BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 6

by @maidambu41



Bai dawo gidan ba, sai bayan sallar isha suka shigo da Abba Babba. Suna tattaunawa irin na Uba da ɗa domin har kwanan gobe Abba Babba kallon nashi yake mishi, ɗaukarshi yake kamar babban dansa da fari. Duk sun idar da sallah. Wuri ya nima ya zauna yana faɗin. "Maamah ya aiki?" Hannunta rike da casbi ta ce mishi." Dan albarka Alhamdulillahi. Ya naka aikin dasu Hajjama da su Ummu!" " Alhamdulillahi suna lafiya!" Ya fada yana kallon Naanah Asma'u da ta zo ta zauna a gefenshi. "Ya Moud waya na gani fa!" Ta fada a shagwabe, "eh har da layi na saka miki da yake layi biyu ne." Ya fada yana kallon yadda take murmushi, "zaka koya min amfani da shiiiiiiii?" Yadda ta furta kalmar shiii yasa shi dauke wuta tsigar jikinshi yana wani irin mikewa. "Maamah!" "Ba ruwana" Maamah ta fada da sauri tana tashi a wurin, murmushi yayi don ya fahimci Maamah basu wuri tayi. "Ya Moud na sako muku abinci ne?" "Kin san dare yayi baya cin abinci me nauyi ni dai saka min rabin malmala!" Inji Naanah Asma'u, " Saka mana daya da rabi!" Juyawa Mairoh tayi tana fadin." Kuma idan baku cinye ba ni da ku ne?" " To Hajjama!" Ya fada yana kallon Naanah Asma'u, da take ta fama da wayar. "Ya Moud!" "Na'am!" Nan tayi ta bashi labarin makaranta musamman abubuwan da suka sakata nishaɗi, zuba mata idanu yayi yadda take bashi labarin ayi da hausa ayi da larabci kuma a kara da Tuareg, da yake yayi zaman cikin gidan ya iya sosai. Zabarmanci ne ma bata iya ba sosai ba. Ajiye musu abincin Mairoh tayi ta saka musu cokali ɗaya.  Murmushi yayi yana tuna kuruciyarsu da ita. " Mairoh ya naga cokali ɗaya?" "Didih na ga ai ba yau kuka fara cin abinci da cokali ɗaya ba!" Ta fada mata tana barin wurin. Juya cokalin take tana murmushi, akwai wasu abubuwan da idan ta tuna sai ta ji kamar ta dawo da abin baya. Komawarta makaranta ita da Ya almu haka ya sayo musu ice cream suka sha cokali ɗaya. Idan ya diba sai ya saka cokalin a bakinsa ya juna sannan ya mika mata cokalin bata saba ba, sai ta saka cokalin cikin roban sai ice cream ya bata jikin cokalin sannan take dauka ta sha. Ganin haka yasa shi cewa. "Kina kyamar bakina ko?" Da sauri ta girgiza mishi kai alamar a'a, kamar zata yi kuka. Wani abin da yaso ya aikata yasa a ranar taki yarda su sake haduwa a cikin gidan. Amma bayan kwana biyu sai gashi duk abinda zai kawo mata kusan tare suke ci.   "Tunanin me kike yi?" . murmushi tayi ta ce mishi. "Ba kome!" Ta yanki tuwon shinkafa da yaji wuta ta kai bakinta, sannan ta ajiye da mamakinta ai yanzu sun girma ta jima da daina cin abinci da shi, amma ta ga ya dauki cokalin ya yanka ya kai bakinsa, har rike cokalin yayi a bakinsa. "Ka bani na ci nima!" Mika mata yayi ta yanko zata kai baki ya riko hannunta ya kai bakinsa, yana murmushi. "Wannan cin amana ne akan me zaka ci min abincina." 

