CHAPTER 20
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA ASHIRIN
Taruwa ɗaliban suka yi akanta, ana ta ce-ce-ku-ce, amma an rasa mai ƙoƙarin ɗagata. Wani ne cikin ɗaliban ke faɗin, “Yanzu wannan cirota ma ai sai mutane sun shirya, don ba dai mutum ɗaya ba. In ba haka ba, garin janyota sai kai ma ka faɗa ai.” Suka kyalkyale da dariya.
Sufyan jan Habib ya yi, suka bar wajen. Farida na jinsu, ta ma rasa ta ina za ta fara. Wata irin kunya ta lullubeta, ga azabar da take ji, gashi kuma ta gagara ko motsawa, duk a lokaci guda.
Wasu mata ne a wajen suka haɗu su uku, suka fara ƙoƙarin janyota. Garin janta, ƙarfe cikin kwatar ya ja nikaf ɗin da ke fuskarta ya yage ya fice.
Suna fitowa da ita, jin bakinta ta yi ya yi wani sumtum, kamar an daura wani abu a kai. Hannu tasa da sauri ta rufe bakin, sannan ta ƙara sa ɗayan hannu ta tare fuska. Duk ta kurje, ga jikinta gaba ɗaya ta jiƙe da ruwan kwatar.
Masu gulma na yi, masu dariya na yi. “Bala’i, dama haka matar nan take da muni caɓ.” “Wannan ai dole tasa nikaf, nikam dai ban taɓa ganin mace mai muni irin haka.” Surutan da ɗaliban suke ta yi kenan suna ƙara lekata.
Ganin Hod ne yasa suka dare a wajen. Sannu ya ce mata, suna tafiya da sauran matan har suka kai ta Staff Room. Ta shiga bayan gida ta wanke jikinta, kasa fitowa ta yi don a jike take shakaf. Ta zauna cikin bayan gidan ta dafe kanta, ba abin da idanunta ke haska mata irin yadda ta faɗi cikin tsakiyar ɗalibai, yadda take jiyo shewarsu ana dariya.
Daga kanta ta yi a madubin bayan gidan, ta kalli fuskarta, bakin sai ƙara kumbura yake, ga ta gefen hannunta duk ta kurje. Hod ne yasa aka nemo mata hijabi babba, ya ba wa wata staff mace ta je ta knocking ƙofa ta ba wa Farida.
Karɓa ta yi ta saka. Ko da Hod ya nemi su je School Clinic, kin yarda ta yi, ta ce kawai gida za ta tafi. Ta ja hijabin ta rufe fuska, ta shiga motarta. Zuciyarta na bugawa tana tuki har ta isa gida.
Sufyan na komawa gidan da daddare bai tarar da Farida falo ba, takanas ya je ya tura ƙofar ɗakinta ya dariya, “Ah Madam, ashe kuma abin da ya faru kenan? Sannu ko, an sha kunya, Allah ya kiyaye gaba, manyan mata an ji jiki fa.” Ko daga kai ba ta yi ta kallesa ba har ya tafi.
Ranar kwanan baƙin ciki Farida ta yi, tana tashi da asuba taga an yi mata message a wayarta. Ta duba ta ga wannan lambar ce dai ta ƙasar waje da babu damar kira, kuma kuma babu damar maida amsa. Fara karantawa ta yi, “Barka dai Yar baka, ban san me yasa nake son tunatar da ke wasu abubuwa ba, amma fa haƙuri za ki yi da ni, don ba zan taɓa faɗa miki maganar da za ki ji daɗi ba sai dai in tunzura ki, tunda ta hakan mutane ke galaba a kanki. Domin na lura har yanzu ba ki fara son kanki ba kuma ba ki yarda da kanki ba. Shin wai mutane suka halicce ki? Ke ya kamata ki ba wa wawayyu ajiyar shara, amma kuma sai ya zama ke ce wawiyar. Ni fa har yanzu ban ji cewa kin fara ɗaukar kanki kamar kowa ba. In kin so ki gyara mummunar da ke, jira mutane su yaba ta.”
Farida na gama karantawa ta numfasa tana, “Ni wannan na kasa gane inda ya dosa, so yake in rayu kamar kowa, ko kuwa so yake ya dunga ɓata min rai shima?” Ta yi tsaki ta nufi toilet ta ɗaura alwala.
