Chapter 4
by @maidambu41
Murmushin gefen baki ya yi yana kallon kan shi a madubin da yake parlourn, yana gyara gashin kansa. Kallon gefen fuskarsa ya yi, ba wannan bane yasa aka kira shi, ya sani sarai akwai wani abu a ƙasa.
"La Mayor!"
Bai juya ba ya ci gaba da kallon Fu'ad da ya damke hannunsa wuri guda, yadda yake jin zuciyarsa kowa ma saka bindiga zai yi ya alburushe su, yasan zai samu natsuwa amma ina yana basu lokaci. "Ahhhhhhh!" Ya furta yana kallon kan shi a madubi da kyau.
"Maganar kasuwancina akwai matsala, kayan da ya dace su shigo ta kwatano wai hukumar Nigeria ta rike?"
"Sai me?" Ya furta gar babu tsoro a idanunsa, ya riga da ya fahimci a yanzu da ya kawo ƙarfi Hajiya da Abba Babba da Abba tsakiya sune basu amfani da shi, amma kowa so yake ya yi amfani da shi kawai yadda ransa yake so.
"Amma Yaya maganar aurensa da Mufidah ya kawo ni!" Juyawa ya yi da kyau, ya isa gaban yarinyar ya ce mata.
"Lashe kafana" ya tura mata kafar, wani irin kallo yarinyar take mishi mai cike da tsoro da dan shakka. "Lashe nace!" Ya daka mata tsawan da yasa ta ja baya. Durkusawa ya yi a gabanta ya a shafa kanshi yana kallon yadda take zare ido. Murmushin gefen baki yayi tare da sosa giransa na dama.
"Ni na yi miki kama da kayan gwanjo ne? Ni mace nake nema ba namiji ba!" Ya juya yana kallon Mahaifinsa da Fu'ad, tsaki ta yi ya ce mishi. "Ka basu tsaba!" Gyara zama Uban ya yi ya ce masa "Tsabar hannuna bai da yawa idan kayan suka shigo dole sai na yi cike-cike da zan bawa police de Frontieres. Sannan idan ya shigo iya ka cikin ƙasar dole zan ware wa Administration Des dounane." (Wato hukumar immgration sune police de frontieres, dai administration Des dounane kwastom kenan) Salin alin yasa kai zai fita suka haɗu da Hajiya Zubaida matar Mahaifinsa Uwa ga Fu'ad, wani ɗauke kai ya yi kamar bai taɓa ganinta ba a rayuwarsa kuma sau ɗari idan zai zo gidan wannan shi ne abin da yake mata ba zai fasa ba koda ƙasa zata rufe mishi idanu ne.
Shine mutum na farko da baya iya ɓoye kiyayyar shi, haka idan ya ga abu yana so koda zai rasa ransa ne sai ya cimma abin.
A duniyarsa abu ɗaya ya tsana ƙarya da munafunci, duk abin da zaka yi yana son kawai ka fito kai tsaye ka gaya mishi. Matar nan ta bashi wahala a iyakar tsawon rayuwarsa. Ta azabtar da shi sama da yadda ko labari yake badawa ba za a yarda ba.
Domin shi looking innocent da bata ɗauki duniya da zafi ba. Amma a dark side ɗinta wata irin muguwar mata ce da bata san komai ba sai kanta. Ta dasa mishi tsanar kowacce mace a duniyarsa. Bayan Hajiya mace ta farko da yake so yake kauna, sai Maamah duk da bai cika shiga damuwar matar ba, amma ta mishi abubuwan da har abada ba zai manta ba, ita dai kuskurenta shi ne haihuwar yarinyar can me idanun mage. Ya tsani Yarinyar, shi babban abin da yake bashi haushi kalarta kalar matar Babansa. Irin su idan suka samu wuri ba ƙaramin ta'asa zasu yi ba. Shi yasa yake huce takaicinsa a kanta. Ga 'yan uwanta kowacce tana faran-faran amma ita da yake munafuka ce komai nuƙu-nuƙu kamar wacce take aikata wani mugun abu.
Yadda ya shiga motar shi ƙiran BMW ya fisgeta da mugun gudu. Yana kallon hanya yana tuna ƙuruciyarsa. Sai ya ji komai ya dawo masa sabo. Akwai abin da idan aka tuna yana saka farin ciki. Akwai abin da ana tuna shi baƙin ciki da tsana ce take cika ran mutum. Ya tuna yadda yake takawa da ƙafa tun daga Amarewat zuwa sabon gida, daga gidan Babansa zuwa gidan Hajiya da ƙafa, domin cin abinci ko daga Sabon gari zuwa Azin. Gidan kakanninsa, wani irin bugawa zuciyarsa ta yi ya gangara gefen titin. Ya kifa kai a sitiyerin. Tsanar mata da yake ji ya ƙara cika ransa.
