MARYAMA

Page 65

by @ummufadeela01

 💫MARYAMA💫

65


Ban bari yaran sun fahimci halin da nake ciki ba har suka gama kana nan surutansu suka sanyani a tsakiya muka kwanta, duk da gadon ya yi mana kadan amma haka muka yi kwanciyar kamar masu jin sanyi maimakon bacci, sai wani shafin hirar muka bude suna ta bani labarai dai dai yanzu mafi yawanci akan saurayin Fati ne, wani irin annashuwa da farin ciki na ke ji marar misali, tabbas bature ya yi gaskiya da ya ce, "No place like home" kowa ya bar gida, gida ya barshi.

Washegari, muna idar da sallah karatun qur'an muka gabatar dukkanmu kamar yadda muka saba tun da can mukayi azkar, ban san sadda hawaye ya balle min ba. 

Yaushe rabona da yin azkar da karanta qur'an? Tabbas dole masifu su ringa samuna.

Muna idarwa fati ta mike wardrobe nasu ta bude hadi da fitar da wani babban gora ta taho gareni da murmushi saman face nata ta ce.

"Antinmu kin ga wannan?"


Ta fada tana miko min gorar, dan jujjuyawa na yi ina jin yadda kamshinsa ke bade min hanci na ce.

"Fati ban san menene ba sai kin fada min".

"Kai antinmu, kin manta dai, wannan shower gel na larabawa ne, a saudiyya na saya lastweek don haka yanzu zaki fara amfani dashi, so nake ki dawo asalin antinmu da na sani tun da" 

Bata bani daman fadin komai ba ta wuce bayi, murmushi na yi a raina ina fadin, "Allah mai yadda ya so, irin wannan rayuwar na yi buri lokacin da nake gaban su Innarmu, sai gashi ubangiji ya bawa 'kanwata abar alfahari na.

Bathtub Fati ta cika da ruwa mai dan dumi dumi, sannan ta ringa zazzaga kalolin abubuwan gyaran jiki da ta siya musamman dan bikinta a ciki, sai da ta tabbatar ya mata yadda take so ga kamshi yana tashi ta ko ina sannan ta dawo dakin.

"Antinmu na hada miki ruwa a baho, ki shiga ciki ki kwanta abunki sai nan da kamar minti arba'in by then jikin ki ya jika mai kyau, sai ki juye ruwan, wannan shower gel da na nuna miki sai kiyi amfani dashi akan sponge ki dirje ko ina na jikinki dashi sannan kiyi normal wanka."

"Fati kenan yan mata, duka ni kadai?"

"Ke kadai Antinmu don fa baki ganin mirror ne shi ya sa, amma ai akwai yadda kika zama gaskiya"

Na san gaskiya ta fada, kuma soyayya take nuna min irin na yan uwantaka shi ya sa ban ji haushin abun da ta fadi din ba.

kamar yadda tace haka na yi sai ga wasu irin datti fata fata suna mikewa a jikina tsabar yadda suka ji'ka da na'ukan sinadaran da fati ta zubawa ruwan. Ko da mintuna arbain suka cika kamar yadda ta ce, na gane hakan ne ta agogon dake bayin, ruwan na juye ina mikewa.

Yadda tace inyi da shower gel din haka nayi, na dirje hatta fuskata yadda ya kamata, sannan na yi wanka mai kyau ina karewa toilet din kallo ya hadu har ya gaji, ko toilet na mu dake Dubai bai kai wannan kyau ba.

Babban towel na zara na daura sannan na dauki wani na yafa, sosai na ji dadin jikina, wani lotion mai kamshin gaske ta bani na shafa bayan na gama tsane jikina sai turare na jiki da na hammata, sannan ta bani sabuwar doguwar riga mai kyan gaske kirar Saudi na sanya.

Wani irin sakayau na ji jikina ya dauka har wani lumshe idanu na ke yi.


"Ita waccan kam bata tashi ne?"

Na fada ina nuna Salima dake sharbar bacci abunta"

"Wannan kasar ai Sai ta Allah, dama Hamma Jay ke tashinta da bulala to shima idan ya yi fitar sassafe babu mai takura ta yanzu nan dai yunwar cikinta ta ciyota zaki ganta wajajen sha daya tunda yau babu makaranta."

