Page 69
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela.
69...
A rikice ya furta "Maryama,!"...Wani irin rawa jikina ya dauka, a hankali tray din dake hannuna ya subuce bottles dake kai suka watse kana glass cups din suka tarwatse into pieces a wajen....
Wani irin sarawa kan Jabeer ya yi da karfi, "Hasbunallahu wani'imal wakeel"ya furta a hankali yana taune lip nashi na kasa da karfi tamkar zai hudasu.
So shima ta san shi ke nan?ya yi wa kanshi tambayar yana kokarin danne wani abu dake taso mishi.Wara idanu ya yi da sauri sakamakon wani tunani da ya fado mishi, wannan ai daga portharcourt ya ke, kar dai ace shine mutumin da.
Tunaninshi ne ya katse jin ya cigaba da magana.
"Maryama! is this you?" ya tambaya yana nuna ta da yatsa, sai kuma ya juyo yana kallon Jabeer da kyau,tun ranar da ya fara kallon shi yake mashi kama da wata ko wani amma ya rasa wanene.
Sai yanzu ya tabbata ashe da Maryama suke kama,nuna ta ya yi sannan ya nuna Jabeer da ke jin zuciyarshi kamar zatayi bindiga sannan ya hade yatsunshi yana yaren kurame.
A harzuke Jay ya mike ganin yadda ta tsaya kamar statue a gabansu ko motsi ba tayi. "Get out of here" ya fada yana nuna mata kofa,jikina na mazari na juya da sauri zan bar wajen dan ji nayi gaba daya jinin jikina ya tsotse lokacinda na yi arba dashi.
"Ouchhh wayyo Hamma Jayyyy!!". Na fada jin wani irin ciwo da ya ratsa tafin kafata har cikin kwakwalwata, lokacin da na fara tafiya.
Da hanzari ya juyo gareta ganin ta kai duqe a wajen tana dafe kafa. "Hamma Jay kafata, wayyo kafata!"
take Jabeer ya rikice ya kamo kafar dan ganin menene,kwalbar cup din da ya fashe ne ya shiga mata kafar,ba wani babba bane kuma bai shige duka ba tsabar raki ne kawai irin nata,lallausar kafar nata ya kama da finciko broken glass din da dabara, take kuwa ya fita ya sake kafar yana cigaba da nuna mata hanya.
Ta kasan ido na saci kallon SADEEQ dake ta kallonmu a tsaye har lokacin,zaka rantse da Allah mutum mutumi ne dan ko shaka da fitar da iska baya yi,."Shine ko dai kamace"?,na yiwa kaina tambayar, da kamace ai bazai kira sunanki ba.Zuciyata ta bani amsa da sauri na fice daga palon
Maimakon in wuce wajen Umaimah haka kawai na samu kaina da tsayawa bakin kofar zuciyata na bugawa na kafa kunnena da fatan Allah ya sa inji abun da zasu fada...sai a lokacin Sadeeq ya dawo hankalinshi har da daga hannu kamar zai kamota sai dai ina ta rigada ta fice.
Kallonshi ya mayar kan Jabeer ya ce, "is she your sister or..." sai kuma ya yi shiru.Kakalo murmushin yake Jay ya yi yana gyada kai ya ce, "eh,sister dita ce.do you know her before?".Jagwab Sadeeq ya zube kan kujerar da ya tashi yana lumshe idanu,ya rasa wani irin tunani zai yi.
Jabeer dai ban da tafarfasa babu abun da zuciyarshi ke yi,idan ba gulma ba mai ya kawota nan,ita na ce ta kawo mana ruwa ne? and ta zo sandandan kamar sandan rake ko hijabi babu jikinta,mtsssww" ya ja wani tsakin da ya fito fili.
"Iam sorry ranka ya dade"cewar Sadeeq da ya dauka rashin bawa Jabeer amsa ne ya sashi jan tsaki.
Dan gyara zama Jay ya yi ya ce, "Kasanta ne kafun yanzu?"