          "Akan kin tsaya yanga!" "Ni sai ka biya ni abincina." Ta fada kamar zata yi kuka, murmushi yayi yasan idan har ta ce haka to tana son wani abu ne na musamman idan ba haka ba irin wannan biyar da zai mata ace tana gidansa ta fada ai da matseta zai yi ya juye mata abincin bakinsa.. kallonta yayi kasa-kasa." Ki san me zaki fada idan kika ce na biya ki zan dawo miki da shi amma sai dai ko bude bakinki na saka miki kin yarda!" Shiru tayi tana kallon abincin. A hankali ta zare hannunta zata bar wurin ya riko hannunta ya dawo da ita asalin gefenshi.. kauda kai tayi gefe yace mata. "Ki yi hakuri ba zan kara ba!" "Kayi hakuri?" Ta tambaye shi, gyada kai yayi yana murmushi. "Eh kanwata!" Gyara zama tayi tana cewa. "To sai dai ka bani a baki!" 

  ..... 

"Addah Khamiee!" "Naam Mairoh!" "Don Allah da Ya Almu da Ya Moud wanene yaci dacewa da Didih ne wallahi ina shiga ruɗani." Dariya Khamilah tayi tana fadin. "Da yake Allah ya daura miki gulma da sa ido! Ita Didin ya dace ki fahimta ba soyayyar da take tsakaninsu ba. Ki fahimci wani abu son da suke yiwa juna da Ya Almu kowa ya sani a cikin family, amma sanin cewa bai zama dole su sami juna ba yasa ta raba hankalinta biyu. Musamman da Maamah itama take kin lamarin eh akwai wani abun da har yanzu na kasa tsinkayensa. Kamar ni da Ya Amaan ne ga kuma Fahad. Kin ga dole na zaɓi ɗaya a cikinsu idan farin ciki da nutsuwa Didih zata samu nafi tunanin Ya Moud zai bata, idan kuma soyayya za a bi to ya Almu shi yafi cancanta ga rayuwar Didih, muna yin namu ne amma Allah ya tsara nashi!" Sai suka yi shiru Faɗime da take gadon Didih ta ce musu." Nafi sonta da Ya Almu domin na bisu kasar waje na zama yar can!" "Hauka kike kenan?" "Kai Addah Mairoh!"

    Murmushi Khamilah tayi musu tana turawa Fahad sakon da ya shigo mata. Fahad dan Imam Abdulfahati ne, shima ɗan Kawunta ne. Sanin cewa Maamah bata bata fuska akan Yaran family ɗinsu na Tuareg ba yasa ta bawa Fahad damar har suna waya. Kuma ita ta fahimci abinda Maamah take nufi. 


 A waje kuwan hira suke suna cin abincin, idanun Ya Moud yana kanta duk da shi yake bata abincin, sai da ta fara kawar da kanta ya kyale ta ya karasa abincin yana zuba santi. "Waye yayi girkin?" "Nice na daura ina ga Khamilah ko Mairoh dayansu ya karasa!" Gyada kai yayi yana faɗin. "Sun cancanci a biya su, amma ke ki gaya min me kike so na biya ki da shi?" Saka tafukan hannunta tayi tana mai rufe fuskarta da shi tana yar dariya. "Duk abinda ka bani zan amsa!" "To ni me zaki bani?!" Ya tambaye ta. Duk abin da ka tambaya. "Zaki iya sumbatar kumatuna?" A hankali ta janye daga gefenshi, kafin ta mike."baki san wasa ba ne?" Ya fada yana dawo da ita gefensa. "Amma kasan ai ni ba yar iska ba ce, a matsayin Babban wa na dauke ka. Ban taɓa tunanin banza a kanka ba domin kana da mutunci da kima a idanuna,, don Allah ka daina fadar kome ya fito bakinka!" 

