Page 68
💫MARYAMA💫
By.
Ummu Fadeela.
68
Bayan Maryama Daada ta bi da kallo da fadin, "Ai bari ba shegiya bace da ubanta".
Daga haka ta guntse tamkar ba ita ta yi maganar ba..
A daki kuwa Jabeer ya dade suna tattaunawa da Innarmu a kan auren Fati bayan ta tambayeshi lafiyar su Umaimah da jaririnta.
Duk wasu shirye shiryensu ta sanar da shi, dan haka ya yi addu'ar fatan Allah ya nuna mana lokacin.
*********
Wasa wasa saida na kwashe tsawon sati biyu cur ban sanya Hamma Jay a idanuna ba, da zarar na ji alamun shigowar mota gidan dan zuwa yanzu na fahimci shi kadai ke zuwa da mota, duk abun da nake a compound ko palo ko kitchen to fa zan barine in shige daki, bazan fito ba kuma har sai ya gama abun da yake ya bar gidan.
A gefe daya kuma ga shirye shiryen biki da ake ta yi babu kama hannun yaro, ban fiye sanya kaina a ciki ba duk da matsayin da nake dashi na babbar yayar amarya komai ina yinshi ne gefe gefe dan har yanzu ban gama sakin jiki da mutanen gida ba, kamar bakuwa haka na ke jina har gobe.
Yau ma kamar kullum ina kwance a daki babu abun da na ke yi sai sakawa da kwancewa.
Kofar dakin aka turo, Meerah ta shigo da dan gudunta irin na yara ta haye gadon tana janyoni da fadin.
"Anty Fati tashi ki bani ruwa zan sha, Anti Fati ki tashi".
Ta fada tana janyo ni, mikewa na yi ina kakaro murmushi na ce,
"Baby na Anty Fati bata nan" "laaa Mommyna kina nan kema? shine baki kara zuwa wajen Mommyna ba" ta fada cike da yarinta, shafa sumar ta mai daukar hankali na yi ina kara jinjina kyau da kammanin H.Jay da yarinyar nan ta dauko babu abun da ta mance sai ma wadda ta fishi da.
"Yaushe kika zo" na katse mata dogon surutun da ta fara yimin, ta ce yanzu na zo kuma zansha ruwa shine Innarmu ta ce inzo Anty Fati ta dauka mun ni bazan iya daukowa ba.
"Ohk muje in dauka miki, ina Mommy da Boy nata?" na tambayeta ina dagata akan kafadata, tana bani amsa muka shiga kitchen.
Ruwan gora na dauka mata karami gami da budewa zan tsiyayar mata a cup ta ce, "Ni a bottle na ke so, kuma ba ki daukowa Daddyna ba shima yana dakin Innarmu kuma ya ce in ce da anti Fati ta kawo mishi ruwa shima.
Wani irin bugawa gabana yayi, na dade rabon da in ganshi sai dai in jiyo muryarshi daga nesa, abun da Meerah ta fada yanzu ya sani jin tsinkewar zuciya
"Ki dauka mu kai mishi Mommyna".
Dan waskewa na yi da fadin, "Baby na kinga y..."Katsewa maganata ta yi ganin H.Jay tsaye jiki kofa ya harde hannu a kirji sai dai ba mu ya ke kallo ba.
Cike da izza yake takowa tsakar kitchen din, duk wani taku da ya yi dai dai yake da bugawar zuciyata.
Gifta mu ya yi ya bude fridge bottle water guda ya zaro, sai a lokacin Meerah ta kula dashi,da dan gudunta ta nufoshi.
"Daddyna yanzu zamu kawo maka naka fa" ta fada tana daga mishi hannu wai ya dauke ta, dagata ya yi kuwa ya ce, yana murmushi da fadin "sure daughter"
Daga haka ya fice da ita daga madafar tana mishi surutun bataga Anti Fati ba shi kuma ya biyemata bai masan Maryama tana existing a kitchen din ba.
Wani irin jarumta da karfin hali na aro na yafawa kaina na fito, rasss gabana ya kuma yankewa lokacin da muka yi arba dashi zaune a palo shida Innarmu da Baffa da alama magana suke yi mai muhimmanci.
Kafafuna suna rawa nazo zan gifta su amma kiran da Innarmu ta min ya sani dakatawa da sauri na dawo kaina a kasa na zauna can gefe da su kamar ka ce kyat in ruga da gudu..
