Chapter 35
by @smauta
Remember this you'll see me again ya kara manna mata kiss dakin halim yashiga ita kuma ta tsaya a bakin kofar kusan mintin shi goma a ciki suka fito tare da halim,hajia ummi ina kwana hararar wasa tayi mata tare suka rako shi har bakin mota komawa baya halim tayi hannu ya mikoma manar alamar come 🫴 a kasalance ta taka gaban motar tana mai lumshe idanunta take care of yourself idan kinji ciwon kamar zai dawo just give me a call zan turo dr ya dubaki and cin abinci kinaji na ko..........
Jikinta ya mutu har ga Allah batason tafiyar nan a kwanakin nan da sukayi tare ko nan dacan bataso taga ya matsa haka sukayi sallama batare da kowa nason tafiyar ba,koda ta dawo parlour ta zube kan kujera wasu marayun hayawe suka shiga gangaro mata da tunane tunane bacci mai dan karen dadi ya kwashe ta..............
Bata samu bacci daren jiya ba koda ta farka har azahar tayi da sauri ta nufi dakin ta wanka tayi taji jikinta yayi mata karfi sosai ba kamr dazu ba sai lokacin ta karema dakin kallo tsaf ya haɗu,komai ta bude taga ma'ajiyar shi tana mamakin yadda halim ta maida komai ba komai bane ta auri babanta kuma a kankanen lokaci tayi mata biyayya Allah kenan.................
Su kaka suka fado mata a rai da sauri ta tashi dakinshi ta shiga yadda suka barshi da safe haka yake gabanta ya fadi da sauri ta shiga toilet boxer's da singlet dinshi ta tattara ta saka a washing machine sannan tashiga wankin toilet saida tayi toilet din nan kalkal koda abinci aka zubar a ciki zaka iya ci rag na shanya dake toilet din ta shanya komai ta fito.............
Kitchen ta nufa kayan shara da goge goge ta dauko tadawo dakin tayi ma dakin fess ta canza bedsheets fridge ta bude duk wani guntun abu daya rage ta fito dashi ta sake jera masa sabo komai saida ta juyashi dakin ya dawo wani sabo kamar bashi ba turarukan wutan da halim ta mata order ta dauko da burner tashiga turara dakin harta wardrobe dinshi saida ta turare ta lokaci kankani dakin ya canza launin kamshin turaren sa zuwa turaren wutar komai neat gwanin ban sha'awa...............
Kan sofa ta zaune sannan ta bude wayar ta number Jude tayi dialing harta gama ringing baayi picking ba sai a karo na biyu jude ya daga hello who's on d line???da sauri tace Jude nice manar ce hajia barka ina wuni lafiya lau jude ya jikin kaka?kaka taji sauki gani nan ma zan shiga wurinta bari na hadaku ba bata lokaci ya bama kaka wayar sun dade sosai suna waya sannan akaba dede,nasan kaka da zolaya wai dagasken kun kusa dawowa karkiji wai rana iwar ta jibi muna gida manar ihu ta buga can't wait dede Allah ya kawo ku lafiya ina mijin naki? tambayar taji wani bambarakwai kai dede waye mijina kuma...............
Uwaki nace ni kike tambaya?bayanan fa dede ya tafi lagos dazu sai ni da halim kadai a gidan itama gobe zata tafi Maldives inane malbis kai dede Maldives wata ƙasa ce, Allah ya kaimu lfy yarinyar nan akwai mutunci manara kullum saita kiramu a gaisai kai dan Allah bansani ba kuma bata taba fadaman ba lallai halim zamu hade ke sakarai menene abun alfaharin ki ne,kuna waya da labaran kuwa?ummm ni dede ba wanda nake waya dashi jiya fa aka siyoman wayar nan kawu din kuma nasan yanada number shi bai taba kirana ba,ai gwamma ashe dayaje daurin auren ku kuɗi ya shaka masa manara labaran duk ya saki matan nan nashi ya auro wannan tumammar karuwar a yadda naji lbrn nan ance harda mota ya saya...............
Dariya ma ta kufcema manar tace dede kawun ne da mota😂😂😂dole ya kori su aunty s lantai hmmm kedai bari na dawo kasar wlh saimun maido su dan wannan yar iskar ba inda za'a da kudin nan sun kare guduwa zatayi lantai da mairo sune matan rufin asiri da khalil yayi shawara dani wlh ban yarda ya bashi kudin nan danshi labaran dayaji kudi jikinshi lokacin iskancin shi yake tashi ya dinga zuba iya shege sanka sanka ka girma bakasan ka girma ba shegen kai ciki da furfura rabi mutum rabi shedani🙄😹haka suka shafe kusan hour suna waya sannan suka tsinke wayar...................
Yanmata adon gari ta Prince halan shine ake wayar dashi? Prince ga ummi ku gaisa tayiman kanta waye banida wata bayanta amma ya zanyi da ita yanzu wutsiyar rakumi tai nisa da kasa ummin mu ce yanzu,gaisawa sukayi da Prince sannan aka kashe wayar dagasken tafiyar na nan gobe tana nan tsomakaraina nake kimtsawa nama gama akwatin takalma ya rage kawai na hada,ya jikin naki yatsina fuska tayi da sauki to madallah kinji kashedin da daddy yabar man akanki kici abinci kisha magani shine kika shige daki dan kar in ganki aa ba haka bane na gyaro dakin ne saina tsaya waya dasu dede inacan sake da baki kina waya dasu dede ko ki banisu🙄daddy ne ya kasheman warning wlh😂😂😂tuba nake second mother....................
Dungure mata kafada tayi zaki sani kinci abinci?yeah naci me kikaci ke fura ta bata ansa a takaice tanaso ta tambaye ta ya sauka lafiya tana kumajin kunya ta kuma kasa kiranshi a waya,wata zuciyar tace shiya kamata ya kiraki yace maki ya sauka ma labari sukeyi sosai amma hankalinta na lagos a tare suka idasa parking kayan na halim tsareta halim tayi saida taci abinci ta bata magani tasha