Page 64
💫MARYAMA💫
______________________________
64...
Ya dade tsaye jikin sink din, hannayeshi dafe bisa ruwa yana gangarowa daga cikin gashin kansa zuwa fuskarshi yana diga cikin basin din.
Jan da idanunshi suka yi yana daduwa, ruwan ya kara tarowa da hannunshi ya watsa akan fuskar kana ya zari towel karami ya fara goge daga sumar kanshi zuwa fuskar.
Fitowa ya yi daga bayin ya shiga closet na shi ya canza kaya zuwa na shan iska sannan ya dauko jikakkun ya jefa a laundry.
Leka Umaimah dake baccinta peacefully ya yi saida ya tabbatar baccin ya yi nisa sannan ya zuge wani waje da aka kawata shi da glass sai daukar ido yake, takardu ne a jejjere sinki sinki, ya dade yana bincike kafin ya zakulo wani babban littafi bayanshi ja ne mai kauri, sannan ya rufe wajen, takowa ya yi gaban mirror ya dauki pen guda daya a cikin mazubinsu ya koma saman couch ya na mai kishingida da fara bude DIARY dake hannunsa.
Ya dade yana bin pages din daya ke budewa da kallo kamar mai son tuno wani abu, bude blank page ya yi ya fara rubutu cikin nutsuwa da mai da hankali irin na kwararru.
Tsawon lokaci ya kwashe yana rubutu kafin ya rufe da sauri yana turawa karkashin kujerar da yake zaune, sakamakon motsin da yaji Umaimah ta yi kasancewar tana facing na shi ne.
Mikewa ya yi ya dawo bakin gadon yana kallon yadda take ta yamutse fuska cikin bacci dake alamta bata jin dadin baccin ya zuwa yanzu, filon da ya sanya kafarta a kai ya zare a hankali ganin kafar ya fara sauka, rigar jikinsa da ta kasance armless ya zare faffadan kirjinsa fari sol mai cike da gargasa suka bayyana, ba tare da ya yi wani sound da zata ji ba ya kwanta a bayanta in a romantic way ya janyota jikinshi ya fara shafa tulelen cikinta.
Ya yi hakan ne dan ta samu comfortability, amma a hankali sai wasan ya fara canzawa dan body contact da suka samu really turn him on.
Daga shafa ciki sai ya fara zarcewa hannunshi suka fara yawo a jikinta ta ko wanne bangare, bude idanu ta yi da kyar tana rike hannayenshi dake yawo a jikinta, cikin muryar bacci ta ce, "Hamma jay bacci plsss mana," matso da bakinshi ya yi saitin kunnenta ya ce, "Little tana neman Daddynta gaisawa zamu yi fa Maimahhh".
Da sauri ta juyo dan ta san me yake nufi da gaisawa da little, and i don't take it any longer a halin da nake ciki din nan, juyowar da tayi ya bashi daman kara cusa ti jikinsa a kunnenta ya rada, "Hanya zan gyarawa little fa dan tazo a sauwake basai ta baki wahala ba, kin san haka likita ya sanar dani."
Tana turo baki gaba tace,
"Uhm uhm, na ki wayon," bata karasa abun da ta yi niyyar fada ba, ta tsinci bakinshi cikin nata, wani irin sassanyan soyayya yake bata mai ratsa zuciya, bai samu kololuwar biyan bukata ba, amma ya rage zafi sosai.
kukan da ta sanya ne ya sa shi barinta yana kara kankame ta gam da sauke tagwayen ajiyar zuciya a jejjere.
Bayan wani lokaci ta fara jiyo saukar numfashinsa a hankali alamar ya yi bacci.
Yunwar dake kwakular cikinta tamkar zat ci babu ne yasa Umaimah zare jikinta daga nashi ta maye gurbinta da filo, dan murmushi ta yi ganin yadda ya damke filon, da sand'a ta sauka daga gadon don nemawa kanta abun da zata ci.
Turus ta tsaya jin ta yi tuntu'be da abu kusa da kujerar da ke gefen gadon, Diary dinshi na dazu ne da ya tura kasan kujerar garin sauri ashe bai shige ba, cike da mamakin mai ya kawo takarda wajen nan, dan mawuyancin abu ne kaga tarkace a dakin Hamma Jay kamar yadda nake yawan fada kullum duk yadda akayi Jay yana da alaka ta jini da tsoka shi da tsafta.
Da kyar ta kai duke kasa ta dauko takardar da niyyar ajiye masa a kan bedside inda zai gani da zarar ya tashi, amma abun ta hango sakamakon buduwar da diary din ya yi shi ya dauki hankalinta, kwakwalwarta ta ingiza ta ga duba menene kunshe cikin littafin..