Gyaran murya Baffa ya yi sannan ya dube ni ya ce, "Uwata Hammanki yazo ya sameni da wani magana tun kwanaki biyu da suka wuce, ni a karan kaina ban amince da maganar tashi ba, amma dan kada in yanke hukunci ni kadai sai na tuntubi Innarku,
So Alhamdulillah itama bata amince ba, hakama dai Daada babu dai wadda ya aminta da batun a takaice, duk da ya nuna mana irin yadda hakan ke da amfani a wannan zamani kuma muma mun san hakan amma duba da abubuwan da suka faru a baya shiyasa muka yanke shawarar hakurar shi ya fi, ba komai bane kuma ya kawo shawara ne na nema miki gurbin karatu a jami'ar kasa dake nan Abuja amma mu iyayenki munce bamu amince ba.
bamusan na ki tunanin ba, ko kina da abun cewa?".
"Duk da rashin hankali irin nawa na san maganar Baffanmu na karshe shagube ne ya yimin. Cikin raunin da ya bayyana bisa fuskata na tsugunnar da kaina kasa na ce.
"Kuyi hakuri baffa. A matsayinku na iyayena duk hukuncin da kuka zartar a kaina shi ne dai dai,ina fatan hakan ya zama mafi alkahiri a gareni da rayuwata baki daya." Na fada harshena yana rawa da son tona asirin dake zuciyata.
Cike da mamaki suka zuba mata idanu da ba suyi zaton jin haka daga bakinta ba duba da irin son da takewa karatun jami'a wadda shine ummul'aba'isan shigarta duk wani garari. neman taimakon shiga jami'a ne ya kaita wajen siyama har ita siyama ta yi amfani da damarta wajen cimma wata manufa akan Maryama.
"Tashi kije, Allah ya miki Albarka"
Cewar Baffa yana kauda kanshi daga gareta mikewa nayi na nufi daki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka nake tafiya.
Bayan rayuwar da na gani bayan ilimin da duniya da mutanen cikinta suka koyar da ni bana jin zan kara ganin wata zata bijerewa iyayenta in barta....
Bayan shudewar wasu lokaci muna ta lallaba rayuwa, auren fati sai kara matsowa yake yi, yanzu haka saura baifi sati daya ba dan haka shirye shirye ake babu kama hannun yaro.
An kawo kayan kefe akwati goma sha biyu daga gidansu ango ta bangarenmu ma ba karamar bajinta aka yi ba na tarbarsu da kuma tukuici da aka basu, saura kwana uku Umaimah ta tattara ta dawo gidanmu gaba daya, a cewarta bazata iya jigilar zuwa da komawa ba. duk wani abu da ake a bikin yar gata sai da Fati da sabbin kawayenta da suka hadu a makaranta yawancin su yayan manyan kusoshine suka shirya event ya kai kala takwas daban daban tsakanin bangaren amarya da na ango.
Makudan kudade jabeer ya fitar wajen cakare kanwar tashi da kayan daki na bugawa a jarida shafin farko a nan Nigeria a ka sai kayan duk da yadda Fati ta yi ta sha'awar wani kampanin furnitures a TURKEY amma Jabeer ya ce babu abun da za'a nema a Nigeria ba'a samu ba, ai kuwa kayan da aka mata ko gidan diyar shugaban kasa iyaka abun da za'a samu kenan, ba karamin barin kudi ya mata ba duk abun da ta tambayeshi bata kawai yake yi cikin jin dadi da murmushi, a ganinsa idan kana dashi to lallai yan uwanka su samu bare ma irin wannan da shidin ne dai mai yi.
Sun yi event masu armashi kamar su RAINBOW PICNIC, BRIDAL SHOWER, iya ita da yan matan kawayenta ,sosai abun ya bada armashi, sai KAMU ranar alhamis,Washe gari Jumma'a da safe aka yi WALIMA inda manyan malamai suka dinga wa'azi akan AURE da zaman AURE, sai ka ji wa'azin malamai zaka tabbatar da cewa lallai yanzu ana aure ne kawai ba tare da an san menene auren kanshi ba. shiyasa auren baya karko.
Da dare kuma aka shirya kayataccen DINNER both dangin ango da na amarya, washe gari asabar a daura aure a mika amarya dakinta da daddare sun shirya wani event din kuma tsakanin kawayen amarya da abokan ango kawai wai welcome party da za'ayi a gidan ango,..dukka events din babu wadda ba ayiwa anko ba kuma dukka sun hadu ko da dai ba ko wanne na halarta ba, amma tabbas gaba daya Nigeria ba iya garin abuja ba n san ana bikin dan mataimakin shugaban kasa, biki kuwa na fada aji.
