BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 5

by @maidambu41

Chapter 5


Ta shige tana mita ita ma Hajiyar mita take, tana cewa "Ai yau da ka shigo da safe baka ba ni ko sisi ba, amma ka iya bawa mummunar 'yarka da ta zame mana tambari a cikin zuri'a! Ni ba zaka sauke hakkina ba ballantana na matar da ka ajiye." Ta faɗa tana kallonsa, hannu ya saka cikin ciro dubu uku ya miƙa mata. 

"Hmmm ita kuma Hasiyar fa?"


         Girgiza kai ya yi ya ciro dubu ɗaya ya bata, a wulaƙance ta kalli kuɗin ta cewa Hajiya. "Nan ya bawa 'yar shi da yawa ni kuma matarsa ya ba ni ɗaya." 


  "Keeeee!" Muryan Uban kowa da yake lungun yana zuƙar wiwinsa ya karaɗe tsakar gidan. Shiru ta yi tana kallon Hajiya ita ma Hajiya gyara murya ta yi ta ce "Ai Hasiya ba zaki haɗa kanki da yaransa ba, su jininsa ne, ke kuma daga sama ya kawo ki. 

   

  Kada ki ƙara tun da kika ji Uban kowa yayi magana to kin tsallake iyakar ki kada ki shiga wani iyakar."  Tana faɗar haka ta bi lungu ta same shi ya yi gaba. Tasan mita zai mata akan yadda take yin wani abu. Kafin ya fara magana ta shiga faɗa da nuna masa yadda ta yi shine dai-dai. 


      Shi dai bai ce mata komai ba, ya wuce Parlour ya kwanta a dogon kujera, yanzu ya gano shegen shirun da yarinyar take har da laifin Maamah. Tsaki ya ja yana me juya kansa ya lumshe yana ɗaukar wani shaiɗanin charge yadda babu wanda zai iya cewa idanunsa biyu. Tun yana iya fahimtar abin da Hajiya take faɗa har bacci me nauyi ya ɗauke shi. 


**

Rarrashinta Maamah da Abba Babba suke har ta shirya tana kuka,  zuwan Ya Moud ya shigo har cikin gidan, a parlourn ya same su, tana zaune kanta a tsakanin cinyoyinta. 

"Abba lafiya?" 

"Ita tace zata kwana shi ne Hajiya kasan girma!" 


  Yasan abin da Abba zai faɗa ya ce masa "Ta ce ba zata kwana ba ko?" Gyaɗa kai iyayen suka yi murmushi ya yi ya ce musu.

  "Tazo muje zan dawo da ita kafin isha'i in sha Allah!" 


  "Ai shi kenan ita ce dai bata so haka ba!" In ji Maamah. Zuwa ya yi gabanta ya ɗan durƙusa ya ce mata. "Yar makarantar Maamah taso muje, Naana 'yar Abbanta 'yar makaranta tashi muje." 


   Jan hanci ta yi zata yi magana ya ce mata "Eyee 'yar gudalle! Husnah yar Abbanta ta girma idan kina son na cicgaba da waƙar taso muje!" 


   Murmushi ne ya ƙwace mata. Suka ƙurawa juna ido "Taso muje!" Ya furta a hankali, miƙewa ta yi ya miƙa mata hijab ɗinta, ya ɗaukar mata jakarta suka fita.

  "In Sha Allah zan dawo da ita da wuri."

  "Allah ya tsare!" Abba babba ya faɗa, Maamah ita ma da addu'a ta raka su. Bayan fitarsu, Abba Babba yace wa Maamah.

  "Ki yi hakuri kin ji." Murmushin ƙarfin hali ta yi masa alamar ba komai.

Shiru ya yi kafin ya ce mata. "Ina ga kamar yadda kika nemawa Mahmoud auren Uwata ki gayawa Imran ya sami Yusuf ko Yakubu!" 


  "Ka bashi ko baka bashi ba shi ne abin da nake son ji?" Ta faɗa tana kafe shi da idanu.

" Na bashi har abada!!" 

Murmushin farin ciki ne ya ƙwace mata "Na gode sosai, idan so samu ne a yi bikin bayan sallah ta koma makaranta da aurenta. Tun da ta ce min saura shekaru uku!" 


Murmushi irin na manya Abba ya yi mata ya ce. "Zaki saka shi zirga-zirga daga Agadaz zuwa Niamey kenan!" 'Yar dariya ta yi tana jin wani irin nutsuwa na shigan mata ta ko ina. 


    Ko ba komai Nanah Asma'u ba zata raɓi  inuwar azabar da ta sha ba. 

