Page 70
💫MARYAMA💫
70....
Zubewa na yi bisa guiwata, kukan da na fara ya katse sai juyawa da kai na ke yi.
"Me Hamma Jay ke nufi da kalamanshi? Mei yake damunsa haka yau? Bashi da lafiyane?
Wadannan tambayoyi sunake ta jerawa kaina gefe daya kuma kalmar Dadirona da ya ambata still yana makale a raina, and the moment..
Moment da ya bani hug was something d..
Da hanzari na mike ina kokarin matsar da abun a raina.
Cikin sand'a na fito daga kitchen din ina leke kamar barauniya. ganin babu kowa palon ya sani shigewa dakin da muka zauna da su Fati, wanda yake mallakin Salima ne da meerah a kasa kuma suna da wani dakin a sama.
Dakin yana nan very tidy don haka cikin duvet na shige ina jin wani irin sanyi yana shigata ta tafin kafa.
Ko da ya haura sama shima dakinsa ya shige ba tare da ya sauya kaya ba ya hau saman couch ya kwanta yana lumshe idanu da addu'ar ina ma dai zai iya kuka kamar yadda take yi din nan, may be da ya samu saukin radadin da zuciyar shi ke mishi.
Ganin abun yana karayin gaba dole ya tashi ya nemi maganinshi ya hadiye ya kuma kwanciya.
Jin footstep nashi yana hawowa sama da wucewarshi da kuma sound na rufe kofa ya sanya Umaimah lumshe idanunta a hankali wasu siraran hawaye suka sauka bisa kuncintaa irin wannan yanayi mahaifinta dake birnin yola a yanzu da taimakon Jabeer kawai take iya kira, shike rarrashinta ga shi kuma dare ya yi yanzu. rungume Anwar ta yi a jikinta tana shafa kanshi.
************
Kusan dukkansu yadda suka ga rana haka suka ga wannan dare, sai dai ta bangaren Maryama ya fi muni dan sosai take fama da zazzabi jikinta sai kakkarwa yake har hakoranta suna karo da juna ga cikinta dake ta faman hautsinawa...
Da asuba Jabeer ya sauka zuwa masallacin dake jikin gidanshi, lokacin da ya dawo ya jiyo sautin kakarin amanta a dakin dan dakatawa ya yi dan tabbatar da abun da yake jiyowa kamar zai shiga dakin sai kuma ya fasa ya haura sama, dakin Umaimah ya shiga, tana zaune kan pray mat hannunta rike da qur'an tana karantawa da sauti mai bayyana cewa kuka ta keyi, zaman minti biyu ya yi a wajen ta shafa addu'arta ta mike gami da nade sallayar kana ta kai qur'an din wajen zamanshi.
Bakin gadon ta dawo ta zauna shikuma yana kan bedside, "Ina kwana" ta fada kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta.
Shafa kanshi ya yi yana son kallonta amma taki bashi damar hakan,.
"Plssss Maimahhh"
Ya fada in a low voice, dago kanta ta yi da fadin,
"Plsss for what?"
Cigaba da shafa kanshi ya yi yana kallon jajayen idanunta da suka dan tasa kadan saboda kukan da tai jiya, dagowa ya yi zuwa inda take ya zauna gefenta ya janyota jikinshi.
Lamo ta kwanta kuwa bata ce komai ba, lumshe idanu ya yi kana ya bude ya ce.
"Sorry for what i did to you yesterday night,ba..."
"Shhhttt"
Ta fada gami da tashi daga jikinsa ta ce, " Na sani baka jin dadi ne, kuma ya wuce this is not the first time da hakan ke faruwa, so ya rigada ya zame min jiki kar ka damu".
Pecking na kumatunta ya yi yace, "Thank you dear, ina miki fatan samun farin ciki na har abada a rayuwarki,.
Am inaga kawar ki ta nan fa, na ji kamar motsin ta a dakin Salima. ko zaki je ki dubata?".
Ya fada yana tashi, wara ido Umaimah ta yi ta ce, "wai Pretty? Kuma jiya babu inda ban duba bafa" daga haka suka fita tare shi ya wuce side nashi ita kuma ta sauka kasa.
Sosai hankalin Umaimah ya tashi ganin irin yadda Maryama take kelaya amai ga jikinta dake rawa ta ko ina hade da zafin da ya dauka kamar an kunna oven.