Bance komai ba na koma bakin gadon, jina nake kamar wata bakuwa a cikinsu hakan yasa nake yawan takurewa.

Antinmu ki kwanta mana ki huta, ina zuwa nima"

cewar fati tana fita dakin, ba ta kai ga fita ba na yafito ta, hakan yasa ta dawo kusa gareni ta zauna gefena, cikin murya mai cike da rauni hade da rashin karsashi dake nuna asalin halin da nake ciki na ce.

"Fati kina ganin iyayenmu za su yafe min laifin da na aikata garesu kuwa, kina ganin za su ji kaina su yafemin?

Nasan mawuyan ci ne Hamma Jay ya yafe min domin laifina mai yawane a garesa, duk da na san shi ba mai riko bane, amma yadda ya zama yanzu kwata kwata ba hamma Jay da na sani bane, wannan wani ne daban, wata zuciyar ce daban a gangar jikinsa,amma Innarmu Baffan....." 

Kasa karasawa na yi sakamakon kukan da ya kufce min...

Kar ki damu Antinmmu da yardar Allah za su yafe miki, yanzu dai ki kwanta ki huta kuma kar ki yawaita wa kan ki tunanin ohk?"

Daga haka ta mike ta fita dakin.

Ba tare da tsananta tunani ba na kwanta lamo ina jin abubuwa dayawa suna zagaye illahirin 'bargo da jini da tsoka na, ban dade da kwanciya ba kuwa wani irin bacci mai cike da nishadi ya kwashe ni.

Ko da fitar Fati dakin Innarmu ta shiga, zaune ta sameta bisa pray mat hannunta rike da casbaha tana azkar da ke nuna tun asuba bata tashi a wajen ba.

Bakin gado ta zauna ta jira har ta kammala addu'ointa ta shafa tana nade sallayar ta ce, 

"Ya dai amarya da sassafe haka, ko na samu wani abu ne?" 

Tana bubbuga kafa ta ce, "Kai Innarmu hadda ke, ni fa ba amarya bace babu inda zani in bar ki, sai dai in tare zamu tafi dake,"

"Hmmm dama mana idan baki tafi tare dani ba ai ba za su san sun auro yar lukuta ba"

Cewar Inna tana dariyar irin jikin da Fati ta yi kamar ana hurata.

*Kai dai Innarmu!" 

"Ehmana" Inna ta kuma fada tana zama kusa da ita da komawa serious ta ce, "Lafiya?

Naga kamar akwai magana a bakin ki, ba dai akan Yaseer din ba ne ko?" mijin da za ta aura.

Zamowa kasa Fati ta yi tana zama bisa guiwanta hade da kama hannun Inna duka biyu, cikin maraice murya ta ce.

"Innarmu ba'akan Yaseer ne ba, akan Antinmu ne, Inna ki dubi girman Allah da darajar Manzon Allah S A W ki yafe mata, tabbas duk wadda yaga anti Maryama zai shaida cewa taga rayuwa yadda ya kamata. Inna idan bamu yafe mata muka jata a jiki ba waye zai jata bayan duniya ta juya mata baya? ba don halinta ba, dan Allah zaku tausaya mata Inna idan ba haka ba komai yana iya faruwa da ita ciki harda barazanar rasa rayuwarta dan Allah Innarmu" ta karisa tana hade hannayenta waje daya.

Tunda ta fara maganar jikin Innarmu ya yi sanyi sai dai bata iya tace komai ba har ta kai karshe...

"Kin gama?"


Inna ta tambaya, gyada kai fati ta yi tana marairaicewa.

"To ta shi ki bani waje yanzun nan" ta kuma fada in a seriuos note.

Simi simi Fati ta mike ta fita, dan Inna bata basu tarbiyar yi mata musu ba tun da ma bare yanzu da ta kara zama mai zafi, kana tabo ta zaka sha mazga ne.

Jiki a salube ta shige kitchen dan ganin me masu aikin ke yi, idan taga wadda zata iya ta taimaka musu dan girki yana cikin hubbie dinta, amma acan kasan ranta tana jin dadin weakness da ta gani cikin idanun Innarmu, ko ba komai sakonta ya isa inda take bukata.