A wajen kuwa Hasiya ce ta gama jin komai, tasan Naanah Asma'u zata huta a gidan Mahmoud amma ita bata ƙaunar haka, akwai ɗan uwanta da suke ciki ɗaya kuma Hajiya tasan shi cirani yake zuwa Libya idan ta haɗa kai da Hajiya Innah aka yi ta mata ruwan kuɗi zata amince. Da wannan ta koma ɗakinta ta buga masa waya. Sun jima suna waya dama ana ta binsa ya yi aure amma yaƙi. Sai da ta kira Mahaifiyarta ta gaya mata irin mutanen nan ne da basu yarda da kowa ba sai kansu sai abin da Malaminsu zai faɗa musu. Don haka suka tsara washe gari zata gida ta samu Uwarta da suke kira Innaji. 


---


Ya Moud bai tsaya a ko ina ba, sai nasarawa gidan kakanninsu, babban gida ne mai daɗaɗɗen tarihi zabarmawa. Gidan Malam Zaki, gida ne da suke da alaƙa da sharifai. Wanda ake alaƙanta su da zuri'ar shehu Ahmad Tijjani asalin 'yan ɗariƙar Tijjaniyya ne, wanda ana hasashen suna da kyakkyawar dangantaka da wasu daga cikin zuri'ar Shehu Ahmad Tijjani.


   Idan ka cire karatun da suke yi a gidan da Babban makarantar markazi na Sheikh Zaki, wanda take tun daga primary school zuwa University, babban family ne da Allah ya musu baiwar ilimin Addini da na zamani. Don ko shi Mahmoud yana koyarwa ne a babbar Jami'ar Agadaz. 


           A unguwar nasarawa inda babban makeken family house ɗinsu yake, babu abin da a cikin unguwarsu nan. Sai ka wuce gate ɗin farko da zai sadaka da cikin unguwannin kafin ka shiga asalin Mansion na Zaki Family.  

   A cikin gidan zaka fahimci yadda tarbiyya da ilimin addinin ya yi kane-kane a cikin halin su. Uwa Uba kuma magana da suke madadin harshen hausa ko Faransanci, a'a luggatu Arabia ke tashi a cikin family yadda kana ji kasan ana murza Larabci yadda ya dace. Tun da ta shiga cikin gidan Yaran gidan suka rufe ta. "Ga Didih, Ga Didih." 


  Wannan abin ya sakata jin kwalla a idanunta, yadda ake ji da ita matan Yayun Maamah da Yaransu suka fara fitowa, rungume ta suka yi. Kakarsu Hajjama tana jin ance ga shalele ta zo ita ma ta riƙo sanda ta nufi waje.

   Da dan sauri ta isa gare ta. "Hajjama!" 

"Marhaba Bint!" Da sauri ta isa wurinta ta faɗa jikinta tana kuka. 


"Ya isa haka har yaushe zaki daina kukan zaki zo? Bayan ke ce Uwar gidan Alhaji Mahmoud Zaki!" 


  Girgiza kai ta yi tana kifa kanta tana kuka. "Hajjama kice ya kada ya kai ni gida sai na kwana a wurinki!"


   "Kin san muhimmancin alƙawari, ni mutum ce da aka gina da alƙawari na rayu cikin da. Kada zuciyarki ta makantar dake ga muhimmancinsa. Komai dare zai mai da ki gida kamar yadda Hajiya Asma'u taso."


   Ta faɗa tana jan hannunta suka shiga parlournta. Ko ina fess sai tarin littattafan addini, wanda kana gani kasan an bautawa Allah da girmansa. Kuma an yiwa addini hidima da ƙuruciya. 

      Mace ce da duk abin da zata faɗa haƙiƙanin gaskiya take fada, duk abin da zai fito bakinta Allah ne da Manzonsa zata faɗa. Nasiha da take mata ba ƙaramin taɓa Naanah Asma'u yake ba. Ko Ya Moud da yake zaune a kusa da Naanah Asma'u tana share kwalla ya ce mata. 

  "Hajjama ta zo ganinki sai nasiha kike mata kamar wanda zaki mutu gobe?" 

Murmushin farin ciki ta yi tana cewa. "Mai gida takobi, ai babban alfahari ne da na cimma wannan lokacin, na ganku sannan na ribanci dogon lokaci zuwa yanzu ai Alhamdulillahi. Ka sani ba zan taɓa tsoron mutuwa ba domin na zo dai-dai lokacin da zata ɗauke ni, na bar kyakyawar ƙarshe da ahalin da zasu zama kuratul ain ga al'ummar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Bana tsoron mutuwa na gama cin lokacina ni yanzu mutuwar nake nema ta zo, na gaji da zaman duniyar me cike da ruɗani." 


  Wato idan Hajjama tana faɗar kaunarta ga Allah da Manzonsa, sai ta saka ka jin kamar gara ka koma gare shi. 

