ZAFIN WUTA

BOOK TWO

by @maryamstar248

CHARTER 10

بسم الله الرحمن الرحيم

Durƙushewa ya yi akan gwuiyoyinsa, yayinda kuka da dariya suka haɗe ma sa lokaci ɗaya, sai kuma yakai hannayensa cikin bed ɗin ya tattaro yaran waɗanda keta sharar barci abinsu, ya haɗa su a ƙirjinsa ya rungume kamar wani zai ƙwace ma shi su, sai kuma ya shiga jero addu'o'i ya na tofesu, sannan ya shiga sumbatarsu kamar zai cinye su, bai tsagaita ba sai da ɗaya ya motsa ta na yamutse fuska kamar za ta yi kuka, sai ya yi saurin mayarda su ya kwantar shi kuma ya kwanta akan lallausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a ƙasa ya na sakin ajiyar zuciya a jere kamar wanda ya kubto daga hannun abin cutarwa.

Alhaji Umar kenan, shararen gogagen ɗan kasuwa wanda manya-manyan ƴan kasuwa, gwamnati da al'umaa ke ji da shi, Alhaji Umar sanannen mutumne wanda tauraruwarsa ke haskawa da tsananin haske, haskenda ke tattare a cikin tarin ƙaddarorin da ya shallake kafin haskakuwarshi a sararin samaniyar duniyar kasuwanci, Alhaji Umar mutum ne wanda rayuwarshi ke cike da tari ƙaddararo mabanbanta, tun tasowarshi ƙaddara ke walagigi d rayuwarsa, amma bai sare ba wajen yin tawassali da kuma rungumar ƙaddarar a duk sa'ilin da ta dumfaro rayuwarshi, yakan tsaya tsayin daka wajen ƙasƙantar da kanshi a wajen Mahalicci me kowa kuma me komi, wanda ke aika dukkan abin da ya so ba tare da shamaki ba, manzon Allah ya yi gaskiya da ya ce a cikin wani hadisi, "Allah ya na son bawa me tsoronshi, me wadata".

Tsoron Allah da kuma ƙarfin iymani irinna Alhaji Umar sune suka taimaka ma shi wajen samun ɗaukaka a duniya, Allah ya azurtashi da tarin dukiya wacce shi kanshi bai san iya adadinta ba, sannan kuma Allah ya albarkace shi da farin jini a cikin mutane.

Ƙaddara ɗaya ce Alhaji Umar ya kasa haƙuri da dangana da ita, wacce ta ke neman zautar da shi, ya rasa ƴaƴansa mata har karo biyu, ba rasuwa sukai ba rasa su ya yi ta hanyar son zuciya da kwadayi irin na makusantanshi.

A hankali Hajiya Sadiya ta dire tray ɗin da ta ɗauko goran ruwa gami da cup a ƙasa, sai kuma ta buɗe wa ta ƴar jaka ta ɗauko kwalin magunguna guda biyu, ta buɗe tare da ballawa ta saka a cup ɗin, haka sauran suma ta saka a cikin cup ɗin sannan ta zuba ruka kaɗan ta dama kamar yanda ake bawa yara magani, bayan ta gama ta aje a gefe tare da gyara zamanta ta ɗauki kan Alhaji Umar ta ɗaura akan cinyarta tare da share ma shi hawayen da ke ta faman silalowa daga kwarmin idonshi, a hankali ta janyo cup ɗin tare da bisimilla sannan ta kafashi akan busashen bakinshi wanda laɓɓan suka bushe kamar wanda yai sati ɗaya ya na tafiya ba tare da ya sha ruwa ba, buɗe bakin ya yi ta juye ma shi maganin ya shanye tas, sannan ta kora mashi da ruwa me rangwamen sanyi ta gyara ma shi kwanciya akan cinyarta ta na shafa sumar kanshi a hankali, sai da ta tabbatar da barci me nauyi ya yi awon gaba da shi, sannan ta ja shi da ƙarfin zuciyarta ta ɗaura shi akan makeken bed ɗin da ke ɗakin ta gyara ma shi kanciya sannan ta fice daga ɗakin.

Wajen photon ta je ta tsaya ita ma ta na kuka me ciwo ta na shafa fuskokin yaran ta na sambatu, ta jima a wajen ta na kuka kamin daga bisani ta rarrashi kanta ta tashi ta koma wajen ƴaƴanta da ke kuka ta rarrashe su tare da shayar da su, kwantar da su ta yi a tsakanin ita da mijinta Alhaji Umar, ta jima a kwance ta na tunanin rayuwa, kafin daga bisani barci me nauyi ya yi awon gaba da ita.