Sai after eleven Maryama da Salima suka tashi, lokacin har an gama breakfast Fati ta yi wanka tana zaune gefe tana aiki bisa laptop dinta.

Lallai bacci ya yi dadi, sai yanzu kuke tashi" cewar fati tana murmushi.

Ina hamma na ce, "Me yasa baki tadamu ba har lokaci yaja haka?" 

"Ahh naga kuna enjoying baccin ne that's why," 

Ai gwara da bata tadamu ba antinmu, idan anti fati zata tada mutum a bacci ihu take mishi sai kai ya yi ciwo.

Salima ta yi magana tana sauka zuwa toilet Fita Fati ta yi zuwa kitchen ta hado musu breakfast nasu saman babban tray ta dawo dakin dan tasan Maryama za ta fi sakewa a dakin sabanin dining area duk da babu kowa a palon.

Sosai kuwa ta sake suka ci abinci suka koshi salima ta tattara kwanukan zuwa kitchen, suna zaune a wajen suna hira sama sama mai share share a palon kasa ta shigo, kanta a kasa ta gaishe su tana fadin, "Ana muku magana a waje"

Wani irin zabura na yi na mike da sauri sauran ma suka mike, hannuna Salima ta kama ganin yadda jikina ke rawa muka fito palon.

Baffanmu yana hakimce saman kujera mai zaman mutum uku, sanye da wata dakakkiyar shadda dinkin babbar riga sai daukan ido take yi, Innarmu kuma tana zaune bisa kujera mai zaman mutum daya, sai Daada itama bisa kujerar, yayin da Hamma Jay ke gefen kafar baffa kanshi a kasa Meerah zaune bisa kafarshi Umaimah kuwa da tulelen cikinta tana zaune gefen daada ta mike kafa, take na ji kamar naman jikina yana zazzagowa kasa arba da nayi da Baffanmu, ba tare da tunanin komai ba na saki hannun salima na ruga da gudu na fada a kafanshi ina sakin kuka.

Kaina ya fara shafawa a hankali yana fadin ya isa hakanan uwata ya isa, bisa dukkan alamu baki bukatan wani karin darasi kuma wanda kika samo ya isheki, Daada tana kwakulo hawaye daga idanunta ta ce, "kaima ka fada dai Hassanu, ai yanzu ma tayi kyan gani ta ciko ta murmure,da yadda naganta a asibiti ka ganta sai ka zubarwa diyar nan hawaye, shiyasa na taraku a nan a yayyafi juna ita rayuwa dama ta gaji haka, komai yana zuwa ya wuce kamar ba'ayi ba. 

Wani abu lokacin da yake faruwa sai kaga kamar bazai wuce ba, ko kaga kamar Allah ya manta dakai, kafin ka ankare sai kaga ya zama tarihi wannan shine rayuwa dama. dan haka ku yayyafe ku yayyafe."

Gyaran murya Baffa ya yi ya ce, "Hakane daada, Allah ya yafemu baki daya, babu shakka Uwata ta aikata kuskure mafi munin kuskure da ya zata aikatawa iyayenta shine na gudu daga gabansu a duniya babu wani mahaluki da zai kaunaceki kauna fisabilillahi sama da iyayenki, yaruwa kada ki yadda rudin shaidan da duniya su janyo ki kauracewa iyayenki dan har abada hankalin su ba zai kwanta ba, rashin kwanciyar hankalin su kuma tashin hankalin ki ne da ganin ba daidai ba a rayuwarki dan haka ina fatan yan mata za su dauki darasi daga rayuwar ki Maryama."

Baffa ya karishe yana cigaba da shafa kanta, 


"Thank you Baffa, na gode na gode, tabbas na aikata laifi wanda kaso saba'in a ciki ban san ina aikatawa ba, is like na zamo rakumi da akala da sai yanzu abun ke yawan fado min a raina, rarrafawa na yi gaban Innarmu na durkusa ina hade hannayena duka biyu na ce, "In......"  

"Shhhttt" 

Ta fada tana daura yatsarta saman bakinta sannan ta janyo ni jikinta ina jin kaina a kafarta na kuma fashewa da kuka.

"Na tuba Innata bazan kuma ba, wllh bazan kuma ba ki yafe min dan Allah".

