Page 66
💫MARYAMA💫
66...
A kashe Umaimah,Umaimah zata mutu Jay ya auri Maryama,shine yawancin abun da #teamJaymar suke fada,Umaimah ta mutu for what?,shin kenan duk wacce tayi rayuwar kunci kuma ta yi hakuri bata da riba ko rabo kenan?anya muna yiwa kanmu adalci kuwa,?anya muna karanta littafin da daukar darasin dake ciki ko ko dai sharholiyar ciki kawai muke dauka?.Idan muna karatu mu daure mu dinga hasaso abun a zahiri ba wai rayuwar karya na novel zallah ba da marubutanmu suka gurbata tunaninmu ta hanyar da namiji bai da ikon auren mace fiye da daya a gidanshi,or matar so kawai ake zama da ita,this is so bad,...tabbas Umaimah ta cancanci samun rayuwar farin ciki duba da yadda abubuwa suka sauya mata kuma tayi hakuri, masu bina private kuna fadin dan Allah in kashe Umaimah kuyi hakuri,idan na kasheta sakon da nakeson isarwa bazai fita min yadda nake so ba......duk wadda yayi hakuri da jarabawar rayuwar da Allah ya daura masa tabbas yana da reward a wajen Allah.
__
Juyowa na yi jin kofar a rufe, caraf idanu na ya shiga cikin nashi, duk yadda na so janye nawa idanun bai bani daman hakan ba,a hankali wasu hawaye masu zafi suka fara taruwa a idona na ce cikin rawar murya.
"Zan fita".
Kanshi ya shafa yana kara murtuke fuska ya ce.
"Wayace ki zo dama? da shike kafarki na yawo ne babu wanda ya gaiyaceki amma kin figo kafafu kin taho ko?"
Wani irin zafi na ji a raina amma na danne bance mishi komai ba, na dai yi kokarin juyawa ina ganin waje, kasancewar glass din tinted ne yasa babu mai ganin cikin.
Kanshi ya cigaba da shafawa ya ce, "A ina kika samu wannan turaren da kika shafawa jikinki?"
Still bance komai ba, tsawa ya daka min
"Ba dake nake magana bane kin maida ni marar abun yi, zaki bani amsa ne ko sai na sauyawa fuskarki fasali da maruka, where did you get those perfumes da kika yiwa jikin ki wanka dasu haka?"
Sosai tsawan nashi ya kada min yan hanjina, cikin rawar murya ina tura baki gaba na ce,
"Na Fati ne, ita ta bani dazu kuma ni kadan na shafa"
Yana kallona strictly ya ce.
"Daga yau, i mean from this very moment, kar in kara jin irin wannan turaren a jikinki ohk?"
Ya fada yana zaro min idanu kamar zai ci babu.
Bai bani daman fadin komai ba ya bude motar ya fita har ya yi taku biyu ko me ya tuna kuma ya dawo ya ce sauko yana bude bangaren da nake.
Bance komai ba sai hawayena da nake kokarin mayarwa ina jin wani tukuki a raina, tabbas wannan ba Hamma Jay din da na sani bane, wannan wani ne daban. takawa na fara yi ina bin bayanshi a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki har muka karisa cikin babban kantin. siyayya sosai su Fati sukai yawanci kuma kayan shafe shafe ne da na makulashe dangin sweets da choculates.
Antinmu babu abun da zaki siya ne ke,?" Cewar Salima dake bayana da katon cart nata sai dura kaya take yi.
"Babu abun da nake bukata, kawai na rakoku ne yan matan Inna"
Bari kiga in zaba miki wasu choculate nasan zaki so su sosai,"
Bance mata komai ba har yaran suka gama zabar abun da ya kawosu, har munzo fita na tuna da sakon Umaimah, hakan ya sa na koma da sauri sai dai duk yadda na so daukar mata sakon nata kasawa na yi, dan wani irin kunya na ji ya kamani daga karshe dai bayan su fati na biyo na same su wajen cashier suna biyan kudi hamma jay kuma yana hakimce bisa kujerar da aka ajiye mishi bai ce komai ba sai aikin daddana wayarshi yake.
Mikewa ya yi bayan yaga sun kammala har an fita da kayansu, yana jefa wayarshi a aljihu.
"Ke babu abun da kike bukata ne?" ya watso min tambayar, kai na gyada mishi.