A cikin barcinta ta yi mafarki kamar yanda ta saba aduk lokacin da takai kafaɗarta ƙasa da sunan yin barci, yauma kamar kullum.

Zaune suke a waje ɗaya, cikin wani faffaɗan fili me yalwar bishiyu da ciyayi, fuskokinsu na kallon juna a zahiri, amma a baɗini ba junansu suke kalloba ko wacensu na kallon wani abu daban, su na matuƙar kama da junansu sosai, sai de ɗaya ta kasance fara tas ɗayar kuma me matsakaicin haske, amma baza'a kirata da baƙa ba ko wankan tarwaɗa saboda tana da haske dande ba can sosaiba, Yau kuma ba kamar yanda ta saba ganinsu su kaɗai ba, yau su biyu ne sannan kuma mazaje guda biyu na gefen kowace.

Da Salati ta farka kamar kullum idan ta yi mafarki, sosai yau zuciyarta ta tsinke da lamarin, sai ta ji yau kaɗai ta na so ta tattauna lamarin da wani, to amma kuma wani wah, waye zai dubeta da idon basira ya fuskanci abin da ta ke nufi ba tare da ya yi ma ta kallon mahaukaciya ba, amma kuma ya dace a duba lamarinan gaskiya, wannan mafarkin ta jima ta na yinshi tun shekarun baya, kuma kullum duniya ta kwanta barci sai ta yi mafarkin, ya kamata ace tasan mi wannan mafarkin nata ya ke nufi.

Ita kaɗai ta ci gaba da zancen zucin, ta na lalubawa kanta mafita, kamin daga bisani ta tsaida tunani da nazarin wacce ta dace da tayi shawara da ita, tasan za ta fuskanceta kuma ta fahimceta, ba kowa ba ce face ƴar uwarta Asma'u.

LEGOS.

MUBEENAH.

Yau satina biyu cif a gidan Alhaji Abdallah me gwalagwala, na murje na yi ɓulɓul abina na ƙara zama cikakkiyar budurwa duda kasancewata me ƙaramim jiki da siranta, haske da sheƙin fatata ya sake daɗuwa, ni kaina nakan zauna ina taɓa fatata ina jin daɗin yanda tai laushi gwanin kyau, baƙin gashin kaina wanda daƙyar Mama ke gyara min shi dan sam bana son kitso, yanzu ya sake linka tsayi da baƙi saboda musamman Sulaima ke ware lokaci duk bayan kwana biyu ta gyara min shi tsab, haka nike fitowa kamar budurwar ba'indiya irin masu tashen kyawunan, yanzu kullum zaka same ni cikin ado da kwalliya, ga ƙamshin tsadadun turaruka wanda Pahpah da kanshi ya bani kyautarsu, sannan yanzu na yi wani irin sabo da ƴan gidan, na saki jikina da su sosai, su kuma kullum cikin yaba min suke da godiya akan yanda nike jajircewa akan Fauzan, wanda yanzu jikin na shi yai sauƙi sosai, wannan zafin jikin duk babu shi, kasancewar an canza mashi ɗaki yanzu, da wannan damar na yi amfani wajen saka matakin tsaro daga dukanin abin cutarwa mutum ko aljan, ƙira'a nike sakawa cikin ƙaramin sauti a makeken plasma da aka jingine a bangon ɗaki, sannan da lokacin azkar ya yi da kaina nike canza channel, hakan ya taka rawa sosai wajen dawo da hankalin su Mommy suma suka shiga neman kariyar jiki da neman tsari daga dukkanin abin halitta, duk maricen duniya zaka same su a ɗakin Fauzan su na bin ƙira'ar azkar ɗin da ake yi a Sunnah TV, haka za ka ga kowa ya zauna yana bin ƙira'ar cikin ƙaramin sauti, hatta Pahpah yakan zauna idan ya na gida shima ayi da shi, bayan angama kuma abawa ƴan aiki umurnin cike wajen da kayan ciye-ciye mu zauna ana fira ana ciye-ciye abin gwanin burgewa.

A duk lokacin da na tsinci kaina cikin farin ciki nakan tuno rayuwata ta baya wacce da ni da dabba bamu da bancin, haƙiƙa na yi rayuwa me cike da rashin ƴanci, kyara da rashin samun sakewa a cikin gidanmu, a rayuwata ta baya babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da Abba ya lakaɗa min shege duka ba, sannan ya bini da mugayen kalamai masu kama da ZAFIN WUTA, bani da iko da kaina sai abin da aka gindayamin, ba ni sa zaɓin kaina sai wanda aka zaɓamin, a wajen mutum ɗaya nike samun rangwame har in samu rarrashi da tarairayar da na rasa samu a wajen mahaifina ita ce Mama ita kaɗai ce ke nuna min zallar soyayya wacce babu surki, takan zauna da ni domin ta ji matsalata, takan tayani ɓakin ciki ko damuwa idan wani abu ya same ni, shi yasa har gobe na kasa cire tunaninta, kasa mancewa da ita, kullum sai na yi hawayen kewarta.