Wani irin hajijiya ne ya fara daukarta ta yi hanzarin dafe kujerar dake kusa gareta lokacin da ta fara karanta shafi na karshe dake cikin littafin, amma sai ta yi ta maza ta cigaba da karantawa bayan ta dago daga dafe kujerar da ta yi.
Idanunta ta ji sun fara ganin rubutun dishi dishi kana suna zafi kamar an zuba borkono a cikinsu, daga bayanta ta ji an zare littafin bata bukatar juyawa ta ga waye dan kusancin da suka samu ya tabbatar da waye ne.
Tafiya ya fara yi bata ganin gabanta sosai amma still bata tsaya ba, har ta iso bakin kofa ta jiyo muryarshi cikin rauni kadan ya ce.
"Maimahhh plssss".
Ko karasa abun da yake fada bata jira ba ta bude kofar ta fice, site dinta ta wuce gami da shigewa daki ta datse kofar da makulli.
Kuka take son yi, amma bisa mamakinta ta kasa fitar da ko digon hawaye guda daya, sai ajiyar zuciyar da take saukewa kamar wacce ta yi tseren gudu da wani kwarin guiwa da take ba kanta na fadin
"Bai kamata in yi haka ba, dan nafi kowa sanin waye hamma jay, bayan iyayenshi da Maryama, so bai kamata in ga laifinshi ba dan rubutun da na gani n..
Kugin da cikinta ke yi na neman dauki ne ya sata mikewa da nufar fridge dake gefen gadonta, fresh milk ta dauka tana tsaye a wajen na shanye roba daya, still bata ji daidai ba sai ma harbin da cikinta keyi kamar dan cikin ya samu faffadan wajen wasa ne yana buga kwallo.
Dan tsaki ta ja tana bude kofar da fita, a hankali ta ke taka steps din har ta sauko downstairs na shihe kitchen, kitchen din yana nan very tidy ko ina tsaf,masu aiki sun kammala breakfast basu kai ga shigowa daura na lunch ba, hakan yasa ti dauko noodles leda uku a store ta daura tukunya na fara dafawa, ina bare eggs guda hudu da na dauko na ji shigowarshi kitchen din, na fahimci shine ta hanyar scent nashi da na shaka da ko a cikin dubun maza zan iya bambance shine a wajen, ba tare da na juyo ba na cigaba da aikin da nake yi, takowa ya yi har kusa dani ya tsaya jikin cabinet yana harde hannu a kirji.
Jin noodles nawa ya nuna har ya fara kamawa ya sani budewa gami da jefa eggs din a ciki na jujjuya na sauke, plate mai dan fadi na janyo hadi da juyewa akai na kashe gas din na janyo plate dina zuwa kan doguwar tebur mai zagaye da kujeru guda shida dake tsakiyar kitchen din ina zama mai kyau da zafinsa na fara nadowa a fork ina kaiwa bakina.
Zaro ido Jabeer ya yi lokacin da ta juye taliyar a ranshi ya ce, "Yanzu duk zata iya cinyewa?" a zahiri kuma ya matso ya ce, "Uhmm abincin na rowa ne? babu bisimillah".
Ba tare da na kalle shi ba nace, "Bissimillah, " kamar jira yake kuwa ya dauko fork yana jan kujerar dake kusa da ita ya nadi noodles din da yasha veggies kala kala ga nama zuku zuku da eggs har guda hudu a kai, kadan ya nada yana kaiwa bakinshi, ya hadiye da kyar yana zare idanu da gaggawa ya ce.
Maimah yaji ya yi yawa a abun nan, zai cutar da ke fa, plss ki zubar a dafa miki wani,"
"Haka nake son abuna idan baza ka ciba babu wadda ya maka dole,"bata saba mishi magana irin haka ba, yasan yanzu ma cikin fushi ta ke amma tana kokarin dannewa,hakan yasashi shafa kanshi yana leko fuskarta yace
"Maimahhh plssss mana iam sorry, ban san ya akai hakan ba, i just feel like..." sai kuma ya yi shiru yana lumshe idanu, fork dake hannuna na ajiye ina tsareshi da idanu na,
"Wai akan me kake bani hakuri ne, nice ya kamata in baka hakuri dana shiga hurumin da ba nawa ba, duk abun da ke dakin ka mallakinka ne, bai kamata in bude komai ba tare da izinin ka ba, so kaga dole ni zan baka hak...."
"No Maimahhh da ni da abun da ke dakina duk na ki ne, kina da ikon taba duk abun da kika gani a gidan nan, kece rumfar gidan nan, kece kika rufa min asiri a lokacin da duniya da mutanen cikinta suka nemi tona min asiri, kece ki ka zauna dani a lokacin da wacce muka rayu cikin jini daya da wani bangare na hallita guda daya a jikinmu ta gujeni.