"That's good for you" ya fada in i dont care manner. Daga haka ya fita, bayanshi muka bi booth ya dagawa yaron da ya kawo kayan da keys dake hannunshi muna tsaye gefe na harde hannu na a kirji muna jiran a gama sanya kayan.
Tsalle na yi gefe jin ana cukuikuye hijabi na ta baya, a firgice na juya babu shiri na fara matsawa da baya baya yayinda take biyoni tana kyalkyala dariya da fadin.
Ita ce, ita ce, shegiya ita ce ita ta rabani dashi, ita ce gaba daya mutanen wajen hankalinsu ya dawo kanmu kasancewar da karfi karfi ta ke magana babu kayan kirki a jikinta daga ita sai wani dan kamfai wadda kusan rabinshi a yage. tana sanye da wata riga da ita da babu duk daya, dan ko ina na jikin rigar ya yage kanta babu kyan gani ya yi busu busu bawon rake guntun icce ne babu abun da ya rage bai makale a kan nata ba kafafunta babu takalma makale da wani katon ghana must go a hammatarta da ka ganta kaga typical mahaukaciya, sai sambatu take tana bin Maryama da fadin ita ce, ita ce ta rabani da shi.
Hannu na mika ina nunata da fadin Sameera Sameera ce ai, ban ankara ba na ji ta min wata iriyar damka tana zare idanu da fadin ita ce ta rabani da mijina ita ta rabani dashi.
Da wani irin sauri Jabeer dake kokarin rufe booth din ya karaso gare mu ganin abun da ke faruwa, ga mutane har sun fara yanyamemu a wajen.
Fati da Salima ko sai kiran sunana suke amma sun kasa matsowa, da kyar Jabeer ya murde hannunta da ta kama wuyana da shi har tana cije lebe ya yar da ita kasa.
A rikice na fara shafa wuyar da nake ji kamar ba'ajikina yake ba dan ba karamar shaka ta min ba.
Wani wawan juyi Sameera ta yi gami da mikewa ta kuma nufo ni tana fadin, "Kema sai na halakaki, kin rabani da mijina ke kika shiga rayuwar mu kika rabamu muna farin ciki kafin kizo amma kin zo kin rabamu kema saina kasheki".
Da gudu na fada bayan Hamma Jay na makale shi ta baya ina sakala hannayena akan kirjinshi, murya kasa kasa na ce, "Help me Jayyyy she's the one I told you people ranar da Umaimah zata haihu, ita ce matar mutumin da ya taimakeni ta kashe shi, itace silar zamana gidan yari." banda rawa babu abun da jikina ke yi.
Wasu daga matasan dake wajen ne suka yi kokarin kama Sameera hade da daure hannayenta, wadanda suka santa a area din kuma suna ta mamakin abun da ya faru, don tsawon shekara biyu ke nan take yawo a nan da haukarta kuma babu wadda ta taba attempting kamawa balle ta kai ga shakar mutum, yawanci idan taga namiji dai zataje gabanshi ta ringa fadin, HONEY ,HONEY, HONEY ka dawo? Zamu koma gidanmu?" Idan bakace mata komai ba haka zata juya ta tafi tana ta kyalkyalar dariya amma bata duka.
Kamani Jabeer ya yi ya dura a gaban motar ya kulle sannan su fati ma suka shiga, waya ya kara kunnenshi ya yi magana kadan sannan ya jingina da motar hadi da harde hannayensa a kirji sai faman jijjiga car keys dake hannunshi yake yi bayan shudewar minti goma motoci guda uku manya suka shigo harabar wajen a guje securities na shi ne suka fito ganin yadda suke sara mishi yasa kallo ya dawo kanshi dan mutane da yawa basu shaidashi ba sabida pcap dake kanshi,. Ku wuce da wannan psychiatric sai na neme ku."
Ya fada cike da bada umarni daga haka ya shige gaban motar ya bata wuta suka bar wajen securities din na kiciniyar dura Sameera a mota.
Gudu yake shararawa kamar shi kadai aka yiwa kwalta din, har lokacin kuka nake kamar raina zai fita. al'amarin ya bani tsoro tabbas duniya ba komai bane yanzu Sameera ne wannan?
Duk sadda hotonta time da suke tare da Qaseem ya fado min sai in samu karyewar zuciya in kuma rushewa da kuka.
Kiiiiiiiiiiiii, Jabeer ya yi wani wawan cin taya har muna kokarin kifawa dukkanmu, dago jajayen idanunshi ya yi ya zuba min su cikin fada ya ce, "Will you keep your mouth shut, ko sai na canza miki kammani yanzun nan"?