"Yes i know her, bama iya sani ba har a gidana ta zauna, kaga wannan ya wuce sani kawai.
Ipam the one da na fara sponsoring karatunta a port,may be time din baka nan,ta fara karatu and ta sanadiyan karatun na hadu da ita,I love her from day one da na fara ganinta,i betray my parents choice because of her,but she end up broken my heart into thousands pieces.
Sorry sir it may sound hurt i knw tunda yar uwarka ce, amma Maryama maciyiya amana ce, kan ta kawai ta sani, bata respecting feelings na wani sai nata daga karshe ta zo har tsakar palona ta sanar dani dubai zata wuce yin kasuwanci without the consent of her parent bata dubi girman soyayyar da nake mata ba,bata duba rokon da nai mata ba haka ta tsallaka ta tafi ta barni da jinyar zuciya.....
Tiryan tiryan Sadeeq ya bawa Jay labarin yadda watarana Siyama ta kirashi a waya da rokonshi akwai wata yarinya da zai taimakawa akan harkar kasuwanci da yadda Maryama ta je hotel ta sameshi har sadda komai ya mika suka taho Port tare da Siyama mutuwar Siyama da kuma tafiyar Maryama, ya daura da fadin.
"Bayan tafiyar ta na bibiyi al'amarinta sosai har garinsu na je, amma unfortunately ban samu gidansu ba,inda aka nuna min wani kango da fadin sun tashi gidansu kuma ya kone, da na matsa da tambaya ma barazanar duka wasu yara suka min, da taimakon saurayin Siyama da ya kasance yaro boy nawa muka je gidansu siyamar nan na tabbatarwa iyayenta cewa ta mutu naga tashin hankali waccan ranar amma komai ya wuce, i was depressed a lokacin.
Na yi jinya sosai rashin karewar lokaci ne kawai yasa ban mutu ba.
Iyayena sun dawar dani gabansu inda na bar port bayan na samu sauki na koma, a time din ne kuma yan team nawa da muke harkar crude oil tare suka ha'ince ni har ya yi dalilin haduwata da kai ka taimakeni a court na samu na tsira.
Yanzu haka ina auren yar uwata daya tilo Khadija, muna zaune lafiya da ita da yaranmu guda biyu, gaiyatar da na gani ka yi na daurin auren yar uwarka ne ya sani zuwa nan dan irin hallacin da ka min,and iam Happy Maryama ta dawo gida,ta dawo cikin iyalanta." Sadeeq ya ja dogon numfashi yana karewa palon kallo.
Can bakin window ya hango Jabeer tsaye ya dage curtains yana kallon waje,duk tsiyarka bazaka karanci expression na shi ba.
Wani irin kuka ne ya kwace min da karfi na toshe bakina na bar wajen da gudu,kitchen da na gani a bude na shige ban tsaya a can ba na bude kofar backyard na fita,akan matakala guda uku da zaka hau kafun ka shiga kitchen din ta baya na zauna ina sakin kuka mai cin rai.
Juyowa Jabeer ya yi yana murmushin yake ya ce yana kallon cikin idanun Sadeeq, "Iam sorry on behalf of her.
Ka yi hakuri tabbas bata kyauta ba, amma abubuwa da dama sun faru sanadin abun da ta aikata,sai dai komai yana kasancewa bawa ne bisa zanen kaddararshi,ta wani bangaren zamu iya cewa abun da ta aikata ya zame mana alkhairi dan da bamu baro can ba may be da yanzu bama a wannan matsayin,iam sorry once again". Da sassarfa Sadeeq ya taso yana rike Hannun Jabeer tabbas da ya lura zai tabbatar ba'a hayyacinsa yake ba karfin hali ne, amma bai lura ba.Ya ce, "Yallabai ni ne zan baku hakuri, kuyi hakuri dan Allah."