Ɗago kai ya yi yana kallon hanya. Cizon bakinsa ya yi har sai da ya fashe. Sannan ya ci gaba da tafiya a hankali. Kai tsaye La Coffee shop ɗinsa ya nufa wanda yake Dag Manet, babban shago ne wanda yake da gidan sama da kuma underground building. Duk bala'inka baka isa kace akwai wani abu a wurin ba. Asalima Cartel ɗin shagon shayi ne a saman da ƙasa duk yadda zaka zo wurin ba zaka taɓa gane ana wani aikin assha ba.
Amma ganin gaskiya wurin asalinsa na wani baturen Faransa ne, wanda hukumar ƙasar Nijar ta kore shi. Yana shiga wasu samari biyu suka rufa masa baya, gasu nan ƙosassu kamar masu cin ƙarfe. Buɗe mishi kofa ɗayansu ya yi yana cewa. "Mun samu goran gayyata bikin cin mushe!"
Cak ya tsaya yana kallon kansa ta madubi. "A ina za ayi watandan?"
"Amarewat!"
"Shit!" Ya furta tare da kallon wanda ya gaya masa "Me yasa baku fitar da sanarwar ba."
Nn"Saboda mutumin tsakiya ya motsa an kawo sabon limami!"
"Su kuma Mammun fa?"
"Babu wanda ruwansa ya isa na alwala balle tsarki da ake bukata!"
Shafa kanshi ya yi ya ce musu. "Ina da sabuwar akuyar da na saya. Zan dawo bayan garin ya sarara."
Ya juya ya fita a hanzarce.
----
A can gidan kuwa baki ɗaya hankalin Maamah Hajiya Rukayya bai kawo cewa Naanah Asma'u bata dawo ba. Hankalinta ya fi karkata tana wurin Hajiya. Ita ma Hajiya bata bi ta kanta ba domin tasan ba mamaki daga bangaren Uban kowa ta wuce ɓangarensu. Wurin sha biyu na rana ya dawo, bai leƙa Jajiya ba ya nufi ɓangaren shi. A inda ya tafi ya barta a nan ya same ta tana bacci. Raɓewa ya yi gefenta ya shiga ciro kayansa da yake adanawa.
Ya zuba su akan gadonshi irin royal bed asalin na ƙasar Turkiyya. Wanda ya ji sunan shi royalbed wucewa ya yi ya buɗe wata drower ya kwaso kuɗi masu yawan gaske. Akwai pond na ƙasar England, akwai euro, akwai Yen na kasar China, akwai Naira na Najeriya, akwai dollars na ƙasar Amurka, sai CFA ga bindigu har uku ƙanana da su, sai passport har guda goma na ƙasashen Afirka huɗu kasashen waje shida. Ya zuba sannan ya wuce banɗaki wanka ya yi duk da ciwon da yake cikinsa baya son ruwa amma da yake ya fada hannun mara mutunci ne bakiɗaya dai ya shiga halin ni 'yasu. Shi dama can ciwo don kaniyarta mutuwa yake domin kansa baya ba shi ƙofar da zai ci gaba da rayuwa a jikinsa. Shi ma kansa ciwon ne a rayuwar wasu.
Sanyin tiles ne ya shiga jikinta sosai ta bude idanunta, tana ƙoƙarin neman mayafi ta lullube jikinta. Ai kuwa ta bude ido sosai, ta ga inda take kwance buɗe ƙofar banɗakin yayi tare da isa jikin window ya buɗe labulen da hasken rana ya haska window. Tashi ta yi tana kare fuskarta a hankali ta fara dube-dube can idanunta ya sauka akan yatsun ƙafarshi. Da ruwa yake bi da gudu yana daure da towel. Zuciyarta ne ya yi mugun bugawa saboda bata san yana ɗakin ba, ta zube a wurin tare da rufe fuskarta da idanunta. Kamar wacce ta ga dodo haka ta juyar da kanta. Ai bata kuma zarewa da lamarinsa ba sai da ta ga bindiga da maƙudan kuɗaden duniya. Shakuwa ta fara tare da jin kamar asthma ɗinta zai kawo mata attack. Tana shaƙuwa da wannan numfarfashin. Tana ja da baya daga zaune, shi ma takowa yake har gabanta ya durƙusa yana kallonta.
"Kalle ni!" Ya ce mata, kare fuskarta ta yi da hannu tana shirin fashewa da kuka.
"Me kika gani?"
Kanta har lokacin bata iya ɗagowa ba. "Tambayarki nake me kika gani?"
Wani irin kuka ne ya zo mata ta toshe bakinta. "Ke na yi miki wani abu ne?"
Ya tambaye ta ƙasa-ƙasa, girgiza kai tayi.