Jin abun da ya fada ya kara tunzurani ina sakin wani kuka wadda ya fi na farko karfi da fadin.
"Hamma Jay Sameera ce, wllh ita ce, ita ta kasheshi a gabana ina kallonta, ina kallonta yayarta tana kallonta ita ta zo zata soka min wuka by mistake ta soke shi, wllh Allah itaceeeeee"
Na karishe da sakin wani kukan mai taba zuciya.
Rumtse idanunshi da ke cigaba da sauya kammani ya yi yana kallon su Fati dake bayan motar sai sharar hawaye suke yi suma, hannun Maryama ya kamo. ya ce cikin sassauta murya.
"Is ohk, shi kenan ya isa haka, is ohk ki yi shiru haka ai an wuce da ita asibiti yanzu"....
"To kai kuma kana ta yimin ihu a kaina"
Na fada ina share hawayen da suka ki tsayamin.
Shafa kanshi ya yi yana cigaba da murza hannunta ba tare da yace komai ba. ganin ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa a jejjere ya sashi tada motar suka harba titi.
__________________________________
Har muka iso gida babu wadda ya kara yin magana.
Fitowa muka yi ba tare da munbi ta kan kayan dake bayan mota ba muka shige ciki kowa da abun da yake sakawa a ranshi
jingina da headrest na motar ya yi yana lumshe idanunsa, sai da ya kwashe kusan mintuna goma a haka sannan ya fita motar ya shige shima.
Ko da muka shigo palon babu kowa ciki hakan yasa na wuce daki direct na fada saman gado na cigaba da rera kuka na yaran suna bani hakuri, amma duk sadda na hango hoton Sameera da Qaseem da kuma yadda na ganta yanzu,sai inji na kasa daina kukan.
"Da gaske ni ce na rabata da mijinta? da gaske da ban shigo rayuwarsu ba hakan bazai faru ba, shin da bai taimakeni ba da yanzu suna tare da matarshi cikin aminci da irin soyayyar da take nuna mishi din nan. am i a wicked? Nice na rabasu?"
Wadannan tambayoyi su suke dada tunzura ni.
Astagfirullah, Ya Rabbi ka yafe min. Haka na kwashe wunin ranar sukuku da ni ba uhm ba uhm uhm.
*******
Washe gari isowar jama'ar Niger ne ya sanya ni sakin jikina kadan, rungume ni Inna Lami ta yi tana sakin kuka da fadin, "Maryama ashe rai kan ga rai? kin daga mana hankali kin tafi kin barmu da kewarki ashe zaki dawo,"
Tsungunnar da kaina kawai na yi ina fidgeting fingers dina, da ace ina da yadda zanyi, tabbas zan goge wannan kalmar ta kin tafi cikin tarihin rayuwata dan ba karamar kona raina take yi ba, amma babu yadda na iya, ya rigada ya zama zanen kan dutsi bazan iya gogeshi ba.
Yan Niger mutum biyar suka zo da shirinsu na zama har ayi auren Fati dan ya yi kusa suzo su koma su kuma dawowa, dan haka Daada ta yanke shawara idan an gama taron suna zasu tarkata gaba daya su koma ainahin gidansu inda suke da Inna da Baffa.
A ranar da daddare Fati ta shigo janye da trolley babba tana washe hakora ta ce, "Antinmmu yar gata, matso kiga kayan ki, ni wallahi ma nafara kishi, duk cikinmu babu wadda ya samu kwatankwacin naki fa,"
Ta fada cike da raha tana zuge zip din akwatin.
Kayayyakine dinkakku galla gallah a cike tap da akwatin akalla zasu kai kala ashirin, kama daga lace, atampa, materials, shadda. Babu abun da babu a ciki gashi sun samu dinki wajen kwararren tela sai daukar idanu suke yi.
"Wai duk wannan na waye Fati, ko lefen naki ne zamuga sabon salo amarya da dauko lefe daga gidansu ango"
Dariya ta sanya tana fadin, "Rufa min asiri in mutu maza su binne ni, wannan duka na ki ne fa, ni gaskiya sai mun raba".
Zaro ido na yi da fadin, "Ke Fati waya baki duka uban kayan nan" leke leke ta farayi kamar munafuka ta ce, "Yanzu anti Umaimah ta bani wai in kawo miki, an dawar mata da kayan fitar suna ashe ta bawa tela hadda wadannan wai na ki ne".
