tafiyar su Baffa umarah ne ya sa inna dawowa gidan.

Cakkk ya daga Umaimah ita da cikinta suka haura sama bai direta ko ina ba sai tsakiyar bedroom na shi, kan makeken royal bed dake dakin tana ta turjewa amma haka ya rage mata kayan jikinta sannan ya kawo pillow ya daura mata kafafunta a kansu ya fara matsa mata a hankali hankali, sosai Umaimah take jin dadin yadda yake matsa mata kafafun sannu a hankali wani irin bacci mai dan karen dadi da nishadi ya dauketa. 

Sai da ya tabbatar ta yi bacci sannan ya mike ya na gyara mata kwanciyar yadda zata zama comfortable ya rufa mata lallausan farin duvet dake saman gadon kana ya wuce toilet da sassarfa, gaban sink na bayin ya tsaya ya kunna ruwa ya fara watsawa a fuskarshi ba tare da ya cire agogo ko kayanshi ba, tsawon lokaci yana wanke fuskarshi zuwa kanshi sannan ya dago idanunshi sun yi jajur ya tsaya yana kallon kanshi a mirron dake gaban sink din fuskar tana ta digar ruwa yayinda idanun ke cigaba da kadawa zuwa launin jaaaa.