"Ki daina kuka hakan nan kada kan ki ya yi ciwo, Maryama ita duniya cike take da darasi kala kala, da alama you've learnt your great lesson to the hard.
So komai ya wuce yanzu ina fatan zaki jajirce wajen ganin kin gyara gabanki wadda kika bata a bayan ki,"

Zan gyara Innarmu wallahi zan gyara na yi kuskure bazan kara ba," juyawa na yi kan Daada dake sharban hawaye kafun ince wani abu ta ce

"Ah'a rufamin asiri yan nan, me ki ka min zaki wani rarrafo gabana salon munafurci, ke dai ki nemi afuwar wadanda kikawa laifi ahto, kan Umaimah na juya, kafin ince wani abu itama ta girgiza min kai ta ce


"You did nothing to me frnd, Allah ya kara rufa ma na asiri, nice ma ya kamata in nemi afuwark..."

Ban bari ta karisa ba na rumtse idanu da karfi na cigaba da rarrafawa har gabanshi, yana nan yadda yake har lokacin bai dago ba, amma a kallon farko zaka iya fahintar halin daya ke ciki duba da yadda jijiyoyin kanshi suka tashi rudu rudu..


"H...m.m..ma .."

Kokarin kiran sunanshi nake yayin da ko wacce harafi ta ke katse dan uwanta wajen furtawa, wani irin dagowa ya yi a karon farko ya kalleni da rinannun idanunsa da suka yi jajur tsabar fushi cikin kaurin murya ya ce. 

"Ina cikina? Ina gudan jinina,? Ina dana ko yata da kika tafi da?."

Ba ni da ya yi wa tambayar ba, hatta sauran occupant dake palon saida kirjinsu ya bada sautin dam.

"Dama yasan inada ciki? Inna lillahi wa'inna ilaihiraji'un".

"Me ka ke nufi Jabeeru,? 

Daada ta watso mishi tambayar, ita ta san abun da na fada daada.

Gaba dayan su idanu suka zuba min suna jiran jin karin bayani, takurewa na yi a tsakiya kamar yadda suka kasance zagaye dani, kuka nake rusa kamar raina zai fita, Salima da Fati da Meerah na taya ni.

A hankali na fara sassauta kukan ina share idanuna da bakin hannun rigata na ce.

"A lokacin da na ce ka sakeni, I really don't know what came over me, ban san ya akai ba, ban san me na ke aikatawa ba, only what i know is.

"Siyama, dan tsaigaitawa na yi ina share hawaye na sannan na cigaba.

"Siyama ta bani shawaran cewa idan na dawo gida da takardun can ka tuhume ni in sanar da kai komai, ta nan ne kawai zan samu tafiya makaranta portharcourt, idan ka nuna turjiya ince ka sakeni, in rike kwalar rigarka in kiraka da da abun da na sanar da kai a ranar dole zaka sakeni.

I was like rakumi da akala, kamar ita take juyani dan haka koda na nuna ba zan iya ba sai tace babu ita babu ni, hakan yasa na tsorata har na aikata hakan.

Amma wllhi tun da na san ya kafata na bar gidan ban kara samun peace of mind ba, mai adaidaita da ya dauke ni daga kofar gidanka zuwa gidansu siyama shine mutum na farko da ya fara cimin mutunci akan dari biyu.

Nan Maryama ta fara basu labarin abun da ya faru tun barinta gidan har kawo yanzu ko kalma daya bata boye ba.

Duk taurin zuciya irin na maza sai da hawaye ya surnano daga idanun baffa, yayin da Jay makwogoronsa ke ta hawa da sauka, jan da idanunsa suka yi yana 'karuwa ga zufa dake karyo masa, Inna d su salima ma kuka suke sosai, Umaimah dake gefe itama kukan take risga jin irin rayuwar da Maryama ta fuskanta wani irin hautsinewa cikinta ke yi amma bata maida hankali ba. 

Wani irin kabbarar da Daada ta yi ne tana matse idanu ya janyo hankalin su tana mikewa da kwance habar zaninta ta ce, "ai ni nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya nasan ba banza ba, ina ce muku jifa aka yiwa yarinyar nan amma kunyi mirsisi da idanu kun ki aminta, to ga dai gaskiya ta bayyana, kuma zan kara sawa amin bincike, idan har zargina ya tabbata dangin wannan Siyamar sun shiga uku.