A take jikina ya yi wani irin sanyi Umaimah masoyiyace na hakika a gareni, lokacin da na je dakinta da nufin gode mata hannuna ta kama da fadin kiyi shiru dan Allah, kar ki ce komai, ni ya kamata in gode miki, da na ki rufin asirin nake rayuwa Maryama. Ba zaki gane ba a yanzu sai nan gaba, rungumeta kawai na yi ina jin kuka yana taho min
Tabbas duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba, babu shakka zai godewa azabarsa, da ace na yi hakuri da yanzu nice a matsayin da Umaimah mai sanar da ni gaskiya a lokacin da na ke kauce hanya take ciki yanzu.
__________________________________
Washe gari aka kira sunan yaro Al-Mustapha, Ham Jabeer ya yanka tikeken rago da shanu guda biyu, ya kashe kudi a wannan suna ya yi bajinta iya bajinta, Ba karamin dadi Umaimah taji da da aka sanyawa jaririn sunan babanta ba kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi, fuskarta dauke da fara'a ta ce "Pretty wanne irin suna zamu kirashi da?"
Ina kallon fuskar cute boy din dake hannuna sai wutsil wutsil yake da kafafunsa na ce, "ANWAR".
Allah ya raya mana Anwar ta fada cike da farin ciki.
A ranar Umaimah ta zama tamkar wata tauraruwa cikin taurari. Duk inda ta gifta sai an kalleta tsabar yadda ta yi kyau harta gaji, ga wuyanta da ya sha gwala gwalai sai walkiya suke. Idan ka ganta a lokacin zaka yi zaton ta haura shekarunta na ashirin da biyar da take kai, ko ina a cike dam dam.Kayan barka kam ta amsa har kaman hannunta zaiyi ciwo.
taro ya yi albarka, an ci ansha an gagije duk wadda yazo kuma ya tafi da gift na turmin atampa mai dauke da hoton Anwar da sauran tarkace a cikin souveniers bag.
**********
Bayan kwana uku da suna abubuwa da yawa sun faru sun wuce, muka fara shirin komawa gidansu Innarmu, damkeni gam Umaimah ta yi tana fadin babu inda zanje anan zamu zauna tare. Dan Allah Inna ki ce ta zauna Daada kice wani abu mana idan kun tafi dukkanku dawa zan zauna plsss pretty mu zauna tare."
Daada ta ce, "Kedai Umaimah bakyason gaskiya, taya za'a barmiki katuwar bazawara haka a gida kamar dai bamuda mukabuli, ga dai Salima dama can a hannunki take, kuma babu wadda ya ce zai dauke ta kuyi ta zama tana rike miki dan jinjirin ga kuma gida cike da ma'aikata duk ta inda mutum ya gitta sai an hadu, to nidai iya abun da zan iya fadi ke nan, ita kuma taje can gaban iyayen nata ta daura damarar zawarci idan Allah ya kawo ko mai saida shayi da burodi ne sai a lallaba a turata tunda dai anan rimi rimi muka zo daga niger, a lokacin ma fama ake da bakar talauci ga dai su lami da fai'za nan haka muka tarkato duk abun da muke dashi muka taho aka daurawa yarinyar nan aure da dan uwanta, fyace majina daada tayi tana matsar idanu sannan ta cigaba da fadin, amma haka nan ta fitittike bata dubi girman Allah ba yarinyar nan ta sanya kafafu ta tafi yawon duniya, to tunda ta dawo ai ba zamu mata baki ba sai dai muce Allah kawo ko mai shayi da burodi ko mai gadin makarantar firamare ya aureta ai hannunka bazai rube ba ka yanke shi ka yar.
Still gaba daya mutanen dake falon suka yi dan maganganun daada a hankali jakar dake hannuna ya fadi kasa, kamar wacce aka yiwa allurar karfi na ruga da gudu na fita waje ina sakin kuka mai zafi, sai yaushe ne zan daina kuka akan kuskuren da na aikata ni Maryama.
"Haaan kunga min jaraba ko? daga fadar gaskiya kuma Allah na tuba sai ta wani fita a guje kamar wacce ta yi gamo,? Wannan duka rashin son gaskiya ne irin na yaran yanzu..." cewar Daada....,backyard na nufa na samu wani dan dakali na zauna ina cusa kaina cikin kafata da sakin sabon kuka.
