SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma sha ɗaya

by @dijensy



11



     Anty Baby tana harararta  da jifanta da mugun kallon tace "Yanzu tunda kike da ni da Ummanki kin taɓa gani munyi dunqulalliyar taliya haka?uban wa zai iya cin taliyarnan bai amayar ba irin haukar da kike dafawa ki bashi shi prisoner ki ne ko bawanki?"Jidda tana turo baki ba tare da tasan mai maganar tata zata haifar ba tace "Ai bai taɓa ci ba yau ne nayi wanann..."Bata ƙarasa ba ta yi shiru Anty baby na kallonta "Yau ne kika taɓa ɗora tukunya kike so ki ce ko?"


 Tashi tayi tsaye Jidda ta ja baya kyarat take jira ta xura da gudu don bazata yarda ta sake sauke mata hannunta a baya ba."Zo ko inci miki mutunci zo zo nan!"Ta daka mata tsawa ta maƙale waje ɗaya "Ko ki xo muyi magana ko kuma Baba yaji zancennan".Ta bata zaɓi biyu Jidda ta shiga shawara a hankali ta tako tana zagayowa ta zauna kan gwiwoyinta tana kallon hannunta "Idan ma na dakeki ba lallai ya shige ki ba".


  "Zan baki sati zan dawo gidannan muddin ban ga canji ba Jidda zaki sha mamaki wlh ,kuma kullum sai kin turon girkin da kika dafa idan kika ga dama ki amfani da chatgtp inci ubanki wlh ,safe rana dare kullum sai kin turo shi,ɗaya matsalar kuwa zuwa zan nasaki gaba muje wajen ungozoma ta unguwarmu ta duba min ke tunda ke yar banza ce me kan akuya".Anty baby faɗa ta mata sosai kamar ba gobe kamar zata bigeta ta ɗauki jakarta Jidda kanta a sunkuye Anty baby ta nufi ƙofa tana fita ta bi kayan da ta barta da su da na Umman da kallo hawaye taji ya silalo mata ta sa hannu tana sharewa tana jin rufo ƙofar Anty Baby ta miƙe tsaye tana mai ɗaukan kayan ta kai kitchen ta jerasu kitchen ɗin ya ƙara cika ta fito tana ɗauke sauran turaren da magungunan ta sa a akwatinta ta rufe tana fitowa ta ɗauki warmer ta mayar duka taliyar ta juye wata roba tana sa mayafi ta leƙa waje ta hangi almajiri ta bashi duka ta komo ciki a parlour ta zauna tana ta tunanin Anty baby da ta tafi da fushi kar fa taje ta faɗawa Umma don indai maganar ta isa wajenta kamar Baba yasani ne ba lallai ta ƙyale ba ,hakan yasa Jidda kiran Anty baby a waya sai da ta jera mata 4 miss calls bata ɗauka ba sai can anjima ta ga ta biyo kiran.


 "Mene zan maki?na satar maki wani abu na tafi dashi ne?"Ta tambaya a faɗace.


"Anty baby kiyi haƙuri don Allah zan gyara karki faɗawa su Umma".Jidda ta shiga roƙonta.


"Kar ma ki gyara jidda kiyi saɓanin abinda nace ki sha mamaki sai anjimanki karki dameni kuma"Anty baby ta faɗa ta kashe kiran Jidda ta sauke wayar daga kunnenta.Ƙarfe huɗu da rabi ta shiga kitchen ɗin tana fara haɗa faten doya ta duba a waya ta bi yadda ake yi tana yi tana ɗanɗana ta sauke ta yi snap ta tura mata ta zuba a warmer.Da yamma liƙis hassan ya dawo abunda bai taɓa gani ba ya tarar Jidda ta masu girki da kanta ta kawo a tray tazo ta ajje masa don har yana shirin fita  ya na ta mamaki wani daɗi yaji a ransa daman ya san bazasu dawwama haka ba.


    “Thank you Amirah”.Ya furta ita dai batace komai ba ta dauki wayarta ba maabocin son yaji bane Hassan amma don ya ta ji daɗi sai da ya cinye tass ya kwashe kwanukan ya wanke lokacin magriba yayi ya fita masallaci ya dawo ya sameta parlour gefen kujerar ya zauna”Pretty Jidda kin ci abincin?”Ya tambaya Jidda ta ɗago da idanunta tana kallonsa ta giɗa kai ta mayar duk yadda yaso ya samu suyi yar hira taki yarda ya rabu da ita ya tashi ya tafi makarantar dare bayan ya dawo ya tarar har ta kwanta….