Bayan ta idar da Sallah, kallon fuskarta ta tsaya yi a madubi, kawai sai ta tsinci kanta da sakin murmushin da ba ta san dalili ba.
Washegarin ranar, kafin Sufyan ya fito, har ta shirya ta bar gidan. Yana zuwa ya shiga class ɗinsu ya tarar da ita zaune da papers a hannu. Ya nemi seat ɗinsa ya zauna, tana jawabi, “Wa innan takardun test ɗinku ne, na ware na waɗanda suka san me suke yi a gefe, na ba wa class rep. Sauran kuma, da ba a iya tsinana komai sai dumama benci da rako abokai da ƙawayen, ga naku nan, zan kiraku ɗaya bayan ɗaya ku zo ku amshi abunku.”
Sufyan na jin hakan, gabansa ya faɗi, don ya san bai tsinana komai ba. Kiran sunaye take, tana faɗin mark ɗin daga suka ci, daga masu 1, 2, sai 3, har ta gama ba ta kirasa ba. Yana hamdala, sai kuma ta ɗauki jakarta ta ciro wata takarda.
Tana, “Ga wanda ya fi kowa shirme, wanda ya fi kowa rasa abin yi, kuma wanda ya fi kowa dumama benci…”
Ta ɗan yi shiru, tana kallon class ɗin, kafin ta faɗi da murya mai ɗauke da tsokana,
“Mr. Useless himself… wanda mata ke rububi, ba su san kwakwalwar fanko ba ce, ana abun arziki shi ko 1 din bai samu ba, Sufyan!”
Class ɗin ya kaure da dariya.
Sufyan ya daskare a zaune, ya zuba mata ido.
“Me?”
Ta ɗaga gira.
“Na ce ka zo ka karɓi takardarka, Mr. Handsome-with-no-brain. Ko sai na kawo maka?”
Wata dariya ta sake kaurewa a class ɗin.
Ji ya yi duk ƙafafuwansa sun sake, kunya ta lulluɓe shi. Ya ja ƙafarsa ya je ya fisge a hannunta yana karɓa, ya fice daga class ɗin.
Yana fita suka fara presentation.
Motarsa ya ɗauka ya bar School ɗin ma gaba ɗaya, don a tsarge yake.
Daga ranar Farida ta sheda masu ta gama yi masu lecturers ɗin semester, sai dai su haɗu a exams kuma.
Ganin duk ta gama da su, hakan yasa ko ta shiga School ɗin ma sai dai ta je Staff Room su tsara exams ta dawo gida. Shi kuma Sufyan ma ya yi tafiya, a ranar da ta digashi a gaban yan ajinsu a ranar a ka kira sa suka tafi Ball Ghana, hakan yasa hankalinta kwance, ba wata rigima ba, haɗuwa suke ba.
Sai da ya kwashe sati biyu cur. Ita Farida ba ta ma san zai dawo ba sai ganinsa ta yi ƙarfe takwas na dare, kamar daga sama. Suka yi kallon-kallo, ya wuce ɗakinsa.
Yana shiga wanka, sai ga su Baba Haruna, Baba Shuaibu, Kawu Hamza, Inno, Goggo Hansai da duk sauran ’yan dangin, an zo tarbarsa da taya murnar sun yi nasara a ball ɗin da ya je bugawa.
Da mamaki Farida ta bisu da kallo tana sauka daga kujerar da take, tana yi musu sannu da zuwa.
Inno ta tsaya tana kallon Farida, ta riƙe haɓa tana taɓe baki, “Faridatu, fisabilillahi, amanata za ki ci? Ban zo na koya miki kwaliyar tarbar miji ba takanas? Amma jeɓeki, kin zauna buguzum-buguzum kamar kayan wanki.”
Shiru suka yi duka, ana jin jawaban Inno. Goggo Hansai ta amsa da faɗin, “Aiko dai wannan ba daraja ba ne, ace miji ya dawo daga wata ƙasa ya tarar da mata haka.”
Inno ta girgiza kai, “Yoo, ao ni dai kin cuceni Faridatu, kin cuci mijinki da kanki. Maza ki tashi kije ki sa kayan mutunci.”