Maimahh kece kika bani karfin guiwa na cewa in fita in nema mai nema baya rasawa, kece kika sanya na ji a raina cewa mata suna suka tara baduka suka hadu suka zama daya ba, and kece kika bani farin cikin duniyata sanyin idaniyata abun alfaharin wacce duk wani saukar numfashina yana fita ne tare da sonta a doron duniya (NAMIRAH) and now,ya fada yana pointing cikin dake jikinta, Maimahh bazan taba daina ganin girmanki ba har a nade duniya".
Wani irin sanyi na ji yana ratsa ni tun daga kan babban yatsar kafata har tsakiyar kaina, take na nemi bacin ran da nake ciki na rasa,a haka muka lalace a wajen har na gama cinye abincin da duka eggs din, Jabeer ya na min dariya wai zan cinye mishi dan salary din da yake takama dashi a wata tunda na zama acici, niko na ce ba laifi na bane mu biyu da little muka ci, kamar yadda yake yawan fada wai mace zan haifa mishi mai kama dani zai yiwa Innarmu takwara mu dinga kiranta da little, da haka sunan cikin ya zauna har meerah ma ta kama.
______________________________
Bayan kwana uku da faruwar lamarin kullum sai na je wajen Maryama a hospital duk da tsananin kunyarta da nake ji, amma haka nake daurewa, yanzu daada ke jinyarta ko ince daada ke zama da ita dan itama ba wani lafiya ya isheta ba yanzu ga tsufa ya bayyana a jikinta sosai ya zuwa yanzun.
Ga mamakina Maryama ba ta canza min fuska ba, muna hira sama sama kamar farkon kwanciyarta a asibitin.
Yau aka sallamota babu laifi ta dan fara dawowa hayyacinta duk da bata murmure ba, amma ta fara dawowa kamanninta kadan,sai dai har lokacin ko naira biyar bazaka sayeta ba, tsabar rama da figewar da ta yi sai yan idanuwa da doguwar hanci, dan ma tasha drip babu adadi na karfin jiki.
Kamar ko yaushe mota daya Umaimah Daada da kuma Maryama suka shiga securities suka rufa musu baya tamkar mafarki haka Maryama ke ganin lamarin wai securities ke rakiyarsu, bata kara tsinkewa ba sai da ta kuma ganin da gaske waccan gidan da ta tadda Innarmu da Umaima Ham Jay suka nufa, wannan soja din dai na ranar shi ya bude musu gate suka shiga.
Kirjinta ne ya tsananta gudu ganin sun dumfari entrance na gidan, "Ki taka da jiki mana, amma kina tafiya salalo salalo kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ko kwanciyar asibitin bai ishe ki ba halan?".
Cewar daada ganin yadda nake tafiya kamar mai counting steps dina, a zahiri kuma tsoro ne fal raina, tsoro da kunyar iyayena ke damuna, ta ina zan fara? Wa zan fara roko? anya za su yafemin?".
Zaune bisa kujera Innarmu ce ta hakimce kamar ba wannan Innar mai daddawa ba, kyawunta na asalin buzaye ya bayyana da girman shekarunta da jin dadi ya boye, gefenta Salima da Fati ne, Fati ta zama cikakkiyar budurwa Salima ma ta taso sai dai rabin fuskarta zuwa hannunta iya inda nake hangowa da akwai alamar kunar wuta har lokacin tabon bai fita ba.
Sakare na yi a bakin kofar ina kare musu kallo kamar na ga bakin hallita, a tare salima da fati suka mike daga kan aikin da fati din keyi bisa laptop ita kuwa salima tana kwance tana kallon cikin laptop din, da wani irin gudu suka nufo inda nake tsaye suka rungume ni a tare suna sakin kuka.
"Antinmu ina kika tafi kika barmu? Ina kika je ki ka barmu mu kadai muna ta kewarki?".
A tare suka min tambayar, bayansu na ke shafawa a hankali bance komai ba,.
"To ku sake ta haka nan malamai, ku baku ga yadda ta zama bane, kuskure kadan zaku iya karyata yadda kuka ha'bake kuke ta hauhawa kamar farashin nan".Cewar daada dake tsaye gefe itama bata kai ga zama ba.
Da sauri na sake su fati kirjina yana rawa ganin Innarmu ta mike tsam zata wuce wani daki, ban san yadda akai ba, kawai ganina na yi kusa da ita na kai duqe kasa hadi da kama kafafunta ina kara rusunawa kamar zan yi sujjada, jin hannaye na jikin Innata ya sani jin wani irin rauni ya dabaibayeni harshena ya min nauyi kamar bishiyar da ta kafa jijiyoyi. Wani irin sanyi na ke ji yana ratsa ni har cikin bargo na,..