  Ta ja numfashi ta ci gaba da magana "Mai gida takobi, tsorona ɗaya shi ne, shin ayyukana sun yi kyau? Sun isa ga Ubangijina? Ya Allah zai duba ayyukana? Na bautawa Allah shi ɗaya, na bautawa aure, kuma na zauna da Kishiyoyina har zuwa yanzu da ƙasa ya rufe musu idanun bana nadamar zamana dasu domin basu cuce ni ba ban cuce su ba. 

   Kasan duk wata rigima a kare ta tsakanin Allah da bawa, kada ka sake hakkin wani ya hanaka haɗuwa da hasken Ubangiji." 


  Gyaɗa kai suke tana musu nasiha tana ciro musu abin da ta ajiye musu domin tun da Naanah Asma'u ta ce zata zo gidan Hajjama ya gaya mata tana da baƙuwar birni! Tana zuwa ta shiga sakawa a yi mata duk abin da Naanah Asma'u take so. 

      Can bayan kamar minti goma sai ga abinci daga gidansu Ya Moud an shigo da shi an kawo wa Naanah Asma'u, can aka kawo daga gidan Kawu Nuhu, aka sake kawowa daga gidan Kawu Abdulfahati. Ai kafin ƙanƙanin lokaci an cika Parlourn Hajjama da abinci. Murmushin farin ciki ne y lulluɓuta. 


  "Naanah Asma'u 'yar gata, gashi nan an cika miki gaba da abinci daga yau baki ya rufe sai kuma nan da kwanaki ashirin da tara ko talatin cif." 

  Gyaɗa kai ta yi suka sha hira bayan ta ci abincin, ta kunce tsarabar da ta zo musu da shi, turare tazo wa da Kawunnanta maza da shi, matan kuma ta kawo musu Humrar da ta saya a wurin Bakhoor by Seemah,  ta yi ta raba musu suna godiya suna saka mata albarka.  Hajjama ta haɗa mata kayan azumin da aka tattara na Maamah har da kayan sallah akwati guda. 


     Har yau Naanah Asma'u tana mamakin me Maamah ta gani ta auri Abba Babba, domin duk yadda ta juya sai ta ga yadda Maamah ta fito a tsakanin maza biyar ita ce ta shida kuma ƙarama a cikinsu sai ta ga kamar akwai wani abu da yasa aka bawa Abba Babba auren Maamah, eh to mace kamar Maamah ta fito babban gida haka ga ilmin Addini ga na zamani ita kanta Maamah tana musu larabci, wani abin da ya ƙara fahimtar da ita Hajjama Bahaushiya ce daga birnin kano, ta auri Malami irin Sheikh Zaki. 


  Ana kiran sallah Magariba kiran Ya Almu yana shigo mata, da wutsiyar ido Ya Moud yake kallonta. Buɗe mata gaban mota ya yi ta shiga ta zauna ya je ya buɗe gefensa ta shiga har wurin motar mutanen gidan suka zo mata sallama.

   Ta yi ta godiya, har suka bar gidan. Wayarta ce ta yi ta ƙara, ƙin ɗauka ta yi tana ta wasa da wayar.


   "Ki ɗauka mana!" 

Ɗauka ta yi tare da cewa "Hmm!"

  "Shi ne baki ɗauki kirana ba?"

"Ina hanya ne!" 

"Kin fita ne?" 

"Hmm!" 

"Uhmm!" Ya faɗa shi ma. 

Murmushi yabyi marar sauti "hmm ya kika kira ni ma dazun?" 

Satar kallon Ya Moud da yake tuƙi ta yi ta ga ya saka abu a kunnensa sai ta ji ba daɗi.

  "Idan na isa gida ka kira ni!" Ta faɗa tana kashe wayar.


   Hannu ta kai ta cire Bluetooth din kunnensa murmushi ya mata yana cewa "Kin gama?" 

"Eh!" Saka Bluetooth ɗin ta yi a kunnenta, karatun Dr Ahmad Didat yake saurare a hankali, wanda aka fassara da France! Lumshe idanunta ta yi yana tuƙi sai kallonta yake. 

  Bai san me ta ɗauke shi ba, amma shi tun tana tsumar goyo yake renon zuciyarsa da ita. Abubuwa da yawa suna iya sauya ƙaddara amma shi ya yarda a duniyarsa ita ce Ƙaddaransa.

  

   Wani lokaci sai ya ji kamar ya rungume ta ko zai ji sauƙi a ransa. Wani lokaci sai ya tuna shi musulmi ne, mai cikakken addini. Haka suka ci da tafiya yana tuƙi har suka isa gida. Har ya yi parking bata buɗe ido ba cire abin ya yi a kunnenta, ta juya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi me wani shegen kashe zuciya, ji ya yi kamar zuciyarsa zata fito waje. 

"Husyyy!" Kallon shi ta yi tana 'yar dariya. 

  "Kin yi farin ciki?"