Rikicewa ta yi ta ma rasa mai zata farayi, sannu kawai take mata amma da alama bata ma cikin hayyacinta.
Da dan gudu ta fita zuwa palon Jabeer, tsaye ta same shi palon sai kai da kawowa yake yi tace, "Hamma Jay ai bata da lafiya, she's vomiting gabadaya ta sake duk inda ta kama. Sauko mu kaita asibiti da sauri.
kamata Jay ya yi ganin yadda ta rikice ya ce, "Ta kimtsa sai kuje asibitin zan yiwa driver magana". Plsss Hamma Jay muje tare plsss plsss bata da lafiya sosai".
Yaushe kika fara yimin musu Maimahh? kin manta yau daurin auren fati ne? and mutane dayawa a wajen bakina ne, so jeki kaita zan yiwa driver magana.
Ba don taso ba ta juya jiki babu karfi, da taimakonta Maryama ta kimtsa ta kira daya daga cikin ma'aikatanta da basu wuce gidansu Innarmu ba ta bata gyaran inda aman ya bata ta fitar da Maryama har zuwa wajen motar da tuni har driver ya fitar, a back seat ta kwantar da ita, ciki ta koma ta sauya kaya daga na bacci zuwa wata atamfa gami da goya Anwar dake bacci sannan ta dawo suka wuce asibiti.
Lokacin da suka fito garin dulum dulum har yanzu bai gama washewa ba dan haka a take suka iso asibitin inda nurses wadanda suka yi night duty suka karbeta.
Ruwa aka fara daura mata sai allurar bacci dan likitan ya fahimci damuwa mai tsananine ya haddasa mata zazzabin.
Sosai ta samu bacci, Umaimah tana son sanar da Innarmu amma batason daga mata hankali cikin taron jama'a.
Tana cikin tunanin ne kiran Innar ya shigo wayarta, "Umaimah ina kuka shiga ne haka? gida ya cika makil amma babu yayyun amarya?" cewar Inna, dan ajiyar zuciya Umaimah ta sauke ta ce, "Inna gamu nan tahowa yanzu insha Allah, an dan samu akasi ne shi ya sa amma muna zuwa.
_____________________________________
Sosai daurin auren Fati ya samu halartar manyan kusoshin gwamnati, yan siyasa, sarakuna,da masu rike da madafun iko daga bangarori daban daban na kasar nan harda makwabta kasaacewar uban angon dan siyasa, hakama ta bangaren Jabeer yana rike da babban mukamin da kowa ke son damawa dashi da ganin ya mishi wani abu da zai san da zamanshi.
Ba karamar kyau ya yi ba cikin wata lafiyayyar menlace light blue mai maiko da kallo daya zaka mishi ka fahimci ba kananan kudi ya lakume ba.
Ya murza hula kirar dara sai sheki take yi, yana zaune gefen Baffa cikin masallacin misalin karfe sha daya na safiya, fuskarshi fal farin ciki lokacin da yake bawa wakilin ango auren Fati a matsayin da baffa ya daura mishi na waliyin amarya. Biki ya yi biki an daura aure lafiya sai san barka.
**************
A cikin gida kuwa ba karamin tashi hankalin Inna ya yi ba ganin har lokacin babu Maryama babu Umaimah, duk da akwai yan uwa da abokan arziki da ma yan bani na iya da ba'a gaiyaccesu ba cike gidan, amma sai tana jin babu dadi dole ta kuma zagawa baya ta kira wayar Umaimah wannan karon gaskiya Umaimah ta sanar mata cewa suna asibiti Maryama babu lafiya amma da sauki don ma an daura mata ruwa kuma ta samu bacci har yanzu bata farka ba.
Ba karamin tashi hankalin Innarmu ya yi ba, amma ta yi kokarin dannewa don jama'ar dake cike gidan, inna lami ta nemo ta sanar mata abun da ke faruwa cikin sirri ta sulale ta tafi asibitin. Haka dai daurin aure da kai amarya ya wuce su dan har dare suna asibitin ba'a sallamosu ba.
Zuwa lokacin mutane da dama sunji maganar rashin lafiyar, hakan yasa ake ta diddikowa zuwa dubata.