Farida na tashi, idon Inno a kan cikinta. Za ta tafi ɗaki, Inno ta dakatar da ita, sai kuma ta gyada kai, “Je ki dawo.”
Kafin Farida ta sa kaya har Sufyan ya fito daga wanka. Sun gaisa, ana ta hira.
Farida na fitowa, Inno ta yi rau da fuska ta ce, “Ni dai ina da damuwa.”
Dukansu hankalinsu ya yi kanta. Baba Haruna ya ce, “Wacce damuwa kuma Inno?”
Ka yi rau da fuska ta yi tana matse idanunta, ta kalli Farida cikin yanayin damuwa ta ce, “Har yanzu aljanun Sufuyanu sun ƙi sake ɗan cikin Faridatu da suka kwantar, ya ƙi tashi, kuma kullum cikin magani muke, amma ba ci gaba.”
Abba Shuaibu ya ce, “Inno, amma wai likita ne yace akwai cikin nan ko kuwa?”
Caraf Goggo Hansai ta ce, “Ban da abinka Shuaibu, ai ciki ba sai likita ya sanar ba. Inno ce ta fahimci hakan.”
Inno ta ce, “Ni dai yanzu alfarma guda nake nema wajenku. Tunda mun yi na Hausa nan ya gagara, to aje asibiti a lalubo a tado jaririyar cikin nan.”
Aunty ta ce, “Inno, ba sai an kai ga asibiti ba. Akwai buƙatar a tabbatar da cikin tun farko. Yanzu zan ba da a siyo tsinken da ake gwada ciki mu gani, don kar ayi gaggawa ko?”
Inno ta ce, “Me kike nufi? Kenan na yi ƙarya, babu cikin?”
Baba Haruna ya ce, “Aa dai Inno, akwai buƙatar a tabbatar. A likitance, kafin a kai ga zuwa can ɗin ko? Kin ga ai ita ma malamar asibiti ce.”
Inno ba don ta so ba ta haƙura a gwada, don ita damuwarta kawai aje asibiti su ɗago da cikin.
Guda biyu Aunty ta sa aka siyo. Farida ta yi fitsari a ƙasa, na farko ya nuna babu. Gudun rikicin Inno yasa Aunty ba ta faɗa ba sai da aka ƙara gwadawa, shi ma ya nuna babu. Aunty ta tambayi Farida ko akwai cikin da gaske. Farida ta ce, “Wallahi babu Aunty, kuma ita ma Inno na faɗa mata, ta ƙi yarda ne.”
Ɗaukan tsinken Aunty ta yi, suka koma falon. Ta ce, “To, batu na gaskiya dai babu wannan cikin, domin gashi nan mun gwada har biyu, babu yake nunawa, kuma ita ma na duba ta ko’ina, babu alamun ciki.”
Inno ta fara mitsitsika idanu, “Babu me? Ban son rayuwar husuma. Ta yaya za a ce babu cikin kwatakwata?”
Aunty ta ce, “Allah kuwa Inno Babu komai.” Ta fada tana kara daga tsinken da ke hannunta.
Inno ta ja numfashi tana kokarin lumewa cikin kujera.
Da sauri Goggo Hansai ta tare ta tana , “Aa Inno rufa mana asiri.” Duk a ka yo kanta.
Tana kishingide jikin Goggo Hansai ta ja majina tana, “Hansai zan iya haɗiye zuciya. Kenan tun tuni duk kai-kawon da nake yi babu wani abu? Aa, kai laifinka ma nake gani, Sufuyanu.” Ta ƙarasa maganar tana nuna shi da yatsa, kafin ta ci gaba,
“A ce mata kusan wata huɗu ba ciki? Aa, ba a taɓa haka ba a tarihin danginmu. Kowacce mace na cika wata tara a gidanta ne da jaririnta a hannu”
Baba Haruna ya ce, “Inno wannan ai ba abun damuwa bane, ki kwantar da hankalinki don Allah, kar jininki ya hau.”
Taɓe baki ta yi tana tashi daga jikin Goggo Hansai tana goge majina da gefen zani ta ce, “aiko dai dole in damu haruna, dole in damu fa.” Ta kalli Safiyan tana dafasa ta ce, “Faɗa mini gaskiya Sufuyanu wai ka gagara yi mata cikin ne, ko kuwa ba ka da lafiyar yi? Faɗa mini, in nema maka magani. Don dai da daga Faridatu ne, magungunan da na dunga dirka mata, da ko babu cikin sai an samu. Wannan matsala daga gareka ne.”