      "Naji Hafizah Naanah Asma'u, amma ni dai ban yarda da matsayin da kika bani ba ki bar shi a matsayin wanda." Shiru yayi itama bata ce kome ba, sai ya karasa da cewa. "A matsayin wanda idan ya ga kare dai dauki dutse ya kwala mishi!" Ai kuwa suka fashe da dariya, "Ya Moud kai abokina ne, kai ne abokin shawarata. Duk wani abinda zan ji ko na gani ina son mu tattauna da kai ne, idan har akwai wanda ya fahimce ni bayan kai sai Ya Almu. Kai a matsayin na musamman na dauke ka. Kuma ina kallonka a matsayin na musamman a rayuwata." Mikewa yayi yana mai saka hannu a aljuhun wandonsa. Yana murmushi ya sauka akan taburman, kai plat din kitchen din waje. Sannan ta dawo ta shiga cikin gidan ta kawo mishi ruwa. Amsa yayi da hannunsa ya janyo ta ganshi. D'ago kai tayi tana kallon fuskarsa a a cikin hasken farin wata." Duk matsayin da zaki ajiye ni ba laifi ko ajiye, amma ina son ki kusanta ni da zuciyarki!"  A hankali tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta."Da gaske nake maganata, ba zan iya riƙewa koda yaushe ba na gaya miki gaskiya ne, saboda ki san yadda nake jinki a raina har na tsawon wani lokaci zan fitar da abinda yake raina? Ko zan cigaba da kallonki a matsayin da na saba ne! A duk lokacin da kika ji nutsuwa da nishaɗi ki kira ni zan zo na taya ki murna da kuka zan taya ki dariya da bakin ciki. Domin tun ranar da na ganki na alakanta ki da zuciyata, duk yadda zaki kalle ni ba laifi amma kece madadin wasu sirrikan da na addana!" Daga haka ya juya yana me barin gidan, tana tsaye a wurin kamar wacce aka dasata, ta kasa motsin wannan abinda ta binne a ranta take jin yana wani irin taso mata da kuka me karfi yana zuwa mata. Tana tsaye a ƙarƙashin farin wata. Tana jin tashin motarshi har zuwa lokacin bata ja kafarta zuwa ciki ba. 

       Motsin Abba Babba ne ya fito ya ganta tsaye har lokacin. "Naanah Asma'u!" "Na'am Abba!" Nuna mata mata taburman yayi ya zauna, itama ta zauna a gefenshi. " Me nene?" Ajiyar zuciya take saukewa a hankali tana wasa da yatsunta. "Akwai wani abu ko?" Girgiza kai tayi, "Mahmoud da Mustapha ko?" Kifa kanta tayi a cinyarta, tana jin wani irin kuka yana zuwa mata, bata yi kukan ba sai ajiyar zuciya da take ta saukewa. "Kiyi hakuri ni da Maamahnku mun yanke shawarar ki tsayar da Mahmoud!" Da sauri ta d'ago kai tana kallon Abbanta. Jinjina mata kai yayi yana faɗin. "Mustapha ɗan ɗan uwana ne, sai dai bana son  damuwar da zata hana ki farin ciki, duk abinda zai janye miki farin ciki ina gudunsa. Dangina basu amshe ki a matsayin namu ba, ke jinina ce amma ban san wacce ƙaddaran tasa kika kasa samun soyayyar dangina ba. Ina sonki ina son farin cikinki, kace abu na farko da na fara mallaka a rayuwata, na same ki a dai-dai lokacin da ban zata ba, kina zuwa kika kara jefamu cikin farin ciki. Kece mabudin duk wata nasara da cigaban da nake gani, ba iya y'a nake kallonki ba ke tsokar da take Qalb dina ce. Nayi ƙoƙarin kamantaki da sauran Yaran sai na fahimci bayan ke sai Hajiya da Mahaifiyarki." Jingina kanta tayi a kafadarshi. "Duk wanda yasan mahaifinmu ya ganki abu daya yake faɗa wacce irin jini ne da mahaifinmu da ya tafi aka kaifi me yanayi da shi. Nasan da yana raye ba zai bar kome haka ba, ki yi hakuri ban da karfin da zan muku kome kamar na sauran yaran dangina ba, amma in sha Allah daga abinda zaku saka zuwa wanda zaku ci ba zai fi karfina ba. Ina kiyaye dukiyar al'umma da yake hannuna ne, amma ace dukiyar nan tawa ce ai ba zan taɓa barinki har ki yi kuka ba. Allah yasan yadda nake kaunarki kuma nake tausayinki." Haka suka yi ya hira can Matarshi ta fito ganinsu tare yasa ta yi kwafa tana faɗin "wallahi na kasa gane wannan abin, Yarka ce ko." Tashi Naanah tayi tana naɗe taburman domin shima Abba ya tashi yana nufar matarsa da ta haɗiye maganar, shiga cikin parlournsu tayi ta rufe kofar tana jin lokacin da Hasiya take bashi hakuri can kuwa ta fashe da kuka tana rokonsa, ta kai shi bango ne. 