Wato dan kar asirinsu ya tonu shine uwar ta biku da sharri bayan bokanta ya sanar da ita abun da ya faru ko, to wallahi zasu san sun taba jikata kuma sun tabo tsuliyar dodo....

Wani karan da Umaimah ta yi ne ya kara janyo hankalin gaba daya mutanen falon izuwa gareta, murkususu kawai take yi da yarfe hannu zufa na diga daga goshinta.

"Subhanallah, sannu Umaimah, ko dai haihuwar ce,?" 

Cewar Inna tana kamata, babu kunya Jabeer ya matso duk ya rikice shima ciccibarta ya yi yana fadin Innarmu haihuwace, tun sati daya da ya shige dama lokacin da aka bamu a anti natal ya cika amma bata sauka ba, yana magana ne yana fita daga dakin, Hijab Inna ta dauko da sauri daga daki yayin da Daada ta mara mata baya suka bi Jabeer da har ya sanyata a bayan mota yana kokarin shiga driver seat, Allah ne kawai ya kaisu lafiya tsabar irin gudun da yake tsulawa bisa kwalta, da gudu gudu nurses suka turo gadon daukar marasa lafiya aka daura Umaimah bisa suka gungurata zuwa labour room.

  ________________________________

Wasa wasa sai da Umaimah ta kwashe awanni uku a labour room ga haihuwa ga haihuwa amma shiru, su Inna sunyi tofi har sun gaji amma babu labari sai wahalar da take sha kawai,ganin wuyar da take sha ya yi yawa ne babban likita ya nemi jabeer dake ta kai kawo a bakin labour room din da ya sanya hannu aimata CS Idan ba haka ba za'a iya rasa uwa ko abun da ke cikinta ko ma a rasasu gaba daya.

Take kuwa ya sanya hannu a wajen yana jadaddawa likitan ya yi duk yadda zaiyi ya ceto mishi matarshi ko da ko za' arasa babynne.

Ba bata lokaci aka shirya Umaimah zuwa theater room, sai dai wani hukunci na Ubangiji ba akai ga fara aikin ba, ta yi wani nishi mai karfin gaske sai ga da ya fado su'bul.a hanzarce drs din suka zubar da kayan fidar da suka kwaso suka karbi dan, cikin lokaci kadan aka goge yaro kyakkyawa jajur dashi kamar uban ya yi kaki ya tofar sak dashi.

Nurse ce ta fito dashi nade cikin towel sauran likitocin kuma suka fara duba Umaimah cike da fara'a likitan take mikawa Jabeer babyn, amma shi baya ta kan yaron tambayarta yake ina matata?" 

"Ranka ya dade tana lafiya ana kimtsata ba akai ga tsagata ba dan ya fito dan ya matsu yaga babanshi, dariya suka sanya Inna tana karbar yaron, leko fuskarshi Daada ta yi ta ce, 


"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen, wannan da sak ubanshi, haka aka kawo min shi lokacin da aka haifeshi leko ka ganshi Jabeeru kamar an...Wayam suka gani babu jabeer babu labarinshi.

Tuni ya shige dakin nurse tana sanar dashi ba'a shiga amma ko sauraronta bai yi ba, hannun Umaimah da'ake yiwa dinki sakamakon tear da ta samu ya kama yana murzawa a hankali da fadin, "Sorry Maimahhh".

     ***********

Lokacin da aka tafi da Umaimah hospital sosai muka rikice sai baffa ke kwantar mana hankali, tashin hankalin da kowa ya shiga sanadin labarin da na bayar sai ya koma kan halin da Umaimah ke ciki, kuka Meerah take yi iya karfinta tana kiran Mommyna Daddyna,rarrashinta muka dinga yi amma taki yin shiru daga karshe Baffa ya dauketa suka bar gidan.

Zugum zugum muka yi a palon dukkanmu kowa da abun da yake saqawa a ranshi,bayan wani lokaci Inna ta sanar da Fati Umaimah ta sauka ta haifi da namiji ta hanyar kiranta a waya.