*****




       Yau ma da safe da wuri yaji Jidda a kitchen tana ɓuruntu ya sameta zata yi abin karyawa yana kallonta yayi murmushi ta tafasa ruwan  shayi Hassan yace zai taya ta tace ya barshi haka ya rabu da ita tayi abinta ita kaɗai tunda hakan ta buƙata ta yi toasting bread a frypan irin yadda ta gani a wasu video da ta yi saving shima sai da ta ɗauka bayan ta gama ta turawa Anty baby na jiya ma ta ga ta bude batayi reply ba dai.Jidda bayan ta kammala ta kawo parlour ta ajje a gabanshi yana zaune yana duba littafi da tasan na islamiyya ne ya ɗago yana kallonta ya rufe littafin “Sannunki jazakillah kaira “.Ya furta yana ganin zata tashi bayan ta gama ajje komai ya riƙo hannnunta yana sata zauna ta zauna tana janye hannunta daga rikon da yayi mata Hassan da kansa ya haɗa mata shayin ta ga ya zuba toasted bread ɗin dayawa faranti ɗaya kafin ya haɗa nashi tea ɗin hakan ya tabbatar mata yana so su ci faranti ɗaya ne ba tare da ta ce komai ba tasa hannu ta fara ci.Har suka gama Jidda bata yi magana ba ya so suyi hira da ya yi magana sai ta amsa shi a ciki ciki hakan yasa ya gane bata son maganar yasa bai matsa mata ba,shi ya tattare kwanukan ya ɗauraye kafin ya fita islamiyya jidda ta shiga ɗaki tana mai duba magungunan da Anty baby ta kawo mata ta na dudduba su bata san ta ina zata sake jiki ta zauna da Hassan ba takaici kamar zai hallakata tana jin haushin yadda suka ƙi ganewa bata son auren Hassan zata yi amfani dasu amma har abada ta ɗau alwashin hassan bazai samu soyayya daga gareta ba sai dai gangar jikinta.Ƙarfe ɗaya da rabi ya dawo gida ta gansa shi da su Usman ya kawo mata su daga makarantar bayan ya tashi ya ɗakko su ,ta ɗora girkin rana a sannan yaran suka gaisheta ta amsa suna faɗa mata Anty Ruƙayya na gaisheta.A parlour suka zauna ta kawo musu ruwa ta koma bayan ta kammala girkin ta kira Amal ta ɗaukan musu ta zubawa Hassan ta kai masa ɗaki ta tashi xata fita ya kirata yana nuna mata gefensa kamar bazata zauna ba ta tako tana zama ba ta raɓeshi ba dai ta bar tazara Hassan yana kallonta “Mai akai miki faɗa min nayi miki laifine?”Ya tambaya a tausashe ta girgiza masa kai “Tohm naga ba kya kulani abinci kawai kike bani”Wani kallo ta jefesa dashi “Kawai ne abincin?”Ta tambaya yayi saurin girgiza kai “A a baki fahimceni ba na tuba ba haka nake son cewa ba ,ina jin daɗin hidimta min da kike Ammirahty amma idan kina shiru shiru zan ɗauka fushi kike dani kin dena cewa na siyo miki komai uhmm faɗa min mai aka miki?”Shiru Jidda tayi maganganunsa suna neman tasiri a gareta ta tashi “Na bar yara su kaɗai”.Ta furta ta fita ta zuba nata abbincin ta dawo ta zauna parlour bata iya cinyewa ba nata bai mata daɗi kamar wani ya dafa ta kalli Amal ta ga suna ci a hankali “Ku ,ba daɗi ne?”suka yi saurin girgiza kai a tare Jidda ta ƙara loma tana so ta gano ko mene babu cikin abincin sai da ta haɗiye ta tuna gishiri kawai tasa ta waro ido  yaran suna ta ci a haka ta tashi ta shiga kitchen tana tsaki ta ɗakko maggi dunƙule ta barbaɗa musu ta shiga ɗakin tana kallon ya buɗe nashi “Ka ƙara bai ji maggi sosai ba naga”.Ta miƙa masa tana basarwa yayi murmushi ya karɓa ta juya ta fita.Hassan tun da ya gama cin abincin ya fita ya barta da yaran  wajen asr sai gashi ya shigo da fankar da ya mata alƙawari da cover wayarta guda buyu masu kyau ya bata ba wata godiya da tayi.Su Amal bayan fitarsa masallaci ya dawo ya maidasu gida.



 ~~~~~



