Page 67
💫MARYAMA💫
By.
Ummu Fadeela.
67
Matukar kina son ganin farin cikina, kada ki kuma kawomin magana makamanciyar wannan.
Ke kadai kin isheni rayuwa Maimahhh.
Ya fada cikin sassauta murya kamar wadda aka zare wa laka.
Bance komai ba na koma inda Anwar ke kwance na dagashi zuwa karshen gadon na kwantar gami da sanya mishi pillow a bayanshi, tura laptop din ya yi gefe yana jinginar da kai Jikin gadon dan gabadaya ya ji ya daina fahimtar aikin da yake yi.
Closet na shiga na shirya cikin kayan bacci na masu kauri riga mai doguwar hannu da wando dogo har kasa, gashina na cusa cikin hula kana na fito zuwa bakin mirror na yi yan shafe shafen turaruka na ban kalli ko shiyyar da ya ke ba na hau gado can kusa da Anwar na kwanta abuna ina janyo duvet da rufa.
Sai a lokacin ya dago da kanshi, zaro idanu ya yi ganin inda ta kwantar da yaron, da dan yanayin da bai sake shi ba har yanzu ya ce,
"Maimahhh ya zaki kwantar da shi a nan, ba gadonshi yana daki na ba? Kawo shi mu wuce kawai kinga ma dare ya yi".
"Yau anan zamu kwana, kai kana iya wucewa dakin naka".
"What?
Ya fada da dan firgici, this is impossible, taya zaki kudindine min yaro a can kamar tsire, ta so plsss".
Ko uffan ban kara fadi ba na yi shiru ina jinshi yana ta magana.
Ganin bazance komai ba yasa shi mikewa yana daukar coffee cup da ya sha ya ce, "To ba ki fitar da cup din ba, ga wajen nan ma ya baci da coffee baki goge ba"
"Duk zaka iya yi just for today, ai a zaman tare akwai taimakekeniya"
Na fada gami da jan baki na tsuke.
Shafa kai Jay ya fara yana kallon bayanta ta cikin bargon da ta rufa musu kafin ya kada kai ya fita da cup din, da mopper ya dawo ya goge inda ya furzar da coffee dazu kana ya dauki laptop nashi ya fita a dakin. Tsawon minti ashirin ya dawo dakin nata cikin shirin bacci ya hawo gadon kusa da ni yana tashina a hankali,
"Maimahh plss ta shi mu koma can ki sanya shi cikin bed nashi, kinga nan babu net and maybe a samu mosquitos a nan din,"
Dariya t yi a zuciyarta wai mosquitos, idan aka samu sauro a nan ai ba kanta, amma a zahiri ta ce.
"You don't worry, dan sun zije shi na yau kawai babu damuwa, zuwa safiya sai in dawar da gadon nashi zuwa nan."
"Damn it!"
Ya fada yana kwanciya a bayana gami da janyoni jikinshi sosai
"To Wai fushi kike da ni ne Maimahh,for what?."
Bance komai ba, kamar yadda ya yi shiru, tsawon lokaci ban yi magana ba shima baiyi magana ba sai dukan da nake ji kirjinshi na yi da sauri sauri kamar zai fito waje, har na fitar da ran cewa zai ce wani abu dan an ja lokaci na ji ya ce.
"Maimahh bakya kishina ne? Na dauka ko wani kika ji ya ce in mayarda Pretty sai in da karfinki ya kare wajen ganin kin hana tabbatuwar hakan, but sai gashi ke kike min tayin hakan. kin manta duk abubuwan da suka faru?
A gaban ki ta yi komai fa, shin bakya tausayi na ne..."
Shiru ya yi na wasu dakikai kamar ya gama magana sai kirjinshi dake cigaba da luguden daka, sai kuma ya cigaba da magana wannan karon sosai raunin dake muryarshi ya bayyana
"The worst part of it Maimahh is dake ta bamu labarin irin rayuwar da ta yi, irin abubuwan da tayi bayan barinta gida, she said a gidan namiji ta zauna a porthacourt shi ne mutumin da ya dinga bibiyar rayuwarta a gidan aurena,kin san iya abunda suka aikata?