Yanzu ma da suke zaune cike dakin makil da jama'a Daada sai bambamin fada take yi wai Innarmu bata zo duba Maryama ba, "sai kace a kanta aka fara haihuwar yar fari, ni dai gaskiya Dijah ta zo ta fadamin idan son yarinyar ne bata yi in dauketa mu koma nijar kawai. haba tunda yar nan ta dawo take ta wani sha mata kamshi uwa ita bata taba yin wani kuskure ba a rayuwarta, bata sanyata cikin sabgoginta tsakaninsu gaisuwa sai zaman kurame, yanzu kuma ga ta kwance rai a hannun Allah amma funfurus taki zuwa sabgar bikin yar gata ne a gabanta ta nunawa duniya kuru kuru cewa waccar din take so".
Kamshin da ya cika dakin ne da shirun da jama'ar dake ciki suka yi yasata sanyawa maganarta ta linzami.
"Ah'ah su waye wadannan kuma?"
Cewar Daada tana kallon su Jay da suka shigo dakin dauke da sallama, ko bangaren da take bai kalla ba ya janyo kujera yana kokarin turawa Sadeeq.
Sadeeq dinne ya dan tsugunna kadan da fadin, "Mune Kaka, barka da dare ya mai jikin kuma?". Kasa kasa Daada ta ce, "Jimin mutum, rusheshe dashi wai kaka, wannan ai da kadan Alhassan zai girme masa" a zahiri kuma ta ce.
"Ah madallah, sannunku mai jiki da sauki dai amma gata kwance har yanzu kamar matacciya, ba uhm ba uhm uhm, to Allah dai ya sauwake mana cuta ko wacce iriya, Allah ya maka albarka ai kafi waccan da ya ja tunga ya tsaya kamar soja a fagen yaki.
Jabeer dai bai ce komai ba har lokacin. saman kujerar Sadeeq ya zauna yana kure Maryama da kallo ya yinda mutanen dake dakin suka fara gaishe su da kokarin fita, daya bayan daya suka fita ya rage daga Jabeer sai Sadeeq sai Maryama dake kwance idanunta lumshe amma ba bacci take ba, sai dukan tara tara kirjinta yake yi. hatta da Daada ta fita.
"How you feeling now pretty?".
Ta ji muryarshi ya doki dodon kunnenta. ba zata taba manta muryar ba kamar yadda bazata manta mai muryar ba,a hankali na bude idanuna gefen da nake jiyo kamshin turaren Jay ya fi yawa na fara satar kallo, karaff muka hada idanu yana tsaye harde da hannu a kirji yana sanye da bakar jeans da riga longsleeve mai gidan dara baki da fari, sai agogo baki da ke daure a tsintsiyar hannunshi. Hararar da ya balla min ne ya sani saurin mayar da idanuna na rufe ruff numfashina yana fita da sauri sauri.
Maimata tambayar Sadeeq ya kuma yi.
Cikin rawar harshe na ce, "Jiki da sauki Alhamdulillah, ya su mama?"
Da sauri Jay ya dago kanshi ya kalleta,vibrate da wayarshi ya fara ne yasashi katse kallon ya fitar da wayar gami da yin pick ya kara a kunnenshi, yana magana cike da nutsuwa amma hankalinshi yana kansu.
Murmushi Sadeeq ya yi ya ce, "Suna lafiya, thou Mom bata ji dadi ba kadan but tana samun sauki sosai da tare zamu zo ma, So how was Dubai?"
Wani irin tsinkewa zuciyata ta yi har saida na ji yawun bakina yamin daci sai dai bance komai ba, shima bai kuma bi ta kan tambayar ba wayarshi ya fitar ya dan daddana sannan ya matso da kujerar kusa da gadon da nake kai saura kadan zuciyata ta shige cikin cikina lokacin da ya matso wayar ya juya min ina kallon hoton dake bisa screen din mace da kyawawan yara guda biyu kallo daya na ganeta ita ce suka taba zuwa da Mamarshi port, "This is my family" ya fada yana murmushi.
"Nice family" na furta ina jin yadda idanun h.Jay ke yawo a kaina.
Wayar ya kuma mikamin, "saka min digit na ki idan na koma zan hadaku ku gaisa," cewarshi yana miko min wayar.
Ban fara gangancin karba ba,,sai satar kallon jay da nake ta wutsiyar idona wayarshi da ya sauke daga kunne ya jefa cikin aljihun wandonshi sannan ya fara takowa toward us.