Dariya ce ta kusa subuce wa Farida, ta yi saurin kunshe ta.
Aunty ta ce, “Ai ba lallai bai da lafiya bane Inno ta yiwu Allah ne kawai bai kawo ba tukunna.”
“To fada mun Allah Zara’u tunda dai ni ban san sa ba, ni fa ba a wannan gangancin da dani, neman magani dole ba fashi.”
Abba Shuaibu ya ce, “Inno, ai yanzu ba kamar da ba ne, wasu sai su kwashe shekaru ma kafin su haihu.”
Inno ta wage masa idanu, “To, Shuaibu, faɗa mini abin da ban sani ba, nuna mini gadara akan ɗanka ka ji.” Ta ƙarasa ta ja zani za ta goge hawayen da babu shi.
Baba Haruna ya ce, “Ka dakata Shuaibu, ka ba ta haƙuri.”
Abba Shuaibu ya ce, “Ki yi haƙuri, ki yafe ni Inno.”
Goggo Hansai ta ce, “Na ga dai gata Inno ke yi wa yaranku.”
Inno ta numfasa tana ƙara goge fuska da zani ta ce, “Gobe za mu je ƙauye a fara bincika masa magani, don ni dai ba zan mutu ban ga yaran Faridatu da Sufuyanu ba. Waya sani ma tun yarinta cinnaka ta yi masa illa, kuna wasarere da rayuwar yaranku. Ni dai Allah na gani, na yi iya yin na husuma, kauce mata nake a kullum.” Ta ƙarasa tana fashe da kuka.
Goggo Hansai ce ta fara ba ta haƙuri tana ba ta baki, duk sauran suma suka haɗu aka rarrasheta, kafin dukansu suka watse, kowa ya nufi gidansa.
Da dariya Farida ta tashi tana kallon Sufyan tana, “Alhamdulillah, na rabu da alƙaƙai sai kuma a dage da neman magani ko?” Ta faɗa tana wucewa ɗakinta, shi ko Sufyan don takaici ma ya rasa ina zai sa kansa.
Washegari da sassafe Inno ta zo ta ɗauki Sufyan, suka tafi ƙauye neman magani.
Farida na falo zaune tare da Azima. Ta zo mata, suna hira. Sufyan ya shigo sun dawo, fuskarsa sam ba annuri, ya wuce ɗakinsa.
Azima ta ce, “Ke, yanzu ba za ku daure a cika wa Inno buri ba, a haifo mata ƙawayen?”
Farida ta yi guntun tsaki, “Azima, ni fa ko zan mutu, sai dai in mutu haka, amma yaron nan bai isa in haɗa jiki da shi ba. Ke kin manta ne, ba na faɗa miki ba? Yanzu ko barbadaɗancin ma fa ba a iya yi, tunda kunama ta yi aika-aika. Kin ga kuwa, ai ya gama aiki. Kila yanzu in Inno ta taimaka aka yi maganin ya koma daidai, sai ya je can su ƙarata. Amma ni ke, ko a mafarki hakan ya faru, zan iya mutuwa ba tare da na farka ba.”
Azima ta ce, “Ni ban san lokacin da za ku juyar da wannan ƙiyayyar taku ba, Farida. Na gaji da faɗa miki gaskiya wallahi.”
Sufyan na jinsu daga ɗaki ya yi kwafa.
Sai da suka sha hirarsu kafin Azima ta tafi, suka yi sallama.
Farida na kwance, har ta fara barci wajen ƙarfe sha biyun dare, ta ji ana taɓata. Buɗe idanun da za ta yi, taga Sufyan ne, daga shi sai gajeren wando. Tashi ta yi a zabure ta bigesa, ya ƙara matsawa kusa da ita yana faɗin, “Ina kin ɗau alwashin duk ranar da kika haɗa jiki da ni za ki mutu? Yaro ko?” Ya yi wata irin dariya.
“To, ki shirya wa mutuwa a yau, don wallahi babu makawa sai na cire renin da ke tsakanina da ke.”