      Maamah tana dakinta ta shiga ta zauna a dogon kujeran dakin. " Me yasa kike janyo abinda zata fadi maganar banza akan Abbanku ne?" "Kiyi hakuri Maamah!"

      Murmushi tayi daga haka ta mata. " Je ki kwanta! "  "Sai da safe Maamah!" " Allah ya tashe mu lafiya!" 

Tana shiga dakinsu ta cire kayanta, ta shiga ban ɗaki tayi wanka da alwala sannan ta fito ta shimfida abin sallah.  Sai da tayi shafa'i da wutir, ta jima tana niman zaɓin Allah akan rayuwarta. Yadda tayi addu'ar kamar yadda ta saba sai da tayi ta kuka. Bata jin dadin rayuwarta bakiɗaya laifin da bata aikata ba take amsa, ƙaddara bata mata adalci ba, ita bata yi laifi kome ba amma sai zafinta ake ji, yadda ake hantararta da jin haushinta zaka rantse da Allah ba jinin gidan ba ce.  "Didih ya isa haka mana!" Inji Khamilah da tayi maganar cikin magagin barci, shiru tayi bata kara ko motsi ba, duk abinda yake faruwa. 


 Uban kowa yana jingine a bayan window da take kwance. Yana jin yadda take shashekar kuka. Idanunsa a lumshe yana jin kukanta, yana ganinta a yadda take kome amma wannan shine karo na biyu da ya sha zuwa ya saurari kukanta, yana jin lokacin da take addu'a bayan ta idar da sallah. Tabe baki yayi yana d'aga kafadarshi ita ta sani shi dai damuwarshi dukiyarsa da take hannunta kada ta bari wani ya gani balle har a fara mishi kallon mutumin banza, domin bakiɗaya unguwar ana bala'in respect dinsa shi yasa ko shan taba da wiwi da yake yi a cikin gidan yake bata ya taɓa fita waje a ganshi. 


         Wucewa dakinsa ya wuce ya zauna yana kallon agogon hannunsa. Cire rigar jikinsa yayi ya kwanta a gadon. Murmushi yayi wurin karfe ɗaya na dare sakamakon jin an daki kofar dakin da yake. Bai motsa ba saboda suna shigowa zasu tsammanin yana kokarin ɓoye wani abu ne. Haska mishi Torchlight ɗinsu me mugun karfi da haske. Kare fuskarsa yayi yana murmushi. "Kun makara da minti arba'in da biyu!" Ya fada yana kallon agogon hannunsa. "Kai mana shiru!" Komawa yayi ya kwanta yana kallonsu suka gama hargitsa ɗakin. "Ina ka ɓoye kuɗaɗen nan?" Dauke kai yayi yana me gyara kwanciyarshi a gadon yana karkad'a kafarshi. "Kai ana magana kayi banza damu!" "Nawa aka biya ka ka nuna min bindiga!" Ya kaiwa jami'in wani irin duka tare da juya bindigar hannunsa. 


    Bakiɗaya suka nuna mishi bindigar, murmushi yayi yana mai shakar bindigar. "Kirar Rasha nauyin saba'in da digo biyar, harshen gwamnati goma sha biyar. Gaskiya da alamu gwamnati tayi kyakyawar shiri akan tsaro." Ya fada yana mika musu bindigar. "Ina da mutunci a cikin gidan nan da unguwar nan kada wani abu mara kyau ya faru."