Yana kallon Sadeeq ya ce.
"Zaka yi missing flight fa mr man"
"Aiko dai babban yaya wai da ina son kafa gwamnati nane kafin in koma.
Hannunshi dake rike da wayar da yake ta faman tura min in sa mishi lamba hamma jay ya kama da fadin, "Ai bata rike waya yanzu, duk sadda tayi waya zan tura maka digit din now time yana wucewa kar ka rasa jirginka,".
"To oga " cewar sadeeq yana mikewa, da haka ya janye shi suka wuce ba tare da yace min ya jiki ba, sai ma hararar da ya ke ta aika min.
wani irin tunani ne ya fado min a rai, a da ina ganin Sadeeq a matsayin attajirin mutum da babu kamarsa, har ina raina Jay a kanshi, sai gashi yau a gabana yana kiran Jabeer Oga, what a life?"
Bayan kwana biyu Alhamdulillahi jikina ya yi kyau dan haka aka sallamoni.
Gaba daya yan biki sun watse,yan nijar kuwa washegarin da aka sallamoni suka wuce cike da abun arzikin da hamma jay da innarmu suka cikasu dashi, Daada dai anan take, Jay ya dade da daukota, dan haka muka zama mu kadai yanzu, ni kadai a daki babu Fati Salima kuma dama a wajen Umaimah take, don haka na lallaba na koma dakin Daada...
bayan wani lokaci kadan munje mun gano dakin fati ni da Umaimah, gidanta kam sai san barka.
****************.
Rayuwa tana ta tafiya, yau dadi gobe akasin haka ina kokarin kiyaye kaina daga haduwa da Hamma jay, dan duk sadda muka hadu gani gashi, sai ya fadamin maganar da sai na yi kuka.
A kwana a tashi auren Fati ya kai wattani takwas, wadda yayi daidai da wattani goma da dawowata, sosai na canza, kyawuna na ainahi ya dawo har ma fiye da da kasancewar cima mai kyau da waje mai inuwa. abubuwa da yawa sun faru ciki har da warkewar Sameera daga hauka saboda kudin da Jabeer ya zuba aka yi mata magani, da bakinta ta furta ita ta kashe Qaseem da farko a wajen yayarta falmata take suna zaman lafiya kafin kai kayi ya koma kan mashekiya maganin da boka ya basu ta zubawa Maryama tun waccan lokaci idan ta tsallake shikenan zata haukace, shine kwalbar ya fashe watarana sunje tattara kayan dake gidan qaseem by mistake ita ta tsallake shi babu bata lokaci kuwa ta haukace Falmata kuma an samu labarin mutuwarta dalilin barayi da suka shiga musu sata watarana mijinta ya dawo daga kasar waje suka bindigesu har lahira.
Jabeer bai yi kasa a guiwa ba ya sa aka mika Sameera kotu dan yi mata hukunci, bayan zaman kotu da kwararan shaidu aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Wani abun da ya faru kuma shine kawo kudin gaisuwar Salima da aka yi gidanmu da nufin idan ta gama sec za'ayi bikin ta cigaba da karatunta a dakinta.
Wannan al'amari ba karamin tayarwa Daada hankali ya yi ba har ma da Innarmu dan ganin har lokacin babu wadda ya taba zuwa da sunan yana sona koda ko almajiri ne, kai ko irin samarin nan na karya da ke tare yan mata a hanya su latsa din nan ni ban taba samu ba, ga kyau din ga dukiya akwai a gidanmu amma babu mashinshini, wani irin bakin jini ne dani tamkar abun da na aikata yana rubuce a goshi na.
Umaimah ta yi korafi har ta gaji akan Jabeer ya maida Maryama amma yaki kulata, ita kuma nauyin Maryama take ji ba zata iya mata maganar ba.
Ko yau ma da tazo duba Daada dake fama da rashin lafiya da ya hadu da tsufa tana son yiwa pretty maganar amma ta kasa, haka ta wuni da dare Jabeer da ya zo duba daadan shima ya dauketa suka wuce.
Washegari kuwa jikin Daada ya kuma rikicewa har ta fara barin wasiyya, "Mairamu kira min Alhassan da Dijah suzo yanzu" cewar Daada tana tamke hannuna dake rike cikin nata, tun ban tashi bama Innarmu ta shigo rike da kofin da ta dama mata kunu a ciki,a hanzarce ta ajiye kofin ta karaso kanta tana fadin "sannu Daada".