Komai Jabeer bai ce ba,ya debi ruwan da ta zubar ya gyara musu zama ya ce, "Let me get you another cup" bai jira cewarshi ba ya fita da hanzari ya rike kujera jin yana neman kaiwa kasa,sosai zuciyarshi ke gudu da karfi da karfi,ya dau kusan mintuna biyar a wajen sannan ya mike,kitchen ya shiga ya dauki cup,har ya juya zai fita ya jiyo kamar sheshsheka a backyard,dakatawa ya yi,tabbas kuka ne kuma ya gane mai kukan,cije lips nashi ya yi gami da fita ba tare da ya lekata ba.Sun dan juma da Sadeeq bayan ya kaimishi cofin sai dai dukkansu ransu babu dadi,Jabeer kam ma zazzabine rau a jikinshi amma yake dannewa da nuna mazantaka,shigowar Umaimah cikin zumbulelen hijab nata ne ya sa su daurawa fuskokinsu fara'a dukkansu, Jabeer ya yi karfin fadin"Meet my wife,Umaimahhh". Yana murmushi sosai ya ce, "Barka da dare ranki ya dade" a tsanake suka gaisa kana Sadeeq ya mike yana zura hannunshi a aljihun wandonshi ya ce, "To ni zan wuce masauki na dama na zo mu gaisa dake ne Madam."...Masha Allah muna godiya da ziyara,amma ya bakazo mana da maman baby ba?" wllh munso zuwa tare harda mom ma, to ita Mom dince bata ji dadi ba so dole Madam dince a wajenta thats why."Eyyah Rabbi ya bata lafiya" cewar Umaimah murmushi dauke fuskarta.Daga haka Sadeeq ya fita Jabeer ya na mara mishi baya,har wajen motar da ya zo dashi ya rakashi inda ya shiga ya wuce Sheraton Hotel inda ya sauka,juyowa ciki Jabeer ya yi tamkar bai son tafiyar dan yadda yake ji.
**********
A palon kasa din ya samu Umaimah zaune tana jiransa har lokacin.
Kokarin boye damuwarshi ya yi ya ce, "Ba kiyi bacci ba har yanzu Madam?". "Ina fa zanyi bacci ina jiranka mu wuce wajen dinner,ga Anwar ya tsaida ni da ihu da kyar na samu ya yi bacci yanzu".Dan juyawa ta yi kamar mai neman abu,"Ina pretty, daga na ce ta taimaka ta kawo muku lemu Anwar ya rikeni shikenan ban kara ganinta ba har yanzu,kusan gaba daya sama da kasa na yi checking na ta ban ganta ba, kar dai ace wucewarta ta yi ba ta jirani ba ga shi babu waya a hannunta?".
Tabbas da tasan yadda surutun da take yakebkara hauhawar ciwon kan da yake ji da tayi shiru.Hannunshi ya buda mata alamar bai sani ba yana jingina da kujerar da ke kusa dashi.
"Daddyn Meerah ka kira ko wayar Fati dinmana muji ko taje,kasan ba ko ina ta sani ba,gashi dare ne yanzu,kuma na duba ko ina ban ganta ba".Jin ya yi shiru bai bata amsa bane ya sata yin shiru ta tabbata yan miskilancin suna kusa kenan,ko kuma akwai abun da ke damunshi,amma sai tayi shiru sanin idan yana cikin irin wannan halin baya son takura.Bayan shudewar minti biyar babu wanda ya ce wani abu,Umaimah ta yi karfin halin fadin, "Akwai abun da ke damunka ne?ko baka da lafiya ne?".
Dago kanshi ya yi ya ce, "Iam fine Maimahh just that ina bukatar kasancewa ni kadai plsss".Lumshe idanu ta yi ta bude,wannan ba sabon abu ne ba a wajenta,yasha yi mata fiye da haka ma farkon aurensu kuma ta yi hakuri ta shanye,tsam ta mike da fadin, "Anyway, akwai abun da kake bukata yanzu?" girgiza mata kai ya yi baice komai ba,itama bata ce dinba ta juya tana jin zafi a ranta amma ta danne,har ta kama karfen stairs zata haura ta jiyo muryarshi cike da rauni yana fadin.
"Maimahhhh plsssss".
