RIKICIN DUNIYA

Chapter 3

by @meenatyandoma

*RIKICIN DUNIYA...*

©️ Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

CHAPTER 3
...Ganin wayar na niyyar shan ƙasa, cikin zafin nama Nadiya ta cafkota. Tana mai aikawa Wasila mugun kallo.
"A yau na fahimci abin da kike boyewa cikin zuciyarki. Wasila ko dai kina bakin ciki ne na samu saurayi wanda ya kece sa a?" 
Dafe ƙirji Wasila tayi.
"Ni! Aa wallahi kinsan ba a saba riki waya irin wannan ba kada ki ga laifina don jikina ya dauki kyarma. Wallahi har na shiga tashin hankali saboda idan na fasa wayar nan kinsan kashina ya bushe"
Murmushin mugunta Nadiya ta yi.
"Kwarai kuwa, tsaf zan sanar da wanda ya kawota ya aiko jami'an tsaro har gida a tafi dake"
"Ni kaza! Ki rufa mini asiri da me zamu biya wayar nan? Ko kin manta Mahaifina ɗori ne Sana'arsa ita ce ɗaura mutane idan sun karye ko sun goce."

"Ya za a yi in manta bayan a tare muka tashi, ke fa gidanku duk da kin girma ko irin ‘yan samarin nan masu kuɗi ki samu kiyi amma har yau shuru kake ji, Malam ya ci shurwa"
Ɓata fuska Wasila tayi tare da jan birki.
"Nadiya! Don Allah me kike nufi dani? Tun bayan haduwarku da Kasim kike neman wulakanta ni, ko dai kin manta tare muka taso?"
"Banyi miki gardama ba. Amma abin da nake so ki gane shine, yanzu a tsakaninmu akwai tazara kin gane. Dole ki fara bani wani girma saboda ni ɗin a yanzu matar manya ce Allah ya 'yanta ni"
Idan Wasila ta ce bata ji zafin maganganun nan ba tabbas ta yi ƙarya. Tunawa da tayi yaƙi ɗan zamba ne sai ta yi murmushi
"Haka ne fa Matar mai girman daraja Kasim. Dole muyi biyayya mu dangwali arziki, wa ma ya sani a cikin abokansa ni ma In yi wuff da ɗaya"
"Wannan haka take kawata. Da kaina zan samar miki wani mai kwaɓi. Saboda ba zai yiwu ba ina auren attajiri ba ke kuma a ce kina nan a talauce ina impossible"
Dariya suka yi a tare.
Napep suka tsaida sai ga kiran Kasim. 
Bata shiga ciki ba fuskarta dauke da fara'a ta fara waya da shi.
"Wasila fito ga Kasim nan zai zo ya sauke mu a school daga nan sai ya wuce Katsina."
Sallamar mai Napep suka yi ba su jima ba sai ga Kasim.
Kacokam hankalin Wasila ya sha'afa ga kallon Kasim ta ma manta Nadiya na wurin.
Sai da Nadiyar ta zungurota kafin ta dawo cikin hayyacinta.
Gaisawa suka ta shige gidan baya Nadiya kam tuni ka kame a gaban mota.
"Kyakkyawan saurayi aikin farko, ga kudi wanda tsabar su kallonsa kadai za kayi ka fahimci sun jima da zama a jiki da kuma fatarsa. Me ya gani jikin Nadiya baka ba wani jiki ne da ita ba, iyakaci wannan dogon hancin mai kama da bushasshen karas. Diri da haske duk na fita amma ita Kasim ke so, kada ki damu tamkar yadda ake kwace goruba a hannun kuturu haka zan kwace shi"
Ta karasa maganar zucin tana mai kallon gefen gefen hanya.
A bakin Get ya sauke su bayan ya cika masu hannu da kudi, abinda ya kara ta'azzara mummunar manufar Wasila ta mallakarsa ta ko wace hanya.
Sallama suka yi da shi suka shige makarantar.
"Wasila kin san wani abu?"
"Aa sai kin fada"
"Anya kuwa ba ni ce ta farkon yin iPhone 12 a cikin makarantar nan ba?"
"Haka nake tunanin domin yau mako daya cif da fitowar ta. Ke kam Nadiya kin samu duniya saura ƙiyama"
"Ita ma zamu samu"
Tafawa suka yi suna dariya har suka karasa inda students suke. Nan fa ido ya dawo kan Nadiya tuni aka fara ihu Kasancewar mata da waya sai Allah. Hotuna suka hau ɗauka ana kara fasawa Nadiya kai, itakuwa sai faman hura hanci take yi.
Wannan lamari shi ya kara hura wutar kiyayyar da ke zuciyar Wasila, a daddafe suka baro makarantar kai tsaye gidan Malam Bawa suka nufa. Sai dai abin da Nadiya bata sani ba shi ne, tuni Wasila ta debe kasar da zasu kaiwa Malam Bawa ba tare da ta sani ba.
Ƙasar ta mika masa zuciyarta gal da farin ciki. Wasu tofe tofe ya yi Surkullen shi ya haɗa wani turare mai karfi ya mika mata.
"Ki zuba cikin ruwan wankanki a ranar da zai zo, sannan ki tabbatar kin shafe fatar jikinki da turaren nan ya ji kamshinsa. Da zarar ya shaƙi kamshin magana ta kare sai yadda kika yi da shi."
Tsabar farin ciki Nadiya hannunta har kyarma ta karba ta saka a jikka. 
Kudin da Kasim ya ba su shi ta fito da shi ta ba boka.
Bayan sun fito Wasila gabanta faduwa ya rika yi sakamakon abin da Boka ya fada mata.
"Kada fa Nadiya ta rigani shiga cikin zuciyar Kasim"
Ta karasa maganar zucin tana mai kallon Nadiya da ke ta faman washe baki.
"Kawata!" Wasila ta fada.
Kallonta ta Nadiya ta yi saboda ta san magana mai muhimmanci ce zata fada.
"Amma kina ganin maganin Malam Bawa ya na aiki sosai?"
Jim Nadiya ta yi kafin ta amsa mata.
"Me kika gani ne?"
"Kawai dai tambaya nayi"
"Ke ma kin sani ya na aiki tunda ai tare ya ke mana aiki, duk in exam ta zo ke ce shaida"
"Kuma fa haka ne Nadiya, mu dai Allah ya kai mu lokacin bikin nan Dutsin-ma zata girgiza da biki mai capacity"
Dariya Nadiya ta kwashe da ita. Saboda Indai kana so ka ga farin cikinta, to ka riƙa koɗata kana mata kirari yanzu zaka ga ta dawo cikin annushuwa.