      Daga waje ya ji muryan Hajiya Innah, " shit;" ya furta. " Su waye a dare nan? Me kuke bukata ba don Allah kada ku cutar da shi, makaho kana ina zi ga yan fashi ne wayyo Allah jama'a a kawo mana ɗauki! "

" Hajiya mu ba yan fashi ba ne, jikanki zaki gargad'a duk ranar da ya sake muka kama da laifin da yake aikatawa sai ya fuskanci mutuwa da rayuwa. " Daidai zuwan Abba Babba da Maamah sai Naanah Asma'u da take bayan Maamah tana kallonsu. "Lafiya officer?" "A yanzu bamu samu kome a tare da shi ba, amma gaba idan muka same shi koda kuwa da ƙaran taba ce zai fuskanci matsalolin da bai zata ba, muna da record na baya, a yanzu kuwa mun samu labarin ya shigo da wasu kwayoyi masu hatsari wnada har an fara!" Wani bangaza da ya kaiwa Captain ɗin yasa shi fadawa ai kuwa team ɗin suka rufe shi da mugun duka, zai iya ɗaukar wannan dukar da akan a zubar mishi da mutunci a idanun mutane da yake ganin girmansu. 

             Ana dukansa amma saboda taurin kai idanunsa yana kallon Naanah Asma'u da jikinta yake wani irin rawa, sai kifa kanta take a bayan Maamah, tana rike hijab din Maamah. "Maamah!" Ta furta a sanyayye tana kuka. "Mara mutunci tsagera, yaki laushi. Ko a haɗa da ƴan gidan ne Sir?" Inji daya daga cikin jami'an tsaron, daya ya kai hannu ya ture Abba babba tare da nufar Maamah da Naanah Asma'u. "A'a fa! Kada ka fara yaƙin da ba zaka iya dakatar dashi ba. Ni na yi laifi kada ka fara kana da Yarinya da take aji biyar na gaba da primary,  kana da yaro da yake aji daya a jami'ar Maryam Abatcha. Dukkanku ina da sani a kanku kada ka daura hannunka akan Matar da yarinyar bayanta." Ya fada yana zuba gwiwarshi a ƙasa. Jini na zuba a kanshi, "baku kama ni da wani abu ba, idan na shigar da wannan abin da kuka yi ga DST zasu bi min hakkina." Buga mishi kasar bindiga daya daga cikinsu yayi ya fadi kasa, wanda ya janyo fasa ihu da Naanah Asma'u tayi. "Shiiiiii! Dare ne Maamah wuce da ita bangarenku!" Wani mara mutunci a cikinsu ya ce mishi. "Ina zasu ai sai ka bamu abinda kake da shi domin an gaya mana ka zo da kaya! Ko kuma mu tube yarinyar a gabanka!.. "

 Dariya yayi yana tofar da yawun bakina da ya fashe." Da kuwa har abada duk wanda ka ji zai aikata haka zaka ce mishi kul wannan ba abu ne mai kyau ba. Da kayi mugun gani. Ku kira Darakt kuma ku bar mana gida ko abinda baku zata ba!" "Kai Ina waye ya tsaya maka ne"


     Wayar dayansu ne ya dauki kara, ya mikawa babbansu. Yana sakawa a kunne ya sara kamar mutumin yana gabansa ya ce.." kuskure aka samu, ba mu sami kome ba sir ayi hakuri. " Yana fada ya kalli sauran team din.." shafaffe da mai ne muje ana jiranmu!" Duk suka saka kai zasu fita daya daga cikinsu ya tsaya.." yarinyar nan tayi min, tana yi min ka shirya min ita ka kawo min ita ko kuma na saka a kawo min ita;"

       "Wannan shine mafi girman kuskuren da kayi domin ita wannan ba ganima ba ce. Sai dai ka jira sakona zai iso gare ka kayi kuskure na kallon yarinyan nan" ya kara takawa gabanshi. Ya kai bakinsa daidai kunnensa. Ya fada mishi wata magana yana murmushi..........