Fati ta yi kyau har ta gaji, ta sanya suturu na alfarma kamar dawisu, duk wani soshiyal media da ka bude hotunan event events nata ne kawai ke trending, "Ya Rabb.Irin wannan na so a lokacin da muke cikin talauci amma Allah bai yi ba, sai gashi kanwata ta samu, tabbas babu wadda zai taba yin tsalle ya wuce wuyanshi, kana babu wadda zaiyi gudu ya wuce inuwarshi.
Da daddare muna zaune a dakin da yake mallakinmu nida Umaimah kirjin biki dan tayi kane kane akan komai, duk abun da za'ayi sai an nemi shawararta kana komai tana ciki a matsayinta na matar babban yaya kuma mai fada aji wanda da aljihunsa ake shagalin, bamu dade da idar da sallar maghriba ba ina shirya Anwar yaro dan wattani biyu amma idan ka ganshi zaka dauka ya yi wattani hudu dan yadda ya yi bul bul dashi Umaimah kuma tana bakin mirror ana tsantsara mata kwalliya na tafiya dinner idan mun gabatar da isha,dan tuni wasu ma sun fara wucewa wayarta dake gefena ne ya yi tsuwwa alamar shigowar kira Daddyn Pretty naga sunan dake yawo bisa allon wayar hannu ta miko min ina mika mata wayar ta kara a kunnenta da sauri.
"Shiru ta yi tsawon minti daya bayan ta amsa sallamar da ya mata.
Cikin kasa kasa da murya ta ce, "Plsss mana Daddyn meerah ba mun gama wannan maganar ba tun jiya, and i promise you zan sanya nikab kamar yadda kace, so mai kuma ya rage gashi har an fara tafiya fa, bai kamata ace ban je ba plssss yanzu haka ma shiri muke yi zamu wuce."...
Ke da wa kuke shirin?"
Ya tambayeta "Ni da pretty mana kasan mune manyan yayyu tafiyar mu na musamman ne."
"Ohk baki yarda da abun da na fada ba ke nan, iam serious baki na yi unexpected, gashi babu kowa gidan kuma kinga bai kamata ba, musamman kuma daurin auren ya kawosu daga waje mai nisa Maimahh, ki shirya yanzu driver zai zo daukarki may be idan kun gaisa ma sai ki wuce wajen dinner din daga nan idan da hali ma muje tare"
Ya fada yana guntse dariyarshi, "Really, da gaske zaka je?" Yesss ke dai ki jira driver yanzu yana zuwa.....Yauwa am ehhm kina jina?" ina jinka cewar Umaimah, yana shafa sumar shi ya ce, "Ku taho tare da ita kinga sai kuji dadin wucewa wajen dinner din tare".
Na san wa yake nufi da ita din don haka to kawai nace mishi ina yanke wayar,.
Tunda suka fara maganar na tsaida sanyawa Anwar kayan da na fara na kura mata idanu kamar da ni ake wayar kirjina na dan sauri sauri, sai da ta ajiye wayar sannan na dawo duniyar mu da hanzari na cigaba da sanya mishi kayan.
"Pretty kinji Rigimar Hamma Jay ko,?"
Nan ta kwashe komai ta sanar min.
Wllh dama da kyar ya barni zuwa dinner din nan wai sai na sanya nikab,a hakan ma to gashi nan yanzu kuma wai muje mu gaisa da bakinshi kafin driver ya wuce damu wajen taron.
Murmushin yake da yafi kuka ciwo na yi ina tuna farkon aurenmu da shi da yadda yake sanya ni dole in rufe fuskata da nikab.
Hawayene ya taru gefen idanuna da dabara na sanya hannuna na goge. na ce,
"Ke dai ki wuce kawai nikuma zan tafi da su Inna lami da sauran jama'a, dama ba son zuwa wajen nake ba Umaimah kece kika tilasta ni zuwan".
"Ah ba wannan maganar pretty, baki isa ba,auren Fati kice ba za ki Dinner ba. idan baki je ba wa zai je to?"
Bance komai ba har aka gama mata light makeup din ta shirya cikin doguwar rigar lace dinkin bubu, sosai Umaimah ta yi kyau kai kace matar gwamna ce, duk yadda mai make up din taso yi min ki nayi, da kyar sanda Umaimah ta nuna fushinta sannan na zauna nanma cike da ka'ida akayi kwalliyar da daga powder sai eye pencil da pink lipstick da ta goga min sama sama akan lebena, eyebrow kuma da brush kawai ta gyara min, amma ba karamar kyau na yi ba, duk da har lokacin ban dawo hayyacina sak maryamar da ba, amma tabbas na san kwanciyar hankalin da na fara samu da zama cikin rabar ac da cin lafiayyayen abinci ya taimaka wajen dawo dani cikin kamalata.