Rumtse idanu Inna tayi ba tare da ta juyo ba ta janye kafafunta daga rikon da nai mata ta shige dakin ta rufe hadda sanya makulli, a rikice na daura hannu bisa kaina ina zaman yan bori na sanya wani irin kuka mai taba zuciya, Fati da Salima ne suka yo kaina suna kamani amma na ki tashi sai rarrafawa da na fara jikin kofar dakin da Inna ta shiga, ina kiran sunanta da fadin na tuba bazan sake ba, amma babu alamar cewa ta jiyo abun da nake fada.
Saida daada ta fara zazzaga min ruwan bala'i tukunna na mike ina bin su Fati dake jana har cikin wani daki dake gefen wadda Innarmu ta shiga, sosai na ci kuka na koshi suna ta bani hakuri.
Janyo yaran na yi gaba dayansu ina makale su jikina na cigaba da kukan. Ganin da nai suma sun fara kuka ne ya sani yin shiru na koma basu hakuri.
Har wajen karfe uku ina dakin da taimakon fati na yi wanka, ta wanke min kaina da ya zama kamar sabbon mahaukaciya da mayukan wankin gashinta masu dadi, tun tana wankewa da hankali da dadin rai har dai bakinta ya subuce da tambayar, "Antinmu ina kika shigar da kan ki haka?
Dubi yadda ya zama?" ni dai ban ce uffan ba, a kalla sai da ta karar da shampoo gora daya da conditioner gora daya amma kan bai yi haske ba, haka ta lallaba ta dauraye da fadin.
"Gobe sai muje saloon, you really need it! gaskiya".
Sosai na dirje jikina a bayin, sai na ji ni wata sakayau kamar an sauke min kaya, amma dakon dake zuciyata tana nan daram.
Kayan fati na sanya bayan na fito, ga mamakina yawo na dinga yi a cikin kayan tsabar yadda ya min yawa.
Ban kara leko palon ba, duk da yadda nake muradin komawa wajen Innarmu haka na hakura, abinci ma har daki Fati ta kawo mana, tare muka ci ko ince na tsakura, rabona da jin farin ciki irin na yau bana tunawa.
Wajajen karfe bakwai da rabi Umaimah ta shigo dakin sanye da wani maternity gown, kanta sanye da hula, as usual fuskarta dauke da murmushi, zama ta yi bakin gadon ni kuma ina tsakiyar gadon da kan salima bisa cinyata fati tana kan bedside sai hirar abun da ya faru bayan bana nan suke min, wani inyi kuka wani inyi murmushi.
"Kaga amaryar gobe" Cewar Umaimah tana kallon fati da sigar zolaya, ita kuwa ta sunkuyar da kai da sauri,
"Kai dai maman twins banaso" ta fada cike da kunya, wara ido na yi ina kallon Umaimah, nan take sanar dani bikin fati saura wata biyu, kuma zata auri dan mataimakin shugaban kasa abokin Hamma Jay ne tare suka yi karatu, kuma ta dalilinsa ne ya samu aikin da yake kai a yanzu.
Sosai maganar yamini dadi, yayin da wani bangare na zuciyata ke tsarkake girma da ikon ubangijin talika mai yadda yaso a lokacin da ya so.
Muna zaune dakin muna hira har wajajen sha daya na dare, duka hirar kuma labari suke bani, kamar daga sama aka tura kofar dakin, kafin ya shigo kamshin turarensa ne ya fara isowa.
A take nasha jinin jikina, inda Umaimah take ya nufo ba tare da ya amsa gaisuwar da Fati da Salima suka hada baki suna mishi ba, hannun rigar baccinsa da ya kasance dogo ya fara nadewa yana kallon Umaimah cikin low voice ya ce.
"Naga alamar ke baki san kara ba, kin barni ni kadai a daki kamar gauro alhali ina da mata,"
Daga haka ya daga ta cidak ko nauyin ta baiji ba, da kafa ya bude dakin ya fita Umaimah tana ta rokonshi da buga kirjinshi akan ya sauke ta zata iya tafiya amma bai yi hakan ba, dariya yaran suka sanya Fati tace,
"Hoo Hamma Jay ya zama marar kunya yanzu wllh".
A hankali na zame na kwanta a inda nake ina damke filo da karfi, ji nake kamar zuciyata zata yi bindiga dan yadda take kumburowa, tamke idanuna na yi da karfi dan hana hawayen dake shirin gangarowa zuba
I deserve more than this, i deverse it, tabbas na cancanci fiye da haka ma, zuciyata ke kara tabbatar min.....