Gyaɗa kai ta yi.

  Ya cire ɗaya kunnen ya matsa kaɗan har tana iya jin ƙamshin turaren shi mai suna Sadauki, ya saka mata wani irin shock ta juyo ta kalle shi, idanunsa a cikin nata. Ƙamshin turaren shi da nata ya wani haɗe a wurin yanayin gap da fuskarsu ya bada ba wani tazara ba ce, domin yadda yake kallon fuskarta idan da zata motsa.

   Bakinsu ne zai hadu da juna. A hankali ta yi kasa da kanta. Goshinta a daidai bakinsa. Motsawa kaɗan yayi ya sumbaci goshinta. 


   Da sauri ta ɗago kai suka kalli juna, daga shi har ita wani irin bugawa zuciyarsu take a lokaci guda. Ita bugawar da take ji na matsayin da ta ɗauke shi ne ɗan uwanta da suka fito ciki ɗaya uwa uba amininta wanda suke kuka tare su yi dariya tare bata kai shi wani matsayi bayan nan ba, har abada ba zata sauya masa wannan matsayi ba domin kallon Babban wa take masa.

  Sai dai yau haɗuwar fuskarsu yasa tana jin wani baƙon lamarin da ya danne mata zuciya da bata taɓa jinsa ba, amma kuma wancan matsayin da take kallonsa ya zama hijabi ga wannan baƙon lamarin. 


  Ina ba zata iya ba, a matsayin Babban wa yake a gare ta nono ɗaya ne basu sha ba amma duk tarbiyyar mace ɗaya suka samu har abada shi Yayanta ne. 

  Shi kuma bugawar da zuciyarsa take wani abu ne na musamman da yake jin sa a cikinsa kamar kullum. Zuwa yanzu ya kara hango duniyar da yake shirin faɗawa. 

  Juyar da kai ta yi tana ƙoƙarin buɗe motar. Ya koma inda yake zaune yana jin kamar zuciyarsa zata fito waje.

 

   "Zaki shiga gida ko?"

 Gyada kai ta yi. 

Buɗe mata ƙofar ya yi ta buɗe a hankali ta zura ƙafarta waje.


   "Baki ji ba!" 

Kallonsa ta yi ya juya bayan motar ya miƙa mata paper bag, amsa ta yi tana kallon waje. Yadda ya riƙe jakar yasa ta janye idanunta daga wajen ta juya suna kallon juna.

  "Me kake buƙata Ya Moud!"

 Murmushi ya yi ya sake mata jakar "Ba kome!" Ya furta a sanyayye yana murmushi. 

"Idan kina son wani abu ki yi magana!"

 "Na gode sosai!" Ta faɗa tana ƙoƙarin barin motar shi ya fito, Lokacin har an shiga masallacin kofar gidan. 


 Uban kowa ne ya fito daga gidan ganin yadda take ciro kaya daga motar, Ya Moud yana amsa yana ajiyewa. Ta zo juyawa suka yi karo da Ya Moud ɗin abin da ya bakanta ran Uban kowa da y aji dole yayiwa tufkar hanci ya ce mata.

 "Mummuna!" 

 Sake jakar hannunta ta yi tana kallon Ya Moud, shan gaban shi Ya Moud ya yi yana kallon shi ita kuma tana bayan Ya Moud. 

 "Malam gafara!" Ya faɗa yana ƙoƙarin ture Ya Moud a gaban Naanah Asma'u. 

 "Me kake nufi ne? Yarinyar nan 'yar uwata ce." 

 "A gidan Uban wa ta zama 'yar uwarka? Kai zan daddanna maka ashar, ka ji wani wasa banza kawai irinka, ka saka yarinya a cikin mota zaka lalata mata rayuwa!" 


  "Da alamu kai jahili ne, banza mahaukaci irin ka, ko ina bin mata na haramtawa kaina bin Asma'u dalla matsa ka bani wuri!" Ya ture Uban kowa.

  Abin da ya fusata Uban kowa kenan zai kai mishi naushi a fuska Naanah Asma'u ta shiga tsakiyarsu, dukar da bai samu damar sakewa Ya Moud ba.


   "Ka yi hakuri!" Tsaki ya yi ya wuce zuwa masallaci da ya rage saura raka'a ɗaya a yi sallama. 

"Ya Moud ka yi haƙuri ka ji!" 

 "Ina babu abin da ya same ki?" Ya tambaye ta yana ɗaukar kayan zuwa cikin gidan, girgiza kai tayi tana cewa.

 "A'a!" 

 Suka shiga har tsakar gidansu inda aka shimfiɗa babbar tabarma!" 

 Duk suna sallah Magariba, ajiye kayan ya yi ya kuma fita ya kwaso sauran ya kawo sannan ya tafi masallaci.




©️Mai Dambu