Nima doguwar rigar na sanya wadda tare dama Umaimah ta mana anko sa dai ni gyale na yafa akan nawa sabanin ita da ta zumbula hijab har kasa.
Fita Umaimah tayi wajen Innarmu ta sanar mata abun da Jabeer ya fada, don haka su daga can zasu wuce, gyada kai Inna tayi da fadin.
"Ya kirani dazun ya sanar dani abokinshi ne yazo daga can.."Shigowar wata daga cikin yan biki ne ya katse Inna daga maganar da ta fara.
"Wai drivern ya zo" cewar yarinyar daga haka na mike kawai na ce, "Innarmu zaki zo wajen dinner din ai?"
Na fada da dariya saman fuskata. Dakuwa ta min da fadin "Ja'ira, wato gaba daya Umaimah kin maidani kakar ki ko? Inje wajen dinner har ace me?" kai Innarmu haka ake yayi fa, kida na mussaman mc zai sanya miki ma idan zaki yiwa ango liki".
Ganin Inna tana laluben pillow ne yasani fita a guje...Da kyar Umaimah ta jani muka tafi, dan haka kawai na samu kaina da faduwar gaba da tsinkewar zuciya mai tsanani.
Lokacin da muka iso kuwa sai da ta rikeni dan wani irin sarawa kaina ke yi ga wani daci da nakeji a kan harshena.
A haka muka karasa ciki, wani irin iska na shaka da karfi na fitar da sauri, a hankali nake taka stairs din har muka haura, sashen Umaimah muka shiga na zube a palonta ina sauke numfashi.
Kallon mamaki ta min, "wai me kike yine haka pretty?
Kamar wacce ta yi tafiyar kafa?"
Hummm baza ki gane bane Umaimah"
na fada ina jingina da kujerar hijab nata ta zare itama tana kokarin zama da fara feeding Anwar dake kuka ta ce.
"To Allah ya kyauta, kin ga shikuma kuka zai fara min kamar na dakeshi".
Shigowar Jabeer ne ya katse ni daga bata amsa kallon umaimah ya yi ya ce, "Madam dinner, taso ki bawa bakina ruwa"
"wai ko ruwa baka bawa bakin ba, amma dai ka zama marowaci gaskiya" murmushi ya yi yace.
"Ta so ke kam ma yi wannan maganar daga baya."
Bai kula da Allah ya yi ajiyata a wajen bama ya fita daga haka, ni kuma ban gaisheshi ba sanin gaisuwar bashi da wani amfani.
"Plsss pretty help me, bari in basu ruwa inzo," cewar Umaimah tana miko min Anwar, aiko yaro ya tsanyara wani irin ihu kamar an cire mishi idanu, da sauri na mayar da hannuna nace.
"Ji yaron nan yasan mahaifiyarshi, ina ga bai koshi bane dan Allah ke ki hada ruwan ki kai musu suna palon baki a kasa plsss pretty." cewar Umaimah tana marairaice min.
"What, lallai baki da kai,kin ga ya sanyani a lamuransa ne da zaki ce in kai musu ruwa, kawo shi dai ko bai so ke ki kai ruwan," na fada ina kawar da kai gefe.
"Plsss mana pretty, ba zai yadda ba ai bai koshi bane, ruwan kawai zaki mika musu kizo dan Allah."yadda ta yi da fuska sai naji bazan iya yi mata musu ba kuma.
Salalo salalo na fita na sauka kasa, kitchen na shiga gami da daukar babban tray na bude fridge, bottle water na dauka guda uku sai five alive babba guda daya da kuma hollandia babba guda daya shima na daura cups na glass a kan tray din na fito.
cike da nutsuwa na taka cikin sitting room din ina jin zuciyata na zillo kamar zata fado kasa ban kuma san dalilin hakan ba. Cikin siririyar muryata na yi sallama kamar mai tsoron kar a kamata haka nake shigowa da sand'a,suna zaune su biyu Hamma Jay da wani suna hira da gani kasan akwai sanayya sosai a tsakaninsu dukkansu dagowa suka yi a tare suna kallona lokacin da na shigo tsakiyar palon.
Mikewa bakon ya yi yana kallona baki a bude, a take jikina ya dauki kyarma cikin kasa da second daya tray dake hannuna ya subuce kasa cups dake kai suka tarwatse into pieces a wajen bottles dake kai suka watse a tsakar palon.
Da kyar ya iya bude baki ya ce, "MARYAMAA!".