"To me yasa lokaci guda kike min kuka?"
"Ka yi hakuri!"
"Keee!" Ya ɗauko bindigar ya riƙe a hannunsa, nan take ta fara wani irin jan numfashi saboda tsananin tsoro.
Ɗana mata ya yi a goshinta. "Na miki kama da ɗan fashi ne?"
Girgiza kai ta yi tana jan numfashi ta hanci da baki, cilla mata inhelar ya yi ta yi maza zata kai bakinta ya buge hannunta da bindigar. Ɗago kai ta yi da sauri ya nuna mata inda abin yake ta kai hannu zata ɗauka ya rigata.
Zuwa yanzu kan numfashin ƙoƙari yake ya bar gangan jikinta. Ya buɗe tare da danna mata a bakinta, tana shaƙa ta wani ja numfashi, wanda sanadin haka idanunsa suka sauka kan fuskarta zuwa kirjinta dauke kai yayi kamar baya ƙaunar ƙara ganinta a rayuwarsa ya ce mata.
"Kwashe kuɗin da bindigar ki nema musu matsuguni mai kyau idan kika sake aka kama ki da su, hukuncin kisa za su yanke miki!" Ya miƙe a gabanta, jikinta yana rawa haka ta yi ta kwasar kuɗin har zuwa lokacin da jikinta ya yi azabar sanyi ga gajiyar tashin da ciwonta ya yi. Haka ta ɗauka ta fita da shi. Gyara kwanciyarsa ya yi tare da ɗaukar earpom a kunnensa. Yana murmushi.
Sallah kaɗai yake ɗaga shi daga gadon kuma a irin wannan yanayin baya son ya fita baƙinsa su shigo gidan.
Naanah Asma'u
Lokacin da ta shiga cikin gidansu, ba kowa a parlourn tasan Maamah ba zata fito ba sai wurin biyu na rana. Haka yasa ta shigowa parlourn. A hankali take takawa Habibi yana ganinta ya fara kukan yana jin yunwa. Tana shiga ɗakinsu ai kuwa ya sha gabanta, tuntuɓe ta ci kayan suka zube bakiɗaya tayi saurin tattarawa. Tana jin muryan Mairoh tana tambayar.
"Waye?"
"Ni ce!"
"Didih me ya samu muryanki? Asthma ta tashi ko?"
Da sauri ta tura kayan kasar gadon, tana me kallon Mairoh tana yake. "Eh wallahi!"
Mairoh bata kawo komai a ranta ba, ta wuce tana neman kayan da zata suturta jikinta.
"Didih Ya Almu ya kira, haka Ya Moud ma ya kira ki!"
Janyo wayar da yake jikin powerbank ta yi ta shiga dailing number Ya Almu. Mairoh tayi murmushi. ita dai Allah ya daura mata son romantic kamar ta cinye kanta ɗanye.
"Didih baki raba mana tsaraba ba!" Nuna mata jakar ta yi, ta mata alama ta ɗauka ta kaiwa Maamah. Fita ta yi tana fadin.
"Ubangiji ya barki da Ya Almu!" "Amin!" Ta furta daidai lokacin da aka kashe kiran, ta kalla kamar yana gabanta.
"Haba cherry!" Ta furta a hankali, tana kallon wayar idanunta ya fara kawo kwalla, tuni ta manta da wani zancen Uban kowa da kayansa. Kiran da ya shigo ne yasa ta sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya. A hankali ta ɗauka tare da cewa. "Ka yi haƙuri!" "Me ya same ki? Asthmarki ya tashi ne? Me kika shaka?"
"Hmmm!" Yasan tun da tace haka ba zata taɓa yarda ta gaya mishi ba sanadin tashin ciwon ba shi ma shiru ya yi sun kai kusan minti biyu kafin ya katse shirun da cewa.
"Yanzu ya wuyarki? Da fatan inhelarki tana tare da ke?"
Sai lokacin ta tuna da inhelar da Ya Adam ya cilla mata, sauƙowa ta yi daga gadon ta janyo ƙunshin kayan ta ciro shi ta ce mishi "Uhm!"
"Ki tafi asibiti su miki allura!"
"Da sauki cherry!"
"What?" Ya tambayeta kin amsa mishi ta yi tana murmushi, "Naanah Asma'u! Beauty ni kika kira da Cherry?"
Kashe wayar ta yi bata kuma daukar kiran da ya mata ba, sai da ya gaji don kansa ya dakatar da kiran.
Can kuwa kiran Ya Moud ya shigo mata, "Asma zan zo an jima!"
"Hmmm zan tafi nasarawa gidan Ya Binto!"
murmushi ya yi mata ya ce mata "To na zo na kai ki?"