Dakatawa ta yi daga haurawar da ta fara,tabbas yana cikin damuwa,idan ya aikata mata abu makamancin haka maimahhh plsss kawai yake iya fada mata cike da tausayawa dan haka ta jijjiga kanta kawai ta haura ba tare da ta juyo ba.
Zamewa ya yi ya kwanta saman kujerar ya harde hannayenshi akan kirjinsa.
********
Ko da Umaimah ta haura sama wayarta ta dauka gami da kiran Fati,sai dai har ta katse bata dauka ba,sau uku tana kiranta bata dauka ba hakan yasa ta sauya akalar kiran kan Innarmu,sai dai itama har ya katse bata dauka ba.
Awa daya Jabeer ya kwashe a wajen ba tare da ya rumtsa ba kuma bai juya ba,agogon bangon dake palon ne ya buga karfe goma na dare,a hankali ya mike yana jin kamar iska zai kadashi ya nufi kitchen din,bisa mamakinsa yanzu baya jiyowa kukan nata,takawa ya yi har bakin wundo ya leka,tana zaune a first step ya yinda kanta ke daure bisa second step din kamar tana bacci.
Kofar ya bude ya fito,wajen akwai sanyin sosai bana wasa ba kasancewar yanayim sanyi ake ga kuma garden a gefe.
Tsugunawa ya yi a gaf da ita, har ya sanya hannu zai tasheta sai kuma ya fasa yana mikewa da sauri, kafarshi ya sanya gami da ture kanta dashi.
A firgice Maryama da bacci ya sureta tana cikin ta farka hadi da mikewa,baki ta wangale zata kurma ihu ganin inuwar abu tsaye kanta kasancewar babu wadataccen haske a wajen Jabeer ya yi saurin sanya tausasan tafin hannunshi ya rufe bakin nata dashi,rikicewa ta kuma yi da kokarin fizgewa yace, "Ke,ki nutsu kafin in babbalaki a nan"...Cik ta tsaya kuwa jin muryarshi,sai dai rawar da jikinta ke yi da ke bayyana madaukakin tsoron da take ciki.sake ta ya yi ganin ta nutsu ya kama hannunta gami da janta har cikin kitchen din,jikin cabinet ya jefata ya harde hannayenshi a kirji yana kallon jajayen idanunta da suka koshi da kuka ya ce.
"Me kike yi a nan?ko dadiron naki kike jira ya zo ya sameki ku wuce dan daurawa daga inda kuka tsaya,zaro ido na yi a lokaci daya kuma kirjina yana bada sautin Dammmmm.
"Yess,abun da kika ji shina tambaya,shi kike jirane?"ya fada da karfi wannan karon har jijiyoyin kanshi suna tashi,sai da na toshe kunnuwana ina girgiza kai da sauri,
"To me kike yi a nan har yanzu?"ya kuma fada a harzuke.
Jikina yana rawa sosai idanuna na zubar da kwallah na kalmar dadiro na da ya ambata kana zuciyata cike da ciwo da rauni na ce bakina yana katse jimlar ko wacce gaba ta kalmar,.."Ba...aaa.Bu..Ka.wai kuka na ke yi Iam so...rry...bazan ka...Ra ba.Hamma jayyyyyy!" na karasa da fashewa da kuka sosai.
Banyi aune ba kawai na ji ni kwance cikin faffadan kirjinshi ya matse ni gam yana numfashi da sauri sauri, "Why,Pretty!? me yasa kike wujijjiga rayuwata?me yasa bazaki barni in huta ba tun daga yarinta har girma ba,why pretty why?". Ya fada yana kara matse ni kamar zai ballani.sosai na ke jin yadda zuciyarshi ke bugawa fiye da kima a jikina.
Wani irin kuka na kuma kecewa dashi jin abun da yake fada da alamun fitar hayyaci a tattare dashi ga zafi da jikinshi ya dauka.
Ya dade yana rike da ni kafun ya cika ni bai kuma kallona ba ya rufe kofar bayan da makulli ya zare ya fita daga kitchen din da sauri.........