Ta kuma sanar da mu ta bi wani sun tafi Dubai and shima namijine, kuma a club ta hadu dashi.
Rumtse idanu ya yi da karfi yana jin ciwon zuciyarshi na barazanar dawowa,rabon da ya ji irin haka ya dauki lokaci tun bayan wani treatment da ya karba a Cairo. She even said that ta yi AURE, an mata aure ta zauna a karkashin inuwar wani, Maimahhhhhh I can't, I can't. ba zan iya ba Maimahhh.
Ya fada yana kankameni da karfin gaske kamar zai sanya ni cikin cikinsa,...
"I can't, ba zan iya ba, ba zan iya ba Maimahhh its hurt, really hurt, ina da kishi,ina kishin duk abun da na ke so".
Gaba daya ya rikice sai kara cusa kanshi yake cikin gashina da hular da na sanya ya zame jikinshi yana rawa, murmushin takaici na yi ina juyowa yanayinsa ya bani tausayi, na fahimci halin da yake ciki, don haka na mike na zauna tsakiyar gadon gami da daukar kanshi na dora bisa kafata, ina shafa lallausan sumar shi na ce.
"Is ohk, ya isa haka bazan kara yi maka magana makamanciyar hakan ba, duk da zan so ace ka yiwa labarin da ta bamu kyakkyawar fahimta ba gurguwar fahimta irin wannan ba.
Baice komai ba sai dadin yadda take shafar Kanshi da ya keji.
********
Washegari da ya kasance Monday misalin bakwai da minti arba'in ya sauko tsaff cikin shirin office sanye da suit bakake da necktie masu daukar ido da covers suma bakake fuskarshi a cunkushe har lokacin da ke nuna alamun baya jin dadin ranshi.
Duk abun da Umaimah ta saba yi mashi bata rage ko dai ba da taimakonta ya yi breakfast sannan ta rako shi har bakin kofa rike da briefcase nashi, tana daga mishi hannu, pecking na gefen fuskarta ya yi yana dan murmushin da iyakarshi saman lebenshi.
A office Jabeer ya wuni ranar saboda aiyukka da wasu mitin mitin da suka dinga shiga.
Wajajen karfe biyar ya baro office din, direct gidan su Innarmu ya umarci driver ya wuce dashi dan baije gaishesu da safe ba. lokacin da ya shigo palon muna zaune dukkannimu Inna lami na murje jikin Fati da hade hadensu na mutanen nijar.
Kamshinsa ne ya fara isowa kafun shi,hakan ya sa na lumshe idanu na ina budewa.
"Dan albarka yanzu kake tafe?" Cewar daada dake hakimce bisa kujera ta daura kafa daya kan daya, zama ya yi yana gaishesu daya bayan daya
kafun Fati ma ta gaishe shi, da fara'a ya amsa yana tsokanarta da Amarya ita ko ta sunne kai.
Kasa kasa nafurta, "Barka da wuni"
Amma ko kallo na bai yi ba, kuma sarai ya jini dan mun hada idanu dashi, ina da tabbacin sauran mutanen dake palon ma sun jini shareni da ya yi sai na ji wani irin takaici ya kamani dan kara tabbatarwa ko dai bai ji ba hasashe na ne kawai na kuma fadin.
"Ina wuni hamma Jay" idan dutse yana magana to babu shakka hamma jay ya tankamini, ko bangaren da na ke bai kalla ba sai ma mikewa da ya yi yana takawa zuwa dakin Innarmu ganin bata palon ya tabbata tana dakinta, rumtse idanu na yi da karfi a kokarina na maida hawayen dake son zubo min, saidai tamkar na kara kiransu ne haka suka cika kwarmin idanuna babu shiri na mike na fada dakinmu na saki kukan da ban san dalilinshi ba.