A hankali na tsagaita da kukan jin kamar kamshinsa nake shaka gaf da ni da sauri na dago kaina shidin ne kuwa, yana tsaye a kaina ya sanya hannayenshi cikin aljihun wandonshi, a rikice na mike na fara ja da baya dan haka kawai yanayin fuskarshi ya bani tsoro wani irin shakkarshi yana dirar min, baya nake yi shikuma yana matsoni har na hadu da jikin gini hannu daya ya sanya ya dafe bangon yana rankwafowa kadan da karkata kai gefe ya ce.
"Yau kuma me aka maki sarkin masu hawaye?"
Cikin kukan na matsar da kaina gefe sannan na ce
"Hamma Jay Ko ba Daada ba ce ta ce wai na fita yawon duniya kuma mai saida shayi da bread ne zai aureniiiii"?
Na kare da fashewa da kuka.
Murmushin gefen baki ya yi sannan ya ce,
"To karya aka miki ne? ba ki fita yawon kin zubarwa kattin banza mutuncinki a Dubai bane, in ba mai sayar da shayi da bread din ba wane mai hankali ne ki ke tunanin zai aure ki a haka"
Kuma fashewa da kuka na yi harda sheshsheka ina fadin Wllh Allah kenan Hamma Jay na tuba bazan kara ba."
"Uhmmmm"
Kawai ya fada yana tafiya ya ce, "kije suna jiranki"
Bayanshi na bi da kallo zuciyata tana bugawa da karfi da karfi, har ya bacewa ganina.
Shi ke nan na rasa Hamma Jay kenan, na rasa waccan dumbin soyayyar da yake nuna min kamar ya bani numfashin sa.
Da gaske ne kenan BA'A 'BARI A KWASHE DAIDAI, Da gaske shi mutunci madara ne idan ya zube saidai ka kwashe samanshi? Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un...
Da kyar na iya jan sagaggun kafafuna na koma gaban gidan, a gaban motoci na same su har su Inna lami sun wuce ni kadai ake jira,..
"Shikenan mairamu daga fadan gaskiya kuma sai ki kullaceni?" cewar Daada, ko shiyyar da take ban gani ba har muka shiga motar Salima tana daga mana hannu,yayinda hawaye ke fita daga idanun Umaimah, ta cikin madubi nake hango yadda Jay ya rungumeta yana share mata hawayen dake fita daga idanunta kana ya jata zuwa cikin gida.
Dafe saitin kirjina dake barazanar bullukowa na yi ina jajantawa kaina.
Gidan su Innarmu kyakkyawan gida ne na kin kari da ko a mafarki ban taba hangomu a irin wannan gida ba, babu abun da zai nunawa gidan da muka baro na Jay sai kasnacewar wancan gidan sama yayin da wannan ya kasance duplex mai girman gaske, babu ce kawai babu a gidan.
Lallai dan Adam bai san abun da ke boye a gaba ba, kwannan mu biyu a gidan amma ban farfado daga maganganun da Jay da Daada suka fadamin ba, sai ma wani jinyar zuciya da nake yi cikin dare, ga wani irin kewarshi da nake just kwana biyu da ban ganshi haka Kawai kamshinsa ke bakuntan hancina a ko wanne second.
**********
Bayan kwana biyu misalin karfe tara na dare Umaimah tana chanzawa Anwar diaper Jabeer yana zaune gefen gado laptop a gabanshi yana aiki, lokaci lokaci yana sipping hot coffee da ta kawo masa, dan matsowa ta yi kusa dashi ta ce.
"Hmmm aiki ake ne baban little?" Da sauri ya dago ya ce.
"Lallai yarinyar nan kinci abinci amma zan rama ne, jira kawai nake wannan dinkin ya warke in baki little din nawa ai".
Dariya ta yi da fadin, "Am dama akwai abun da nake son fada ne idan babu damuwa"
"Oya go on, fadi duk abun da ki ke so a duniyar nan matukar bai fi karfina ba zan baki shi my princess".
Lumshe idanu na yi da fadin "Really?"
"yess ke dai fadi."ya fada yana kurbar coffee nashi.
"So na ke ka maida aurenka da Maryama".
A rikice ta mike sakamakon wanka da ya mata da coffee din dake bakinshi, kafin ya fara wani irin azababben tari, da gudu ta nufi fridge gami da dauko ruwa tana sanya mishi a baki, babu musu ya karba ya shanye yana kallonta da rinannun idanunshi ya ce.
"Kar ki sake min magana makanciyar wannan matukar kina son ganin farin cikina.
Ke kadai kin isheni rayuwar duniya Maimahhh,.....