Shiru ta yi sai kuma ta ce mishi. "Oo!" "Ki yi haƙuri nasan laifina ban zo ba ko?"
"To ka zo da wuri ya wuce ka kai ni gidan Hajja ma kawai!" Sautin murmushinsa ta ji yana cewa "Naanah Asma'u ki shirya da wuri!"
"Ina jiranka!" Ta fada tana gyara murya.
"Asthmarki ta tashi ko?" Dariya ta yi masa "Ya Moud ƙura na shaƙa fa!"
B "Innalillahi wainnalihir rajoun, jira ni gani nan zuwa!"
"Da sauƙi fa!" Ta faɗ a shagwabe, lokaci guda ya ɗauke wuta ya ƙara rikice mata. "Don Allah nazo na kai ki asibitin?"
Wani murmushi ne ya ƙwace mata, ta ce mishi.
"Ya Moud kai kam ko! Da sauƙi sai kazo an jima!" Ta faɗa tana kashe wayar, rufe ɗakinsu ta yi ta nemawa kuɗin nan mazauni da kyau da bindigar, sannan ta fito parlourn ganin Maamah tana kallon kayan da tazo da shi yasa ta cewa."
"Amma baki san zafin kuɗin da kike kashewa ba ne ko?"
"Maamah ba kuɗina bane, Ya Amaan ya kai ni kwanakin da zamu gama jarabawa na kwaso muku!"
"Naanah Asma'u meye kike so ne? Mustapha, Mahmoud, ga Amaan kuma?"
Kamar ta yi kuka ta ce mata "Maamah babu komai a tsakanina da Ya Amaan fa, kuɗi Ya Almu ya bashi muka yi sayayyar fa!"
"To ya batun Yarona?" Maamah ta kafe ta da idanu.
"Maamah zamanin yanzu da zamaninku akwai bambanci, kuma ai ke da Abba Babba kuna son junanku ita Didih a barta da wanda zuciyarta yake bugawa mana!" Wucewa kitchen ta yi ta bar Mairoh da amsar da Maamah zata bata.
Dariya Maamah ta yi ta ce mata. "Ni Abbanku ban ce ina son shi ba, Manyana suka yanke abin da ya dace musamman da ya kasance mutum mai amana da nagarta. Wanda nake hango yarona yana da duk abin da nake hangowa a wurin Abbanku. " "Maamah Ya Moud!"
" Maryama ba zan sauya maganar da na saka a gabana ba!"
Shiru parlourn ya ɗauka ita kam Naanah tasan hakan ce zata faru.
Kafin ƙarfe huɗu na yamma ta gama, dai-dai shigowar Abba Babba, sai da ta gaisshe shi, sannan ta ce masa" Abba Babba, ina son zuwa na gaida Hajjama."
Shiru ya yi yana kallonta, " Uwata ciwonki ya tashi ko?"
Sai lokacin Maamah ta saka musu baki. "Ni ma na ji muryanta a dishe tun ɗazun!"
Idanunta ne suka yi ƙwalƙwal. "Yaushe za ki dawo?"
"Abba zan kwana biyu a can!" Murmushi ya yi ya ce mata. "Allah ya kai ki lafiya, k gaishe ta!" Ya saka hannu a cikin aljuhun rigarsa ya ciro cfa dubu biyu ya bata yana cewa "Idan bai isa ba ki gaya min!"
Gyada kai tayi tana fadin. "Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, na gode sosai Abbana!" Ta yi ta godiya, shiga ɗakin su ta yi ya shirya cikin doguwar farar atamfa kusan tun da ta fahimci kalar fatarta sai ta sakawa kanta saka duk wani kaya me haske da zai ƙara haska fatarta.
Tun daga can tsakar ɗaki take jin muryar Hajiya Innah, gabanta ne ya faɗi. Ta fito riƙe da farin hijab ɗinta tana jin wani ƙarfin hali da son zuciya irin na Hajiya Innah. "Ban yarda ba, kuma ban amince ta kwana gidan waɗancan hausawan ba."
Kallon Hajiya Innah take kamar zata yi kuka. "Ni kuma waye zai kula da ɓangarena? Wato jikar tawa Meramu zata nuna min iko da ita idan ta je awa ta dawo kai Magariba ta yi mata a gidan nan!"
Cikin wani irin karyayyen murya ta ce mata. "Na haƙura ma!" Ta juya zuwa ɗakinsu ta zube a gadon tana kuka.
"Hajiya idan kika mutu sai a binneki da Didih tun da na lura da bata nan ma ai binta kika yi zuwa Niamey!" Inji Mairoh tana wani ɗauke kai.
"Ke kada ki mini rashin kunya na saka ubanki ya zane mini ke!"
"Lallai ma hajiyar nan samun wurinki ya yi yawa sai ki yi kuma!"
©️Mai Dambu