A hankali na saukar da kaina daga kallon jikin miron da nike, cikin nutsuwa na sagala mayafin kayan da na saka, sannan na zira takalmina ina sake daidaita fuskata na fice.

Har yanzu na kasa sabawa da bugun zuciyarda nike tsintar kaina aduk lokacin da na tunkari ɗakin Fauzan, abu ɗaya ne na kasa sabawa da shi tun zuwana gidan shine, kaifafa idanuwan Fauzan bana sakewa idan ya kafe ni da su ya na kallona, shikuma muddin idanuwansa biyu to ya dinga kallona kenan kamar sabon maye, yanzu haka da nike ƙoƙarin shiga ɗakin sai da naɗanyi jimmm a bakin ƙofar tare da ɗaure fuska sannan na yi sallama cikin ƙaramin sauti na tura kaina cikin ɗakin.

Tun sanda na tsaya jikin ƙofar ƙamshin turarena ya riga ni shigowa ɗakin, da sauri ya buɗe idanuwanshi ya na jiran ƙarasowata, da yake yau tun safe da na bashi magani ban sake bi takanshi ba sai yanzu d nasan kowa na gidan na daf da hallara dan mu zauna kamar yanda muka saba dan gudanar da azkar.

Daddaɗar sautin muryata ne ya ratsa can cikin ƙoƙon kan majiyar sautin kunnuwansa, a hankali ya sauke nannauyan ajiyar zuciya, wata iriyar kewar sanyin jikina na baibayeshi, sanyin da ke tattare da ni wanda ke samar ma shi da nutsuwa na mamaye ɗakin.

Kamar kullum wai ma bai amsa sallamar a fili ba, amma naga lokacin da jajayen laɓɓansa suka yi motsi kaɗan, da sauri na sauke kaina ƙasa tare da ƙarasawa wajen shi, ba tare da na kalleshi ba na hau haɗa ma shi maganin marice, bayan na gama na gyara zamana tare da fuskantar inda ya ke kwance amma fuskata na kallon gefe, na wani maze sannan na ce.

"Magana nike so inyi da kai, amma dan hasken musulinci ka daina kallona hakanan, idan kana kallona bazan iya faɗin abin da nike so imfaɗi ba."

Nai maganar ina cuɗanya ƴan yatsuna, amma koda kuskure ban kalli inda yake ba.

"Ki na da kyau me fizgar hankali, bazan iya janye idanuwana akan ki ba muddin zamu kasance waje ɗaya, kallonki na rage min zugi da raɗaɗin ZAFIN WUTAR da bai gama hucewa a jikina ba, please ki yarjemin kallonki a koda yaushe."

Yai maganar cikin salon da ke saka ni jin wani abu ya tsarga tun daga tafin ƙafata har zuwa ƙoƙon kaina, mazewa na yi na daure na hana idanuwa da ke ƙoƙarin bani kunya akan satar kallonshi, sannan na ce.

"Ban san iya adadin watannin daka shafe a kwance cikin halin ciwo ba, amma kai nasan za ka iya tuna lokacin, ina so in tunatar da kai yanzu Alhamdulillah ka samu sauƙi sosai, sai nike ganin ya kamata ace ka fara ramakon sallolin da aka biyoka, ba dole sai ka yi kamar yanda ka saba yi abaya ba, zaka iya yi a kwance ta hanyar ayyanawa a zuciyarka, sai kaga sanadiyar sallar Allah ya sake baka lafiya mawadaciya."

Tun da na fara magana ya kafe ɗan mitsitsin bakina da kaifafan idanuwansa, ya na kallon yanda nike zaro magana cikin amon da ke saukar ma shi da kasala, da wani yanayi me wuyar fassarawa.

Bai ce komi ba amma na jiyo sautin fitar murmushinshi, sai na tsinci kaina da jin haushin shirun da ya yi min, dan harga Allah da wannan kallo da yake min gwara ya dinga yimin magana, saboda ina jin daɗin amon muryarsa, sannan ina tsintar kaina cikin matsanancin farin ciki aduk lokacinda ya yi min magana.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