Nan suka dinga tsallen murna harda rawa, a hankali na sulale daki, ban tsaya ko ina ba sai bathroom na rufe kaina na zauna bisa toilet wani irin kuka ya tahomin, toshe bakina na yi saida nayi kuka mai isata na godewa Rabbul'Arshi sannan na yi wanka na fito.

Kallo daya Fati ta min ta fahimci irin kukan da naci amma ta kauda kai kamar bata gani ba, tabbas ina kishin Umaimah kishi mai tsanani, amma kuma kaunar da nake mata yafi kishin yawa, a bangare guda kuma ina ganin Jabeer ya min nisa, yamin nisa irin nisan da sama ya yi wa kasa, a duk sadda na kalleshi ko na tunashi na kanji ni kan tamkar almajira a gabanshi ko ince tamkar sarki da baiwa, 

"ya Allah" 

na furta lokacin da na ji kirjina ya yi wani irin suka kamar an jefa tsinin mashi ya caki saitin zuciyata.

Sai yamma muka shirya zuwa hospital din inda driver ya kaimu, duk yanayin da nake ciki, kallon farko da na Yi wa wannan boy din da fuskar Hamma Jay ke kwance sharr saman nashi na ji komai nawa ya saki. 

A take wani irin son shi ya huda kirjina, damke shi na yi a jikina ina jin wani irin nishadi, ban san ya akayi ba sai ji nayi na furta.

"Umaimah ke kam kin dace, plss ki bani wannan yaron,"

Murmushi ta yi ta ce. 

"Ai dama dan ki ne pretty, idan kina so ki dauka na baki shi halak malak har yaumuttanadi"

Da sauri na bude idanuna ina wara su akan ta, murmushi tamin mai shiga zuciya ta ce, abun da na haifa na ki ne Pretty. 

"A wacce ruwayar ki ka samo wannan kuma 
Maimahhh?"

Cewar Jabeer dake shigowa yaji komai a kunnenshi,

"Ahto kaima ka fada min dai, ni na taba ganin haka? ah'ah kowa ya yi zuciya ya haifi nashi" Inji daada dake gefe tana sakace hakori.

Wani irin rawa zuciyata ta yi jin furucin ta na karshe, na san habaici ta min amma sai na danne, Innarmu dake gefe tana hada kaya itama murmushi ta yi, Jabeer dai Sakare ya yi baice komai ba kafin ya rankwafo kai na har muna jiyo numfashin juna, lumshe idanu ya yi sannan ya zare yaron a hankali daga jikina.

       *******

Kwanan Umaimah biyu a asibiti aka sallamota gida, nan gida ya kacame da yan barka. kawayen Umaimah da matan abokan Hamma jay manyan mata wadanda ake damawa dasu a gwamnati wayayyu suka dinga diddikowa kamar me.

Wadannan suna kara sawa inji na raina kaina a gabansu...

Yau kwana biyar da haihuwar ina zaune kamar kullum rungume da yaron a jikina wanda shan nono kawai ke kai shi hannun uwarshi, ko bacci yake idan na shigo dakin haka zan tada shi inyi ta kallon kyakkyawar fuskarshi.

Yanzu ma kamar ko yaushe ina zaune rike da shi a hannuna sai kallonshi nake Umaimah tana bathroom bata juma da shiga ba.

A hankali na dago kaina jin kamshin taurarensa da ya yawaita a ramukan hancina, yana tsaye ki kam a bakin kofar ya harde hannayensa a kirji fuskarshi babu murmushi ko kadan a ciki.

Hada idanu muka yi na yi saurin kawar da nawa idon, takowa ya fara yi zuwa inda muke, at the same time kofar bayi da kofar shigowa suka bude, Umaimah ta fito daga bayi yayinda Salima da Fati suka shigo dakin suna washe hakora na ganin Hamma Jay a dakin.

Kauda kai Umaimah ta yi kamar bata ga abun da ya yi niyyar yi ba.

Yallabai akwai abun da kake bukata ne?" Ta tambaya gana kallonshi.


No kawai nazo cheking na lafiyar ku ne, ya fada yana shafa kanshi as usual.

"Hamma jay daga site naka muke dama baka nan ashe kana anan," 

Salima ta fada tana sosa keya. Uhmmm kawai ya fada idanunshi kan Umaimah dake tsaye itama har lokacin.

"Am ehm dama so muke ka bamu kudi muje shopping na shir