Gidansu Wasila
Umma na cikin daki yunwar cikinta ta isheta. Motsin da ta fara ji ne ya tabbatar mata da mahaifin Wasila ne ya shigo gidan, da sauri ta fito tana gyara zaninta dake kokarin kwancewa.
Kara mai uban yawa ta ga ya fiddo ya na ta shafeshi da garin magani ya saka Umma yin dariya. "Tsumma maƙunshin cuta! Ai tunda na ji motsinka nasan yau mugunta kake shiryawa."
Dariya malam ɗayyabu maɗori ya yi.
"Kwana biyu babu karaya bare tsagewar ƙashi, shuru kake ji yau kwana hudu rabon da mu dora tukunya. Ki zuba ido ki gani yadda na sha ta wadan nan kararen bada jimawa ba za ki ga an fara dandazon kawo masu karaya da tsagewar ƙashi. Bari ki ga in Kara juya su yadda zasu sha rana da yawa"
Garin ciki ne ya mamaye zuciyar Umma ko ba komai tasan yau zasu dora tukunya.
Sallamar Wasila ta saka su sakin zancen da suke suna mai amsawa.

Murmushi tayi. "Yau gidan nan akwai dora kutunya."
"Ka ji yar nema wato.kin fahimci karatun"
"Sosai ma kuwa Baba, tun Ina yarinya nake ganin kana wannan abin. In haddace ai ya isa a ce na haddace"
"Kwarai kuwa don ma kinki mayar da hankali in koyar dake ko bayan ba raina in Samu magani tunda ke daya Allah ya mallaka mini. Haka nan kike rena wannan sana'ar amma akwai samun kuɗi Indai kasuwa ta yi albarka, hatta karatun ki da su nake biya miki"
Yamutsa fuska ta yi.
"Ni dai kada kayi mini Baki, ni zanyi wata sana'ar dorin Allah ya tsari Gatari da sauran shuka. Ina auren miji mai kudi kaima barinta zaka yi"
"Allah ko yar Baba"
Ya karasa maganar ya na watse haƙora.
"Sosai ma lokaci kawai nake jira"
"To ya isa uwar yan surutu. Jeki watsa ruwa musan hanyar da zamu samu abin watsawa uwar hanjinmu"
"Kai Umma na manta ban fada miki ba. Kasim ya bani kudi dazu"
Waro ido waje Umma tayi
"Kudi kuma? Ko har ya fada komarmu?"
Ya Musa fuska Wasila ta yi
"A'a fa Nadiya ya Zo dauka ya kaita makaranta, shi ne bayan ya sauke mu ya ba kowaccen mu kudi"
"Haba ai da yayyafi kogi ke cika, da sannu zai zo hannu. Yi maza ki shirya mu dauki hanya da zafi zafi ya kamata mu je wurin Bakurmi"
Malam Ɗayyabu yda ya ji maganar an samu kudi amsa yayi ya siyo musu taliyar yara. Umma da kanta ta dafa masu suna gama ci shuka fice ba tare da sanar da Ɗayyabu da ke faman aikin gyara karaya inda suka nufa ba.
Kasancewar yau da kudi a hannunsu Napep suka nufa kai tsaye suka nufi wurin Boka...

Meenat A. 'Yandoma
***