Gyada kai Daada ta yi cikin yanayi na galabaita ta ce, "Dijah kira min Alhassan da Jabeeru yan zunnan, ina ganin lokaci ya yi,yi maza ki kira min su su zo yanzu yanzu". To Daada baffansu bai dade da shigowa ba, shi Jabeer dinne dai sai an laluboshi a waya ungo maza Maryama lalubo minshi a waya" cewar Inna tana mika min wayarta dake zaune gefe guda.
Wayar na amsa ina share hawayena na fara neman layinsa bugu biyu kuwa ya amsa da fadin
"Barka da safiya Innarmu, yau ban samu shigowa da safe ba wani meeting na gaggawa ne ya same ni shiyasa na ce sai ina komawa zan shigo".
"Ba Innarmu ba ce, Hamma Jayyy".
Da sauri ya mike har kamar zai kifa da desk dake gabanshi, a rikice ya ce,"me ya faru ina Innar? Me ya sameta ina Baffa? Gabadaya ya rikice hakan ya kuma rikita Maryama ta fashe da kuka, dan sassauta murya ya yi ya ce, "Ohk, shikenan, bawa Innar wayar ina take? sai kuma ya zaro ido tuna wani abu, ina Daada? Ya fada da wani rikicewar" Hamma jay wai Daada ce tace ka zo yanzun nan mutuwa zata yi..."
Bai jira yaji karshen maganar ba ya yanke kiran gami da fitowa elevator ya hau zuwa kasa,bai jira kiran driver ba ya shiga motar a dari da sittin ya bar ma'aikatar ba tare da yabi ta kan meeting da 'ake shiryawa ba.
Lokacin da ya iso gidan duk muna zaune jugum jugum a dakin har kusa da Daada ya zo ya durkusa gaban gadon da take kwance yana mata sannu da fadin su wuce asibiti kawai ko a kira dr gida?"
Lalubo hannunshi ta yi ta rike gam ta ce,
"Kaiya Jabeeru, babu asibitin da zani, ina ganin lokacine ya yi, abin da yasa nace a tara min ku shi ne ina son rokar ku alfarma dukkanin ku ku taimaka ku min ko da ko shine abu na karshe da zaku min a rayuwa.
Alhassan Dijah ina so ku tayani rokar Jabeeru da ya maida auren Takwara a yau ba sai gobe ba, na tabbata idan kun min haka zanyi farin ciki har cikin kabarina.
Gabadayanmu a wajen babu wanda kirjinsa bai harba ba, "Alhassan kunyi shiru dukkanku" ta kuma fada cikin magagi.
Gyara zama baffa ya yi ya ce, "Daada ni a karan kaina ba zan iya cewa Jabiru ya kuma auren Uwata ba, dan a ganina yanzu Jabeer ya yi mata nisa irin nisan da sama ya yiwa kasa.
Ya wuce da matsayinta da kilomitoci masu yawan gaske, ma yi mata fatan samun wani daidai da ajinta amma tunda kince haka bazan taba yi miki musu ba, gashi nan a gabanki sai abun da ya ce.
Rumtse idanu na yi da karfi jin abin da Bafffana ya fada wasu hawaye suka cigaba da tsere saman kumatuna.
Inna ce ta karbi maganar da fadin, "Nima bana goyon bayan Jabeer ya kuma daukar Maryama, ya samu farin ciki da warakar jinyar da ta tafi ta barmishi yanzu yana tare da mace ta gari wacce zata iya zama dashi a kowanne mataki na rayuwa da ya samu kansa.
Amma Daada tunda kince haka gashi nan gabanki ni babu abin da zan ce a kai.
Sarawa kan Jabeer ya yi, ya tabbata alkunya iyayen nashi suka mishi, babu kuma abun da zai aikata a wannan duniyar ya saka musu irin dawainiyar da suka yi dashi ba tare da ya taba yin kukan maraici ba.
Dago kai ya yi yana kallon cikin idon Maryama da ta kafeshi da su tana jiran jin abun da zai furta, kirjinta na bugu kamar zai faso ya fado kasa yace, "Kamar yadda kika rokeni in mayar da ita, na amince da bukatar ki Daada"...........