     Jidda ta ji maganar Anty baby  yanzu an ɗan samu canji tana girki idan yana nan ya tayata ko ma ya yi mata haka ma aikin gida kusan shine ƙarfin yi kafin ta yunƙura tayi ya wanke banɗaki yayi mata wanke wanke ko shara.Baba ya zo ya ga gida da Umma jikinta har rawa yake Jidda ta nutsu ta kawo musu abinci da abin sha tana ta fargaba ko faɗa suka zo mata har suka tashi tafiya bata ji sun mata zancen da take tsammani ba suka tafi ta har da kiran Anty Baby tana mata godiya.


  “Ina abinda na kawo miki?”Ta tambaya.


 “Ina amfani dasu”Ta amsa tana fatan bazata sake titsiyeta da tambayoyi ba ta mata sallama Jidda ta sauke wayar tana jin shigowar Hassan ya ƙullo ƙofar gate ɗin bayan ya raka su waje jarabawa suke a makarantarsu ɗaki ya shiga ya cigaba da tsara tamboyin jarabawar ajinsa.Yau tuwo take son gwadawa ta ɗora ruwa ta tuƙa semo ta goga ƙubewa tana haɗa miya kwata kwata bata lura da hancin kuɓewar da ta yar ƙasa ba ta taka da takalmintsa slippers ya zamar da ita rimmm ta zube ƙofar kitchen hannunta na bugun gefen ƙofar kitchen ta kwala ihu Hassan ya fito ba shiri ya sameta a yashe tana kuka ko bayani ta kasa in banda hannu da take kira ya shiga duba hannun yana taɓawa ta fasa ihu tana hanashi ya shiga mata sannu kamar ya ɗauke mata ciwon.


 “Gani kawai zanyi bazan taɓa miki ba”.Ya faɗa ta maƙale kafaɗa hawaye na gangarowa daga idanunta “Kai likita ne”Ta faɗaa tana ƙoƙarin tashi ta kasa sai da ya taimaka mata suka shiga ɗaki ta zauna kujerar parlour yin duniya taƙi bari ya ga hannun kuma ta kasa motsashi da kyau.


“Ban karye ba ko?”Ta tambaya tana kallonsa da firgici a idanunta “Jidda kin hana ni gani idan na gani shine zan sani”.Tana matsar hawaye ta kallesa “Ka duba a hankula toh”.Ya jinjina kai yana riƙe hannun ya yi straigtening ta kwala ƙara tana kwace hannunta duk yadda yaso ta bari ma ya gani taƙi ƙarshe sai fita sukai wajen mai  ɗori aka ga buguwa ce Jidda ƙiris ya rage bata yi fitsari a wando ba don azabar kama wajen  suka dawo gida ko magana bata yi sai sannu yake mata kamar suyi musanyen ciwon.


   “Mai kike son ci?”Ya tambaya ta girgiza kai “Hutawa zan kawai”Ta faɗa ya jinjina kai ya tallafa mata suka shiga ɗaki ta zauna kan katifar tana yaye mayafinta da hannun hagun duk tayi gumi ya karkata mata fankar saitinta ta na kaɗa rigarta “Ko zaki canja kayan?”Nan ma kai ta gida tana kallonsa ya ɗakko mata mara nauyin riga me kamar vest ya zuge mata zip na rigar jikin nata ta kau da kai daga kallonsa har ya gama cire mata bra ta isheta amma kunya take ji ta karbe vest ɗin “Ka je zan sa”.Ta faɗa Hassan ya tashi kamar yadda ta buƙata ya fita ta shiga kici kicin sawa da hagu ta kasa gashi ta cire bra ɗin tana cusa kanta a wuyan vest ɗin ta kasa ƙarasa sawa garin haka ta jogane hannun daman ta sa kuka ya komo ɗakin ba batun korarsa wannan karon ta sunkuyi da kai tana barin ya sa mata vest ɗin “Sannu”Ya faɗa bayan ya sa mata vest ɗin ta giɗa kai ya gyara mata pillow ta kwanta ya zauna daga gefe yana kallonta can an jima Jidda ta ji fitsari ya matseta tun tana daurewa har ta kasa ta miƙe zaune ba shiri Hassan ya sauri ya matso wajenta yana tambayarta “Zafi yake maki?”


 “Fitsari”Ta furta bata yarda sun haɗa ido ba ya ce “To zo muje banɗakin”A zuciyarta ta shiga tunanin yadda za ai koda yake ai hagun kalau yake amma ta ya zata yi tsarki ita kuwa ifact ba iya fitsari ba cikinta ya murɗa har kashi take ji yanzun…..



Share

Comment